← Book details Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 22

Sashe 3

Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifin Fadila da mahaifiyarta zaune suna fira,mahaifin Fadeela ya kalli mahaifiyarta ya ce"Ina yaran nan?, dan gidan Sale mai kifi?"Mahaifiyar Fadeela ta jinjina kai alamun ta tuna shi,ya ci gaba da cewa"Tom yau ina kasuwa mahaifin yaron ya zo ya saman akan yaron yana son abashi izinin zuwa wajan Fadila"Tom,ai shi kenan ,yaran yana da hankali ba laifi"Cewar mahaifiyar Fadila.Nan dai suka ci gaba da zantawa akan maganar.

Fadeela na zaune da wani littafi anhunta tana dubawa mahaifiyarta ta shigo d'akin.
Mahaifiyar Fadila zama ta yi gefan Fadilar.
Fadila ko ganin haka tasan magana ce mahaifiyar tata ke tafe da ita,hakan ya sa ta aje littafin hannunta.

Mahaifiyar Fadila shiru ta yi kamar mai tunani ,sannan ta ce"Fadila ,akwai wanda kuke tare ne? Ma'ana wanda kuka yi wata magana da ta shafi aure?" Kai Fadila ta girgiza.
Manaifiyarta kuma ta ci gaba da cewa"Dama Babanku ne ya ce in sanar da ke koda yau she zaki ga bak'o,dan haka ni abin da zan ce miki nasan yaran da mahaifinki ya yi magana akanshi dan haka in ya zo ki amsheshi hannu biyu,dan abisa alama da na gani mahaifinki sun yi magana mai k'arfi da mahaifin yaron,kuma nasan yaran yana da hankaki sosai da natsuwa sannan yana da abun yi"
Fadila shiru ta yi ta rasa abin cewa,sannan dai gudin kar ta yi laifi ta ce"Tom, Mama"

Fadila na zaune mahaifinta ya aiko kiranta ta je waje ta yi bak'o.

Fadila tashi ta yi ta sa Hijab dinta ta fita.

Zaune ta sameshi kan mashin din shi ,ba yabo ba fallasa Fadila ta gaida shi.

Bayan sun gaisa ne,ya fara jero bayanai kamar haka" Malama Fadila,na dade ina ganinki kina wuce ni kullum da safe in za ki wajan aiki,tuntuni na so bayyana miki hak'ik'anin gaskiyar abin da ke raina,amma Allah bai yarda ba sai yanzu, ina fatan za ki amshi tayin soyayyata hannu bibbiyu?"

Ya idasa maganar ya na mai kallan Fadila.

Jin shuru bata tankamai ba,kamar ma ba zata tanka ba ya ce cikin fargaba "Malama Fadila,kin yi shiru?"

Nan ma dai shirun ta yi kamar ba zata tanka ba, sai zuwa can ta ce"Ka yi hak'uri dan Allah ina da wanda nake so zan aura,ina mai baka hak'uri"

Fadila na fad'in haka bata saurari amsarshi ba ta tafi ta bar shi nan tsaye.

Tun daga ranar kullum sai ya zo wajan Fadila fira,inda har ya yi maganarshi ya gama bata tanka mai,dan fitowar ma sai in mahaifiyarta ta yi mata dole take fita.

Ana cikin haka kuma mahaifin Fadila ya sanar da Kabiru in dai ya shirya to ya aiko kawai a tsaida ranar auransu.
Kabiru bai yi k'asa agwiwaba ana sanar da shi ya sanar da mahaifinshi,inda washegari iyayan Kabiru suka zo .Atakaice dai a ranar aka tsaida auran Fadila da Kabiru.

Fadila ta ga dai mahaifinta ya yi bak'i amma bata san wainar da ake toyawa ba.
Zaune take suna waya da abokin aikinta yana mata magana akan MD fa ya matsa mai akan maganarta dan Allah ta ba shi dama,shigowar mahaifiyarta ne ya sa ta ce mai "Ina zuwa "ta kashe wayar.

Mahaifiyar Fadila bayan ta zauna ne ta wurgoma Fadila tambaya kamar haka,ta ce"da wa kike waya?" Jamilu ne abokin aikina"Shiru mahaifiyar Fadila ta yi,sannan zuwa can ta ce"Fadila, mahaifinki ya amshi kud'in auranki,dan har sun tsada ranar aure wata uku"
Fadila cikin alamun mamaki da tsaro ta ce"Mama ,kud'in aurena kuma? Da wa to?" Da Kabiru mana"Mahaifiyar Fadila ta bata amsa kai tsaye.
Fadila da sauri ta tashi ta zuk'unna kusa da mahaifiyarta ta kamo hannunta ta ce"Mama,dan Allah ku yi hak'uri ku k'ara min lokaci ,Wallahi ba na son wanda kuke k'ok'arin had'ani da shi,ki yi ma Baba magana ya ya janye dan ..."Aure babu fashi,kuma babu mai sawa in janye koda ko kin kawo min wanda kiki so,inda na riga na fita hak'inki sai da na baki zab'i"Cewar Manaifin Fadila kenan da ya na bakin k'ofa ya na jin maganar da Fadila ke yi.

Fadila da ta rasa abin cewa fashewa da kuka ta yi.

Haka Mahaifin Fadeela ya ci gaba da shiye-shiryan auran Fadila,inda ta b'angaran Fadila kuma har yanzu tana nan akan bakarta na ba zata aure Kabiru ba.
Dan yanzu ko wajanta ya zo ko gaisuwa bata had'asu,abin da ya fara ba Kabiru tsoro kenan,amma da ya sa mu mahaifin Fadila akan zai hak'ura ya ce "Kabiru,ka yi hak'uri ina sane da abin da Fadila kema,kuma daga zarar kun yi aure in sha Allah zata bari,hakan duk ta na yi ne dan ka ce ka fasa"Wannan maganganun da Mahaifin Fadila ya yi sai suka k'ara ma Kabiru kwarin gwiwa sosai.

ADAMAWA STATE

Usman jin alhaji Sagir kamar ba ya cikin hayyacinshi hakan ya sa ya kastse kiran ya kira Muhammad amma bai d'aga ba,ganin haka ya sa ya tashi ya d'auki mota ya yi gidan Muhammad d'in in da ya san alhaji Sagir na can in da ance shi da iyalinshi za su raka Muhammad d'akin amarya.

Yana tafiya a mota ya yi tunanin kiran 'yan sanda ya sanar da su dan gaskiya yanayin yadda ya ji muryar alhaji Sagir ba lafiya ba .

Usman bai yadda ya shiga gidan ba har saida 'yan sanda da ya Kira suka k'araso sannan suka shiga tare. Suna shiga gidan shiru ,dan lokacin alhaji Sagir har ya sume shi ma. Tun kafin su k'arasa cikin d'akin su ka ci karo da d'ige-d'igen jini ,cikin tsallake jinin suka k'arasa cikin d'akin.Inda suka iske su duk asume ,sai alhaji Sagir da ya suma kan gawar Hafsat da ke kwance cikin jini an mata yankar rago.

Haka suka kama alhaji Sagir da Muhammad da hajiya baturiya su ka yi asibiti da su. Gawar amarya kuma suka d'auki hotunan da za su d'auka sannan itama su ka yi asibiti da gawar.

Alhaji Sagir da iyalanshi ana kaisu asibiti aka basu taimakon da ya dace,inda cikin lokaci aka samu kansu duk kansu.
Alhaji Sagir na farkawa ya fara kiran Muhammad, ahakan ya sa dole aka kai shi wajan Muhammad d'in wanda shi ma farkawarshi kenan.
Alhaji Sagir cikin danne yadda ya ke ji ya karasa wajan Muhammad wanda ke kwance yana fusge-fusgen shi sai an barshi ya je ya ga Hafsat ,wato amaryar shi kenan.
Ana cikin haka ne aka shigo da alhaji Sagir d'akin. Alhaji Sagir da sauri ya k'arasa inda Muhammad d'in ya ke. Cikin danne yarda ya ke ji game da abin da ya samesu ya fara magana kamar haka"Muhammad, ka yi hak'uri mu je gida Hafsat na gida ka ji"
Muhammad kallan mahaifinshi ya yi ya na girgiza kai ya ce"A'a Daddy ,Sun kashe min Hafsat? Su waye daddy?"Alhaji Sagir so ya ke ya yi ma Muhammad magana amma ya kasa ,saboda kukan da ke son kwace mai,hakan ya sa ya fita d'akin da sauri ya koma motar Usman ya na kuka.

Ya dad'e ya na kuka sannan ya samu ya lallashi kan shi ya yi shiru.Hafsat ta kasance ita kad'aice ta rage mai wadda zai kalla ya tuna da kanwarsa, ga shi itama ta tafi ta bar su ko kuma an rabasu da ita lokaci guda.

Alhaji Sagir sai da ya yi kuka mai isarsa sannan ya fita shima sakamakon Kiran da Usaman abokin Muhammad ya yi mai ne.

Usman cikin sanyi ya kalli alhaji Sagir ya ce"Daddy,dole abin akwai tashin hankali da tsantsar damuwa amma za mu iya barin haka a matsayin lokacin Hafsat ne ya yi,saboda wani bai isa ya kashe wani ba sai in kwananshi ne ya k'are. Yanzu kaga 11:49 PM, bari in kira Muhammad mu je gida"
Alhaji Sagir kallan Usman ya yi da jajayan idonshi sannan ya ce"Ina hajiya baturiya fa?" Ita da Muhammad ga shi nan za a fito da su mu tafi"

Alhaji Sagir da Usman suna nan tsaye aka fito da Muhammad da hajiya baturiya,hajiya baturiya hannunta rik'e da na likitar da ta dubata,inda Muhammad hannun shi ya ke rik'e da na d'aya daga cikin police d'in da Usman ya kira da ya ke abokinsu ne.Shiga su ka yi su ka tafi.
Hajiya baturiya na kuka kad'an-kad'an,in da kukan nata ke kuma d'aga hankakin Muhammad da alhaji Sagir.
Lura da hakan da Usman ya yi ne ya sa ya ce"Mommy,dan Allah ki yi hak'uri duk mai rai dama mamaci ne Hafsat lokacinta ne ya yi ,yanzu addu'a ya kamata mu bita da ita"Haka Usman ya yi ta lallashin hajiya baturi da kyar ya samu ta yi shiru.Shi ko uban gayyar Muhammad ajiyar zuciya kawai ya ke ja ,kallo daya za ke mai za ka hango tsantsar tashin hankalin da damuwar da ya ke ciki.Ahaka dai suka isa gidan alhaji Sagir mai shadda.Suna fitowa daga cikin motar dukansu suka nufi part din alhaji Sagir.Suna shiga idonsu ya yi tozali da photon Muhammad da Hafsat da ya ke manne jikin kusurwar d'akin,wannan photon da Muhammad ya gani sosai ya k'ara d'aga mai hankali hakan ya sa lokaci guda jikin shi ko ina ya fara rawa ,ko kafin Usman ya taro shi har ya yanke jiki ya fad'i awajan a sume.

Muhammad har gari ya waye bai farfad'o ba,hakan ya sa daddyn shi ya sa aka yi da shi wata private hospital dake kusa da su.

Gawar Hafsat ko anyi duk wani aune-aune da gwaje-gwaje da za ai an bada gawar dan a yi mata sutura .

Ko kafin a iso da gawar Hafsat gida gidan ya kuma cika da mutane dama kuma da akwai sauran mutane da ba su watse ba na biki.Isowa da gawar Hafsat sosai ya d'aga hankalin mutane,hakan ya sa gaba d'aya gidan ya rud'e da koke-koke.
Hajiya baturiya ko ta na ganin an shigo da gawar Hafsat ta yanke jiki ta fad'i.
Haka dai jama'a akaita koke-koke dan Hafsat kowa na tane bata da damuwa.

Cikin lokaci aka yi zana'idar Hafsar aka kaita gidanta na gaskiya ,in da aka bar folisawa da bincike.

Muhammad ko sai da ya yi sati biyu a asibiti kafin ya fara dawowa daidai.Yaune aka dawo da shi gida dan alhamdulillah jikin nashi,saidai rashin k'arfin jiki wanda hakan ya farune a dalilin rashin cin abinci da kuma rashin kuzari da ke faruwa da duk Wanda akai mai rashi irin haka.
Chapter 3 · 0% Book details