← Book details Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin lokaci motar folisawa ta iso gidan.

Atak'aice dai nan 'yan sanda su ka yi bincike- binciken su sannan suka d'auki gawar su ka yi asibiti da ita.

Duk wani bincike an gudanar akan gawar Maryam sannan aka yo gida da ita.

Haka aka yi zana'idar Maryama aka kaita gidanta na gaskiya. Har aka yi aka gama daga Alhaji Sagir har Muhammad basu san abin da ake ba saboda allurar barcin da likita ya yi musu.

Iyayan Maryam lokacin da idonsu ya yi tozali da gawar Maryam sun yi kuka sosai da danasanin had'a auran Maryam da Muhammad da su ka yi.

Muhammad ba shi ya farkaba sai gaf magriba, inda Alhaji Sagir har lokacin baisan wanda ke kanshi ba sai can cikin dare ya farka.

A wannan lokacin abin ya fi tab'a Alhaji Sagir dan har ya farka baya magana, saidai ya kalli mutane.

Muhammad na kwance kan shi a sama, yana tunanin me ke faruwa da rayuwar shi haka ne. Yana a wannan yanayin ne Hajiya Baturiya ta shigo. Kallan Muhammad ta yi tana shafa kan shi ta ce "Muhammad, kar ka sa kanka cikin tunani wani mugun ciwan ya zo ya kamaka, sannan ni kaina idan ina ganinka haka hankalina ba zai kwanta ba"

Muhammad tashi ya yi ya zauna yana kallan
Hajiya Baturiya ya ce "Mommyna, soda dama ba zafin ciwo ake ma kuka ba, tunanin halin da ake ciki ne .Sannan, mommy duk jarumtar Jarumu ba kowana rad'adi yake iya juremawa ba" Hajiya Baturiya kai ta d'aga ma Muhammad alamun haka ne, ya ci gaba da cewa "Mommyna, na rasa yadda zan lallashi kaina in yi hak'uri da rashin Hafsat a rayuwata. Amma da na yi wani nazari sai naga ko ba wannan lokacin ba Hafsat zata mutu watarana,sai na yi tunanin fara ba kaina hak'uri in amshi Maryam a matsayin mata, saidai ina cikin tunanin hakan ne zuciyata na gaf da amince min da ita suka kasheta suka rabani da ita itama" Muhammad shiru ya yi kamar mai tunani ko mai son tuna wani abu, sannan ya ce"Mommy! Su waye ne? Waye ya kashe su? Me su kai musu ? Shi nake son san..." Hajiya Baturiya rufe bakin Muhammad ta yi tana kuka, ta ce "Ka yi shiru Muhammad, karka sa kanka cikin wata damuwar, koda ace abin da mahaifinka ya mallaka zai kare ne sai an binciko wa inda suka aika haka, ni na san haka. Ka tashi mu je ka ga mahaifinka abun nashi ya fara bani tsoro, baya magana tun da ya farka na yi na yi ya k'i yin magana"

Muhammad cikin daure yadda yake ji da tsoran karya rasa mahaifin shi ya nufi bayan Hajiya Baturiya suka yi falon Daddynshi.

Kwance ya samu mahaifin nasa kansa a sama kamar mai k'okarin tuno wani abun da ya shege mai .

Muhammad cikin k'arfin hali ya kalli mahaifinshi ya ce"Daddy, ka tashi ka ci abinci plz"Alhaji Sagir da sauri ya mai da kallan shi kan Muhammad .
Ya dad'e yana kallan Muhammad d'in sannan ya ce "Muhammad, ka ci abinci kai ?" Kai Muhammad ya d'aga mai.

Muhammed Hajiya Baturiya ya sa ta kawo mai tea ya ba Alhaji Sagir. Kad'an dai su ka samu ya sha.

BAYAN SATI D'AYA DA RASUWAR MARYAM .

Ma sha Allah. Yanzu Alhaji Sagir da Muhammad sun fara kwantar da hankalinsu.

Bincike ko har masu gadin gidan an kama amma babu wata hujja ko d'aya da aka samu daga kan rasuwar Hafsat har ta Maryam.

KADUNA GARIN GWAMNA.

Yau Sati d'aya da kenan da komawar Fadila aiki.Saidai kullum cikin takurar Oganta ta ke.Dan tunda Jamilu ya sanar da shi ta amince da soyayyarshi tun daga nan ya fara ta kurata. Haka dai Fadila ke daurewa ta na biye mai suna fira badan tana jin dad'in firar da shi ba.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya Fadila kullum sai ta je aiki.Mahaifinta kuma babu tasa dole ya kauda kai da surutan mutane.

Babu laifi yanzu suna rayuwarsu da sauk'i .Dan kullum Fadila ta tashi aiki sai gogannata ya bata kud'in mashin din zuwa gida, tom da sune take kaiwa su yi cefane.

WATA UKU KENAN DA KOMAWAR FADILA AIKI.

Yanzu Fadila ta saki jikinta sosai da Ogan nata duk da bata wani son shi ta fara tunanin auranshi, dan wa'adin da mahaifinta ya bata yana gaf da cika.Kuma har yanzu mahaifinta kullum cikin k'ara tunatar da ita yake akan yana nan fa akan bakarshi daga wa'adin da ya sa mata ya cika ko ta yi aure ko kuma ta bar mai gida.Wannan ya sa ta fara sakar ma ogan nata fuska, idan ta ga ba hali ta yi hak'uri ta aure shi.

Yanzu har gidan su Fadila sun san soyayyarta da ogan nata.

Yau Fadila bayan ta dawo aiki, mahaifinta ya kirata .Ya dad'e ya na kallan Fadila kamar mai neman wani abu a jikinta, sai zuwa can ya ce"Fadila, yau saura wata biyu wa'adin da na baki ya cika, amma har yanzu bikice min komai ba?"
Fadila shiru ta yi gabanta na fad'uwa.Haka dai ta daure ta ce"Eh, Baba ban manta ba"Ya yi kyau"Mahaifin Fadila ya ce.

Fadila ranar haka ta kusan kwana tana tunanin mafita, abu d'aya da ta sani shi ne bata son Ogan nata, saidai za ta yi hak'uri haka nan ta aure shi in da bata da wata mafita.Haka Fadila ta yanke ma kanta auran ogan nata ba wai dan tana son shi ba sai dan mahaifinta da ya hura mata wuta.

Washegari Fadila ko da taje aiki zama ta yi shiru, kallo d'aya za ka yi mata ka gane tana cikin damuwa.
Jamilu abokin aikin Fadila, da zuwan shi kenan cikin tsokanar Fadila ganin ta yi nisa a tunani ya ce"Alamar tambaya ta na ga mai yawaita tunani, musaman in ya shiga halin soyayyar zamani , ya...." Kallan da Fadila ta yi ma Jamilu ne ya sa ya yi shiru yana dariya ya ce"Ko za ki cemin wannan shurun naki ba soyayya ba ce sila?" Ba ita bace hasali ma k'i ne sila"

Jamilu zama ya yi ya ce"To fa, ba ni in Sha?"Fadila cikin sanyi kamar za ta yi kuka ta ce"Jamilu zan auri MD ba dan ina son sa ba saidan banda wata madafa"Jamilu ko da har kullum bai ga wani aibun MD d'in ba ya ce"Fadila, ki kwantar da hankalinki MD ba shi da wata matsala, sannan shi d'in masoyi ne gareki na hak'ik'a"

Haka dai Jamilu ya yi taba Fadila kwarin gwiwar auran MD d'in.

Fadila bacin ta tashi aiki kamar kullum sai sun tab'a hira da Ogan nata sannan take tafita gida.Tom yau acikin firar ne take sanar da shi ta bashi dama koda yaushe zai iya aikowa gidansu.

Murnar da MD ya yi kad'ai ta k'ara tabbatar ma Fadila da son da yake mata.

Cikin tsantsar farincikin da ya kasa b'oyewa ya kalli Fadila ya ce"Zan iya aikowa gobe kenan?" Kai Fadila girgiza mai ta ce "Gobe Baba zai yi tafiya saidai in ya dawo "

Haka Fadila suka rabo da MD d'in akan daga mahaifinta ya dawo daga tafiyar da zai yi za su aiko.

Washegari mahaifin Fadila da wuri ya shirya tafiyar da zai yi zuwa Gombe.

Fadila da mahaifiyarta su ka yi mai rakiya har tasha. Sai da motarsu ta tashi sannan suka dawo, in da Fadila ta nufi wajan aiki mahaifiyarta kuma ta yo gida.

Satin mahaifin Fadila d'aya ya dawo.

Yau Fadila bayan ta tashi daga aiki ne MD ya rakota kamar yadda ya saba ya kalleta ya ce"My Fadila, har yanzu Baba bai dawo ba?" Fadila ji tai bata buk'atar sanar da shi yanzu in da tasan maganar aikawa zai mata, hakan ya sa ta ce " Bai dawo ba "

Kallanta ya yi ya ce "Sai yaushe kenan?" Duk lokacin da ya dawo zan sanar da kai" Fadila ta ce atak'aice.

Sai da Fadila ta samu keke-napep ta hau sannan MD ya juya ya tafi.

ADAMAWA STATE

BAYAN WATA UKU DA RASUWAR MARYAM.

Ki manin wata uku kenan da rasuwar Maryam. Yanzu Muhammad ya dangana har ya koma bakin aikin shi.

Alhaji Sagir zaune yana danna waya Hajiya Baturiya ta kallai ta ce "Alhaji, ban ji dadi ba da ka hana Jibirin dawowa, yanzu ace Muhammad ya yi aure har biyu duk ba matan amma ace be zo ba" Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce"Tom ba gashi ba yanzu ya gama karatunshi lafiya lau, ko da ya zo me zai mai? "Alhaji Sagir suna cikin haka ne Muhammad da ya je airport d'akko Jibirin suka shigo tare bakunansu d'auke da sallama.

Alhaji Sagir cikin washe baki ya ke cewa"Ka ga mutanan Turai, jibirin ka ganka ko har ka fara komawa kalarsu"Gaba d'ayansu dariya su ka yi sanna Jibirin ya zauna suka gaggaisa da iyayan nasa.

Alhaji Sagir kallan Jibirin ya yi ya ce"Jibirin ku je ka ci abinci ka ga isowarka kenan.

Jibirin tare da Muhammad suka ci abincin, dama kuma komai nasu tare su ke yi.

Dawowar Jibirin tasa Muhammad ya kuma sakin ranshi sosai ya fara mantawa da duk wata damuwarshi.

Alhaji Sagir zaune da su Muhammad suna fira, kamar yadda suka saba kusan duk dare in Alhaji Sagir na gari.Alhaji Sagir ya kalli Muhammad ya ce"Muhammad ina so in baku shawara kai da Jibirin, duk kanku ya kamata ace duk kun yi aure, duk da dai kai Muhammad ka yi amma Allah da ikon shi ga abun da ya faru, amma duk da haka hakan ba zai zama hujjar da zaka rik'e kace wai ba za kai aure ba, gara ma Jibirin k'aninka ne "

Muhammad kamar zai yi kuka ya d'ago yana kallan mahaifin nashi ya ce"Daddy, dama za ka kuma iya yi min maganar aure? ,Daddy, na za ci kai kanka ka hak'ura da wannan batun, wa kake gani yanzu zai iya ban auran 'yarsa ma? " Muhammad ya idasa maganar kamar zai fasa ihu.

Jibirin cikin tausaya ma Muhammad ya dafa kafad'ar shi ya ce"Ni na yi imanin babu wadda za ka je naiman auranta ta k'i Muhammad, kuma ta bakin Daddy haka ba hujja ba ce ka jaraba naima ka gani mana"
Chapter 8 · 0% Book details