← Book details Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 22

Sashe 15

Fadeelah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyar Fadila suna zaune da Aisha suna fira da Jamilu ya yi sallama ya shigo. Bayan sun gaisa ne Jamilu ya ce " Mama , Fadila ce ta haihu bayan an yi mata theater an ciro yaron , yanzu haka tana nan Asibitin sawa , shi ne na zo in sanar ko Aisha ta je gudin karta farka ba kowa kusa da ita " Mahaifiyar Fadila wadda tun da Jamilu ya fara bayani kirjinta ke dukan uku-uku . Hannuta ta d'aga sama tana godiya ga Allah tana cewa a cikin rawar murya mai son fidda kuka " Alhamdulillah ! Allah na gode maka da ka amsa rok'ona kasa Fadila bata zubar min da wannan bak'in jinin anan ba " Mahaifiyar Fadila mai da kallanta ga Jamilu ta yi ta ce " Allah ya raya abun da ta haifa ya kuma bata lafiya , amma babu wanda zai je acikinmu " Mahaifiyar Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke zubar mata.

Jamilu shiru ya yi dan ya rasa abun cewa ,sai zuwa can ya ce " Mama , dan Allah ki y....." ? Mahaifiyar Fadila d'aga ma Jamilu hannu ta yi ta ce " Jamilu , sai an jima ka sanar da ni haihu tom na yi mata addu'a da ita da abun da ta haifa , tom sai me ye kuma ya rage ? " Ta fad'i maganar da alamun ranta a b'ace yake.

Jamilu tashi ya yi bai kuma cewa komai ba.

Har ya tafi mahaifiyar Fadila ta ce " Ka sanar da ita katta dawo min nan bana buk'atar kara zama da ita "

Jamilu ganin idon mahaifiyar Fadila ya rufe ya sa bai k'ara cewa komai ba ya tashi ya tafi.

Aisha k'anwar Fadila goge hawayanta ta yi ta ce " Mama , ki yi hak'uri ki bar Aunty Fadila ta dawo nan ta zauna , idan kin koreta ina zata ? "

Mahaifiyar Fadila cikin kuka ta ce " Aisha , zuciyata ba zata iya jurewa ba inga Fadila da yaron shege tana raino , ina ba zan iya daure haka ba , ku yi hak'uri karku sake rok'ona wata alfarma akan Fadila ta zauna , idan kuma kun matsa sai dai ni in bar muku gidan "

Aisha shiru ta yi bata k'ara cewa komai ba.

B'angaran Fadila ko lokacin da ta farka ba kowa kusa da ita . D'akin ta bi da kallo, daga gani dai Asibiti ne hakan ya sa ta shafa cikinta da sauri sai jin shi ta yi wayan ba komai. Fadila cikin jin dad'i ta ce " Alhamdulillah . Allah kai ne abun godiya Allah na gode maka " Fadila ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke zubar mata dan ita ta yi tunanin cikin da ke jikinta ya zube ne .
Fadila na a wannan halin ne d'aya daga cikin likitocin da suka dubata ta shigo ringume da jaririn yana kuka.

Fadila d'aga kai ta yi tana kallan Jaririn da ke a cikin tsunma a hannun likitar. Fadila cikin rud'ewa da ganin jaririn ta ce " Jaririn waye ? " Murmushi likitar ta yi ta ce " Jaririn da kika haifa kenan, amsarshi ki shayar da shi" Ta fad'i maganar tana d'ora ma Fadila jaririn akan k'afarta.

Fadila duk'ar da kai ta yi tana kuka sosai ta kasa magana. Likitar ko dama ta riga ta gama fahimtar Fadila babu aure ta haihu , hakan ya sa ta ce " Kukan me kuma kike yi bacin mai faruwa ta faru? Yanzu saidai ki rungumi yaronki gaba kuma kin kiyaye, dama abun da ake hangar muku kenan ake muku fad'a kuke ganin kamar takura muku ake yi "

Suna cikin haka ne Jamilu ya shigo . Jamilu zama ya yana yi ma Fadila ya jiki .

Fadila bata samu damar amsa mai ba saboda kukan da ta ke yi.

Haka Fadila ta yi ta kuka Wanda Jamiku ya kasa ce mata komai yana zaune yana sauraranta .

Jamilu d'akko jaririn ya yi jin yana kuka . Babu kalar jijjigar da bai yi ma jaririn ba amma ya dage sai kuka ya ke gaba d'aya ya cika Asibitin . Inda kukan jaririn ke k'ara tun jira Fadila tana k'ara nata kukan itama .

Jamilu gyaran murya ya yi sannan ya ce " Fadila , yanzu fa maganar kuka ta riga ta k'are , kukan nan babu wani magani da zai miki , ni shawarar da zan baki ki yi hak'uri ki bar sa ma kanki damuwa saboda tsoran wani ciwo.." Jamilu shiru ya yi saboda sugowar likita, likitar kallan Fadila ta yi ta ce " Bi ki ji baby na kuka ba ? Ki d'auke shi ki shayar da shi mana " Fadila ci gaba da kukanta ta yi ta kasa d'aukar jaririn.

Ana cikin haka ne MD ya shigo da flask babba a hannun shi da kuma ledar kayan tea.

MD da kan shi ya had'a ma Fadila tea ya mik'a mata. Kacan cewar Fadila na jin yunwa bata musa ba ta amsa ta sha.

MD d'aukar jaririn ya yi ya yi masa hud'u ba sannan ya kalli Jamilu ya ce " Nasa ma baby boy d'inmu Ahmad " Allah ya raya shi" Jamilu ya ce.

Fadila na gama shan tea d'in MD ya kalleta ya ce " Mu je in kaiki gida " Jamilu Kallan MD ya yi ya ce " MD , idan babu damuwa akwai maganar da nake son mu yi " MD tashi ya yi suka fita.

Bacin sun fita ne Jamilu ya kalli MD ya ce " MD , Fadila fa ba zaiyuwu ta koma gida da zama ba , saboda a halin yanzu mahaifiyarta tana cike da jin zugun zafin haihuwarta , gani nake idan zaiyuwu ka sama mata wani wajan ta zauna kafin nan da ta sakko "

Shiru MD ya yi baitanka ba sannan ya koma d'akin da Fadila ta ke ya ce ta shirya yanzu zai zo "

Shiru-shiru MD bai dawo ba , Jamilu kasa jurewa ya yi ya tafi gida ya ce mata yana zuwa.

D'aya daga cikin likitocin ko jin kukan jaririn ya yi yawa ya sa suka tursasa Fadila ta shayar da yaron.

MD ba shi ya dawo ba sai 10:40 PM dan Fadila ma har ta cire ran dawowar shi.

D'aya daga cikin likitocin ce ta rungume jaririn ta rakasu har motar MD sanna ta juy.

Fadila da mamaki ta bi MD da kallo ganin ya d'auke wata hanya daban maimakon hanyar gidansu. Hakan ya sa ta ce " MD ina zaka kai ni kuma? " MD bai tankama Fadila ba.

Daidai wani babban gida MD ya yi parking , Fadila dai kallan shi kawai take batace komai ba . MD kuma fita ya yi daga cikin motar ya bud'e get d'in gidan sannan ya dawo ya shiga da motar.

MD kallan Fadila ya yi ya ce " A nan gidan za ki ci gaba da zama har zuwa lokacin da Mama zata yi miki afuwa ki koma ku ci gaba da zama tare "

Fadila kallan MD ta yi wanda ke rungume da jaririn ta ce " Mama, ta hana in ci gaba da zama da ita ko ? " Ki yi hak'uri komai zai wuce watarana m...." Barka da zuwa ranka shi dad'e, har kun iso ? " Cewar wata karfaffar dattijuwar mata da ta fito daga cikin gidan ta katse maganar da MD ke yi.

MD jaririn hannun shi ya mik'a mata sannan ya ce " Ga mejegon nan ki bata duk watakulawa da ta kamata " In sha Allah , ranka shi dad'e "

MD mik'a matar nan jaririn ya yi ya kalli Fadila ya ce " Ni zan tafi Allah ya sawake " Fadila kai kawai ta iya d'ama mai ya juya ya tafi , ita kuma ta bi bayan matar nan suka shiga cikin gidan.

Three bedroom plate , ma sha Allah gidan ya yi kyau. Fadila zama za ta yi dattijuwar matar nan ta ce " A'a jikata, kar ki zauna mu je ki gasa jikinki " Matar nan goya jaririn ta yi sannan suka shiga bayin ta gaggasa Fadila suna fitowa ta kai Fadila har d'akin da yake mazaunin nata .

Fadila da mamaki ta bi dak'in da kallo dan komai sabo ne na d'akin , bud'e manyan jakunkunan da ta gani ta yi , d'aya cike take da kayan sawa kamar nata , d'aya kuma da kuma kayan jariri ne cike . Fadila na nan tsaye tana mamakin kayan, matar nan ta shigo da jug cike da kukun gyad'a ta kawo ma Fadila ta ce " Ga kunun gyad'a nan na yi miki ance sai zuwa gobe za'a fara baki abinci shima ba mai k'arfi ba in da an yi miki theater ne"

Fadila cikin sanyi ta ce " Tom, na gode "

Matar nan fita ta yi shima jaririn ta wankoshi tas kamar dai yadda ake ma jarirai sannan ta yi mai gashin cibi ta kawo ma Fadila shi ta fita.

Fadila tagumi ta yi ta tasa yaron gaba tana kallo tana kuka . Sai da ta yi kukanta ta gaji sannan ta kwantar da shi ta zuba kunun gyadan tasha ita ma ta kwanta , take barci b'arawo ya saceta.

Cikin dare jaririn ya tashi yana ta kuka amma kasancewar barci mai nauyi ya d'auki Fadila bata ji ba, sai Baba Lami ce ta ji ta shigo d'akin Fadilar .
Bubbugata ta yi ta tashi ta mik'a mata yaron sannan ta fita.

Fadila aduk lokacin da zata kallin yaron sai ta ji hawaye na zubar mata . Goge hawayan ta yi tana kallan yaron ta ce " Ina tausayinka sosai araina, ina tausaya maka yadda zaka tashi ka rayu babu uba , ina ji maka gorin da zaka rik'a fuskanta wajan jama'a , saidai ba zan gajiya ba wajan rok'a maka Allah ya nisantamu ni da kai ya kaimu duniyar da za mu rayu babu gorin zama'a acikinta " Fadila ta idasa maganar tana kuka sannan ta kwantar da yaron ta kwanta gefan shi , har aka kira Sallah barci ya gagari idon Fadila.
Chapter 15 · 0% Book details