← Book details Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 33

Sashe 33

Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Safwan ya kallesa yace Abokina nafa manta ban fad'a makaba,
Na kusan zama Daddy Dan kuwa Allah yayi najefa kwallo a cikin raga,
Saura Kai, a gaskiya ya kamata kayi k'ok'ari daren yau kada kayi bacci har sai kasamu kajefa kwallonka a cikin raga."

Had'e fuska sauban yayi ba alamar dariya a tare dashi yaci gaba da dannar wayar hannunsa,
Jiniyar motocin sarki sukaji hakan ya tabbatarwa sauban Abba yadawo kenan."

Shima Safwan yanajin hakan ya mik'e yace "Abokina nizan tafi domin kuwa kasan banason Ina Jan dogon shak'o bana kusa ga love d'ita bare Kasan yanzun laulayi mukeyi,
Ya d'an sunkuya gefen kunnen sauban kamar zai fad'a masa wata magana Wacce bayason kowa yaji,
cike da tsoKana yace "wai kasan wani abu kuwa gani nakeyi kamar 'yan uku ne na zuba Mata a mahaifa."
Yana kaiwa nan yasaki dariya yayi tafiyarsa."

Da kallo sauban ya bishi dashi har sai da ya daina ganinsa snn ya girgiza Kai ya mere baki,
ya tashi yanufi part dinsa domin ya d'auro Arwalar sallar magariba yatafi masallaci,
Domin yana son ganin maimartaba, yanason yaji halin da Safna take ciki,
Murmushi yasaki wata zuciyar tace wata k'ila an d'auro Auren,
Dam gabansa ya fad'i a lokacin da wnn tunanin ya fad'o masa rai."

*pls kuk'ara hakuri dani wlh jikin ne nawa har yanzun sai a hankali pls kucigaba da tayani da Addu'a*

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301
Chapter 33 · 0% Book details