← Book details Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 33

Sashe 28

Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro ido safna tayi tana mamakin a Ina take? Wacece wnn?" Ya akayi tasan sunanta?"
Anan take komai yadawo mata sabo cikin razana ta motsa tana neman ta firgita, tare da kallon hannunta tana fad'in macijin ya sareni ko?"

Murmushi matar tasaki tace "bai sarekiba ki kwantar da hankali,
Ta mik'a mata Akushin dake d'auke da waina tace 'ga abinci kici."

K'amshin abincin ya daki hancin safna a nan take cikinta ya k'ulle akan yunwa ta tina da rabon ta da abinci har ta manta, ta karbi abincin ta Faraci, citakeyi tana lumshe ido domin ba kad'an takejin dadin abincin ba,
Sai da ta cinye wainar gaba d'aya snn tasha ruwan pure water dake ajiye a gabanta,

Murmushin matar takeyi tana kallon safna cike da tausayi,
Itama safna kallon matar takeyi, tana tinanin a ina tasan wnn fuskar tabbas ko a inane tab'a ganin wnn matar kuma tasanta sosai."
A mafarki wata zuciyar ta fad'a Mata,
Tabbas a mafarki kika santa anan kike ganinta, da zarar kinshiga damuwa ita ke zuwa tana lallashinki tare da kwantar maki da hankali."

D'aga kai tayi ta kuma kallon matar wacce take sakar mata murmushi tace "Safna kin tinani?" Kin tina inda Kika sanni?"

hawaye suka soma gangarowa safna ta taso tazo gabanta ta durkusa tace "Inna bazan tab'a mantakiba domin kina taimakona a duk lokacin da nafad'a cikin k'unci da damuwa,
Ke wacece?"

Murmushi matar tayi ta dafa kan Safna tace "zakisan KO ni wacece idan lokacin sanin yayi, kafin nan kitashi kitafi domin akwai sauran k'alubale a rayuwarki,
Ta nuna Mata wata hanya tace "kibi nan kiyitafiyarki domin tsiratar da rayuwarki,
Snn kiya wai ta Addu'a a a duk halin da kika tsinci kanki a cikinsa sai wata Rana."

Share hawayen fuskarta safna tayi, tayi matar godiya,
Matar ta bata silifas tasaka Wanda tanemi zugin zafin da takeji a k'afarta ta rasa,
Snn ta nufi hanyar da aka nuna Mata tafara tafiya."

Tafiya takeyi sosai tanayi tana hutawa saboda gajiya har yamma ta Mata a kan hanya,
Hakan take tafiya cikin daji, batare da wani tsoro ko fargaba a tare da itaba,
Kwatsam ta ganta a tsakiyar hanya akan wani babban titi wanda motoci suke wucewa da k'arfi ba batare da sun tsayaba,
Wani Mai sayar da abinci ta hanga a can tsallaken titi taji cikinta yayi kuka alamar yunwa takeji ga kuma kishirwa,
Hawaye ta share a idonta tana "fad'in Allah Sarki Baba Allah ya jik'anka ya gafarta maka.

Ta mik'e tsaye tanufi wurin Mai sayar da abincin,
Tanaso ta k'etara titi tsoro takeji saboda yanda taga motoci suna wucewa da gudu, sai tazo ketarawa sai kuma ta dawo baya tana sharar hawaye,

A can tajiyo jiniya tajuya ta hango motocine tafe wad'an da basa da iyaka, cikin zafin nama ta nufi kan titin da gudu tana fad'in kafin ku k'araso na k'etara,
Ai kuwa sai dai taji a d'auketa da mota ta fad'i a tsakiyar titi jini yana fita a hancinta da bakinta."

Da sauri motocin suka taka burki suka tsaya,

Wata kyakkyawar macce wacce hutu ya zauna a jikinta 'yar birni 'yar gayu tana sanye da glass a fuskarta sai k'amshi take zubawa wacce shekarunta bazasu wuce 37 ba, tabud'e mota tafito ranta a b'ace take kallon direbanta tana "fad'in yahuza baka ganine ko idonka a makance yake kadiba kagani aikin da akayi d'an Adam ba dabba bane."

A nan take Tabawa escort d'inta masu take mata,baya umurni tace "ku dauketa kusakata a mota mutafi asibity da ita."

Cikin sauri aka tallabi safna aka sakata a mota suka d'auki hanyar babbar asibity dake zaman kanta a cikin garin Adamawa."

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍

🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴

Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)

*Page 29*

******* A lokacin da aka nufi asibity da Safna ba rai bare numfashi a tare da ita,
Kai tsaye Emergency aka nufa da ita cikin gaggawa likitoci suka k'arb'eta suka duk'ufa a kanta domin ceto rayuwarta da tsayar da jinin dake fita a hanci da bakinta."

Sosai hajiya LAILA ta girgiza da ganin yanayin da yarinyar tashiga, danko fuskarta bata tsaya ganiba hankalinta a tashe yake matuk'a."

Hajiya laila mace ce mai mai tausayi mai son 'ya'ya,
haihuwarta d'aya a duniya 'yarta d'aya macce mai suna *SUHAILAT* wacce ta b'ata tin lokacin da ta haifeta bikin sunanta kawai akayi washe gari aka wayi gari babu ta ba alamarta tab'ata."

B'acewar da har yanzun ba labarinta bare a san dalilin b'atan nata,
wacce a kullum hajiya laila take kukan rashin 'yarta kwaya d'aya tilo wacce take tunanin itace kwanta a duniya, tun daga gareta KO b'atan wata bata kumayi ba, amma sai dai tanaji a jikinta Suhailat d'inta bata mutuba, tana raye domin tana yawan mafarkin 'yarta ta girma tana cikin mawuyacin hali."
A kullum Addu'a takeyi Allah ya bayyanar mata da tilon yarta cikin k'oshin lafiya"
Cire glass din idonta tayi ta share hawayen dake zuba a idonta,
snn ta mayar da glass din a fuskarta,
takoma cikin mota ta zauna tare da jinginawa akan kujera,
Wayarta ta d'auka kira mijinta Alhaji *HABIB SANI NAIRA*,

*RINGING* d'aya zuwa biyu Alhaji Habib ya d'auka, a lokacin yana office suna mitting tare da yaransa akan cigaban da aka samu a kanfaninsa,
Yana ganin kiran nata Saida yasaki murmushi ya kalli wayar,
Snn ya tsayar da maganar da yakeyi,
Snn Ya d'auki wayar , Cikin so da k'aunar matarsa, kuma Amaryarsa yake fad'in "Amarya bakya laifi koda kin kashe d'an masu gida, da fatan kin isa lafiya."

Murmushi tasaki tana fad'in "Alhajina akwaika da tsokana shekara goma shatakwas kake kirana da Amarya,
Da ace Suhailat tana raye aida munfara shiga sahun iyaye dan kuwa kasan kamar yanzun mun sami suriki."
Murmushi yasaki domin shi kansa ta tayar masa da dafin b'atan 'yarsa wacce tafi soyuwa a ransa,
Itama yanzon yasan tashiga cikin damuwar domin yasan da zarar akayi zancen suhailat sai ta zubar da hawayenta,
Gyaran murya yayi yace "Amarya kamar yanda yake kiranta meyafaru dake ne?" domin najiya a jikina kina tare da matsala."

Share hawayen dake zuba a idonta tayi, cikin da sanshinyar murya tace "Alhajina muna kan hanyar tafiya,
munzo gaf da fita cikin gari muka samu matsala,
Yahuza direba ya bige wata yarinya 'yar fulani tana sanye da kayan fulanin a jikinta , a lokacin tana k'ok'arin k'e tara titin, yanzun hakan muna Asibity."

"Subahanallahi Alhaji Habib Naira yace,
Tare da mik'ewa tsaye a firgice,
yayiwa yaransa Alama da hannu akan sutafi sai ya k'ara nemansu,
Cikin Sauri yanufi hanyar fita , Da waya a kunnensa yana fad'in wacce asibityn kuke a halin yanzun?"
Hajiya laila ta fad'a masa sunan asibityn."

OK gani nan zuwa yace "yanufi wurin motarsa escort dinsa suka bud'e masa yashiga,
Suma suka shinshiga cikin nasu motocin suka nufi Asibityn."

***************

Kwance yake akan gadon Asibityn Sauk'i yasamu garesa Dan kuwa ba abinda yakeji yana masa ciwo a jikinsa,
Likita kawai yake jira yashigo ya sallame shi,

Gabansa yakeji yana fad'uwa akai akai,
Da zarar yaji hakan ba wacce take fad'o masa a rai sai Safna,
Tabbas yasan tana cikin mawuyacin hali,
Musamman rashin ganinsa da batayi ba, bataga yatura wurin maigariba domin a tsayar da ranar aurensu, dolene tashiga cikin damuwa."

Runtse idonsa yayi yanajin wani abin yana bugar masa zuciya wanda yarasa ko meye shi,
Babu abinda yake gani sai Fuskar safna yake kallo a idonsa,
a lokacin da take ce masa , "Yarima inasonka zanyi biyayya a gareka, zan zama tamkar baiwa a gareka,
Kada kajuyamun baya idan katina DA ni shigeyace bana da iyaye."

Hawaye suka shiga zuba a gefen idonsa,jikinsa yasoma rawa,
ji yakeyi kamar ya tashi ya tafi k'auyen a d'aura masu aure da ita ya d'aukota ya taho da ita domin yabata gata tabbatar da cewa *MARAYU MA 'YA'YA* ne kamar kowa.,

Hajjah tana ganin zubar hawayensa wanda har tagaji da ganin suna fita a idonsa,
tin Tana Tausayinsa tana tambayarsa damuwarsa har ya Kai ta zuba masa ido tana kallonsa,
Dan tasan halin sauban sarai akwaishi da zurfin ciki, idan zai shekara dubu da abu a ransa yana damunsa baxai tab'a furtawa ba, hakan zai barshi a ransa yayita damunsa, yana ramewa sai dai idan kai ka fahimta da kanka snn ka magance masa matsalar cikin salama."
Hakan yayi a lokacin Auren Saudat bai furta baya sonta ba,
Sai da akayi bikin yashiga cikin damuwa yana ramewa,
Tambayar duniya ba wacce ba'ayi masaba akan ramar da yakeyi kodai auren da akayi masa ne baya so,
Hakan zai girgiza kai alamar yanaso shi ba abinda yake damunsa,
Sai daga baya da hajjah ta saka masa ido anan ta fahimci baya son Saudat shine dalilin ramar tasa,
Hakan tayita kwantar masa da hankali akan ya rik'e matarsa hannu biyu tinda anriga da and'aura auren har ankawota gidansa,
Dole ne Ya koyawa zuciyarsa soyayyarta illaso daga baya idan yasami wacce yakeso sai ya aure ta."

sai gashi shigowar Saudat gidan lokaci d'aya tashiga ran hajjah saboda tsananin son da takeyiwa sauban wanda bata iya b'oyeshi a duk inda take ko a gaban waye,
Snn shigowar saudat cikin gidan lokacin sauban yasami kwanciyar hankali da zama a lafiya a cikin masarautar dan kuwa gimbiya jamila tsoron mahaifiyar saudat takeyi."

Maimartaba ya turo k'ofa yashigo da sallama,
Ganin hawaye suna zuba a idon yarima ya dakatar da fadawa akan kada sushigo su dakata waje ya mayar da k'ofa ya rufe."

Cikin takon mulki yake takowa ya isa gaban gadon sauban ya sanya hannu ya dangwalo hawayen dake fita a gefen idonsa,
ya dubesu da kyau cike da mamaki ya tabbatar da tabbas hawaye ne ke zuba a idon magajin sarki,
Cikin gid'ima sarki yake kallonsa bakinsa yana rawa yace "magajin Sarki hawaye a idonka?" Ina raye a duniya?"
Meyafaru?"
Ina yake maka ciwo?"
Sam ba girma bane hawaye su dinga fita a idon gwarzon namiji kuma magajin Sarki, tashi zaune muyi magana."

Jiki a sanyaye sauban ya tashi zaune yana kallon mahaifin nasa,
Hannu Sarki yasaka ya shafe masa hawayen fuskar tasa,
Yana kallonsa yace "bani labarin abinda yake damunka Wanda inada raina da lafiyata magajina yake zubar da hawayena akansa."

Kallon mahaifinsa sauban yayi ya sunkuyar da kai yace "Abba damuwata safna ce."
Chapter 28 · 0% Book details