← Book details Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 33

Sashe 22

Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Share hawayen da suka zubo Mata a fuska tayi tace
"kamar yanda nafad'a maka sunana Safna,
Ni 'yar garin Nan ce, mahaifina sunansa Jabiru ana kiransa da JAURO,
tinda na tashi bansan dad'in rayuwaba, a kullum cikin kuka nake da k'unci tare da wahalar rayuwa Mai tsanani a wurin uwar rik'o na,
Wacce a farko na d'auka itace mahaifiyarta sai daga baya da BABA yake fad'amun cewar ba itace mahaifiyata ba,
Sabida yaga irin wahala da tsangwamar da nakesha a wurinta
Yasa wata Rana ya zaunar Dani a lokacin Bata Nan tafita wurin biki,
Yake fad'amun cewar nayi hakuri da duk abinda INNO zatayimun nasani cewar ba itace mahaifiyata ba, asalima Bata tab'a haihuwaba Dan hakan yasa Bata San zafi da darajar 'ya'ya ba,
Yace "SAFNA Kiyi hakuri da kaddarar rayuwa da tasameni domin kuwa har ni Nan banine mahaifinki ba,
Na tsinceki ne a k'ofar gari a lokacin nadawo daga kasuwa misalin k'arfe 8 na dare a lokacin nayo Daren dawowa gida,
Anan Naga wani kwali a jiye bakin hanya jariri Yana ta faman kuka a cikinsa,
Lek'a kaina nayi a cikin kwalin naganki kwance kina sanye sanye da kayan sanyi da hula da Safar hannu da k'afa masu shegen kyau
An dunkuleki da towel Mai kyaun gaske kasancewar lokacin sanyi NE hannunki Yana sanye da zoben zinari Mai tsadar gaske,

Tausayina ya kamashi ya duka ya daukeni ya rungumeni a jikinsa yanufi wurin maigari Dani,
Anan yayiwa maigari bayanin a inda ya tsinceni."

Sosai maigari ya girgiza da maganar,
Hakan safiya ta waye a ka shiga cigiyata ko Allah yasa za'a Gane iyayena a tunaninsu Koda barayine suka shiga wani gida suka satoni idan iyayena sukaji sanarwa zasuzo su karbeni."
.shuru ba Wanda yazo yace yasan ko Mai Kama Dani,
Washe gari maigari ya yanke shawarar akaini birni a ajiyeni a gidan marayu."

Baba ya nuna Yana sona zai rik'eni domin baitaba haihuwa ba, shekararsa 20 da matarsa,
Hakan maigari ya Amince yabawa baba ni,
Ya kaima matar sa INNO."

INNO batayi farin cikin amsoni da baba yayi ba, Dan da farko cewa tayi bazata amsheni ba, sai da taga zata rasa igiyar aurenta snn ta amsheni."

Tin Ina makaramata nasan wahalar rayuwa domin da zarar nayi Kashi ko fitsari Inno zata dinga dukana tana zubamun ruwan sanyi a jiki,
Tin baba Yana fad'a Yana magana har ya Kai ya daina yashiga Jin shakkunta Wanda da alamar takaishi an d'aure Masa baki a wurin boka."

Hakan na girma duk wani aiki na gida nice keyinsa Dan Gane da girki d'ibar ruwa kiwo faskaran iccen da za'ayi sawwa dashi duk nice keyinsa,
lokaci take d'ibarmun da zarar lokaci yacika bandawoba zan Sha wahala a wurinta zata Sanya bulala ta dakeni daga k'arshe bazata bani abincin da zanciba a ranar da yunwa zan kwana"

Allah yayi Mai farin jinin jama'a
A yanda naji ana fad'a cewar ni kyakkyawa ce duk cikin k'auyen Nan ba Wanda ya kaini kyau, Dan hakan ake mantawa da rashin asalina saboda kyawona masoya suke turuwa a kaina."

Duk Wanda yazo neman aurena INNO take korarsa musamman idan ta fahimci Dan gidan mutumci ne, Wanda tasan idan ya aure Ni zanje na huta."

Duk abin Nan da akeyi baba bai San abinda akeyiba,
Shi a ganinsa rashin samun mijin aure da banyiba,
Wata k'ila Aljanu suka aure Ni, Dan kuwa duk sa'ata sunyi aure wasu har sun haihu, Ni har yanzun shuru ba miji gani kyakkyawa ajin farko."

Mutum d'aya ne ya jure korar jummai da tsangwamarta ya nace akaina cewarsa tinda Yana Sona sai ya aureni babu Wanda ya Isa ya Hana,
Sunan shi AUDU."

Audu D'an sarkin kiwo ne dake cikin k'auyen mu,
Sosai Yan matan garin suke ruguguwa a kansa domin yace Yana sonsu bai furta hakan ba sai a kaina."

Bana son Audu sam a Raina domin ni duniyar ma gaba d'aya taficemun a Rai fatana Akoda yaushe Allah yayi mun mafita, ta Alheri ya bayyanarmun da iyayena domin naji dad'in da yasa suka jefar dani a lokacin da nake da buk'atarsu." Hakan Nan nake kula Audu nasanyawa rayuwata zan aure shi Koda bana sonshi, kodan na huta da azabar Inno."

Ana hakan D'an maigari JARMAI JAN WUYA shima yafito neman aure na,
Sosai Inno tayi farin cikin fitowar Jarmai domin tasan da zarar sun Kara da Audu wurin shad'i,
ba makawa zai cinye Audu, dele a d'aura mun Aure da Jarmai,
duk yarinyar da jarmai yace Yana so a garin Nan sai ya aureta Koda Bata sonshi Dan kuwa, za'ayi zab'en fidda gwani a filin shad'i kamar yanda Al'adarmu ta fulani take duk akayi shad'i Jarmai keda nasara,
duk mutunen garin sun San da hakan,
Yanzun shekara 7 kenan duk shad'in 'akayi shine ke cinyewa, Kuma a Nan take za'a aura Masa yarinya, dare D'aya Yake farketa batare da yaji tausayintaba sai ya gama biyan buk'atar gareta har na tsawon sati daya snn yake sakota wasu yaran mutuwa sukeyi wasu Kuma sukan kamu da ciwon yoyon fitsari, wasu Kuma Allah ya taimakesu su gyaru,
yarinya bakwai Jarmai ya aura a cikin garin Nan duk hakan yake masu."

Ta share hawayen fuskarta taci gaba da cewa, "yanzun saura wata biyu ayi shad'in mu, zasu Kara tsakaninsa da Audu duk Wanda yacinye shi zan aura, nasan jarmai ke da nasara domin duk mutanen gari sun shaida hakan."

Tin daga ranar da aka saka ranar shad'inmu duk Wanda yagani, ya rabeni da sunan yana sona, ko yana mun magana indai namijine sai Jarmai yayi Masa bugun mutuwa."

Mutum biyu Yana kashewa Akan sun furta suna Sona,
Hakan ya Hana Audu yin magana Dani,
Shi kad'ai Yake magana Dani duk a cikin garin Nan, Dan hakan idan nafito kowa baya son ya ganni bare yayimun magana Domin gudun wahalar Jarmai,
Idan nafito kiwo zai dinga zagayena duk ranar da Mai rabon wahala yasa yayimun magana a ranar sai dai uwarsa ta haifi wani."

Wnn dalilin yasa nadinga fad'a maka Kayi nisa da rayuwata gudun kada ya ganmu a tare yayi maka illah sai gashi kasayeshi da kud'i a lokaci d'aya."

Ta fashe da kuka Mai sauti tace "tayaya zaka taimakeni?"
Kabarni kawai har zuwa lokacin da mutuwata zatazo ta daukeni Dan kuwa bana da gata, iyayena sun zubar Dani a lokacin da nake da buk'atarsu."

Sosai idon Sauban yacika da hawayen tausayinta,
Ashe a duniya akwai Wanda yafishi shiga cikin matsalar rayuwa?"

Saurin goge hawayen fuskarsa yayi Dan gudun kada tagansa,
Yasanya handkichif yashiga share Mata hawayen dake zuba Akan fuskarta ji Yakeyi kamar ya janyota ya rungumeta, shima ya fad'a Mata damuwarsa,
kukanta ya tsaya cak jin hannun D'an birni a kan fuskarta Yana share Mata hawaye,
Sai da ya goge Mata hawayen tas snn ya juyo da ita suka fuskanci juna yace "daga yau kukanki ya k'are, bana son ganin zubar hawayenki."

Safna Kin Amince Dani?"

Ta d'aga kai alamar eh."

Ya Dan saki murmushin gefen Baki, yace "yanzun a wane wuri Audu yake Zama?"

Tace "Audu baya gari yatafi binni sai ana gobe shad'i zai dawo."

Girgiza Kai yayi alamar gamsuwa zaiyi magana Kenan wayarsa ta dau ringing yacirota yayi a gaban Aljihunsa ya duba safwn yagani yaja dogon tsaki ya d'auki wayar tare da karawa a kunnensa yayi shuru batare da yayi maganaba ,
"Muryar safwan yaji Yana fad'in "aboki kana Ina ne nadubaka banganka ba."

"Meyafaru?" Sauban yace."

Tambayar me yafaru tabawa safwan haushi, yace ai Kaine zan cewa meyafaru sabida a yanda naji muryarka baka cikin natsuwarka
Kana ganin la'asar ta gabato kazo muyi Shirin tafiya, kamanta ne har zamfara zamutafi, Wai kana Ina ne hakan?"

"Bansaniba Domin baka aikeniba,
Kajira gani Nan zuwa yanzun.
idan kuma a matse kake kana iya komawa gida,
Dan nasan abinda zaka cemun kenan."

Dariya safwan yasaki, wacce yasa Sauban yayi saurin kashe wayar tare da Jan dogon tsaki,
Mik'ewa tsaye yayi Yana kallon Safna yace "ki waita Addu'a kisanya Allah a gaba domin shine Mai yin komai,
Ki daina ganin laifin mahaifanki domin bakisan dalilin da yasa suka jefar dakeba."
Ki daina yawan kuka saboda kuka yakan haifar da matsaloli a lafiyar D'an Adam."

Snn ki yawaita zagayowa wurin Nan saboda a Ko wanne lokaci zan iya zuwa nemanki a Nan."

Ya juya yayi tafiyarsa har yayi nisa ya juyo ya kalleta yaga shi take kallo tana murmushi, D'an murmusawa yayi yace "kicire tsoro Jarmai a ranki domin babu wani abu da ya Isa yaimaki Kuma insha Allah bazaki aure Shiba,
Ya juya yayi tafiyar sa."

Tafiya yakeyi tunaninta yake tare da juya magagganun da ta fad'a Masa dangane da rayuwar ta,
Tabbas tana buk'atar taimako."

A hakan har ya Isa gidan gonar ba Wanda yaga dawowarsa Kai tsaye d'akinsa yanufa ya fad'a kan gado yayi filo da hannunsa yashiga duniyar tunani,
Ba abinda yake tunani sai ta wacce hanya zaibi domin ya taimaketa,
D'an karamun bakinta yashiga hangowa yanda take juyashi tana Masa magana, tare da manyan idanunta masu zubar da Hawaye,
Tabbas Safna tana da kyau domin ko a turai baitaba wacce tayi kyantaba, wahalace da danti yasaka kyawon nata ya kusan disashewa."

Dogon tsaki yaja ya Kuma mirginawa, tare da janyo filo,
Sai mutum yaji a kan filon,.
D'aga idonsa yayi domin ganin ko waye,.safwan ya gani kwance Yana kallonsa cike da mmki."

Tsaki ya Kuma ja Yana fad'in "meye hakan safwan?"

Safwan yace "meye hakan Sauban da ka kusan Hawa kaina."
Me Yake damunka ne Naga duk ka birgice kashiga duniyar tunani kamar Wanda ya fad'a soyayya a lokaci Daya Ina kafito?."

Jan tsaki Sauban yayi ya Kai Masa harara."

Dariya safwan yasaki tare da sauka daga Kan gadon yace "ko tsaka da tayi tsaki Allah sai da ya tsine mata,
Malam katashi tinda kadawo mu fara Shirin tafiya kasan inada iyali."

Kallonsa Sauban yayi yace "sai gobe zamu bar nan, ba yau ba."
Daga hakan ya mik'e ya bar Masa d'akin, domin Yana da buk'atar Zama yayi dogon tunani Wanda yasan indai safwan Yana a wuri surutunsa bazai barka kayi wani nazariba,

_kai Safwan a rage surutu kayi hakuri Sauban Nima hakan nake fama da nawa safwan din har ciwon Kai Yake sakani_🤦🏻‍♀

Bin bayansa safwan yayi Yana fad'in "dakata malam Wai meyake damunka ne munzo lafiya k'alau lokaci d'aya duk ka wani birkice."
Chapter 22 · 0% Book details