← Book details Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 33

Sashe 29

Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki yasaki wani murmushin irin nasu na manya,
Hajjah taja dogon tsaki ta juyar da kai gefe, domin ita wlh ta d'auka wani abin can daban yake damunsa ko yake masa ciwo wanda yake sakashi yana zubar da hawaye.
Ita tarasa ko yaushe sauban ya susuce yazama raggo hakan DA. har yake zubar da hawayensa Mai tsada a kan macce."

Sarki ya juya ya kalli hajjah yasaki murmushi snn ya nemi wuri ya zauna a gefen gado a kusa da sauban ya kallesa yana murmushi yace "fad'amun meyasami safna d'in?"

Kallonsa sauban yayi ya sunkuyar da Kai k'asa yace "inaji a jikina akwai wani mummunan abu da yasameta,
Abba Safna abar tausayice bata da iyaye bata da kowa sai Allah saini dana d'auki Alk'awari Zan taimaketa,
Abba bawai son safna nakeyiba kawai ina tausayin halin da take cikine,
DA kuma Wanda zata shiga idan tarasani,"
Abba Ina neman Alfarma a Karo na farko a wurinka itace katura fadawa yanzun nan sutafi k'auyen domin a tsayar da ranar aure na da Safna,
domin gudun kada asami Matsala a cikin Al'adarsu."

Murmushi Sarki yasaki Wanda har sai da hakoransa suka fito,
Yana kallon sauban cike da wauta wai ba sonta yakeyi ba, bayan ga soyayyarta nan ya gani k'arara a cikin idonsa,
Murmushi Sarki ya kuma saki yana kallon sauban Yace "hakan kakeso a aiwatar yanzun magajin sarki?"

D'aga kai sauban yayi alamar eh."

Sarki yace to "idan maigari yace a lokacin yake so d'aura
auren naku a tsaya a amso maka aurenta ko kuwa abarshi rana kawai kakeso asaka maka?"

Shuru sauban yayi ba amsa.
Sarki yasaki dariya wacce yasaka sauban shima ya d'an murmusa cike dajin kunya,
Sarki yace kabani amsa kai nake saurare domin da kaina zantafi ba aikeba "

Cikin jin kunya sauban ya sunkuyar da kai yace "duk yanda kace ranka ya dade a aiwatar da hakan."

Sarki ya kuma sakin dariya yace "wnn amsar kai zaka bani ita,
Saboda a lokacin da kake zubar da hawayen k'auna baka nemi shawara daniba."

Cike da jin kunya sauban ya kuma sunkuyar da kai sarki yana ganin hkn ya had'e fuska cike da zulaya yace "to shikenan Zan fasa tafiyar zan tura fadawa Zan ce masu da zarar suntafi akace za'a d'aura aure a lokacin zance kabada umurnin "kada a d'aura kai baka ra'ayin hakan, rana kawai kakeso asaka maka,
Idan sukace ba hakan sukeyiba,
Zance kace kabarwa duk Wanda yake sonta a d'aura dashi."

Da sauri sauban ya d'aga Kai ya kalli Sarki yaga da gaske yake ba wani alamar wasa a tare dashi yace "ranka ya dad'e ba hakan nake nufiba, a d'aura auren dani, sutaho tare da ita."

Dariya ta sub'ucewa sarki wacce tasaka sauban jin kunya,
Yayi saurin kwanciya tare da juya baya yana murmushi cike da jin kunya."

Hajjah tana jin duk abinda sukeyi bata tanka masuba domin ta dade da sanin Sarkin Abdullah shi yake sakanta sauban yake yin duk abinda yaga dama."

Sarki ya mik'e tsaye yana murmushi ya kalli hajjah yace "umma zamutafi karb'owa jikanki Aure a k'auyen gidan gonarsa, saiki shirya tarbon kishiya ta biyu."

Mere baki hajjah tayi tace kafin a d'aura ayi binciken asalinta da abinda ya kashe iyayenta domin naji yana fad'in bata da iyaye,
Snn a tabbatar da asalinsu mai kyau ne tafito a cikin gidan asali, da daraja basa da wani abin fad'a,
kodan samun zuri'a mai tsafta,
Snn kada ka manta a cikin gidan sarauta zata shigo shi kuma gidan sarauta duk Wanda kagansa yashigo cikinsa a matsin matar Sarki KO d'an Sarki KO jikan Sarki dolene ya zamana yana da asuli Mai kyau.
Idan babu wnn to tabbas bata cancanta da zama matar saba dole ne ya barta duk son da yake mata."

Gaban sauban ya fad'i dajin furuncin hajjah."

Sarki yace "tabbas hakan ne umma,
Sai dai inaji a jikina kamar farin cikin da mahaifiyarsa take fad'ar masa zai samu a cikin gidan gonar sa,
Ina hasashen shine ya fara bayyana a garesa." Domin samun macce ta gari babban farin cikin d'a namiji, yasami rabin duniyarsa domin kullum cikin farin ciki zaiyi ta zama har k'arshen rayuwarsa

Yanufi k'ofar fita yace "muntafi,
Hajjah tace "adawo lafiya."

Snn Sarki yafita ya bawa fadawa umurnin sushiga mota,
ya fad'a masu inda za'a tafi,
Suka d'auki hanyar k'auyen Lassa."

Suna fita daga asibityn Anawa Sarki jiniya,
Alhaji Habib Naira shima yashigo da tawagarsa sarki yabada umurni a tsaya,
hakan shima Alhaji Habib yaba da umurni a tsaya, anan suka fito daga motar suna dariya suka shiga gaisawa da juma cike da farin ciki da kewar juna,
Tare da tambayar yaushe rabo,
Domin Alhaji Habib business dinsa baya barinsa zama yau yana wannan k'asa gobe yana wancan k'asa jibi yana wancan k'asa."

Anan Alhaji Habib yake tambayar Yaya Sauban?" Ai yanzun
Yasan yaron ya girma sosai."
.dariya sarki yasaki yana fad'in sosai kuwa har yayi aure,
Yanzun hakan k'arb'o masa auren mata ta biyu zamu tafi muyi."

Kuma tab'awa sukayi suna dariya Alhaji Habib yace "yaro yayi gadon ajiye mata da yawa,
kaine baya ko ni."

Sarki yasaki dariya yana fad'in lafiyar kenan, ai duk Wanda ya ganmu yasan ba rangwanci a tare damu."

Suna dariya tare da zolayar juna sukayi sallama ko wanne yashiga motarsa Alhaji Habib yana fad'in abokina kafin natafi zan shigo fada domin asakamun Albarka,

Sarki yana dariya yace "badamuwa sai ka shigo,
Sukaja mota suka tafi cike da farin cikin ganin juna domin abokanaine sosai kasuwanci ne yarabasu da junansu."

Sarki yana fita daga asibityn likita yashigo ya k'ara duba jikin sauban yaga yasami lafiya,
Anan take ya sallamesu direba tare da fadawa suka d'aukesu a mota suka nufi gida su."

****************

Dawowar dakaru da labarin da sukaje dashi na tarwatsa k'auyen su safna ba k'aramun farin ciki yasaka Saudat da mahaifiyar taba,
Musamman dasukaji cewar Safna ta mutu domin,
Sunce dajin da tabi da gudu anan ne maciji ya kashe biyu daga cikin mutanensu, suma dakyar suka sha,
Suna da yak'inin ko gaggar jikin safna baza'a gani bare gawarta shikenan ta mutu sai dai wata ba itaba"

Wayyo dad'i a ranar Saudat kid'a tasaka a b'angarenta saboda farin ciki sai cashewa takeyi tana rawa, tana juyawa Yau duniya tamata dad'i, gaba d'aya ta manta da mijinta dake kwance akan gadon asibity."

Har sauban yadawo gida batasaniba,
Hakan ya nufi part d'insa ya shiga toilet yayi wanka yafito, yasaka k'ananun kayansa marasa nauyi farin wando riga bak'a,
Yunwa yakeji amma babu abinci a b'angaren nasa,
Hakan ya janyo 'ya'yan itatuwa ya soma ci,
Ciyakeyi yana lumshe ido
Babu abinda yake masa yawo a kai sai magagganun da hajjah tayi akan Safna, sune suke masa yawo sunaso su birgita masa,
kwakwalwa,
Wad'anda take cewa _dole ne a binciko asalinta atabbatar da suna da kyakkyawan asali basa da wani abi fad'i, domin duk wacce taza shigo gidan sarauta dolene sai in tana da cikakken asali mai kyau_

To yanzun idan sarki ya shiga bin ciken asalinta yasami cewar tsintar ta akayi a gefen hanya,
ana nufin bata da asali shegiyace Shikenan."

Rasa zaiyi bazai taimaki rayuwarta ba?"
Runtse idonsa yayi yanajin zuciyarsa tana k'una,
Jiyakeyi duk abinda zai faru sai dai yafaru amma bazai tab'a barin rayuwar safna ta sallawanta ba, akan wani dalili can nasu na masarauta."

sautin kid'a yakeji yana tashi a part d'inta Wanda duk ya damesa ya hanashi sukuni bare yayi tunanin mafitar abinda yake damunsa, kwakwalwarsa da kansa duk sun har gitse,
Cikin zafin rai yafita yanufi part dinta,
Har ya tura k'ofa yashiga batasaniba abinda baitab'ayiba shiga d'akinta."

Manyan mata yagani su hud'u kwance a kan gadonta KO wacce ba kayan kirki a jikinta,
Tana tsaye a tsakiyar d'aki sai rawa takeyi tana juyawa, irin rawar da turawa sukeyi idan suna cikin farin ciki."

Wani bak'in ciki ya kamasa ya kashe soket d'in,
Jin shurun da tayi ba sauti t
Yasa ta juya a fusace domin ganin Wanda ya kashe mata sauti."

Ido biyu tayi dashi tsaye a bayanta,
Anan take gabanta ya fad'i,
Ta juya da sauri ta kalli matan da ta ajiye a kan gadonta."
ajiyar zuciya ta sauke ganin ba abinda suke aikatawa a kwance kawai suke,

Kallonta yakeyi cike da tsana da takaici da ace shi ma'abucin dukan macce ne da yau babu abinda zai gana ya daki saudat yayi mata duka irin na mutuwa."

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍

🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴

Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)

*Page 29*

******* A lokacin da aka nufi asibity da Safna ba rai bare numfashi a tare da ita,
Kai tsaye Emergency aka nufa da ita cikin gaggawa likitoci suka k'arb'eta suka duk'ufa a kanta domin ceto rayuwarta da tsayar da jinin dake fita a hanci da bakinta."

Sosai hajiya LAILA ta girgiza da ganin yanayin da yarinyar tashiga, danko fuskarta bata tsaya ganiba hankalinta a tashe yake matuk'a."

Hajiya laila mace ce mai mai tausayi mai son 'ya'ya,
haihuwarta d'aya a duniya 'yarta d'aya macce mai suna *SUHAILAT* wacce ta b'ata tin lokacin da ta haifeta bikin sunanta kawai akayi washe gari aka wayi gari babu ta ba alamarta tab'ata."

B'acewar da har yanzun ba labarinta bare a san dalilin b'atan nata,
wacce a kullum hajiya laila take kukan rashin 'yarta kwaya d'aya tilo wacce take tunanin itace kwanta a duniya, tun daga gareta KO b'atan wata bata kumayi ba, amma sai dai tanaji a jikinta Suhailat d'inta bata mutuba, tana raye domin tana yawan mafarkin 'yarta ta girma tana cikin mawuyacin hali."
A kullum Addu'a takeyi Allah ya bayyanar mata da tilon yarta cikin k'oshin lafiya"
Cire glass din idonta tayi ta share hawayen dake zuba a idonta,
snn ta mayar da glass din a fuskarta,
takoma cikin mota ta zauna tare da jinginawa akan kujera,
Wayarta ta d'auka kira mijinta Alhaji *HABIB SANI NAIRA*,

*RINGING* d'aya zuwa biyu Alhaji Habib ya d'auka, a lokacin yana office suna mitting tare da yaransa akan cigaban da aka samu a kanfaninsa,
Yana ganin kiran nata Saida yasaki murmushi ya kalli wayar,
Snn ya tsayar da maganar da yakeyi,
Snn Ya d'auki wayar , Cikin so da k'aunar matarsa, kuma Amaryarsa yake fad'in "Amarya bakya laifi koda kin kashe d'an masu gida, da fatan kin isa lafiya."
Chapter 29 · 0% Book details