← Book details Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 33

Sashe 31

Dan Sarkin Sauban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki yana fita daga asibityn likita yashigo ya k'ara duba jikin sauban yaga yasami lafiya,
Anan take ya sallamesu direba tare da fadawa suka d'aukesu a mota suka nufi gida su."

****************

Dawowar dakaru da labarin da sukaje dashi na tarwatsa k'auyen su safna ba k'aramun farin ciki yasaka Saudat da mahaifiyar taba,
Musamman dasukaji cewar Safna ta mutu domin,
Sunce dajin da tabi da gudu anan ne maciji ya kashe biyu daga cikin mutanensu, suma dakyar suka sha,
Suna da yak'inin ko gaggar jikin safna baza'a gani bare gawarta shikenan ta mutu sai dai wata ba itaba"

Wayyo dad'i a ranar Saudat kid'a tasaka a b'angarenta saboda farin ciki sai cashewa takeyi tana rawa, tana juyawa Yau duniya tamata dad'i, gaba d'aya ta manta da mijinta dake kwance akan gadon asibity."

Har sauban yadawo gida batasaniba,
Hakan ya nufi part d'insa ya shiga toilet yayi wanka yafito, yasaka k'ananun kayansa marasa nauyi farin wando riga bak'a,
Yunwa yakeji amma babu abinci a b'angaren nasa,
Hakan ya janyo 'ya'yan itatuwa ya soma ci,
Ciyakeyi yana lumshe ido
Babu abinda yake masa yawo a kai sai magagganun da hajjah tayi akan Safna, sune suke masa yawo sunaso su birgita masa,
kwakwalwa,
Wad'anda take cewa _dole ne a binciko asalinta atabbatar da suna da kyakkyawan asali basa da wani abi fad'i, domin duk wacce taza shigo gidan sarauta dolene sai in tana da cikakken asali mai kyau_

To yanzun idan sarki ya shiga bin ciken asalinta yasami cewar tsintar ta akayi a gefen hanya,
ana nufin bata da asali shegiyace Shikenan."

Rasa zaiyi bazai taimaki rayuwarta ba?"
Runtse idonsa yayi yanajin zuciyarsa tana k'una,
Jiyakeyi duk abinda zai faru sai dai yafaru amma bazai tab'a barin rayuwar safna ta sallawanta ba, akan wani dalili can nasu na masarauta."

sautin kid'a yakeji yana tashi a part d'inta Wanda duk ya damesa ya hanashi sukuni bare yayi tunanin mafitar abinda yake damunsa, kwakwalwarsa da kansa duk sun har gitse,
Cikin zafin rai yafita yanufi part dinta,
Har ya tura k'ofa yashiga batasaniba abinda baitab'ayiba shiga d'akinta."

Manyan mata yagani su hud'u kwance a kan gadonta KO wacce ba kayan kirki a jikinta,
Tana tsaye a tsakiyar d'aki sai rawa takeyi tana juyawa, irin rawar da turawa sukeyi idan suna cikin farin ciki."

Wani bak'in ciki ya kamasa ya kashe soket d'in,
Jin shurun da tayi ba sauti t
Yasa ta juya a fusace domin ganin Wanda ya kashe mata sauti."

Ido biyu tayi dashi tsaye a bayanta,
Anan take gabanta ya fad'i,
Ta juya da sauri ta kalli matan da ta ajiye a kan gadonta."
ajiyar zuciya ta sauke ganin ba abinda suke aikatawa a kwance kawai suke,

Kallonta yakeyi cike da tsana da takaici da ace shi ma'abucin dukan macce ne da yau babu abinda zai gana ya daki saudat yayi mata duka irin na mutuwa."

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍

🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴

Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)

*Page 30*

*ALHAMDULILLAH ALLAH NAGODE MAKA DOMIN KAINE ABIN GODIYA,*
*INA KUKE MASOYA DA ABOKANAN ARZIKI INA GODIYA A GAREKU DOMIN KUN NUNAMUN KULAWA BABU ABINDA ZANCE SAI DAI NAYI MAKU FATAN ALHERI A DUK INDA KUKE, DA MASU KIRAN WAYANA DA MASU TUROMUN MASSAGE DUKA NAGODE ALLAHU YA BAR K'AUNA NAJI SAUKI SOSAI ALLAH YABANI IKON FARANTA MAKU NAGODE NAGODE NAGODE*🤝🏻🤝🏻

******* kallon tsana Sauban yaci gaba da wurgawa Saudat, cike da jin haushi da tak'aicinta,
yaja dogon tsaki ya juya ya bar wurin yanufi d'akinsa,
Kan gado ya kwanta rigingine ya rufe ido yana tunanin mugun hali irin na Saudat."

Saudat kuma tana ganin ya yafita,
A fusace ta juya ta kalli 'yan matan dake kwance a kan gadonta ta sakar masu harara cike da bak'in cikin ganin da mijinta yamasu a hakan, wani irin kishin mijinta taji ya taso mata, taja da baya ta jingina a bango tana sauke numfashi da sauri da sauri kamar wacce tayi gudu, hawayen bak'in ciki suka shiga kwarara a idonta, bakad'an taji zafin ganin da sauban ya masu cikin tsinanun kayan dake sanye a jikinsu ba,
Bud'e idonta tayi wad'anda suka rine zuwa launin ja, ta d'orasu akansu, ta warga masu kallon tsana,
A fusace ta daka masu tsawa tace "kutashi kufita na tsaneku, bana son nasake ganin fuskokinku,
Kuma kusani sai kun d'and'ani azabata mai tsanani sakamakon ganin tsaraicin da mijina yayi maku
Tin yanzun kuzab'awa kanku horo mafi tsanani kafin na zab'a maku da kaina."

Gabanta suka kai durk'ushe tare da had'e hannayensu wuri d'aya alamar ban hak'uri,
Suna fad'in ranki ya dad'e tuba mukeyi,
Ki gafarcemu bazamu sake ba, bamusan yarima zai shigoba ayi hakuri ya uwargijiya mai Adalci,

"Kufita nace tare da nuna masu k'ofa waje,
Cikin sauri suka fita suka bar d'akin."

Juyawa tayi tafita tanufi d'akin yarima,
tura k'ofar d'akinsa tayi sannu a hankali da sallama a bakinta,

Jin shuru ba'a amsa bata ba yasa taja ta tsaya tana kale kale a ina zata ganshi
A can kan gado ta hangosa kwance yayi rigingine idonsa a rufe tamkar Wanda yakeyin bacci,
Ajiyar zuciya ta sauke tashiga takawa sannu a hankali ta nufi wurinsa,
A gefen gadon taja ta tsaya a dai dai saiti kansa ta d'an sunkuyar da kanta tana kallon kyakkyawan gashin kansa wanda yake kwance a kansa tamkar gashin kan jariri,
Hakan ya kuma sanya fuskarsa tayi kyau da adon,
sajensa Wanda yake zagaye da fuskarsa har zuwa bakinsa, tashiga kallo anan take tsikar jikinta ta tashi tafarajin wata irin matsananciyar sha'awarsa tana dirar Mata,
Tana' tsananin son gashin bakinsa, tana son tayita kallon kyakyawar fuskarsa mai cike da Annuri,
A hankali ta sanya hannu ta shiga shafa masa gashin bakinsa tana fad'in "Sadaukina kayi hakuri idan na b'ata maka rai."

Idonsa ya bud'e ya d'orasu a kanta ya wurga mata wani irin kallon tsana snn ya mayar da idonsa ya rufe."

Firgicewa tayi da kallon da ya Mata,
Ta kuma narkewa tana basa hakuri,
Shuru yayi bai tanka Mata ba,

sai da tayi magiya ta gaji, ganin baya da niyar tanka mata yasa ta tashi nufi kicin domin shirya masa abinci wata k'ila yunwa yakeji, ko ganin hakan zai sanya zuciyarsa tayi sanyi."

******************

Alhaji Habib Naira yana shiga cikin Asibityn gaba d'aya idon mutane sukayo kansa,
Anan take masu Neman taimako suka zagayeshi domin shi mutumin jama'a ne, mutum ne mai Alheri da tausayi
Dan hakan da zarar jama'a sukayi ido biyu dashi to kukansu ya kare domin Alhaji Habib Naira zaiyi masu kyautar girma da ban mmki."

Hakan aka zagayeshi sai kud'i yake bawa mabumuk'ata, da gajiyayyu,
Da gyar escort nashi suka da katar da sauran jama'a snn yasami hanyar wucewa ya isa wurin matarsa Hajiya laila wacce take zaune a cikin mota tana kallonsa."

Motar da take ciki escort nashi suka bud'e masa ya shiga,
Idansa akanta yana sakar mata murmushin so da k'auna a duniya bayan iyayensa babu abinda yakeso da ganin farin cikinsa kamar hajiya laila,
Janyota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta yashiga share mata hawayen dake zuba a idonta, cikin sigar lallashi yake kwantar mata da hankali akan ta d'auki kaddara akan duk abinda ya faru ta daina sanyawa ranta damuwar b'atan suhailat."

Doguwar ajiyar zuciya Hajiya laila taja snn tasakarwa mijinta murmushi tare da rik'o hannunsa duka biyu ta saka a cikin nata hannun ta d'an matse kad'an cike da shauk'i
tashiga fad'in na daina mijina ina Addu'a a koda yaushe Allah ya k'aramun dauriya da dangana a kan rashin tilon yata danayi."

Dariya Alhaji yasaki yace "Ameen tare da kashe mata ido d'aya yana fad'in insha Allahu wnn dawowar danayi sainayi k'ok'ari nabaki wata Suhailat d'in kinga shikenan na kashe bakin magana."

Dariya tasaki tana fad'in "kai Alhaji bakada dama mezan iya tsofai tsofai dani."

Hararar wasa ya sakar mata yana fad'in "a Ina tsofan yake, a yanda nakejinki kinfi sabuwar budurwa dal a leda komai,
Dan kuwa duk Wanda ya kalleki yasan nayi dace nayi sa'a a cikin maza samun kyakkyawar macce mai tsafta da iya ado uwa uba ga k'amshi, ni kuwa me zanyi da wata macce a duniya idan kina tare dani."

Murmushin farin ciki take saki domin tana yawan jin wnn yabon a bakin gwarzon mijin nata,
."nagode mijina Allah yaci gaba da faranta maka kamar yanda kake farantamun."

Ameen yace tare da cire hannunsa cikin nata yana fad'in "mutafi naga marar lafiyar Allah yasa ta farfad'o."

Hakan suka bud'e k'ofa suka fita fuskokinsu cike da farin ciki escort suka take masu baya suka nufi d'akinda Safna take ciki a kwance cikin mawuyacin hali."

Wurin gadonta suka nufa inda Alhaji Habib naira yana yin ido biyu da fuskarta sai da gabansa ya fad'i, yayi saurin k'arasawa wurin gadonta yana kallonta,
Hajiya laila kuma ta juya tana bawa escort umurni akan su dakata a waje kafin sufito,
Snn ta juya ta cewa Alhaji mutafi, ganin baya kusa da ita, yasa
Cikin sauri d'aga kai ta hangosa a bakin gadon safna yana k'are mata kallo cike tausayi,
Wurin ta nufa taja ta tsaya a kusa dashi tana fad'in Alhaji kaga yarinyar ko gwanin ban tausayi,
Dam gabanta ya fad'i da tayi ido biyu da safna wacce a lokacin ta farfad'o daga allurar baccin da akayi mata."

Cikin sauri hajiya Laila tanufi wurin safna tana kallonta ido ciki ido Wanda itama safna kallonta takeyi hawaye suna mata zuba a gefen idonta,

Sannu yaya jikin naki Hajiya laila tace."
D'aga Kai safna tayi alamar da sauk'i,
Hawaye kawai kezuba a idonta ga wani irin fad'uwar gaba da takeji tarasa sanin kona meye."

Suna tsaitsaye akan gadon safna ba Wanda ya kuma yin magana dukansu su uku gabansu sai fad'uwa yakeyi bakinsu ya rufe ba Wanda ya kuma furta kalma d'aya,
Likita ya turo k'ofa yashigo tare da sallama."

Gaida Alhaji yyi snn yanufi wurin safna,
yacire mata ruwan da ya k'are ya kuma juna Mata masu,
Ido kawai safna take bin koya dashi tana kallo hawaye suna Mata zuba,
Gyaran murya likita yayi ya kalli hajiya yace "Alhmdulillah ba wata matsala a tare da ita,
Duk iya gwaje gwajen da mukayi mungano buguwa ce kawai tayi a kanta Wanda insha Allah nan da kwana biyu zata sami lafiya."

Alhaji yace Allah ya k'ara bata lafiya."

Suka amsa da "Ameen."
Chapter 31 · 0% Book details