← Book details Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

```Gamasu buk'atar A tallata musu hajjarsu k'ofa bud'e take zaku iya Aiko tallanku A rubuce nasaka muku cikin shafin littafaina Akan farashi Mai sauk'i, .. Inakuke Y'an kasuwa Kuma kuzo Inayin logo graphics ko wanne iri had'ida cartons Art's design kudai kugarzayo domin mallakar naku cikin sauk'i...... Domin magana dani A WhatsApp 07064904617 OR 07031012948 ✍️ Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 Queen 👸 of Writer's Hausa novels 📚📖📚 And design graphics```

```Ina kuke ma'abota ƙamshi Mata da Maza nesa tazo kusadaku BINTOUR ALIEY PERFORM Duniyar ƙamshi Cikin rahusa da Rangwame muna maraba da masu dasayen ɗaya koma Y'an sari muna turaruka kamar:~
sandal flasks, sandal wood, sandal bangi, Senegalese kajiji, kabbasa, humra fara, da brown,musk, turaren gogawa Kala Kala, turaren tsinke, dadai sauransu.... Zaku iya Nemanmu A 07048605381, Or 07040154174 Whatsapp ko kira,... BINTOUR ALIEY PERFORM, DUNIYAR ƘAMSHI DA KECE RAINANI...... MUNA MARABA DA ZUWANKUUUU....

Haka kuma munada kayan gyaran jiki kala kala, magungunan mata ma zaku samu garemu masu kyau da Inganci 💯, banan muka tsaya ba domin Kuwa muna da Alaƙa da GHT COMPANY magani kan ko wacce cuta H.I.V, SIKLER, HAWAN JINI, CIWON BAYA, MATSALAN IDA NUWA, da sauransu.... Kayan kitchen kayan sakawama duka zaku samu garemu, kudai kawai ku hanzarto neman mu kan ko wacce matsala zamu tsaya domin baku maganin ta in sha Allah.... Zaku iya tuntuɓarmu a 07064904617,.. mungode!........```

_JULLY 2026_

```JIGON LABARIN
Labarin wani matashi mai suna BINASH wanda ya taso cikin talauci amma yana da burin zama babban ɗan jarida. A cikin aikinsa, ya fuskanci cin hanci, barazana daga masu iko, yaɗa ƙarya a kafafen sadarwa, da ƙalubalen neman gaskiya. Duk da haka, ya tsaya kan gaskiya har ya zama sanannen ɗan jarida wanda ya taimaka wajen ceto rayukan mutane da kawo gyara a al'umma. BINASH Kenan ƊAN JARIDA
(THE JOURNALISM)......```

*PAGE 16 TO 20*

Washegari da safe ya tafi aikinsa ya bar Kowa lafiya, itadai Banasha tana kan hutun amarci.

Bayan wasu a wanni yana kan aikin sa wayar ta soma ƙara.

Yana ɗagawa sai ya ji kuka.

Binash ce matar sa

"Dear... Dear..."

"Me ya faru?" Cikin tashin hankali yayi tambayar

Sai ta fashe da kuka.

"An buge Umma da mota!"

Duniya ta juya wa binash

Wayar ta kusa zamewa daga hannunsa, da ƙyar ya iya aro na tsuwa yace"kuna wace asibitin"?

Cikin kuka tace "Amana hospitals"

Kashe wayar yayi cikin sauri ya fito ƙaramin mashing ɗin sa ya hau ya nufe asibitin

Bai ma san yadda ya isa asibiti ba, Allah ne kaɗai ya kaishi lafiya domin hankalin sa tashe yake.

Kiranta ya sake fitowa tayi suka shiga tare

Da ya shiga ɗakin jinya, ya ga mahaifiyarsa kwance cikin ciwo.

Jikinta ya ji rauni sosai.

Likita ya nemi gani a ofis ɗin sa yaje bayan yabashi izini ya shiga suka gaisa ya faɗa masa Shine babban ɗanta, "dan Allah Dr meke damunta Yanzu,"?

Likita ya ce:

"An yi sa'a ta rayu, saidai taji raunuka gaskiya."

"Dan Allah Dr ka taimaka mun bana son rasata itace kawai tamun saura,"

Murmushi yayi"kada ka damu ai ta tsallake hatsari in sha Allah, yanzu kulawa sai shan magani akai akai akwai take buƙata, kuma mutum mai gaskiya da ɗaukaka kamar dai kai ai za'a taimaka wa alhalinka duk inda ka shiga Allah dai ya bata lafiya Mlm binash. *ƊAN JARIDA "THE JOURNALISM)*" cikin sigar zolaya ya ƙarasa maganar

Murmushi binash yayi tare da masa godiya ya koma inda umma take

Zaune ya gasu binash da Fatima suna sharan kwalla

Binash ya kama hannun mahaifiyarsa.

Hawaye suka zubo masa.

Amma a zuciyarsa ya fara zargin cewa...

Wannan ba hatsari ba ne.

An shirya shi ne domin tsoratar da shi.

Kuma ya rantse.

Ko da zai rasa komai...

Ba zai taɓa sayar da gaskiya ba.

Wayar sa ce tasoma ƙara barin ɗakin yayi kafin ya ɗaga

Ɗayan bangaren akace

"Ka gode Allah abun ya tsaya iya raunuka kawai baikai ga mutuwa ba Saboda haka kayi kuka kaɗan kafin kayi kuka mai yawa, na sha faɗa maka wanda ya san sirrin mu baya samun kwanciyar hankalin wanda ya so tono gaskiyar mu mutuwa ita ce mafi dacewa dashi, ka saurare saƙo nagaba *ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM)* Kai mai Gaskiya ko," ya fashe da dariya kafin ya kashe kiran.

Ɗago kansa da zaiyi yaga wani yana kallonsa daga waje suna haɗa ido mutumin ya tada mashing ɗin sa ya gudu,

Cikin nuna damuwa yazad yazo saidai binash yayi mamaki ganin Sadeeq baizo ba kuma bai kirashi ba shi koda ya kira shi kuma bata Zuwa,

A haka sukayi jinyar Umma harta warke babu Abinda Ya sake faruwa. Saidai a kwanakin yana tsoro da mamakin rashin samun Saddeeq gaba ɗaya, bayan sallamar umma ya nufe gidansu saidai bayanan wai yayi tafiyar gaggawa daga gurin aikin sa, yayi mamaki sosai ganin bai faɗa masa ba kuma ba'a samun sa..

A daren da mahaifiyar Aminu ta kwanta a asibiti, zuciyarsa ta cika da zafi fiye da ko yaushe. Bai taɓa jin rauni irin wannan ba. Kuma abin ya kasa fita daga zuciyar sa, har yanajin zai sare kawai domin bazai iya juran wani abu ya same ta ba,.

Zaune yake a gefen gadon mahaifiyarsa, yana riƙe da hannunta, Cikin alamun karaya yace:

"Umma, ki yi haƙuri nine silan duka komai na kasa ya fewa kaina, Umma Ba zan iya rayuwa babu ke ba."

Hawaye suka zubo mata ita kanta ta fara karaya da tsoron kadama shi tarasa shi domin bazata iya rashin sa ba, amma saita ɓoye raunin ta tareda ƙara masa Ƙwarin gwuiwa tace:

"Binash... ka riƙe gaskiya ko da me zai faru kada ka sauya kuma ina tareda kai..."

Wannan kalma ta sake shiga zuciyarsa kamar wuka, kuma ta ƙara masa Ƙwarin gwuiwa gamida jajircewa dajin lalle zai iya.

A waje kuwa…

Sadiq yana zaune a cikin mota tare da Alhaji Kabiru. Bayan sun tura masa ragowar kuɗin sa,

"An yi aikin da muka ce dai ko?" Alhaji Kabiru ya tambaya cikin sanyi.

Sadiq ya yi shiru na ɗan lokaci.

"Eh… amma..."

"Amma me?"

Sadiq ya haɗiye yawu.

"Mahaifiyarsa ta tsira."

Alhaji Kabiru ya yi murmushi mai cike da mugunta.

"Ba matsala, ai wannan sai ya ƙara masa zafi kuma zai ɗauka gargaɗi, kuma somin taɓi."

Sai ya juya masa ido.

"Mataki na gaba?"

Sadiq ya ce:

"Za mu sa a kai hari kansa da kansa."

Dariya Alhaji Kabiru yayi

Hahhha "lalle kai Sadeeq mugune ashe haka ka iya mugunta,"

Hah "alaji kuɗi ne fa, kuɗi masu gidan rana tare da kece raini, kaga Kuwa saboda kuɗi babu abinda bazan ai kataba, shi kanshi saboda taurin kai ya masa yawa ne shiyasa yaƙi, yo ai ko mahaukaci ba zai ƙi ba, kawai shima bashida rabo ne alaji,"

Hahaha"Kai kuwa gashi kanata dan gwalan arziki abin ka ba, kayi dumur-mur abinka, amma dai kaci gaba da ɓoyewa kada labari ku haɗu a yanzu kabari sai haƙanmu ya cimma ruwa,"

"Haba dai ai babu yadda za'ayi mu haɗu, duk da yazo har gida nemana amma na saka ance masa nayi tafiya kamar dai yadda na faɗa a gida cewar tafiyar gaggawa daga gurin aiki ta kamani,"

Hahhha"lalle kai mugune kasan salon mugunta,"

"Dukan mu dai alaji." Ya ƙarasa suna dariya

Washegari.

Binash ya dawo ofis da zuciya mai nauyi, da yawan tunani, q haka yazad yazo ya samesa duk Sallaman da ya kwaɗa sam bai jishi ba domin yayi nisa cikin tunani,

Zama yayi a ɗayan kujera yana faɗin:

"Abokina, me ya faru? Kana cikin damuwa sosai, na shigo baka sani ba nayi sallama har na zauna amma Shuru Kodai jikin Umma ne?."

Ɗagowa yayi tareda jan dogon numfashi, yana ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yace:

"bakomai umma taji Sauƙi."

Murmushi yazad yayi "yaushe nazama abin gudu da ɓoyewar Sirrin ka Binash, kana wani tunani kaina ko? Hmph da Sannu dai za'ayi Walƙiya ai nahin masoyan ka zasu Bayyana, zaga tantance wanda ya fidda maitarsa a fili da kuma wanda ya ɓoye yake ai kata zagon ƙasa, in sha Allah watarana zan yi maka amfani kuma zakayi alfahari dani Kuma ina son kasani cewar, Ba kai kaɗai ba ne, nima Yazad Ina tare da kai."

Cikin mamaki ya kallesa

Gyaɗa masa kai yayi tare da ficewa,

A karon farko ya ji cewa yana da wanda zai jingina da shi, domin yazad yafi kowa kusanci dashi da Sanin lagonsa, saidai yana jin tsoron kada su zo su saye imaninsa.

Sai dai a wancan lokacin…

Wani labari mai ban tsoro ya fara fitowa a jaridu.

“DAN JARIDA BINASH BN ZAIN YA KARƁI KUƊIN CIN HANCIN NAIRA MILLION 1,600 ƊARI DA SITTIN”

Tare da saka Hoton sa akan JARIDA dama Social media.................

PLEASE KUYI COMMENTS MAI ƊAUKE DA SHARHI TAREDA SHARING LITTAFIN TAREDA LIKE DA REACTING.

_BASEERATA ITA CE ARZIKINA 😍_

WHATSAPP NUMBER 07064904617 OR 07031012948

ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 🔥 07064904617.

*ƊAN JARIDA*
_(THE JOURNALISM🧑🏻‍💻)_
*FREE BOOK*

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥)
Chapter 5 · 0% Book details