← Book details Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 14

Sashe 1

Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ƊAN JARIDA*
_(THE JOURNALISM🧑🏻‍💻)_
*FREE BOOK*

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥)

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA..(32) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (33) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (34) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (35) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is (36). TANGARAS.... FAD'I KAFASHE PAID BOOK (37). BARRISTER NAZEEYAH PAID BOOK (38).. (39) CAPTAIN AMEESH FREE BOOK....(40) DAREN HANA BACCI ☠️ 💀 ☠️ (41) BARRISTER ARMAN! (42) TARKON SO!
(43) RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA!!! INA NAN DAWOWA (44) (45) ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM🧑🏻‍💻) Free book.
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM)*

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM TAKUCE🥰🥰*

................................✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

........................

*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM)*

```Gamasu buk'atar A tallata musu hajjarsu k'ofa bud'e take zaku iya Aiko tallanku A rubuce nasaka muku cikin shafin littafaina Akan farashi Mai sauk'i, .. Inakuke Y'an kasuwa Kuma kuzo Inayin logo graphics ko wanne iri had'ida cartons Art's design kudai kugarzayo domin mallakar naku cikin sauk'i...... Domin magana dani A WhatsApp 07064904617 OR 07031012948 ✍️ Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 Queen 👸 of Writer's Hausa novels 📚📖📚 And design graphics```

```Ina kuke ma'abota ƙamshi Mata da Maza nesa tazo kusadaku BINTOUR ALIEY PERFORM Duniyar ƙamshi Cikin rahusa da Rangwame muna maraba da masu dasayen ɗaya koma Y'an sari muna turaruka kamar:~
sandal flasks, sandal wood, sandal bangi, Senegalese kajiji, kabbasa, humra fara, da brown,musk, turaren gogawa Kala Kala, turaren tsinke, dadai sauransu.... Zaku iya Nemanmu A 07048605381, Or 07040154174 Whatsapp ko kira,... BINTOUR ALIEY PERFORM, DUNIYAR ƘAMSHI DA KECE RAINANI...... MUNA MARABA DA ZUWANKUUUU....

Haka kuma munada kayan gyaran jiki kala kala, magungunan mata ma zaku samu garemu masu kyau da Inganci 💯, banan muka tsaya ba domin Kuwa muna da Alaƙa da GHT COMPANY magani kan ko wacce cuta H.I.V, SIKLER, HAWAN JINI, CIWON BAYA, MATSALAN IDA NUWA, da sauransu.... Kayan kitchen kayan sakawama duka zaku samu garemu, kudai kawai ku hanzarto neman mu kan ko wacce matsala zamu tsaya domin baku maganin ta in sha Allah.... Zaku iya tuntuɓarmu a 07064904617,.. mungode!........```

_JULLY 2026_

```JIGON LABARIN
Labarin wani matashi mai suna BINASH wanda ya taso cikin talauci amma yana da burin zama babban ɗan jarida. A cikin aikinsa, ya fuskanci cin hanci, barazana daga masu iko, yaɗa ƙarya a kafafen sadarwa, da ƙalubalen neman gaskiya. Duk da haka, ya tsaya kan gaskiya har ya zama sanannen ɗan jarida wanda ya taimaka wajen ceto rayukan mutane da kawo gyara a al'umma. BINASH Kenan ƊAN JARIDA
(THE JOURNALISM)......```

_2/7/2026 THURSDAY JUNE 2026_

*PAGE 1 TO 5*

.......Ruwan sama ne yake sauka a hankali yayin da Aminu yake zaune a bakin taga yana kallon yadda mutane ke ta kai-komo a kan titin da ya cika da laka. Zuciyarsa cike take da burikan da suka fi ƙarfin shekarunsa.

Binash maraya ne. Ya rasa mahaifinsa tun yana ɗan shekara goma sha biyu. Tun daga lokacin rayuwa ta sauya masa. Mahaifiyarsa, Hajiya Safiya, ita ce ta ɗauki nauyin rainonsa da ƙanwarsa Hairana.

Duk da talauci, Aminu bai daina mafarkin zama babban ɗan jarida ba.

Zaune suke kamar kullum da yamma suna ɗan taɓa hira tsakaninsu,

CIkin sanyin sa yace "Umma wata rana zan zama wanda zai kare gaskiya kuma ya taimaki marasa ƙarfi,"

Kallonsa umma tayi tareda murmushi ta shafa kansa tace

"Allah Ya taimake ka ɗana. Ka tuna, gaskiya tana da tsada, amma sakamakonta ya fi zinariya." Ko kaɗan umma bata kawo komai a ranta ba na burin binash,

Kalaman Umma kuwa sun samu mazauni a ransa, Kullum ƙarin azama da son cikar burin sa yake.

Haka suke rayuwa dukansu daɗi da Babu da daɗi, ba umma kawai ba shi kanshi kullum fafutukar gyara rayuwar su yake, da ƙananan shekarun sa amma kuma wahala kala kala yakan iya jure kuma yana dako kala kala domin rufawa kansa a siri, dangin mahaifinsa kuwa da jimawa suka watsar dasu gadon ma handamewa sukayi iya gidan ne kawai suka samu suka tsira dashi..

BAYAN WASU
Shekaru sun shuɗe.

Binash ya kammala karatu cikin ƙwazo. Daga ƙarshe ya samu aiki a wata babbar kafar yaɗa labarai mai suna Haske Media.

A ranar farko da ya shiga ofis, ya haɗu da wata kyakkyawar budurwa mai suna Banasha,

Banasha tana da fara'a, ilimi da nutsuwa.

Cikin ƙarfin hali yace

"Assalamu alaiki."

Cikin murmushi ta amsa da

"Wa alaikasalam."

Murmushin da ta yi ya sa zuciyar binash ta buga da sauri.

Saurin ɗauke idansa yayi domin yanayin bugawar zuciyar nasa, cikin dauriya ya zauna inda nan ne ma zaunin sa, cikin dakewa yace "Sunana Binash Bn Zain, kuma nine sabon ma'aikacin da zai fara aiki anan"

Ƙara yalwantar da murmushin ta tayi Cikin fara'an da ya zame mata jiki tace "Masha Allah ina tayaka murna Allah yasa ka fara kan Sa'a, ni sunana Banisha Sa'id najima ina aiki anan a ƙalla zan kai shekara uku koma fiye da hakan,"

"Ah Masha kice zan ɗauke darasi dai a gurin ki"

Dariya tayi"a'a ko alama bayan kaine shugaba sama dani kaine fa Babba akaina so kaga nice mai koyo, fatan zamu samu ƙarin experience"

Shima murmushin sa mai kyau yayi"to ai zama babba bashine aiki ba kuma kinga dole akwai abubuwa da yawa da kika sani wanda ni bansansu ba, kuma in sha Allah zamuyi aiki cikin amana da gaskiya"

Shigowar shugaban gurin yayi, hakan ya katse musu fira

Meeting ya haɗa ya kira duka ma'aikatan gurin ya gabatar da binash da abokinsa yazad tun na yarinta komai tare suke kamar wasu ƴan biyu saboda shaƙuwar su da amincin su, siyasa ko yanzu suka fara aiki tare, wanda mahaifin Alaji Rabi'u shine yayi musu ƙafa a gwamnati suka samu, domin yana da sanayya da ƴan siyasa. Kuma Alhamdulillah takardunsu sunyi Kyau musamman Binash hakan yasa aka ɗaukesu take kuma ya zama shine babba sama dasu duka saboda kyawun takardunsa da level ɗinsa, bayan gabatar dasu da kuma faɗa musu tsarin aikin kafin kuma Kowa ya koma ɓangaren sa, domin Kowa da inda yafi ƙwarewa.

Tun daga wannan rana suka fara aiki tare, saidai a cikin kwanaki ƙalilan sun fahimce binash mutum ne mai ƙwazo da ƙoƙari gamida jajircewa ga gaskiya duk abinda bashida alaƙa da halak ɗinsa binash baya cinsa, duk labarin da bai yarda dashi ba ko ingancin sa ba za'ayi shi dashi ba kuma zaiyi ƙoƙarin hanawa, Cikin lokaci kaɗan ya soma samun ɗaukaka mutane dayawa suka fara ƙaunar sa musanman talakawa, halinsa ya ƙara janyo Banasha cikin kogin soyayya sa, kuma ta koyi halinsa na gaskiya.

Ba da jimawa ba soyayya ta fara shiga tsakaninsu mai ƙarfi, kala ma aikata gurin basu fahimta ba har suka sani, soyayya mai yau da tsafta suk, suna cikin farin ciki da nishaɗi..........

HUNMMMMMM SAIDAI KUMA BA'A NAN GIZO YAKE SAƘAR BA .
Chapter 1 · 0% Book details