← Book details Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA..(32) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (33) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (34) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (35) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is (36). TANGARAS.... FAD'I KAFASHE PAID BOOK (37). BARRISTER NAZEEYAH PAID BOOK (38).. (39) CAPTAIN AMEESH FREE BOOK....(40) DAREN HANA BACCI ☠️ 💀 ☠️ (41) BARRISTER ARMAN! (42) TARKON SO!
(43) RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA!!! INA NAN DAWOWA (44) (45) ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM🧑🏻‍💻) Free book.
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM)*

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM TAKUCE🥰🥰*

................................✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

........................

*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM)*

```Gamasu buk'atar A tallata musu hajjarsu k'ofa bud'e take zaku iya Aiko tallanku A rubuce nasaka muku cikin shafin littafaina Akan farashi Mai sauk'i, .. Inakuke Y'an kasuwa Kuma kuzo Inayin logo graphics ko wanne iri had'ida cartons Art's design kudai kugarzayo domin mallakar naku cikin sauk'i...... Domin magana dani A WhatsApp 07064904617 OR 07031012948 ✍️ Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 Queen 👸 of Writer's Hausa novels 📚📖📚 And design graphics```

```Ina kuke ma'abota ƙamshi Mata da Maza nesa tazo kusadaku BINTOUR ALIEY PERFORM Duniyar ƙamshi Cikin rahusa da Rangwame muna maraba da masu dasayen ɗaya koma Y'an sari muna turaruka kamar:~
sandal flasks, sandal wood, sandal bangi, Senegalese kajiji, kabbasa, humra fara, da brown,musk, turaren gogawa Kala Kala, turaren tsinke, dadai sauransu.... Zaku iya Nemanmu A 07048605381, Or 07040154174 Whatsapp ko kira,... BINTOUR ALIEY PERFORM, DUNIYAR ƘAMSHI DA KECE RAINANI...... MUNA MARABA DA ZUWANKUUUU....

Haka kuma munada kayan gyaran jiki kala kala, magungunan mata ma zaku samu garemu masu kyau da Inganci 💯, banan muka tsaya ba domin Kuwa muna da Alaƙa da GHT COMPANY magani kan ko wacce cuta H.I.V, SIKLER, HAWAN JINI, CIWON BAYA, MATSALAN IDA NUWA, da sauransu.... Kayan kitchen kayan sakawama duka zaku samu garemu, kudai kawai ku hanzarto neman mu kan ko wacce matsala zamu tsaya domin baku maganin ta in sha Allah.... Zaku iya tuntuɓarmu a 07064904617,.. mungode!........```

_JULLY 2026_

```JIGON LABARIN
Labarin wani matashi mai suna BINASH wanda ya taso cikin talauci amma yana da burin zama babban ɗan jarida. A cikin aikinsa, ya fuskanci cin hanci, barazana daga masu iko, yaɗa ƙarya a kafafen sadarwa, da ƙalubalen neman gaskiya. Duk da haka, ya tsaya kan gaskiya har ya zama sanannen ɗan jarida wanda ya taimaka wajen ceto rayukan mutane da kawo gyara a al'umma. BINASH Kenan ƊAN JARIDA
(THE JOURNALISM)......```

*PAGE 61 TO 70*

Mama Kuwa sai washe gari da safe suka dawo tareda kawu Bala ƙanenta, sun yi mamaki sosai ganin Banasha bata gidan kuma Ƙofar a karye, amma kuma suna kan saurin halartar zaman kotu yasa basu kawo komai ba suma daga nan suka ɗunguma zuwa kotu, mutane da sauran ƴan jarida sai zanga zanga suke kusa da kotun an hana su shiga sai faɗin suke: "MUNA BUƘATAR ADALCI AYIWA BINASH ADALCI! MU A DALCI MUKE SO A SAKE MUBA BINASH," kalmomin da suke ta maimaitawa kenan domin i zuwa yanzu gaskiya ta gama bayyana kansu Alhaji Abubakar da Gwamnan magu harda kisan da suka ma mahaifin sa,

Tuni aka kamo Alhaji Kabiru inda gwamna labaran magu ke ƙoƙarin tserewa shima aka kama shi Sadeeq ne kawai aka rasa ba'a Ganshi ba,

Bayan sauraren duka ɓangaren biyu nan kotu tagano gaskiya, aka yanke shari'ar, Gwamna Labaran magu shike da aiki inda Alhaji Kabiru shike da ɗaukar aikin kota yanke musu hukunci ɗaurin rai da rai da aiki mai tsanani, kuma aka baza ƴansanda kan su nemo Sadeeq duk inda yake akawoshi gaban kotu, shi kuma aka wanke shi daga zargi.

Sosai su umma suke Cikin farin cikin, mu tane waje sai murna da ihu suke, kyauta kuwa da tayin gurin aiki ya shasu, take ya samu ɗaukaka fiye da dada sunan sa ya zama ko ina shine abin faɗa da koya,.

Yayi mamaki sosai ganin basa tareda da banasha yana son tambaya amma kuma yana jin kunya, bayan zuwan su gida yaga bata nan, anan ne ya kasa haƙura ya tambaya amma basu san inda take ba, neman ta yashiga amma ba labari gurin aikinta yaje can ya tarar suma neman nata suke, nan mlm Bashir yake faɗa masa irin bala'in da tajefa kanta Saboda ganin ya fito gashi yanzu shi ya fito ita ko ta faɗa halaka, neman yazad ya fara nan yaji shima ya ɓata ai nan ya fahimce lalle suna tare, tashin hankali ya koma faɗawa tareda sake faɗawa cikin Neman su, Tareda sanarwar ƴansanda halinda ake ciki..........

A ɓangaren su, Banasha da yazad suna gudu cikin duhun titi, iska tana dukan fuskokinsu. Sautin takun mutane daga bayan su yana ƙara kusanto su.

Banasha ta tsaya na ɗan lokaci tana haki.

“Ba zan iya ƙara gudu ba… Yanzu kam wallahi yazad nagaji sosai ga yunwa da ƙishirwa” ta ce cikin rauni tana neman zama inda take.

Yazad ya kama hannunta da ƙarfi.

“Idan muka tsaya yanzu, wallahi zasu gama da mu. Ki zo!”

Suka ci gaba da gudu har suka shiga wani tsohon rukunin gine-gine da suka ruguje.

Suka ɓuya a ciki.

Cikin duhun wurin, Banasha ta kalli yazad da idanu masu cike da hawaye.

“Ka gaya min gaskiya yanzu,” ta ce a hankali. “Waye ai nahin mai binmu?”

Shiru ya ratsa tsakaninsu kafin ya zauna a ƙasa, ya sauke numfashi mai nauyi yace:

“Sunan mutumin da ke bibiyan mu kan komai… ba Danladi ba ne,”

Banasha a ta matsa kusa dashi tace:

“Waye?”

Ya ɗago kai a hankali.

“Shugaban asalin wannan tsarin… shi ne wanda kowa ke jin tsoro… Alhaji Sani Kura.”

Zuciyar Banasha ta buga da ƙarfi, cikin rawar baki tace:

“amma Ban taɓa jin sunansa ba…”

Yazad ya girgiza kai yace:

“Domin yana ɓoye ne a bayan mutane kamar Danladi. Shi ne yake sarrafa komai.”

Banasha ta miƙe da sauri.

“Don haka duk wannan wahala… saboda shi muke yi?”
Yazad ya kalleta da idanu masu nauyi.

“Eh. Kuma yanzu ya san mu, Ya san duk abin da muke yi.”

Ba a gama maganar ba, sai wayar yazad ta fara ringing.

Ya kalli screen ɗin wayar.

Unknown Number

Banasha ta ja baya cikin tsoro tace:

“Kada ka ɗaga…”

Amma Yazad ya ɗaga tareda saka handsfree.

“Na ji kuna magana a kaina.”

Shiru ya ratsa su.

Banasha ta riƙe numfashi.

Muryar ta ci gaba da cewa:

“Yazad … ka manta da yarjejeniya?”

Fuskar Yazad ta fara canzawa.

Banasha ta kalle sa cikin tsananin mamaki, fargaba da tsoro, cikin rawar baki tace:

“Wace yarjejeniya?”

Yazad ya kasa amsa mata tareda ɗauke kansa daga kallonta

Muryar ta sake cewa:

“Ka kawo ta nan… idan har kana son sake cigaba da rayuwa a duniya.”

Wayar ta yanke.

Shiru mai nauyi ya biyo baya.

Banasha ta kalli yazad.

“Me suke nufi?”

Yazad ya soke kai ƙasa

“banasha … akwai abin da ban faɗa miki ba…”

Ta matsa kusa da shi da ƙarfi tace:

“Ka faɗa min yanzu!”

Ya kalleta da idanu cike da nauyi.
Chapter 11 · 0% Book details