Sashe 14
Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
"Okay you will see, waiting for me,"
Kitchen ya nufa ganin yadawo da wuƙa a hannu tasaki ihu tana runtuma wa a guje da aka ta sai ƙaramin trouser da Best.
Jennifer kenan sabuwar budurwar Saddeeq da tunda lamarin ya fara tsamari da kama su Alhaji kabiru ya gudu Zuwa nan Garin Lagos, domin ɓoye kansa nan ya cigaba da sharholiyar sa, kasan cewar Lagos garin kowa hakan yasa bai samu matsalan komai ba kuma gashi da kuɗi, tun a can garin ya jefar da tsohuwar wayar sa da layukan duka ya haƙura da Kowa da komai.
Yanzu ganin bayyanar binash da kuma yazad ya san cewar dole zasu neme sa Bama kamar Binash akwai nacin tsiya, tsawon lokaci ya ɗauka Binash yana can prison a she yayi free ya sani dole yanzu zasu maida hankali kanshi tunda yayi free gakuma goyon bayan jami'an tsaro da al'umma, ya zama dole ya ƙara nausawa gaba domin hankalin sa kuwa ya kasa kwanciya.
Ɗaukar duk wani abu mai mahimmanci nasa yayi da sauran kuɗin sa ya zuba a jaka, dama gidan haya ya kama shi kaɗai, kai tsaye ya gudu tasha ya koma ya tare mota wadda zata ƙara nausawa kudu........
A can gida Nigeria Kuwa case ɗin aka sake buɗewa domin Alhaji Kabiru ya bayyana Sadeeq shine wanda ya kashe mlm sani mahaifin Binash, hakan yasa aka raba photonan sa ko ina har gidan TV ana neman sa, tareda kuɗi masu nauyi ga wanda duk ya kamoshi ko labarin inda yake.
Bayan fitar Jennifer cikin mamaki ta wuce gidansu anan taga photon Sadeeq da kuma kuɗin da aka saka ga wanda ya bada labarin inda za'a sameshi,
"Kenan Saboda haka yasa ya koreni, He na wow ai wallahi kuɗin zanci."
Ɗaukar number tayi takira ta bada information ɗin,
Cikin ƙanƙanen Lokaci aka bugawa ƴansandan can da taimakon Jennifer suka isa gidan saidai wayam bayan an dai samu wasu daga cikin kayan sa hasashen bindiga guda ɗaya wanda ga alama baisan ya faɗi ba,
Sauran jama'an kan haya aka kira a ka soma binciken ko ina .
Suna cikin tafiya saiga ƴansandan hanya Saida gaban sa ya buga,
"Kaga driver tsaya zan sauka anan."
"Zaka sauka nan bayan kace zaka shiga ondo."
"Ina ruwan ka wai nace na zan sauka anan Kanada matsala ne."
Ya faɗa cikin tsawa da hushi
"A'a Kodai bakada gaskiya ne bawan Allah".
Wani ya faɗa Cikin mamaki
Motar bata tsaya ba Cikin fushi ya ɗaura bindiga kan driver
"Wallahi idan baka tsaya ba saina fasa kanka yanzu."
Ihu suka ɗauka suka shiga tsoro abunka da bayarbe cikin rawar jiki ya tsaida motar
Fitowa yayi cikin sauri yana riƙe da jakarsa ya nausa cikin dajin da gudu
Driver yana isa gurin ƴansanda ya faɗa ai Kuwa suka bi Bayansa
Sunyi gudu sosai tareda musayar halbi inda ya kashe ƴansanda biyun ganin baida niyar tsayi cikin samun Sa'a wani ya halbe sa, take ya faɗi rai yayi halinsa,
Gawarsa kawai suka ɗauka suka fito da ita, aka wuce da ita can Nigeria.
Iyayen sa sunyi kuka sosai da nadamar kasan cewar sa ɗansu gashi yaja musu abin magana da gori dole suka bar garin suka koma inda ba'a sansu ba suka cigaba da rayuwa..
BAYAN SHEKARA BIYU
acikin Shekara biyu abubuwa da yawa sun faru, masu daɗi da akasin hakan,
Binash ya buɗe makeken gidan jarida wanda su biyu ne suka haɗa guiwa shida yazad,
Haka kuma Banasha ta haihu kuma tanada wani cikin
Anyi bikin yazad da Hauwa yanzu haka tana da ciki
Inda Fatima ƙanwar sa ta aure wani Abokin yazad itama tanada ciki,
Sun sauyawa mama gida cikin farinciki suke rayuwa da kwanciyar hankali,
Sun samu labarin mutuwar sadeeq, Allah ya kyauta kawai Binash yace domin bazai iya yafiya ga wanda ya maida shi Maraya kan Abin duniya ba,
Kuma yanzu ya gane mutane ba Abin yadda bane, mafi kusa dakai ma sune suke cin amanar ka, ya koyi darasi sosai ga rayuwar Mutane.
Dukansu sunzo gidan Binash suna babban palourn suna cin abinci,
Banasha ta aje musu ruwa cikin murmushi da sigar zolaya tace:
"ƳANN'JARIDA (THE JOURNALISM'S) na samo sabon labari Saidai akwai mutuwa aciki."
Dukan su suka kwashe da dariya lokaci ɗaya..........
TAMMAT BIHAMDULLAH.
Anan nakawo ƙarshen wannan littafin nawa ina fatan Allah yasa mu Amfana dashi dukanmu.........
DARUSSAN DA YAKE ƊAUKE A CIKIN LABARIN.........
MUHIMMANCIN GASKIYA.
ILLAR YAƊA LABARAN ƘARYA.
HAƘURI DA JAJIRCEWA GURIN NEMAN NASARA.
RIƘE AMANA GASKIYA CIKIN KO WANNE IRIN AIKI KO SHIGA WANI HALI.
TASIRIN YAƊA LABARAI GURIN GYARAN ALUMMA.
GASKIYA TANA DA ƘARFI, AMMA ZAƁIN MUTUM NE KE ƘAYYADE KO DUNIYA ZA TA RAYU DA ITA KO BA TARE DA ITA BA..........
_BASEERATA ITA CE ARZIKINA 😍_
WHATSAPP NUMBER 07064904617 OR 07031012948
ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 🔥 07064904617.