← Book details Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yasha ganin wasu motocin da bai sani ba sukan tsaya kusa da gidansu, Wani lokaci kuma sai ya ga wasu mutane suna kallonsa cikin wani irin yanayi mai ban tsoro.

Duk da haka, ya ci gaba da aikinsa, ya watsar dasu.

Banasha ce kaɗai take ba shi kwarin gwiwa, sai mahaifiyar sa wadda Kullum take masa addu'ar kariya, yazad Kuwa cike yake da tsoro har yasoma nisantar wasu lamurran Binash saboda yaƙi ɗaukar shawaransa kan ya daina,

Banasha tunda tagano suna da saka hannu gurin mai dashi maraya tadaina tsoro taci gaba da bashi Ƙwarin guiwa tana yawan faɗa masa

"Kar ka ji tsoro, dear Gaskiya ba ta mutuwa."

Binash ya yi murmushi.

"Na gode lover. Da ba ke ba, da watakila na karaya."

Banasha ta sunkuyar da kai cikin kunya da tarin soyayyar sa.

Tun a lokacin soyayyarsu ta fara zurfafawa, kuma lokacin auren su yayi aka ɗaura, mutane dayawa suka halarta domin binash ya samu ɗaukaka sosai da kuma tarihin kuɗi daga Wasu manyan ƙasa kuma maganar ɗan takaran Gwamna Labaran magu tana kotu sun fara zama yanzu haka,

A gefe guda kuwa...

Mutanen da Aminu ya tona wa asiri suna zaune a wani katafaren gida.

Alhaji Kabiru ne shugaban taron.

Fuskarsa cike take da fushi, yace:

"Wannan yaron ya raina mu ya rasa dawa zaiyi sai mai neman takaran gwamna labaran magu Excellency guda!"

Ya bugi tebur da ƙarfi.

"Wajibi ne a dakatar da shi."

Daya daga cikin mutanen ya ce:

"Za mu iya ba shi kuɗi."

Alhaji Kabiru ya girgiza kai.

"Mutumin da yake son gaskiya ba ya sayuwa da kuɗi."

Sai wani ya ce:

"To me za mu yi?"

Alhaji Kabiru ya yi murmushin mugunta.

"Akwai hanyar da ta fi sauƙi..."

"Amma dai bazan rasa samun kujerar ta ba ko,"?

"Kada damu Excellency komai da zamuyi saboda cigabanka zamuyi,'

"Ina tare daku kuma na shirya kashe ko nawane domin cikar burina"

Dariyan mugunta sukayi dukansu.

A washegari.

Binash ya samu baƙo a ofis.

Mutumin ya ajiye wata jaka a gabansa.

"Menene wannan?" Binash ya tambaya

"Kuɗi ne miliyan hamsin ne, wanda inada tabbacin gaba ɗayan rayuwarku har dangin ka Babu wanda ya taɓa koda ganin kuɗin balle mallakarsu, amma Kuma yau gasu gabanka kuma matsayin mallakin ka."

Cikin mamaki binash yace:

"Meyasa?"

"Ka daina binciken da kake yi, kuma kaje a media ka ƙaryata kanka sannan ka janye zaman koto."

Binash ya tashi tsaye Cikin fushi yace:

"Ka ɗauki kuɗin ka ka fita."

Mutumin ya yi dariya, tareda cewa:

"Ka yi tunani sosai, ɗan Samari Domin Wannan babbar dama ce kasamu kai koda basu ishe ka bane zan iya ƙara maka Zuwa Millon 100"

Cikin ƙara fusata binash ya dake tebur yana faɗin"get out a said "ya nuna masa ƙofa.

"Kada ka zama daga Cikin marasa rabo mlm *ƊAN JARIDA....(THE JOURNALISM)*"

Cikin tsawa binash ya sake maimaita masa

"Na ce ka fita."

Hunmph"zakayi dana sani ɗan Samari domin ba'a wasa da wuta" ya tattara jakar ya miƙe, har ya kusa fita kuma saiya waigo yace:

"Mutane da yawa sun mutu saboda ƙin irin wannan Babban tayin." Kafin yasa kai yafice a hanyar fita suka haɗu da yazad sukayi kallon kallo kafin ya wuce , shimuma ya shigo ofis ɗin

Zaune ya taran dashi ya ɗaura hannu akansa ya faɗa kogin tunani,

"Ai wallahi shiga damuwa baka fara ba binash saboda kaine kaje fa kanka cikin Wannan hatsarin, waima Meye wannan mutumin yazo yi inda kake naganesa da jaka kardai hasashena ya zama gaskiya ace kuɗi ne cike da wannan jakar amma kayi reject,"

Cikin takaici ya ɗago "jeka kabishi tun baiyi nisa ba saika karɓe kuɗin kai," mtswwwwww yaja dogon tsaki yabar shi gurin zaune.

A daren ranar.

Binash ya zauna tare da babban abokinsa Sadiq wadda aiki ya haɗa su har gidansu sadeeq ya sani kuma ya yadda dashi domin bai taɓa ganin maitarsa kan kuɗi ba amma ya ganta a tareda tsohon amininsa Yazad.

Tun suna yara suke tare, saidai amincin su da yazad yafi girma amma inda Sadeeq yake aiki daban ne, ya yarda dashi sosai baya ɓoye masa komai,

Binash yana ɗaukar Sadiq kamar ɗan uwansa.

Bayan sun yi hira, Sadiq ya ce:

"Binash, kana shiga haɗari sosai."

"Na sani."

" To Me zai hana ka daina?"

Binash ya girgiza kai.

"Ba zan iya ba. Saboda ina son gaskiya ta bayyana, zan baka wannan plash ɗin ta addancinsu Alhaji kabiru da magu yana ciki inason abin ya zama safe gareka domin kai basu san kaba kuma bazasu taɓa tunanin na baka ba, inason koda sun hallakani dan Allah ka kaishi kotu gaskiya ta bayanan, nasani kaine kaɗai zaka iya mun wannan aikin dan Allah kada kace a'a,"

Sadiq ya yi shiru, yana tunani Kafin ya nisa Hunmph"duk da akwai hatsari Amma zanyi hakan saboda kai abokina,"

Karɓar plash ɗin yayi sukayi sallama ya koma gida,.

Amma abin da binash bai sani ba shi ne...

A daren nan bayan ya rabu da shi, Sadiq ya shiga mota ya tafi kai tsaye gidan Alhaji Kabiru.

Alhaji Kabiru ya karɓe shi da murmushi.

"Ka kawo mana abin da muke so?"

Sadiq ya miƙa masa wannan plash ɗin yace:

"A ciki akwai duk bayanan sirrin binash da yake son kai ku ƙasa dashi, wannan kuma duk wani sirrin sa daya shafe rayuwar sa na duniya a jikin wannan takardar, kama daga,

Adireshinsa.

Lambar wayarsa.

Duk inda yake zuwa.

"Komai na tsara maka amma fa kasani zaka cika mun Alƙawarina nabani dukan kudaɗen kamun alƙawarina,"

Alhaji Kabiru ya yi dariya tareda cewa:

"Madalla, kada kadamu Excellency zai cika maka alƙawarin ka kabani accts number zakaji alerts kafin nan ga wannan saƙon ƙamar kyauta ce daga gareni kajira ta Excellency"

Ya miƙa wa Sadiq kuɗi masu yawa. A jaka

Sadiq ya karɓa, cikin farin ciki da dariya suka rabu

A wannan dare...

Abokinsa na ƙut da ƙut ya ci amanarsa, wanda ya yadda dashi....................

PLEASE COMMENT MAI ƊAUKE DA SHARHI TAREDA SHARING LITTAFIN DA LIKE REACTING DAN ALLAH.

_BASEERATA ITA CE ARZIKINA 😍_

WHATSAPP NUMBER 07064904617 OR 07031012948

ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 🔥 07064904617.

*ƊAN JARIDA*
_(THE JOURNALISM🧑🏻‍💻)_
*FREE BOOK*

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥)

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA..(32) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (33) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (34) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (35) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is (36). TANGARAS.... FAD'I KAFASHE PAID BOOK (37). BARRISTER NAZEEYAH PAID BOOK (38).. (39) CAPTAIN AMEESH FREE BOOK....(40) DAREN HANA BACCI ☠️ 💀 ☠️ (41) BARRISTER ARMAN! (42) TARKON SO!
(43) RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA!!! INA NAN DAWOWA (44) (45) ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM🧑🏻‍💻) Free book.
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM)*

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM TAKUCE🥰🥰*

................................✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

........................

*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM)*
Chapter 4 · 0% Book details