← Book details Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ni ba kawai wanda ya tsere daga su bane… ni na anshe aikin sa na kai tsaye daga Alhaji Sani Kura.”

Banasha ta ja baya kamar an ture ta cikin rawar baki tace:

“Don haka duk abin da muka yi… ka shirya mini tarko ne?”

Yazad ya girgiza kai da sauri.

“A’a! Na fara ne tare da su… amma na canza. Na yi ƙoƙarin fansa!”

Banasha ta fara hawaye.

“Ban san wanda zan yarda da shi ba kuma…”

A waje, motoci suka tsaya kusa da ginin.

Haske ya cika rufin da suka ɓuya a ciki.

Muryar da suka ji ta waya ta sake fitowa daga loudspeaker:

“banasha… fito. Ba mu son cutar da ke. Muna son bayanin kawai.”

Yazad ya tashi da sauri yace;

“Sun kewaye mu gaba ɗaya.”

Banasha ta riƙe flash drive ɗin ta miƙe a hankali.

“Idan na fita… zan mutu, idan na tsaya ma mutuwa zanyi”

Yazad ya kalleta.

“Idan ba ki fita ba… duk duniya ba za ta taɓa sanin gaskiya ba.”

Shiru ya ratsa su.

Banasha ta kalli hanyar fita.

Sannan ta kalli yazad

“Wannan labari… dole ya fito.”

Banasha ta fito daga ɓoyayyen ginin a hankali, zuciyarta na bugawa kamar za ta fito waje. Hasken motoci ya dinga dukan idanuwanta.

Yazad ya biyo bayanta a baya, amma fuskar sa cike da tashin hankali.

"Banasha… ki yi hankali,”

Amma ta riga ta yanke shawaran fuskantar su.

Motoci baƙaƙe suka kewaye su gaba ɗaya. Mutane masu sanye da bakaken kaya suka fito, ba tare da magana ba.

Daga cikin wata mota mai tsada, wani dattijo ya sauko a hankali.

Fuskarsa ta nuna iko da tsoro a lokaci guda.

Alhaji Sani Kura.

Banasha ta tsaya cak.

“Ke ce Banasha” ya ce cikin nutsuwa.

Ta amsa da ƙarfi:

“Eh. Ni ce.”

Ya yi murmushi mai sanyi.

“Kin yi nisa fiye da yadda ya kamata.”

Yazad ya matsa gaba kaɗan.

“Alhaji… wannan bata san komai game da kai bane.”

Alhaji Sani Kura ya kalle shi da idanu masu sanyi.

"Yazad … ka yi ƙoƙari ka zama jarumi, amma ka manta inda ka fito, da abokin ka ke Kuwa mijinki”

ta kalli Yazad cikin mamaki.

“Ka san shi sosai…”

Yazad ya sauke kai.

“Na faɗa miki… na taɓa aiki da su.”

Alhaji Sani Kura ya ɗaga hannu.

“Ku kawo min flash drive ɗin.”

Mutane suka fara matsowa.

Banasha ta ja baya.

“Idan na baka wannan… mutane da yawa za su mutu a sanadin sa!”

Ya kalleta cikin sanyi yace:

“Idan ba ki bayar ba… ke za ki fara mutuwa.”

A daidai lokacin, Yazad ya yi wani abu da ya ba kowa mamaki.

Ya tsaya a gaban banasha

“Ku ja baya!” ya faɗa cikin ɗaga Murya

Banasha ta kalle shi cikin firgici.

“Yazad me kake yi?!”

Ya juya ya kalleta.

“Na riga na bata komai sau ɗaya… ba zan bari a maimaita hakan ba.” ya faɗa mata fuskar sa na fidda na dama

Sai ya ciro flash drive ɗin da yake ɓoye.

Ya ɗaga shi sama.

“Wannan shi ne ƙarshen ku!”

Alhaji Sani Kura ya yi murmushi.

“Ka kuskura ka yi hakan?”

Yazad ya kalle shi kai tsaye.

“Na gama tsoro. Kusani kuma bazau shaba.”

Ya jefa flash drive ɗin cikin kangon gidan da ƙarfi…

Amma kafin ya fadi ƙasa

Wani daga cikin mutanen ya harbe shi, a ƙafa

Banasha ta kurma ihu cikin tsananin tsoro da tashin hankali tace:

“YAZADDDD!!!”

Ya fadi ƙasa a hankali.

Idanunsa suna kallonta.

“Ki gudu… Banasha…”

Hankalin ta ya tashi gaba ɗaya ta rikice

Alhaji Sani Kura ya yi magana cikin fushi

“Ku kama ta.”

Amma banasha ta tsaya a tsakiyar su, hawaye na zuba.

Ta ɗaga flash drive ɗin da yazad ya bari a hannunta ya tsira.

“Ba zan gudu ba, bazan iya barinka ka ba…”

Ta kalli Alhaji Sani Kura tace da ƙarfi.

“Wannan labari… zai fito ko da na mutu!”.................

Banasha ta tsaya a tsakiyar duhun fili, hawaye na zuba amma zuciyarta ta cika da ƙarfin gwiwa. Jikin yazad yana ƙasa, amma kalamansa na ƙarshe suna mata ƙara a kunne: “Ki gudu…” domin i zuwa Yanzu ya zubda jini harma ya daina motsi.

Ta girgiza kai.

“A’a… ba zan gudu ba.”

Ta ɗaga flash drive ɗin da ya rage a hannunta.

“Wannan labari zai fito!”

Alhaji Sani Kura ya yi murmushin mugunta

“Ke yarinya ce mai ƙarfin hali… amma ba ki fahimci abin da kike yi ba. amma ya kamata ki dubi abinda yake gaban ki”

Ya yi alama ga mutanensa.

“Ku gama da ita.”

Mutane suka fara matsowa.

Sai wani abu mai ban mamaki ya faru, domin Kuwa sautin kukan motar ƴansanda ne ya karaɗe gurin..

WIIUUUU… WIIUUUU…

Fitilun ƴansanda suka fara haskawa daga nesa.

Mutanen Alhaji Sani Kura suka tsaya cikin rudani da tsoron kafin suyi wani yunƙuri tuni aka ke waye su.

Cikin tsoro wani daga cikin yaran ya ce.

"An ke waye mu!"..............

_BASEERATA ITA CE ARZIKINA 😍_

WHATSAPP NUMBER 07064904617 OR 07031012948

ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 🔥 07064904617

*ƊAN JARIDA*
_(THE JOURNALISM🧑🏻‍💻)_
*FREE BOOK*

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥)

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA..(32) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (33) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (34) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (35) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is (36). TANGARAS.... FAD'I KAFASHE PAID BOOK (37). BARRISTER NAZEEYAH PAID BOOK (38).. (39) CAPTAIN AMEESH FREE BOOK....(40) DAREN HANA BACCI ☠️ 💀 ☠️ (41) BARRISTER ARMAN! (42) TARKON SO!
(43) RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA!!! INA NAN DAWOWA (44) (45) ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM🧑🏻‍💻) Free book.
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *ƊAN JARIDA (THE JOURNALISM)*

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM TAKUCE🥰🥰*

................................✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

........................

*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM)*

```Gamasu buk'atar A tallata musu hajjarsu k'ofa bud'e take zaku iya Aiko tallanku A rubuce nasaka muku cikin shafin littafaina Akan farashi Mai sauk'i, .. Inakuke Y'an kasuwa Kuma kuzo Inayin logo graphics ko wanne iri had'ida cartons Art's design kudai kugarzayo domin mallakar naku cikin sauk'i...... Domin magana dani A WhatsApp 07064904617 OR 07031012948 ✍️ Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 Queen 👸 of Writer's Hausa novels 📚📖📚 And design graphics```

```Ina kuke ma'abota ƙamshi Mata da Maza nesa tazo kusadaku BINTOUR ALIEY PERFORM Duniyar ƙamshi Cikin rahusa da Rangwame muna maraba da masu dasayen ɗaya koma Y'an sari muna turaruka kamar:~
sandal flasks, sandal wood, sandal bangi, Senegalese kajiji, kabbasa, humra fara, da brown,musk, turaren gogawa Kala Kala, turaren tsinke, dadai sauransu.... Zaku iya Nemanmu A 07048605381, Or 07040154174 Whatsapp ko kira,... BINTOUR ALIEY PERFORM, DUNIYAR ƘAMSHI DA KECE RAINANI...... MUNA MARABA DA ZUWANKUUUU....
Chapter 12 · 0% Book details