Sashe 10
Dan Jarida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuciyarta ta ɗan sami sauƙi, amma tsoro bai ragu ba.
A ƙofar, bugun ya ƙara tsanani.
“Mun san kina ciki, banasha *ƳAR JARIDA (THE JOURNALISM)!”* muryar ta sake faɗa
Ta duba ko akwai taga da za ta iya tserewa, amma gidan ya yi mata tamkar tarko.
Sai ta ji wani sauti daga waje kamar faɗa.
Sannan kuma daga baya shuru ya gifta, shiru.
Ba zato ba tsammani, ƙofar baya ta fara motsi a hankali.
Banasha ta juya cikin firgici.
Sai ta ga yazad ya shigo a hankali, numfashinsa yana sama.
"Banasha!” bamu da lokaci ki zo mu fita yanzu!”
Ta kalle shi da mamaki. “Ta yaya ka shigo?”
Ya nuna ƙofar baya. “Na san hanyar tsira kawai kedai muje Babu lokaci!”
A daidai lokacin, ƙofar gaba ta fara karyewa.
BANG!
Itace ta fara fashewa.
Yazad ya kama hannunta.
“Mu tafi yanzu!”
Suka ruga ta ƙofar baya, suka fita zuwa wani kunkuntar hanya tsakanin gidaje.
Sautin mutane yana bin su a baya.
Suna gudu cikin duhu, banasha ta kasa numfashi daidai saboda ƙaramin cikin da take ɗauke dashi,
“Waye yake bin mu?” ta tambaya.
Yazad ya amsa cikin hanzari:
“Ba su kaɗai ba ne… akwai wanda ke jagorantar su daga sama.”
Banasha ta kalle shi.
“Danladi ko?”
Yazad ya girgiza kai.
“A’a… akwai wanda ya fi shi girma a cikin komai na wannan case ɗin”
Suka isa wani tsohon gini da ya yi shiru.
Yazad ya ja ta ciki.
“Nan za mu ɓuya na ɗan lokaci,” ya ce.
Banasha ta zauna tana huci, zuciyarta na rawa.
Ta kalli yazad
“Ka san komai daga farko ko?”
Yazad ya yi shiru na ɗan lokaci… sannan ya ce:
“Na san kadan… amma ban san gaskiyar gaba ɗaya ba har sai yanzu.”
Banasha ta matso kusa da shi.
“To ka faɗa min gaskiya duka.”
Yazad ya kalleta da idanu masu nauyi.
“Sunan wannan aikin ba cin hanci kawai ba ne… shi ne shirin kawar da duk wanda zai tona asiri.”
Shiru ya mamaye ɗakin.
Banasha ta riƙe flash drive ɗin da ƙarfi.
“Idan haka ne… to dole mu kai ƙarshen wannan labari.”
Yazad ya girgiza kai a hankali.
“Amma hanyar ƙarshe… na iya zama mafi haɗari.”......
Daren ya yi tsit a cikin tsohon ginin da banasha da yazad suka fake. Iska tana ratsa katangar da ta tsufa, tana yin sauti kamar wani yana raɗa musu barazana, masu bibiyarsu kuma basu gano inda suke ba.
Banasha ta zauna a ƙasa, ta riƙe flash drive ɗin a hannu kamar abin da zai iya ceton duniya.
“Yanzu me za mu yi?” ta tambaya a hankali.
Yazad ya duba ko waje lafiya, sannan ya dawo ya zauna kusa da ita.
“Idan muka fitar da wannan bayanin kai tsaye, za su rufe komai, su maida mu masu laifi, kamar dai Yadda sukama mijinki Binash,”
Banasha ta kalle shi.
“To me kake nufi?”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce:
“Dole mu kai shi ga wanda ba za su iya saye ba.”....
Washe gari da wuri, suka bar wurin a ɓoye, suka nufi birni cikin kamanni daban-daban domin kada a gane su.
Suka shiga wani ƙaramin ofishin jarida mai zaman kansa da ba a cika saninsa ba.
A ciki, wata mace mai suna Hauwa, editar labarai, ta tarbe su da mamaki.
“yazad ? Me ya kawo ka nan?” ta tambaya.
Yazad ya kalleta kai tsaye.
“Muna da labari da zai girgiza ƙasa… amma zai iya kashe mu idan ba a kula ba.”
Hauwa ta kalli Banasha sannan ta ɗauki numfashi mai nauyi.
“Ku zauna. Ku faɗa min komai.”
Banasha ta fara bayyana duk abin da ya faru daga kiran farko, zuwa flash drive, zuwa mutanen da suka far musu.
Hauwa ta saurara cikin natsuwa, amma fuskar ta nuna cewa abin ya fi girma.
Lokacin da banasha ta saka flash drive a computer, fayiloli suka fara bayyana.
Bidiyo, sauti, da takardu.
Hauwa ta yi shiru na dogon lokaci.
“Sai dai ku sani,” ta ce a hankali, “idan muka fitar da wannan labari, ba za ku sake samun zaman lafiya ba.”
Banasha ta amsa ba tare da jinkiri ba:
“Mun riga mun rasa shi, ai”
Sai wayar Banasha ta fara ringing.
Ta ɗaga.
Muryar da suka riga suka fara tsoro ta fito:
“Ku dawo da abin da kuka ɗauka… ko kuma ku fara ganin sakamako.”
Banasha ta kalle su, fuskarta ta canza.
Ta sauke wayar a hankali.
“Suna sanin muna nanan…”
Yazad ya miƙe da sauri.
“Sun gano mu!”
Kafin su ankara sukaji motoci suna tsayawa a waje.
Haske ya cika tagogi.
Banasha ta kalli Hauwa.
“Me za mu yi yanzu?”
Hauwa ta ɗauki flash drive ɗin, ta saka shi cikin wata jaka.
“Sai mun raba shi zuwa wurare daban-daban. Idan suka kama ɗaya, sauran za su rayu.”
Yazad ya girgiza kai.
“Wannan yana nufin rabuwa.”
Shiru ya ratsa gurin kowa da abinda ransa yake saƙawa.
Banasha ta kalli Yazad sannan Hauwa, tace:
“Idan haka ne… to kowannenmu zai ɗauki ɓangare na gaskiya.”
Sautin ƙofa ya fara karyewa a waje.
BANG!
Hauwa ta buɗe wata ƙofa ta bayan ginin.
“Ku tafi yanzu!” ta ce da ƙarfi.
Banasha ta yi jinkiri na ɗan daƙiƙa.
“Za mu sake haɗuwa?” ta tambaya.
Hauwa ta kalleta da ƙarfi.
“Idan gaskiya ta yi nasara… za mu haɗu a gefe guda na tarihi.”
Hawaye suka soma wanke musu fuska, Saida suka rungume juna, da ƙyar Yazad Yaja ta suka fice.
Suka rabu da kuka, suka soma gudu.
Motoci suka shiga cikin ginin.
Banasha tana gudu cikin duhu tare da Malik, zuciyarta na bugawa.
“Yanzu mun rabu da hanya,”
yazad ya ce. “Amma yanzu ne mafi haɗari.”
Banasha ta kalle shi.
“Wannan ba ƙarshe ba ne…”
Ya amsa:
“A’a… yanzu ne ainihin farawa.”
Daidai Lokacin kuma sukaji ƙaran tashin bindiga a bayan su wanda ke nuna sun kashe Hauwa...............
Daren ya kara yin duhu, amma banasha da Yazad suna ta gudu cikin kunkuntar tituna, suna jin karar motoci daga nesa.
Numfashin banasha ya fara gajiya, tsayawa tayi kamar zata kife ƙasa tace bugawar zuciyar tace:
“Ba zan iya ci gaba ba…” ta ce cikin rauni.
Yazad ya kama hannunta.
“Dole ki iya. Idan muka tsaya, zasu gama da mu, kuma duka wahalan mu zata tashi abanza harda rayuwar Hauwa.”
Hawaye suka soma zubo mata cikin ƙarfin hali ta miƙe suka cigaba da gudun.
A gefe guda, kuwa sam basu samu Hauwa ba, Hauwa ta riga ta ɓace cikin birni tare da ɓangaren bayanan da ta karɓa, koda suka ga basu ga kowa ciki ba hakan yasa suka yi halbi kan isa cike da ɓacin rai.
Amma ba ta san cewa wani ya riga ya bi ta ba.
Banasha da yazad suka isa wani tsohon masallaci da ya yi shiru. Suka ɓuya a ciki na ɗan lokaci.
Banasha ta zauna, ta riƙe kirji.
Yazad… "ina jin kamar komai yana rugujewa.”
Yazad ya zauna kusa da ita.
“Gaskiya kullum tana da farashi,” ya ce a hankali.
“Amma yanzu mun kusa kai wa ƙarshen lamarin.”
Banasha ta kalle shi.
“Ka yi min alƙawari… ba za ka bar ni ba.”
Yazad ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sannan ya ce:
“Ba zan bar ki ba, in Sha Allah domin ke amana tace.”
A waje, motoci suka tsaya kusa da masallacin.
Haske ya fara haskawa ta tagogi.
Banasha ta tashi da sauri.
“Suna nan!” ta faɗa Cikin tsoro
Yazad ya duba ta taga, Cikin tashin hankali yace:
“Sun kewaye mu.”
Wayar yazad ta fara ringing.
Unknown number.
Ya ɗaga a hankali.
Muryar da suka fara tsoro ta sake bayyana:
“Ka kawo mana banasha… za mu bar ka ka tafi.”
Banasha ta ji.
Ta kalli yazad da mamaki.
“Sun san mu duka ne? Dama sun san muna tare?…”
Yazad ya rufe wayar.
Sannan ya kalleta.
“banasha… suna son ki, domin sun san kece kike da sirrin su, Ni ba su damu da ni ba.”
Banasha ta girgiza kai da ƙarfi.
“A’a. Idan na fita, za su kashe ni.”
Yazad ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sannan ya fitar da wani abu daga aljihunsa.
Wani ƙaramin flash drive.
Banasha ta yi mamaki, tace:
“Me ne wannan?”
Yazad ya ce cikin ƙasa-ƙasa da murya:
“Wannan shi ne ainihin ɓangaren da ban faɗa miki ba…”
Zuciyar Banasha ta tsaya.
“Yazad… me kake nufi?”
Ya kalleta kai tsaye.
“Ni ban bar wannan aiki ba gaba ɗaya ba… har yanzu ina da alaƙa da su.”
Shiru ya mamaye ɗakin.
Banasha ta ja baya a hankali.
“Ka yaudare ni?”
Yazad ya girgiza kai da sauri.
“A’a… na yi hakan ne don na kare ki!”
Banasha ta fara hawaye.
“To duk abin da muka tsira da shi… ya zama ƙarya?"
Waje ya fara girgiza da karar ƙofar da ake ƙoƙarin karya ta.
BANG! BANG!
Yazad ya kalleta da gaggawa.
“ Yanzu Ba lokaci ba ne na yanke hukunci!”
Ya kama hannunta.
“Idan kina son sanin gaskiya gaba ɗaya… dole mu fita yanzu, sannan zan faɗa miki komai.”
Banasha ta yi shiru na daƙiƙa ɗaya kawai…
Sannan ta yarda da shi.
Suka ruga ta wata ƙofar baya.
Da suka fita, suka tarar da hanya mai duhu.
Banasha ta kalli Yazad.
“Idan ka sake ɓoye mini gaskiya… wannan zai zama ƙarshen mu.”
Yazad ya amsa cikin natsuwa:
“Bayan daren nan… komai zai bayyana.”.................
_BASEERATA ITA CE ARZIKINA 😍_
WHATSAPP NUMBER 07064904617 OR 07031012948
ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 🔥 07064904617.
*ƊAN JARIDA*
_(THE JOURNALISM🧑🏻💻)_
*FREE BOOK*
_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥)