Sashe 9
Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gabadaya y'an ajinmu kallon local suke yi mini.
Tunda suna ganin kalata ta yin yanga ce amma kuma na mayar da kaina bagidajiya.
Ni kuwa na ajiye kaina a inda Ubangiji ya ajiye ni.
Sannan halittata ce shiru da rashin sin kwarabniya.
Sannu a hankali na fahimci banbancin Yaya IBRAHIM da Yaya Rabiu.
Yaya Rabiu mutum ne d'an fafa yafi son harka da y'aya'n manya fiye da na masu k'aramin k'arfi irinsa.
Bayan haka shi din yana da kifadi.
A duk sadda zai ga Kyauta sai zuciyarsa ta buga.
Yana jin wani irin abu ya tokare shi.
Amma kuma shi gaskiya yafi son y'ar attajiri.
Ba zai yiwu ya taso a gidan babu ba, sannan ya sake kwasowa kansa y'ar masu k'aramin k'arfin da zasu zuba masa na mujiya akan sana'arsa ba.
Bayan haka yana son ya shiga sahun wadanda za'a musu jere na kece raini ba irin na yaku bayi ba.
Sab'anin Yaya Ibrahim da shi gabad'aya bai damu da komai ba.
Karatunsa da sana'ar da yake ta sayar da kayan wasa a bakin kasuwar k'ofar wambai kawai ya rik'e.
Banbancin ra'ayinsu ya saka rashin shakuwa a tsakaninsu.
Ba wai shiri ne basa yi ba. amma kuma babu aminci irin na kut da kut kamar na iyayenmu.
Bai fasa tsokanata ba, matukar muka had'u.
Wani zubin ma cewa yake yi "Saboda Allah kyauta a hakan zamu yi aure kin ki karbar cigaba da duniya ta zo da shi?
Kullum kina cikin burum burin din hijabi kamar matar limami.
A gida ko a dawa.
Akan me idan kina gida ba zaki dinga cirewa kina shan iska ba?
To gaskiya na fasa domin ni din wayayyen man ne".
Ban tab'a tanka masa ba.
Wani lokacin idan ya ji haushin shiruna sai ya hau ce wa "Irinku ne mata masu ganawa namiji azaba.
Ba dama ku bude baki ku yi magana sai ku yi ta kunbiya kunbiya kafin a ankare mutum ya ji jiki a hannunku.
Mijinki na da aiki Kulsum".
A ranar da ya fara fad'a mini hakan ba k'aramar dariya na yi ba.
Domin kuwa da dukkan zuciyarsa ya yi maganar.
A gaban Inno mahaifiyarsa.
A sanyaye na ce "Yadda kasan damo haka nake fa Yaya."
Ya ce "Yabon kai dai jahilci Kulsum."
A ranar dai ya ce "Wai dan Allah me yasa kika yarda ake ce miki Kyauta ki amsa?
Sunanki mai dad'i da asali amma an wani k'ak'alo na gargajiya an lank'aya miki ke kuma saboda gidadanci har wani mak'ala shi kika yi jikin sunanki a makaranta.
Ba ki ga yadda na dinga yak'ar masu ce mini Rabe ba, har sai da ya b'ata b'at!
Da murmushi na ce "Ai kai d'an gayu ne Yaya."
Ya ji dad'i domin yana son ace masa shi din ya iya wanka ko big guy ne shi.
Bayan haka yana matukar jin dad'in yadda nake ce masa Yaya sak ba sai na had'a da Rabiu ba.
Inno ta yi dariya ta ce "Zan ga dai ranar da zaka rage fafa.
Menene abin k'i a Rabe ban da d'agawa?"
Ya na gyara zaman hularsa da ta had'e da tsalelen farin yadin da ya sanya ya ce "Haba Inno.
Ni din ai Ubangiji bai mini zubin y'an gargajiya ba.
Ya fice ya barmu da k'amshin turarensa da ya baibaye gidan gabadaya.
Na bishi da wani irin kallo ina ayyana sam sana'ar gawayi bata dace da d'an kwalisa irin Yaya Rabi'u ba.
Sai dai sana'ar ta zabe shi, sai fatan Ubangiji ya sanya masa albarka a cikin nemansa.
A lokacin da na kammala aji ukun na sakandire wato junior graduation sai ga memo, da key holder hadi da kuma stika irin wacce ake mannawa a bayan waya.
Ya kawo mini hadi da koriyar shadda da zamu yi ankonta.
Murnar da na yi ba kad'an ba ne, domin kuwa ba yi mini za'a yi ba a gida.
Yaya Usman ya yi mini hidimar walimar saukar kur'anin da na yi watan jiya.
Haka Yaya IBRAHIM shi ya biya kudin allo da sauran k'ananun tsarabe tsarabe.
Babanmu kuwa baya irin wannan al'amarin tunda ba shi da halin yi.
Abin da na sani duk abin da aka ce makaranta ce ta ce dalibai su kai, to Babanmu zai yi dukkan iyawarsa ya ba ni na kai.
Amma baya d'orawa kansa tsirfar dalibai.
Kayan da Yaya Rabiu ya Aiko mini fall leda ya yi matukar tasiri a wajen Babanmu.
Tasirin da ba yadda za'a yi gari ya waye bai ce mini." Kyauta tunda a gida ana so ai bazai yiwu a kai dawa ba.
Ki cigaba da kamewa.
Kowa ya yi nufin tsayar da ke , ki ce ke an yi miki miji."
Bana damuwa da kalamansa domin na gane Yaya Rabiu yake nufin had'a ni aure da shi.
Ni kuma duk yadda nake shuru shuru, hayaniyar Yaya da hargaginsa burge ni suke yi k'warai da gaske.
Nene kuwa fad'i take yi "Rabe ai ba da wata manufa ya yi wannan kayan ba.
Ni yadda nake ganinsa ai bai ajiye kansa nan kusa ba."
Sau d'aya ta fad'i hakan a gaban Baban titi ya dinga sirfa sababi.
Yana fad'in "A ce d'ansa na wajen Saleh za'a yi inkari dan zai bashi aure?
To ko bai ajiye kansa kusa ba, Kyauta bata da mijin da ya wuce shi a wajensa ".
Daga wannan ranar ta kame bakinta bata sake cewa komai akan sha'anin ba.
Ta zuba ido ta ga ta yadda al'amarin zai kasance.
Ta shiga addu'ar zabin Allah.
Ba dan komai Nene take ji d'ar din al'amarin ba sai dan sanin Inno mahaifiyarsa ta d'ora dukkan burinta a kansa, bayan haka shi din d'an fariya ne na gaske.
Gabadaya abokansa y'aya'n manya ne.
Ya kuma sha fad'in gara mutum ya auro wacce zata yi masa silar arziki idan ya zo wajen Yaya Ibrahim.
Shiyasa take shakku a kansa, amma bata zafafa ba.
Babban abin da yake bata mamaki shi bai ce yana sonta ba fa.
Amma yadda ta ga maigidan nata ya fitititke ne yake bata mamaki ainun.
A wannan lokacin Yaya Rabiu ya so jona digiri amma yadda kudin karatun jami'a ya tsefe ya sanya dole ya hak'ura domin ba shi da hanyar samun wadanan makudan kudaden.
Dan haka sai ya mayar da hankalinsa a wajen sana'arsa.
Yaya Ibrahim kam da ya kammala N.C.E. sai makarantar da ya yi Tp suka roki ya dinga zuwa da safe yana bawa y'an firamare darasin Integrated science.
Kamar yadda ya koyar musu a lokacin da yaje koyon Tp.
Bai k'i ba ,tunda zuwa karfe d'aya na tashi sai kuma y'an yamma su shiga.
A haka har headmaster din ya yi masa kokari ya samu gurbin aikin koyarwa ta dindin alabashinsa.
Duk da haka kuma idan ya dawo gida ya yi sallar azahar ya ci abinci zai fita kasuwa.
Samun aikinsa ya yi matukar saukakawa Babanmu wasu al'amarin rikon gidan duk da dai albashin nasa ba wai yawa ne da shi na sosai ba, amma Alhamdulillah an samu sassauci.
Ganin hakan Baba ya ce ya nemo yarinya ya yi aure ya gaji da zamansa haka.
Yaya Usman bai kai shekarunsa da sana'arsa ba ya yi aure.
A yanzu haka yana kasan unguwarmu a k'aramin gidansa a kansa da ya gina da k'yar.
Sana'ar gini yake yi.
Shima yana iyakacin kokarinsa akanmu sai dai da yake yana da iyalinsa shima tiritiri yake yi da nasa gidan.
Matarsa d'aya da yara uku.
A hankali ya ce "To Babah zan duba a kuma cigaba da yi mana addu'ar dacewa.
Matan yanzun ne Mafi yawa masu dogon buri ne.
Basu cika sauraren mai k'aramin k'arfi ba.
Sun fi son tsalalen saurayin da ya jiku da Naira."
Da murmushi Baba ya ce masa "Da sannu zaka samu irin wacce ta dace da kai mai yakana.
Kada ka zarme a wajen masu kyal kyal din nan.
Ka mayar da hamkalinka akan wacce ta siffantu da addinin take kuma kiyaye kaidojinsa.
In Sha Allah zata zama mai godiya ka kuma samu gamsuwa da nutsuwa da ita ".
Nene da take gefe ta ce "Allah yasa, Allah ya had'a shi da ta gari".
Duk da na yi saukar kur'ani ban fasa zuwa makarantar islamiya ba.
Sai na koma ajin hadda.
Hazakar da nake da ita, ta sanya malamin ajinmu ya fara nuna ra'ayinsa a kaina.
Sai dai ko kad'an ban ba shi fuska ba.
Shi kuma bai yi k'asa a guiwa ba, bai fasa cusa kansa cikin siyasa ba.
Kafin ya ce kowa ya biya sai ya ce "Ummu Kyauta.
Hatta y'an ajin sun fara sansanar akwai abin da yake ransa game da ni.
Ni kuwa ban san dalilin da yasa ko kad'an ban ji zuciyata ta buga a kansa ba.
*GARKUWAR MATA*
*BINTA ABBALE*
PAID BOOK
#500via 7084653262....Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank.
A tura sheda 07084653262.
Masu tambayar wannan karon babu Vip ne .
Zan yi amma a talgram kawai za mu kammala littafin cikin kwana goma ko 'kasa da haka da ikon Allah.
Wad'anda suke bukata kuma suna yin talgram din sai su yi mini magana domin jin abinda za su biya.
'Yan Nijar kuma dala d'ari katin airtel sai ku yi magana da momina kai tsaye babbar macace don Allah a kula.
*+227 88 13 77 40*
[12/16, 9:48 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
*M.W.A*
*ADVERT* *HTTPS://INCENSEREPuBLIC.NG*
*KANO NAJERIA*
*GIDAN 'KAMSHI DA FITA KUNYA.
*Ina masoyan kayan kamshi Ina manyan mata? mata 'yan kwalisa? wannan sanyi fah sai da turare trust me kina bukatar turaren wutan Incense republic muna da turaren wutar daki,turaren jiki,turaren kabbasa da kabbasa spray ba a iya turarukan wuta kadai muka tsaya bah muna da humrori asalin humra mai kamshin manyan Hajiyoyi irin asalin kamshin yan Maiduguri ba tsami gaye bah
Ga kuma kullacha maii Tashin kai
wadda zaki ji dadinta a wannan yanayi na sanyi.Sannan muna da oil perfumes da zaki iya shafawa ko a jiki ko a kaya kuma wani abin burgewar a cikin oil perfumes dinmu akwai wanda har maza za su iya amfani dashi.