← Book details Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 16

Sashe 7

Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ni duk lokacin da ya bijiro mini da lamarin bana aminta gudun abinda zai je ya dawo, zahiri dai duk ranar da girki ya dawo hannuna baya daga mini 'kafa cikin kwanaki biyun nan ina jin jiki a hannunsa dan dai na saba da dabi'arsa ne tuntuni shiyasa ban fiye damuwa ba.

Maganarsa ce ta katse tunanin da nake yi.

" Na 'ki na kwanta dake d'in, ai zuru na yi miki sakarya kawai babu abinda ki ka sa a gaba sai kishin jaraba.

Ni ba soko ba ne, a gurin da na fi samun maslaha da nishad'i zan lalace, ki yi nazarin maganata."
Zuru mukayi muna kallonsa yana d'aura agogo a hannunsa babu abinda ya dame shi ya cigaba da cewa" Ita Aliya ai matar rufin asiri ce Dama ku ne kuke 'kokarin lalata mini ita, tana burgeni mutu'ka babu ruwanta da sakarci irin naku, kuma tana Jin maganata saboda haka ita da na auro a bayanku ta fiye mini ku sau dubu tunda zan kafa doka ta bi, kuma ba ta yi mini rashin kunya sakarkaru kawai."
Ya suri mukkulin motarsa ya kama hanyar fita 'kalau da shi sabuwar shaddar jikinsa tana ta motsi!

Tsabar takaici ban iya cewa komai ba na ja jiki na fita daga dakin guiwa a sanyaye, ba yau Yaya Rabi'u ya saba tsinka ni ba, amma zahiri cin mutuncin da ya yi mana a yanzu ya sosa mini zuciya, Rabi'u wani irin ba'aboren mutum ne da duk jarabar mutum ba zai gane ha'ki'kaninsa ba.

A yinin ranar na yi ta zuba ido na ga ko Nafisa za ta tafi gidansu shiru ba ta fito ba sai hankalina ya kwanta cikin zuciyata nake yi mana addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali.

Nafisa ta fita da girki Aliya ta kar'ba a tsakanin kwanaki biyun wata hatsaniya ba ta tashi ba maigidan ma baya zama sosai a dalilin hidimomin da suke gabansa na harkar kasuwanci, idan ya shigo gurina da asuba a tsaitsaye muke gaisawa ya fita.

Ranar da girki ya dawo hannuna ya shigo muka gaisa ya mi'ko mini mukkulin sito na ce." Me zan yi dashi kuma?" Ya ce." Tsarin na canza a gidana duk wacce take da girki zan bata da hannuna idan ta fita na bawa 'yar'uwarta."
Ban ce komai ba nasa hannu na kar'ba.

Ya kama hanyar fita yana gyara zaman agogon hannunsa yau kwalliya aka ca'ba da k'ananun kaya sai ya yi kyau sosai ya dawo matashi babu wanda zai ce ya ajiye 'yar shekara goma sha hud'u dalili yana da jiki mai kyau kuma yana kula da kansa.

Na ce." Adawo lafiya." Ya amsa kafin ya sa kai ya fita daga d'akin.

Dama tsarin gidan namu wacce take da girki ita ke bawa maigidan karin kummalo da abincin dare.

Jummai kuma tana kula da hidimar abinda yara za su ci da safe da rana da wanda za su tafi dashi makaranta.

Towon shinkafa na shirya yi mana da daddare.

Na sa Jummai ta harhad'a mini komai.

Ina idar da sallar la'asar na yi niyyar shiga kicin.

Sai kira ya shigo wayata Maigidan ne, a nutse na gaishe shi ya amsa yana shan toka.

Shiru na yi ina sauraransa Ya ce." Yanzu Yunusa zai kawo kaji inaso ayi farfesu dalili yau Nadiya za ta dawo sannan ki sa Jummai ta 'kara gyara gidan a kunna turaran wuta."
Na ji wani gundumemen abu ya yi kakagida a ma'kogwarona.

Saboda Nadiya za ta dawo shine za a yi farfesu na mussaman sannan a tsabtace gida harda su turaran wuta!

Lallai Lamarin Nadiya a gurin Rabi'u azimun ne."
"Kyauta ko ba kya ji ne?" Ya fad'a a kausashe!

Na daure sosai ina danne zuciyata na ce." Bayan farfesu me kuma za a yi Yallabai?"
"Shi kad'ai na buk'ata." Na ce." To za a yi in sha Allahu." Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake magana ba.

'Kwalla ce ta cika kwarmin idona.

Na nemi guri na zauna k'afafuna duk sun yi sanyi.

Nadiya ta 'kwace mini Yayana hawayen da nake dannewa suka su'bce suka fara falfala gudu kumatuna.

Nasa hannu na rufe fuskata ina ta Kiran sunan Allah kafin na samu sassaucin kishin da yake yun'kuro mini.

Na tashi da rashin kuzari na fita daidai lokacin da yaronsa Yunusa ya shigo hannunsa da buhu muka gaisa sama-sama ya ajiye buhun ya fita.

Na kira Jummai domin ta taimaka mini, kaji ne manya guda takwas a gyare.

Na ce ta markad'a mini kayan miya kafin na zo kansu.

Har na kammala aikina Nafisa da Aliya babu wacce ta fito kowace tana gurinta da yaranta.

Na zubawa maigidan nasa da yawa su Baffah ma na di'bar musu, sauran kuma na bari a kicin din na san duk zulumar mace za su ci su bari, Jummai da ta taimaka mini itama na d'ibar mata rabonta.

Sai da na gabatar da sallar magariba tukkuna na yi wanka na samu kaya marasa nauyi nasa a jikina.

Bayan Isha'i wajan karfe takwas Nadiya da 'Yan uwanta suka dira a gidan.

Baffah da 'Yan'uwansa duk suka fice daga gurina suna ihu Mamanmu ta dawo.

Murmushi kawai na yi na gyara kwanciya ina ta nazarin rayuwar duniya.

Hayaniyarsu har gurina duk da cewa akwai tazara a tsakaninmu.

Ni da Nafisa muna daf da juna Nadiya da Aliya suna kusa haka tsarin gidan yake 'bangaran maigidan kuma yana tsakiyarmu sai babban gate wanda yake d'auke da d'akunun ba'ki da masu gadi da gurin ajiye motaci, cikin gidan kuma akwai babban tsakargida da band'akuna uku d'akin Yara hud'u da kicin mai yalwa, tsarin gidan dama can na zaman mace hud'u ne da kuma gurin da yara za su sake.

Sai wajejen tara da kwata tukkuna na daina Jin hayaniyarsu tabbacin sun gama abinda suke yi sun tafi, mamaki lamarin ya dinga ba ni, sai ka ce wata sabuwar amarya harda yin zuga! gurin dawo da ita.

Ashe mamakin da na ke yi lami ne domin lokacin da maigidan ya dawo kasa tsugun ya yi, ya kai ya kawo sai murmushi yake tauraruwarsa ta dawo.

Ya shigo yana ta yi mini murmushi na babu gyara babu dalili, ni kuwa na sha kunu saboda yanda nake jin bala'in haushinsa kwata-kwata Rabi'u bashi da ta Ido ina tsammanin lokacin da akayi rabon kunya baya gurin.

"Kyauta ki kai mini abincina gurina sannan inaso zan yi magana daku."
"To." Abinda na ce kenan ban kara kallonsa ba.

Ya shiga dakina ya yi minti biyu ya fito kafin ya sake maimaita mini maganar.

Na sake cewa "To." Ban kalle shi ba, sai ya kama hanya ya fita, na bi shi da kallon takaici.

Lokacin da na shiga falon duk sun hallara ita tauraruwar tasa tana zaune kusa da shi ta ca'ba ado da wani lece wuya da hannu gold sai walwali take yi, ga lalle ja da ba'ki a hannu da kafa abinka da farar fata ta yi kyau kamar sabuwar amarya.

Na ajiye tiren hannuna a daddaumar da ya killace domin cin abinci.

Na samu guri na zauna ina d'an satar kallon Nafisa sai kace mahaukaciya Ido ya kod'e da wata koriyar atamfa ajikinta duk ta zazzage ko yari babu a kunnenta balle a kai ga maganar kwalliya ita ga wacce ta yi ta fad'a da miji sai hura hanci take yi.

Ita kuma Aliya an sha k'ananun kaya riga da siket da kitson gaba sai da babu wata 'kira ta matantaka gaba da baya sai shukuran.

Da 'kyar na danne dariyar da take ko'karin 'kwace mini, na sunkuyar da kaina kasa ina nazarin yanayin zamantakewar gidan mata hud'u.

Gyaran murya ya yi kafin ya fara da Bismillah sannan ya kira sunayenmu duk muka amsa, sai ya d'ora Ido a kaina kafin Ya ce." Kulsumu ba zan ga ji da jadadda miki ba cewa; Ke din Wakiliyata ce a ko'ina.

Ba wai don bana sonki na auri Nafisa ba, haka zalika ba don kun gaza ba na auro Nadiya Aliya k'addarata ce, kowacce da matsayinta a gurina.

Kulsumu ke kin fi su sanin waye Rabi'u dalili auran kuruciya mukayi ni da ke, kuma ina sonki duniya ta sheda hakan kema kin tabbatar, ba wai na furta miki hakan ne domin ki yi fuffuka ba, yanda nake sonki haka nake son duk wacce na kawo gidana babu wacce ta fi wata a cikinku sai mai kyautata mini.

Kyauta ina gargadinki da babbar murya wannan ya zama na k'arshe kada sa'insa ya shiga tsakaninki da abokan zamanki ki mi'ka hannu da zummar duka, ba zan lamunta ba zan d'auki mataki a hukumance! domin babu wacce ki ka ajiye a cikinsu.

Ki ri'ke girmanki sannan ki kula mini da amanar gidana. wannan shine gargadina dake.

Ya numfasa kafin ya cigaba da cewa" Nafisa Nadiya Aliya ban amince ba ban kuma lamunta ba wata daga cikinku ta tozarta mini Kyauta, ita din wata baiwa ce ta mussaman wanda ni kad'ai na san hakan, kuma garkuwa ce a gare ni.

Kada ku ga kun hayayyafa ku nemi wula'kanta mini ita ranku zai 'baci muddin na samu labarin faruwar haka.

Itace babba a gidana Kuma mai wakiltata, duk da ba ta wani baku shekaru masu yawa ba, ya zama dole ku bata girmanta Wallahil-azimin duk wadda ta yi kuskuran cin zarafinta sai mun sa kafar wando d'aya.

Saboda haka wannan shine dalilin zamana daku anan, ku zauna lafiya da junanku shine abinda nake buk'ata."
Shiru falon babu wadda ta yi magana.

Sai na daure zuciyata a hankali na ce ." In sha Allahu zamu kiyaye Allah ya Kori shed'an a tsakaninmu." Shi kad'ai ya amsa da Amin.

Kafin ya ba mu umarnin tafiya.

Na koma wurina da tunani mai yawa a tare da ni. da kyar na ci abinci na yi shirin kwanciya domin ban yi tsammanin zuwa d'akinsa ba dalilin dawowar Nadiya a shari'ance ita za ta kwana tare da shi duk da cewa; Ni na yi girki sai kuma ga shi ya shigo Yana fad'in." Kyauta na ce Ya za a yi ne gashi ke ki kayi girki kuma Nadiya ta dawo ai bai kyautu mu yi mata haka ba ko?"
Ina bubbuge zanin gadona na ce." Gaskiya bai kyautu ba, kawai ka kwana a d'akinta ni ban damu ba.
Chapter 7 · 0% Book details