← Book details Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 16

Sashe 11

Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko sunansa aka ambata a gabana sai na ji wani iri.

Ban ta'ba tsammanin zai zo zance gurina duba da yanda ya ke nuna halin ko'in kula akan lamarin.

Yaron ya kama hanya ya fita bayan Nene ta ba shi amsa kan cewa ya ce gani nan zuwa.

Na jima kafin na tashi da sanyi jiki na canza tufafi na fesa turare mai kamshi a jikina sannan na zurma hijabi har 'kasa na fito da dadduma a hannuna.

Nene dai ba ta ce komai ba har na fita daga gidan na same shi a tsaye a soro ya fesa kwaliyya da sabuwar shadda milk da dinkin 'yan birni hankalinsa gabad'aya yana kan wayar dake hannunsa.

A sanyaye na shimfid'a daddumar ina fad'in." Yaya Rabi'u ka zauna."
Gwasale ni ya yi ta hanyar fadin shi fa ba zance ya zo ba menene zan wani shimfid'a masa dadduma.
raina ya 'baci na murguda baki tare da d'auke daddumar na rungume a kirjina ban sake kallonsa ba.

Sai na tsinkayi maganarsa yana fadin.

To in banda abinki Kyauta ai da mayafi mai raga raga ya kamata ki fito domin na duba zahirinki meye zaki zurmo hijabi sai ka ce wadda za ta je gidan gaisuwa.

Shi fa lamarin aure yana buk'atar nazari da tantancewa."
Na 'kulu sosai da maganarsa domin duk kawaicina kasa daurewa na yi na ce." Ai da yake bazawara ce ni. dole na fito da mayafi mai nuna tsaraici domin ka tantance ni."
Murmushi ya yi, ya shafa sajen fuskarsa Ya ce." Ni ban fad'a ba, amma dai kin san ba ni ke aka yi ba ni, na gani ina so ba, dole akwai nazarin da nake so na yi a kan ki."
Kasa daurewa na yi nasa masa kuka ina fad'in." To ni ma ai ba sonka nake yi ba.

Nani'ka mini kai aka yi, kuma saboda farincikin mahaifina na kar'be ka."
Dariya ya kama yi yana kallona kamar wanda kukan nawa yake masa
d'adi!

Nasa gefen hijabina na goge fuskata na yi nufin shigewa cikin gidan sai ya tari gabana da sauran dariyar a tare da shi.

Ya ce." Kyauta ni abinda yake ba ni haushi dake saurin kuka yanzu fisabillahi menene abin hawaye a cikin maganata idan ba shagwa'ba ba."
Hararasa na yi na murgud'a baki na ce." To ai kaine na ji kana wata magana ta daban.

Shiyasa na fayyace maka abinda yake raina ni ma ba wani kwanta mini ka yi a rai ba."
Ya dinga kallon fuskata yana murmushi.

Sai na kasa gane abinda yake kallo Na sake murgud'a bakina na juya masa 'keya.

Ya sake fuskantata yana kallon bakina.

Nan na fahimci abinda ya ke kallo tuntuni! a karo na uku na sake murgud'a bakin ina hararasa.

Ya dinga k'yalkyala dariya Yana fad'in." Lallai kin raina ni, yarinya daga harara sai murgud'a baki ashe haka za mu yi auran kina yi mini tsiwa!"
Uffan ban ce masa na kawar da kaina.

Ya cigaba da zantukansa idan na ga dama na ba shi amsa wani kuma idan na ji da rainin hankali na murgud'a masa baki! tun a nan na fahimci salon dana d'auka yana burge shi. haka mu ka yi zancen a tsaye kusan awa d'aya da rabi duk k'afafuna sun yi tsami.

Yaya Ibrahim ya shigo soron sai ya tsaya Yana kallonmu.

Kafin daga bisani ya mika masa hannu suka gaisa kowanne fuskarsa a d'aure gaisuwar ma dai kamar ta dole sukayi.

Ban ji dadin hakan ba a cikin raina, domin ina so tun kafin tafiya ta yi nisa a tsakaninmu su daidaita kansu komai ya wuce tunda surukantaka ta shiga tsakani.

Da zai tafi ya bani kyautar dari biyar sabuwar kar.

'Kin kar'ba na yi sai kawai ya lalubi hannuna ya saka mini ya fice daga soron ba tare da ya saurari maganar da nake yi masa ba.

Kwanan farinciki na yi a ranar ganin yanda na fara shawo kansa cikin 'kan'kanin lokaci.

Kuma na fahimci akwai 'bur'bushin sona a tare da shi kawai dai ba zai nuna ba ne saboda 'ki fad'i da kuma wane k'udiri da yake cikin zuciyarsa.

Haka muka cigaba da soyayya mai tafe da rigima domin duk hak'urina a wasu lokotan idan ya kai ni bango tutsu nake masa, na daina kula shi ko ya zo zance bana fita.

Dan akwai lokacin da mukayi fad'a ya zo yana fad'a mini irin kalar matar da yake so 'Yar duma-duma kuma wayaiyiya 'yar gayu mai zurfin karatun boko. raina ya soso sosai amma ban yarda na yi masa kuka ba saboda ba na so ya cigaba da ganin lagona sai dai ban kyale shi ba sai da na narka masa ba'kaken maganganu! masu zafi ban saurare shi ba kuma na buge zanina na shiga gida zuciyata kamar ta fashe saboda tsananin kishi.

Fushi ya yi mai tsanani!

Sai na nuna masa na fi shi Koda wasa ban kira shi a wayar da ya siya mini ba, kuma ban yi masa text na kalaman soyayya ba irin wanda na ke yi masa kullum. wata hudu ba ma kula juna har Nene ta fahimci wani abu ta dinga yi mini fad'a akan dole na koyi ha'kuri da juri'a tunda na san halin wanda Allah zai hada ni zaman aure da shi.

Jinta kawai na ke yi amma bana tsammanin zan neme shi domin ya kai ni ma'kura 'kaunar da nake masa ita ta haddasa tsananin kishinsa ba na so na ji yana ambatar wata mace a gabana balle ya yabi surar jikinta. shi kuma ya kasa fahimtar hakan.

Na lura mutum ne shi mai zara da k'ulafucin 'ya'ya mata.

Misalin karfe takwas da minti goma na ranar wata Juma'a muna zaune a tsakargida harda Babanmu da Yaya Ibrahim Muna hira yaro ya shigo Yana fad'in ana sallama da Kyauta inji Rabi'u.

Nene ta ba shi amsa ya fita.

Ta shi na yi na shiga d'aki na kwanta ba ni da niyyar fita minti goma a tsakani na fara jin hayaniya tana tashi a tsakargidan tsakanin Babanmu da Nene Yaya Ibrahim Yana sa baki.

Ina fitowa na fahimci akaina suke rigimar.

Yaya Ibrahim ya kalle ni tare da ba ni umarnin tafiya gurin Rabi'u.

Da sauri na sa hijabina na fito lokacin Nene ta d'auki zafi tana ta sakin maganganu masu kaushi!

Babanmu ya yi mata shiru ya 'kyaleta! dama an ce mai ha'kuri bai iya fushi ba.

Ni dai ganin yanda abin ya zama yasa da saurin gaske na fita hankalina ma duk baya jikina, ina Jin tsoro Rabi'u ya samu Babanmu ya fad'a masa rikicin da mu ke yi lamari ya 'kara dagulewa.

Shiyasa koda na fita na sassauta fuskarta na gaishe shi.

Aikuwa ya amshe da sauri yana ta jana da hira.

Cikin raina na ce iskanci banza haka zan dinga yi maka a duk lokacin da kayi mini abinda ban gamsu da shi ba.

Mun jima muna hira kamar wani abu bai ta'ba giftawa ba a tsakaninmu.Ya d'auki dari biyar ya ba ni kamar koyaushe na yi masa godiya sosai kafin na koma cikin gidan da tunanin lamarina da shi.

Sannu a hankali na kammala sakandire lokacin na kuma yi haddar al'kur'ani mai girma tare da wasu littafan addinin musulunci.

Lokacin auranmu Yana ta gabatowa daga 'bangaran mu komai an tanada lokaci kawai ake jira.

Yaya Rabi'u kuwa abubuwa sun kacud'e masa, babu gurin zama sannan bai gama had'a lefe ba.

Akwatina biyu ya siya masu sau'kin kud'i amma turmin bakwai kawai ya zuba a ciki 'Yan uwansa mata suka zuba masa abinda ya yi saura.

Sai aka fara fafutukar gurin zama domin ya dage shi ba zai zauna a cikin gidansu ba.

Kuma gashi babu kud'in kama haya.

Kuma shi a ra'ayinsa ya fi so ko hayar zai kama shi kad'ai ba ya son wanda zai yi tarayyya da wani.

Lokacin da Babanmu ya ji dambarwar da ake yi da shi sai ya dinga fad'a Yana cewa ai lefen ba dole ba ne.

Tunda ba shi da kud'in kama hayar gurin zama sai ya rushe lefen ya je ya biya gidan da zai zauna turmi uku da takalmi da mayafi ya isa albarka ake nema a aure ba wani abu ba. saboda haka aure fa ba za a 'kara wasu wattanin ba, za a d'aura shi a lokacin da aka gindaya ba za a janye ba.

Babu wanda ya sani a cikin gidanmu Babanmu ya siyar da sabon kekensa da Yaya Usman ya siya masa dan ya dinga zuwa kasuwa.

Ya kira Rabi'u ya bashi dubu hamsin kyan-kyan! a hannunsa yace ya je ya kama hayar dasu.

Sai da aka kwana biyu tukkuna da Yaya Ibrahim ya lura babu keke a gida ya tambayeshi bai 'boye ba ya fad'a masa abinda ya aikata.

Yaya Ibrahim ya ji ciwon lamarin sosai! amma sai ya danne bai ce masa komai ba ya 'kyaleshi duk domin a zauna lafiya.

Haka aka kawo lefena babu arziki sai kace na bazawara mara gata.

Har kuka na yi da naga irin k'ananun atamfofi da takalman wambai da Rabi'u ya zuba mini a lefe sai wasu mayafai kamar abin tatar koko guda hud'u da wando da breziyya rabin dozin.

Kayan kwaliyya masu sau'kin kudi.

Na shiga d'aki na ci kukana na 'koshi kuma ko da wasa babu wadda na gayyata daga cikin 'kawayena akan ta zo ta ga lefe na.

Abinda na ajiye a raina shine; Rabi'u ya yi niyyar tozarta ni ne amma idan ba haka ba shekara biyu da wata sh
ida da sa ranar auranmu ai ya kamata ace ya tanadi duk abinda ake bu'kata gurin neman aure.

Ranar d'aurin aure ya bada sadaki dubu goma sha biyar.

Da shi aka saya mini zanin gado da ledar d'aki.

Saitin gado da kujeru da sauran tarkace Yaya Ibrahim da Usman suka had'u suka yi cikin rufin asiri aka yi mini jeren d'aki a gidan da Rabi'u ya kama haya wanda duk 'kafafarsa bai samu wanda zai zauna shi kad'ai ba, akwai wani a gidan.

Sai yasa akayi masa katangar langa-langa aka zagaye mana gurinmu.falle-falle guda biyu sai kicin da band'aki sai d'an guntun tsakargidan da ba zai isa mu yi kwanciyar zafi ba.

PAID BOOK
#500via 7084653262....Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank.

A tura sheda 07084653262.
Chapter 11 · 0% Book details