← Book details Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya za ki iya sayawa mijinki ko kuma saurayin ki saboda kara dankon soyayya
Turaren wuta
Humra
Kullacha
Kabbasa spray
Turaren Kabbasa
Turaren wanka
Room Freshner
Oils masu kamshi
Souvenirs package mai dauke da Turaren wuta,Humra,Kaskon turare wuta da Lalle da sticker
*Domin neman karin bayani sai a tuntubi wannan lambobin*
Wa.me/2348137369317
0813 736 9317 ko 0904 482 2052.

Na yi nisa sosai a arewa books
*Binta Umar Abbale* https://www.arewabooks.com/chapter?id=67482a18ca3a075ba0996752
13&14
Cikin rashin kuzari nake tafiya da zummar zuwa gidan Inna Hauwa.

Zuciyata na sa'ke-sa'ke da tunanin yanayin da Yaya Rabi'u ya shiga a lokacin da Babanmu ya yi masa gwanintar bashi aurena.

Gabana ya cigaba bugawa! saboda tunanin wani abu da zuciyata take raya mini.

Sai nake ganin kamar hakan da akayi masa ba a burge shi ba ko ga yanayin yanda ya yi godiya kamar an tilasta shi.

Idona ya dinga kawo ruwan hawaye ina dabarar mayarwa tunda a kan hanya nake gabad'aya na kasa iya danne lamarin a zuciyata ina ganin ko da Allah ya kaddara auren da wahala Yaya Rabi'u ya mutunta ni, duba da yadda ya kasa jure kutsen da akayi masa.

Babanmu ya yi hakan ne da zuciya d'aya, Kuma a hasashen da yake a hannun Rabi'u kad'ai zan iya samun nutsuwa, sai dai har yanzu bai fahimci waye shi ba.

Yaya Rabi'u bai ajiye kansa a kusa ba, yanda na fahimta duk tsokanar da yake mini ba ta da ala'ka da abinda Babanmu yake tunani.

Ni kaina na jima ina rokon Ubangiji ya cire mini abinda nake ji a zuciyata dangane da shi.

Amma duk kwanan duniya abin yana nan a mak'ale a zuciyata kamar ana tiri.

Na isa gidan Inna Hauwa a gajiye ga damuwa da ta yi mini dabaibayi.

Zubewa na yi akan tabarmar dake shimfid'e a rumfarta na rufe fuskata da mayafina hawayen da nake dannewa suka fara zuba.

Kukan kad'ai shi zan yi na ji sassaucin abinda yake damuna.

Allah ne ya jarrabe ni da san Yaya Rabi'u duk da cewa; Akwai tarin maza masu nagarta da suke 'kaunata amma ba na Jin su a raina ko kad'an zuciyata ta fi karkarta a zuciyar da ba ni da gurbi.

Da zan iya cire son Rabi'u da tuni na cire na jefar na huta da damuwa.

Inna Hauwa ta shigo rumfar tana fad'in." Kyauta daga zuwa kuma sai bacci, ko idonki biyu ne?"
Shiru na yi mata ina ta ko'karin danne mahaukacin kukan da yake ko'karin kufce mini.

Hannu tasa za ta janye mayafin dana rufe fuskata.

Na ri'ke da kyau ina girgiza mata kai.

Ta ce." Kuka ki ke yi Kyauta me akayi mini?" Zaune na tashi ina kare fuskata.

Ta ce." 'Karya ki ke yi da dalili wannan kukan na ki, ki fad'a mini abinda akayi mini."
Shiru na yi ban ce mata komai ba sai da ta sake magana tukkuna na yi mata bayani wai ko da shawarar da za ta ba ni.

Kawai sai ta fara fad'a cewa; Yanzu an daina haka, auran na gani inaso ma ana samun tangard'a ballanatana na cushe!

Idan tana raye ba zata bari ayi abinda za a yi kuka daga baya ba.

Na so nayi mata bayani amma ta'ki saurarata dama kuma macace mai fad'an tsiya da mita.
da zan tafi ta ba ni humra mai kamshi da dari biyu
Humrar kawai na kar'ba ta yi ta yi dani na 'ki kar'bar kudin.

Na yi mata sallama tana jadadda mini cewa; Na fad'awa Nene gobe ta tsammaci zuwanta.

Na yi dakacen sanar da Inna Hauwa lamarin, domin na riga na san halinta 'yar tada zaune tsaye ce, duk da suna wasan 'kanwar mata da Babanmu hakan ba zai hana ya tsinkata ba muddin akan lamarin Rabi'u ne, ni kuma ba zan so hakan ba, wata'kila ita kanta Nene ta fuskanci 'bacin rai mai tsanani.

Dan haka ko da na koma gida ban tashi maganar ba, har dare dai ba ni da kuzarin kirki.

Ina kwance a rumfa na ji shigowar Yaya Ibrahim gidan.

Babanmu Yana tambayarsa Yaya Usman saboda ya kwana biyu bai zo ba, Yaya Ibrahim din ya ba shi amsa da cewa; Yanzu sukayi waya yana kan hanya.
minti goma sha biyar a tsakani Yaya Usman ya shigo gidan, ina jin suna gaisawa na yi shiru gabana na bugawa! kiran sunana da ya yi shi zaburar da ni, na tashi zaune ina amsawa.

Tsakargidan na fita na raku'be a kusa da Nene cikin ranshin kuzari na gaishe su suka amsa Yaya Ibrahim Ya zuba mini Ido yana kallo kafin ya fara tambayata.

Na ce." Lafiyata lau Yaya." Babanmu ya yi gyaran murya kafin ya fara magana akan abinda ya tarasu.

Ya numfasa ya cigaba da cewa" Ko bana raye a doran duniya ban amince ku aurar da Kyauta ga wani ba face Rabi'u shi na mallakawa ita a matsayina na Ubanta wanda shari'a ta ba ni damar za'ba mata miji nagartacce! wannan shine; dalilin tara ku anan."
Yaya Ibrahim shi ya fara sukar lamarin, Yana ta ko'karin nunawa Babanmu illar hakan da ya aikata, akan wane dalili zai yanke hukunci ba tare da ya saurari ra'ayin wanda akayiwa bajintar ba.

Shi fa ya san waye Rabi'u tare da d'abi'unsa tunda tare suka taso, dalilin da yasa kenan kanwarsu bata ji'kuwa tunda an samu banbancin ra'ayi.

Rabi'u Yana da 'kafafa da izzah uwa uba kuma rashin ha'kuri, gashi dai ubansa ba kowa bane amma bai ajiye kansa a kusa ba.

Sannan duk lokacin da zaman majalisa zai had'a su yana jin irin zantunkan da yake yi akan irin macen da yake so ya aura wayaiyiya kuma 'yar manyan mutane, wannan shine kud'irin Rabi'u, Yana ganin idan a ba shi kyauta kamar an yi masa kutse ne, tunda ba shi ya ce yana sonta ba, zai ajiye a ransa ita din matar ladan noma ce.

Kyauta macece mai ha'kuri da kawaici a ganinsa ba ta dace da zaman aure da Rabi'u azababbe ba wanda duk cikin abokanansu babu wanda bai san halinsa na musu da cacar baki ba, ga zahirin gaskiya Amma idan ana musu dai shi zai k'aryata mutum ya kawo k'auli da ba'adi, kuma ya tsaya kai da fata maganarsa itace daidai duk da ya san 'karya ya 'kir'kira, haka d'abi'arsa take yana da
baki sosai kuma ba a kada shi a magana.

Yana zuwa majalisarsu ta samari take d'aukar zafi. wasu lokotan a tashi lafiya wani sa'in kuma a tashi da hayaniya!

Duk da Yaya Ibrahim ya bud'awa Babanmu asalin Rabi'u, amma sai ya take ya rufe shi da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.

Yaya Ibrahim ya shiga ba shi ha'kuri ganin yanda ransa ya 'baci.

Shi kuwa Yaya Usman fad'i yake Allah ya sanya alheri Ubangiji yasa da mu za a yi.

Nene dai tashi ta yi ta shiga d'aki uffan ba tace ba, ga dukkan alamu al'amarin bai kwanta mata ba, sai ya kasance ni da Babanmu ne kawai muke son Rabi'u, domin duk sukar da Yaya Ibrahim ya kawo a kansa bata samu gurbi a zuciyata ba, abinda nake ji dangane da shi yana nan a jibge ko 'kwarzane bai yi ba.

Washe gari da sassafe sai ga Inna Hauwa.

Nene ta dinga tambayata lafiya domin zuwanta da safe ya bata tsoro!

Ina d'aki a kwance na ji tana yi mata bayani abinda na je na fad'a mata kai tsaye kuma gurin Babanmu ta zo.

Nene dai ba ta yi farinciki da zuwanta ba ko ga yanayin yanda take bata amsa.

Muryar Bababmu na ji a rumfar yana tsokanar Inna Hauwa kamar yanda ya saba.

Suka gaisa tana rama tsokanar da yake mata kafin ta kutso da ainihin abinda yake tafe da ita.

Sai kawai na ji maganarsa a fusace ya juya lamarin kan Nene ya rufe ta da fad'a wai duk wanda zata je ta fad'awa lamarin nan bai isa ya hana shi iko da abinda ya haifa.

Inna Hauwa tana fad'a yana fad'a.

Kawai sai na ji Nene ta fashe da kuka tana fad'in." Hauwa ta shi ki tafi dan girman Allah ki cire kanki daga lamarin nan babu ruwanki, ki kyale shi ya yi abinda ya ga dama."
Ganin tana kuka sai ya fita daga rumfar bai sake wata maganar ba.

Ita kuma Inna Hauwa tana ta nanata maganar tare da fadin kuskuran da Babanmu yake ko'karin aikatawa.

Nene ta ce." Yanda na bi lamarin nan da addu'a Hauwa ke ma ki bi shi da addu'a.

Bana san abinda zai daga mini hankali ko kad'an.

Wannan furucin shi ya sanyayyar da jikin Inna Hauwa ta bar maganar suka shiga yin wata da ta shafi zumuncinsu.

Lamarin ya cigaba da tafiya cikin rashin da'di domin tunda lokacin da Babanmu ya furtawa Rabi'u abinda yake cikin ransa ya d'auke mini wuta, idan za mu had'u a hanya sai ya d'auke kansa.

Hakan da yake mini ya fara sosa mini rai dan na tsani wula'kanci da a rayuwata! wasan da yake mini ya daina, ko siyan gawayi na je gurinsa sai da yasa yara su ba ni, kuma baya kar'bar kudin.

Ganin abinda yake yi mini ya yi yawa yasa na kama kaina.

Gabad'aya ma na daina bi ta hanyar gidansu ko makaranta zan tafi sai da na yi zagaye ta bayan layi.

Na daina zuwa siyan gawayi.

Sai Yaya Ibrahim ya shiga sayo mana buhu guda Yana ajiyewa.

Na ji dadin hakan sosai domin dama neman hanyar da zan nesanta kaina da Rabi'u nake yi.

Tunda maganar aure ya shiga tsakaninmu na daina zuwa gaisuwar Juma'a gidansu saboda ina jin tsoron na riske shi a gidan ya yi mini kallon banza.

Bayan haka kuma ina jin kunyar Inno yanzu gabad'aya ba na so na had'u da 'yan gidansu ko a hanya ne saboda abinda yake shirin wanzuwa.

Watanni biyu kenan ban sa Rabi'u a idona ba.

Na damu sosai, domin ni kad'ai na san ciwon da zuciyata take yi mini a kansa, ina ko'karin dannewa ne kada ya fuskanci yanda nake sonsa ya samu makamin da zai ya'ke ni, shiyasa na d'auki wannan matakin.

Ranar wata Alhamis misalin takawas da rabi na dare sai ga yaro ya shigo gidanmu wai Kyauta ta je Rabi'u yana kiranta.

Na ji gabana ya yanke fad'i!
Chapter 10 · 0% Book details