← Book details Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 16

Sashe 8

Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai tunda ta dawo an yi me wuyar."
Jim ya yi yana kallona kafin Ya ce." Anya kyauta ko dai akwai wani 'kulli a cikin zuciyarki ne ."
Na kalle shi ina jin kamar na farfasa masa hanci na ce." Wai ni Yaya Rabi'u yaushe za ka daina zargina ne? wane irin 'kulli kuma bayan yanzu na ji kana yabona a gabansu.

Kuma fa shari'a ce ta ce hakan, ka je kawai ka yi kwanakinka idan basu isheka ba na baka kyautar nawa."
Murmushi ya yi mai sauti kafin ya tunkaro ni, Yana so ya rungume ni.

Na yi saurin gocewa band'aki na bude na shiga ina jan tsaki.

Sai da na tabbatar ya fita daga d'akin tukkuna na fito.

Na kwanta ina tunano abinda ya shud'e a shekarun baya..........

PAID BOOK
#500via 7084653262....Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank.

A tura sheda 07084653262.

Masu tambayar wannan karon babu Vip ne .

Zan yi amma a talgram kawai za mu kammala littafin cikin kwana goma ko 'kasa da haka da ikon Allah.

Wad'anda suke bukata kuma suna yin talgram din sai su yi mini magana domin jin abinda za su biya.

'Yan Nijar kuma dala d'ari katin airtel sai ku yi magana da momina kai tsaye babbar macace don Allah a kula.
*+227 88 13 77 40*
*GARKUWAR MATA*
*BINTA ABBALE.*
[12/14, 11:04 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!*
*NA*
*BINTA ABBALE ABBALE
*M.W.A.*
Na yi nisa sosai a arewa.
*Binta Umar Abbale*
https://www.arewabooks.com/chapter?id=67482a18ca3a075ba0996752
52U/HARVERT NETWORKING BUSINESS.
*ALHERI NE
Ina masu sha'awar shiga shahararren kasuwancin nan wato 52U basu da hali?

Ga dama ta samu SZARIA tazo maku da sabon tsari domin taimaka ma marasa 'karfi, wato TEAM WORK. da kud'in ki 'kalilin zaki samu abunda zaki taimaki kanki da 'ya'yanki, tsarkakken kasuwanci ne mai ingancin da babu asara a cikinsa sai riba mai gwa'bi.

'Yar uwa maza ki shiga gruop dinmu ga link nan a kasa, domin mu gudu tare mu tsira tare.

Domin 'karin bayani ku tutubi wanan number 08037930727
https://chat.whatsapp.com/CSQ94ZeYnPJ26ppXhBnRII
9&10.

Sunana Ummu Kulsum Adamu Kyauta.

Na samu inkiyar Kyauta ne a wajen mahaifiyata.

Saboda maza biyu da na rako.

Kafin nan kuwa sai da ta yi b'ari uku kafin cikina ya tsaya mata.

Akwai tazara mai yawa tsakanina da yayana da na biyo wato Yaya Ibrahim.

Ina son sunan nawa na kyau
ta.

Shiyasa ma na saka shi a cikin sunana a makaranta.

A makarantar kuwa mafi yawa sun dauka inkiyar Babana ne ko ta kakana.

Dan haka suke fad'in Ummu Kyauta, wasu ma kyauta kawai suke fad'a har malamai.

Shi yasa sunan ya danne Ummu Kulsum tunda a gida kowa Kyauta yake fad'i.

Mahaifina Malam Adamu haifaffen cikin birnin Kano ne.

A unguwar Magashi.

Bai yi karatun boko ba, sai ta allo.

Da ya fara girma sai yake zuwa kasuwar rimi yana sayar da kayan koli, a hakan har ya yi teburinsa a maimakon da farko ya fara dauka a tire.

Da wannan sana'a aka yi masa aure, ya haifomu, muka taso muka ganshi da ita.

Mahaifina mai k'aramin k'arfi ne ainun amma kuma daidai gwargwado muna cin abinci, ba'a tab'a sauke tunkuya a gidanmu ba, yana kuma kokarin bamu abin da ya sauwaka na bukatar yau da kullum.

Mu uku iyayenmu suka haifa.

Yaya Usman sai Yaya Ibrahim.

Sai ni Ummu Kulsum da na zo bayan shekaru goma da haihuwar Yaya Ibrahim
Daga kaina kuma bata sake ba.

Sai dai a yadda na ji labari mahaifanmu sun yi wabi, ma'ana y'aya'nsu sun yi ta rasuwa ne suna k'ananun.

Kafin Yaya Usman ma sai da aka yi biyu suna komawa.

Aminin mahaifinmu kut da kut tun 'kuruciyarsu Malam Saleh asalinsa shima d'an unguwar magashin ne .

Tare suka yi ta fad'i tashin rayuwa. har zuwa lokacin da suka yi aure.

Aka bawa kowa daki a cikin gidansu, tunda gidajen a jere ne.

A haka duk suka yi haife haife.

Malam Saleh ne ya fara kammala gininsa a bayan unguwa.

Ya k'aura da matarsa da y'ay'a bakwai.

Sun so su samu fili a jere su sake makwabtakar juna, sai dai hakan ya ci tura.

Amma sun saya din sai dai akwai banbanci layi d'aya a tsakani.

Mahaifina ne bai samu zarafin tashi ba sai da aka haife ni.

Sannan ya yi k'aura zuwa k'aramin gidansa da ya gina cikin taimakon Allah.

Na taso cikin gatan yayu da na iyaye.

Domin lokacin da nake girma yayyena duk sun girma mussaman Yaya Usman.

Sai na kasance ni ce k'aramar yarinya bayan haka ni kad'aice mace.

Na taso da son karatun islamiya fiye da na boko.

Hakan ya sake janyo mini soyayyar iyaye.

A hankali ina girma ina fahimtar yadda al'amar suke gudana.

Na kuma gane k'arfin amincin da yake tsakanin Babanmu da Baba mai keke.

Domin kaf unguwarmu ba gidan da nake shiga ba'a biyo bayana ba sai gidan duk kuwa da y'ar tazara.

Duk abin da baba mai Keke zai yiwa y'aya'nsa mata sai ya had'a da ni.

Dija ce sa'a ta a gidan.

Matansa biyu.

Inno ce uwargida itace Kuma take da mafi yawan yara.

Domin y'aya'nta tara cif.

Sai da ta yi mata biyu sannan ta haifi Rabi'u, mata suka cigaba da biyo shi sai a karshe ta sake yin namiji ya zama auta.

Dakin amaryarta kuwa da ake kiranta da Yadikko Kamal ne babba sai Khadija sai Asabe.

Da yake akan girmanta ya aureta, ta yi haifehaifenta a gidanta na farko.

Kasancewar Dija ce tsarata kuma kawata sai na fi dabdala a dakin Yadikko.

Basa wani rikici a tsakaninsu sai abin da ba'a rasa ba.

Tun muna yara da mun hango Yaya Rabiu muke guduwa a dalilin shi din azababben mutum ne.

Bayan haka baya wasa da mu.

Shekararmu goma kwatsam annobar amai da gudawa ta dira a wasu yankuna na cikin birnin kano.

Mu dai bata shigo gidanmu ba, amma ta shiga gidan Baba mai Keke ta yi awon gaba da Dija da kuma mahaifiyarsu Yadikko.

Tsiran kwana uku a tsakaninsu.

Duk da ina karama na ji mutuwar Dija domin har cikin zuciyata nake sonta, ba ni da y'ar uwa mace, ba ni kuma da aminiya.

Itace duka a wadannan matsayin a wajena.

Da k'yar aka shawo kan wannan annobar da ta dinga lakume rayukan al'umma.

Mutuwar Dija da Yadikko sai ya sanya gabadaya na daina zuwa gidan Baba mai keke.

Inno da kanta ta zo ta dinga rarrashin na dinga zuwa ina debe mata kewar abokiyar zamanta da Dija.

Cikin rarrashi ta ce "Ai da yara ku yi wasanku, ga yayyenki nan su Jummai, su Asabe ki dinga zuwa kin ji Kyuata".

Na ce "To"
Amma ba dan zan je ba.

Shi da kansa baba mai Keke sai da ya zo bikona amma fir na k'i zuwa domin na riga da na tsorata.

Domin sai nake ganin a gidan mutuwar take, tunda ta dauke mutanena idan ina zuwa ni zata sure.

Yaya Rabiu da Yaya Ibrahim sa'annin juna ne, sai dai basu wani shaku ba, a dalilin kowa mai zuciya ne kamar kuturu.

Bayan haka Yaya Rabiu makarantar kwana ta maza da take garin gaya ya yi, sai ya zo hutu.

Da suka kammala sakandire kuwa kowa makarantarsa daban.

Yaya IBRAHIM yana zuwa F.C.E KANO.

Yayin da Yaya Rabiu yake zuwa polytechnic, yana yin diploma in public administration.

Kafin lokacin kuwa kowa yana buga bugarsa ta neman taro da sisi.

Mafi yawa wadanda suka tashi a cikin k'waryar birni yana wahala ka ga mai zaman kashe wando.

Yaro da babba ana ta sana'a.

Yaya Rabiu gawayi yake kullawa yana siyarwa a bakin titinmu.

Shi kuwa Yaya Ibrahim Kes din caji ne da shi.

A duk sadda na je siyo gawayi sai ya k'ara mini.

Baya kuma hantara ta kamar yadda yake yi mana ni da marigayiya Dija.

Sai kuma ya k'ara mini da wanda ya zarce na adadin kudina.

Tun ina dari dari da shi har na sake.

Da ya fara zuwa makaranta ma bai fasa ba, akwai mai jire masa, idan ya dawo da yamma kuwa zai cire kayansa ya saka na zaman gaban gawayi ya yi ta kullawa tunda kullum abin gaba yake yi.

Da buhu d'aya ya fara amma yanzu har rabin buhu yana siyarwa.

Shekarar da na kammala aji uku na sakandire a lokacin ya kammala diploma.

Tunda ba daga kammala sakandire ya fara ba a dalilin rashin cikakken kudi.

A duk sadda muka had'u da shi, walau a hanya ko gidansu, ko ya shigo namu gidan, ko kuwa na je siyan gawayi.

Sai na tsinci kaina da jin nauyinsa.

Bana iya had'a ido da shi.

Shi kuwa da ya fahimci hakan sai ya fara tsokanata da ce wa "Matar!

Ko kuma ya ce "Matar mai gawayi."
Hakan ya sake rub'anya kunyarsa da rashin sakewa da shi.

Ban fahimci ko ina sonsa ba, nasan dai ina matukar jin kunyarsa.

Baya ga haka bana ganin aibun ba'kar fatarsa.

Idan ka cire shi kuwa, ni bana son bak'in namiji haka siddan.

Na fara zama budurwa .

Domin ni din doguwa ce sambal.

Sannan fara tas, ba ni da kiba, amma dukkan jikina a cike yake, mussaman a yanzu da nake shirin shiga sha biyar komai nawa daukar ido da hankali yake.

Sannan ina da gashi sai dai cikarsa tafi tsayinsa yawa.

Baki ne sosai amma mai k'arfi sosai.

Da ace zan saka masa relaxer da har gadon baya zai sauka.

Bayan haka ni din mai sanyin halice ainun, magana ma ba kasafai na cika yinta ba.

Allah ya yi mini baiwar hak'uri kowa ya shaida hakan.

Ba ni da girman kai ko kad'an.

Har yanzu ban wuce na kai nik'a ko markade ba, sannan bana jin komai idan na tafi aike, sabanin sa'anina da suke ganin sun zama y'an mata aika sai yara.

A zahirin gaskiya Yaya Rabiu bai tab'a furta mini yana sona da gaske ba, sai dai a wasa, sannan bai tab'a yunkurin yin abin da iyayenmu zasu fahimci yana sona ba.

Amma ni kuma wasan da yake yi mini ya haifar mini da wani al'amarin da na kasa tantance shi a zuciyata.

Ba ni da wanda zan tattauna.

Tunda ni ko a makaranta bana yarda na yi doguwar hira.

Ba ni da k'awaye.

Sai dai Wanda za'a yi magana d'aya biyu.
Chapter 8 · 0% Book details