← Book details Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 16

Sashe 13

Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma idan ta je ta tsiro da halayen banza dan tana jin kuna kushe dab'iun mijinta, to ta sani fa itama zata ga ba daidai ba.

Domin Ubangiji da kansa ya girmama sha'anin aure, ya d'aga darajar miji akan mace.

Ina rok'onku, ku fad'a mata hak'uri da juriya ne kawai a cikin ko wanne aure amma dad'insa kalilan ne."
Daga haka ya fice daga gidan gabadaya.

Daga Nene har Inna kowa bakinsa ya mutu murus.

Yaya Usman ne ya ce "Allah yasa alheri mai yawa ya biyo baya.

Sannu KYAUTA".

Da kai na amsa shi tare da daukar ayaba na yi Bismillah na fara ci.

Ana haka Yaya Rabiu ya yi sallama ya shigo.da tarkacen kayan da muka bar masa.

Ya gaida Nene cikin mutunci, ya kalli Inna ya ce "Kun iso lafiya?"
Ta amsa da lafiya lau Alhamdulillah".

Ya sassauta murya ya ce "Sannu Kulsum, ya k'arfin jikin dai?"
Murya babu amo na ce"Da sauki".

Ya mik'e yana addu'ar samun dauwamemmen sauki.

Sannan ya tafi.

Sai da aka yi sallar la'asar Inna Hauwa ta tafi gidanta tare da shirgin kayanta da na biki.

Kwana biyu da sallamo ni, lafiya lau nake jina, amma gabad'aya jikin nawa babu k'arfi.

Da na yi tafiya zan ji na gaji.

Ganin hakan Baba ya jinkirta tariya.

Ya hak'ura ya bar ni sai na ji k'arfin jiki.

Kullum kuma sai Yaya Rabi'u ya zo ya duba ni.

A kwana na uku ya sassauta murya ya ce "kyauta kina da wata matsala ne da jikinki?"
A hankali na ce "kamar ya ya?"
Ya gyara tsayuwar da ya yi ya ce "To me kike yi a nan gidan.

Ai ke Malama ce kinsan dai babu kyau a daura auren yarinya ta cigaba da zama a gidansu.

Kin wani saki jiki kina ta marairaicewa.

Ki tsananta jikinki, a saka ranar tariyar nan kyauta.

Bar ganina haka nima na iya jinya da rarrashi sosai fa".

Na yi dariya na ce "Yayah ke nan.

Ina na rufe baki sai ji na yi ya saki baki ya ce "Kin san Allah akan gadonmu zan kwantar da ke na dinga bin sashe sashe ina yi miki tausa a hankali, ina kuma dunbular abin da yake tsole mini ido."
Gabadaya na ji na rikice, kunya ta ban mamaki ta yanko mini.

A kidime na ja jikina na shige cikin gidan.

Ya bude murya yana kirana da yake baifi taku biyar ba tsakanin zauren da tsakar gidan tunda gidan k'arami ne.

"Kyauta ki dawo ban fadi abin da na zo fad'a miki ba ai".

Nene da ke zaune a rumfa ta yi kamar bata fahimci yanayin da na shigo da shi na kunya na shige uwar dakin ba.

Ga shi ya bude murya yana kirana babu ko kunyar gidan surukai yake.

Yana tsaye Ibrahim ya shigo zauren ya same shi.

Suka gaisa.

Sama-sama ya ce "Ya ka tsaya, ka shiga mana".

Rabiu ya dauke kai ya ce "Ban gane ba, kada ka mayar da ni wani irin mana, shikenan bazan yi kunyar surukuta ba.

Kawai idan ka shiga ka turo mini ita, ban gama fad'a mata kalaman bakina ba ta tsere ta bar ni.".

Yaya Ibrahim ya jijjiga kai ya nuna kansa ya ce "Ni zaka aika na kira maka Kyauta Rabe?"
Ni ban zama surukinka ba ashe, wanne irin raini ka yi mini ne?"
Ya dauke kai ya ce "To ina ce kai abokina ne, kuma gaskiya kada ka sake ce mini Rabe!

Ka sani, bana so, nifa Wallahi zan had'aka da Baban titi ya mana iyaka, ka bala'in matsa mini, tun sadda aka fara maganar aurena da Ummu Kulsum."
Ibrahim ya yi sakare yana kallonsa domin ya yi zaton auren da aka yi masa da kyauta zai sa Rabi'u ya sassauta ya rage rikice masa da gangan.

Suna haka Baban titi ya shigo ya ce "Halan yau ma cece kuce kuke yi."
Nan da nan Rabi'u ya ce "Yauwa Baban titi raba ni da Ibrahim ya matsa mini akan me zaice mini shu surukina ne, ba nine babba ba?

Ance kwana araba'in na ba shi.

To akan me zai titsiye ni wai sai na girmama shi akan shi yayan Kyauta ne.

Ko Yaya Usman da ya yi mini fiko mai yawa bai mini hakan ba.

Gaskiya ya rage shiga hancina".

Ya fad'a da sigar damuwa.

Baban kuwa ya ce "Ibrahim ka daina zungurar Muhammad Rabi'u.

Ba d'an uwanka ba ne?

Ai ba auren kyauta ne ya had'a ku ba.

Bana son rashin gaskiya."
Kan dole Ibrahim ya ce "To Baba zan kiyaye."
Ya juya ya tafi yana gunagunin takaici wanda na takaici yadda ba wanda ya ce masa ga ranar tariya.

Kaitsaye gidansu ya afka, babu sallama.

Inno ta ganshi tamkar jifa sai huci yake yi.

Ta sassauta ta ce "Menene kuma kai da har yanzu ba zaka daina fad'a irin na kumfar baki ba."
Tana d'isa aya ya ce "Inno na rantse ban tab'a ganin kaskantaccen ango Irina ba.

Ta yaya za'a daura mini uare a saka ni kama gida, aje kuma a shirya shi, sai kuma a barni ni kad'ai?

Na tabbatar ko kema ba ki tab'a ganin hakan ba."
Tsaki ta ja tare da mikewa ta bar shi tana fad'in shasha marar kunya kawai!

Ya yi sak'alo yana ayyana menene abin da ya yi na rashin kunya?

Ya make kafadarsa ya fito ya yi waje cikin kunci mai yawa.

Muna zaune a tsakar gida Nene na yin kad'ai da yake tana yin lagwanin risho Babanmu da Yaya Ibrahim suna tafiya mata da shi kasuwa, suna siyarwa.

Ta kalle ni ta ce "Yau dinma sai na ce ki debo maganin sanyin ki Sha?

Wai ke wacce irin yarinya ce haka da ba Kya son magani?

Kina dai Jin yadda innarki Hauwa ta fad'i kyawun maganin da ta yi kundubalar siyowa ta kawo miki, amma sai fama nake da ke ki sha.

Shiyasa ban yi asarar kudina ba.

Tunda ga wanccan hakkin dakan ma ki diba ki sha da madara amma kin k'i dad'in azanci.

Na kyale ki, itama Hauwan ta ce na kyale ki, zaki nema da kanki ne."
Na yi k'asa da kaina domin tunda na fahimci amfanin hakkin dakan da take dirka mini nake jin matsananciyar kunyar na sha a gabanta.

Gara na sanyi na kan sha, kawai ni ina cikin jerin mutanen da basa son magani ko wanne irin ne.

Amma tabbas idan na sha na sanyin ina jin dad'in marata dama jikina, tunda hatta fitsarina canjawa yake yi.

Haka kazar da aka dafa da Saiwowin chadi na cinye duk da dai ba ta dad'i ba ce, amma kuma bata da bauri ko kad'an.

Ku tuntubib wannan lambar 08032773332 don samun naku maganin sanyin sahihi cikin farashi mai rangwame.

Ba iya maganin sanyi ba, dukkan kayan gyara akwai wanda ake kawosu daga Chad.

A daren wannan ranar Baba ya ce gobe da yamma za'a raka ni dakina.

Ina dakina na ji wani irin matsananciyar faduwar gaba a dalilin maganar tariyata.

Haka kawai nake shiga rudu da fargabar zan kad'aice daki d'aya da Yaya.

Tunda aka Shafa mana fatiha yake sakin maganganu masu kunyatarwa da sanya fargaba a zuciyar budurwa mai karancin wayewa Irina.

Na kwanta na dunkunkune ko sallar isha sai tsakiyar dare na tashi na yi.

Da safe haka na tashi salo salo babu kuzari.

Nene ta hau sababin yau ko suma nake yi sai an kai ni dakina ta gaji da iskancina da kuma rashin kunyar Rabe.

Na je na yi jinyar a dakina.

Baba dai bai ce komai ba.

Shi kuwa Yaya da hantsi ya bugo mini waya.

Ina dauka sai cewa ya yi "Tsire za'a tanadar miki ko kaza?"
Zullumin da nake ciki ya sake hauhawa.

Na kasa ce masa kanzil.

Ya numfasa tare da ce wa "Kyauta ki fahimce ni fa.

Ni gaskiya bana son ki zo kina mini gidadanci irin haka?

Na tambaye ki, kin mini shiru.

Menene abin kunya a wnanan maganar fisabillahi?"
Ya yi k'aramar tsaki ya kashe wayarsa.

Ya bar ni da tawa a kunne.

Ana yin azahar sai kawai labari ya iso mana Inno ta yanke jiki ta fad'i an tafi kaita asibiti.

A gigice Nene ta shirya ta bi bayansu.

Har zuciyata na ji rashin dad'in abinda ya faru.

Amma kuma na samu salamar zullimin tariyar da zan yi a yammacin yau, tunda ta lafiyar Inno ake yi tukun.

Ni kad'aice a gida har magariba Nene bata dawo ba.

An idar da sallar Isha sai ga Yaya Rabiu ya shigo.

Ya zauna a akan turmin da nake zaune.

Fuska babu walwala.

Murya babu amo ya ce "Anya kyauta taurarona da na ki ya had'u?

Ta yaya al'amari irin haka zai dinga gittowa da zarar za'a kai ki dakinki?

Jikina ya yi sanyi akan yadda ya yi maganar da take nuni yana da malamai da suke fad'a masa ililimin falaki a karkace.

Wai tauraronmu bai had'u ba.

Dariyarsa ta nemi kwace mini.

Amma nasa k'arfin tuwo na gintseta domin idan na yi sai ta zamo wani abin daban.

Tunda na sha ganin rikicinsu da Yaya Usman akan ya yi masa dariya.

Kawai zuba masa ido na yi.

Ina kallon sa cikin kaduwa ainun.

Ya tsargu ya ce "Ki kalle ni da kyau.

Na san kina mini kallon rainin ajawali ne.

Ni kuwa har zuciyata na karaya da ke.

Idan kinsan canka cakare haka kike zame mini.

Ta Yaya za'a ce ranar daurin aure jinya ta rafke ki, sannan an saka ranar tariya uwata ta fad'i ta samu karaya a hannu.

Sannan an zo har rumfata an sace mini buhun gawayi, ai kinsan ana alamta mini ba zan kwashe k'alau a cikin sabgarki ba".

Idon dai na cigaba da zura masa cike da madaukakin mamaki.

"Ki cigaba da bina da kallon izgili da sannu Ubangiji zai warware mini komai.

Amma yadda na shaida Annabi manzon Allah ne haka na shaida taurarinmu basu jitu ba.!

Ban tab'a jin labarin ango irina da ba'a tashi jarraba shi sai ranar aurensa da tariya.

Idan kuwa ansan kina da jinnul ashiq a fito a fad'a mini domin ina da bulalar bugun ko wanne irin makirin jinni ke har ma da mugayen insu da suke yiwa jinni sharri a gamsu da su".
Chapter 13 · 0% Book details