← Book details Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 16

Sashe 3

Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Yar'uwa maza ki shiga gruop din mu ga link din nan a kasa, domin mu gudu tare mu tsira tare.

Domin 'karin bayani ku tutubi wanan number
*08037930727*
https://chat.whatsapp.com/CSQ94ZeYnPJ26ppXhBnRII
Saura sati d'aya biki ya kawo mana leshina da atamfofi.

A falonsa ya tara mu.

Bisa al'adarsa baya mana tufafi iri d'aya.

Zai siyo ne kaloli hud'u masu kyau mabanbanta kaloli, sai dai masu daraja d'aya ma'ana kudinsu daya.

Ba zabi yake bayarwa na fara zaba ba, illah iyaka shine zai bawa kowacce wacce yake ganin ta dace da kalarta.

Amma idan aka dinka sai ace tawa tafi kyau ko ace ta Nadiya da sauran magaganganun gutsiri tsoma.

Domin matan gidan ga ni suke yi yafi karkata a kaina da Nadiya.

Ita kuwa Nadiya kullum maganarta tsorona yake ji.

Ni kuma sai na ga ita yake so yake kuma shakka.

Da na nutsu sai na gane har abada namiji ba zai fita daga zargi a wajen mata ba, matukar ya ajiyesu da yawa.

Da yake Nadiya ce mai girki na yi godiya na tashi da kayana na barsu a hade.

Na sani kuma k'orafi za su amayar domin kullum a cikin haka suke.

Na sauko da akwatina na ajiye na saka a ciki na goge k'urar da ya yi na rufe, na mayar, domin tuni na tanadi din'kunan da zan saka masu kyau da tsada.

Da yake da tazara a tsakanin gidansu da da nasa gidan amma ba mai tsayin ba.

Sai na roki ya bar ni idan na tafi juma'a da yamma an yi kamu na kwana domin mu yi asubancin d'ora abincin d'aurin aure.

Bai k'i ba, da yake hidimar tasa ce, da hidimar gidanmu ce babu nauyi zai murza gemu ya hana ni kwana.

Kai idan ya ga zirga zirga zata yi yawa hanawa yake yi babu jin nauyi bare kunya.

A hakan nake ta hakuri da baudadd'en halinsa har zuwa lokacin da komai zai zama tarihi kamar yadda ake yawan jaddada mini.

Tsakanina da Allah ko yanzu Yaya Rabi'u ya zama yadda nake son ya zama na ci goruba a hannnusa ba kwakwa ba.

Wani irin mutum ne murdad'de mai wahalar sha'anin gaske.

Kawai na tattara na cire damuwarsa ne a raina tunda ban ga alamun zamu rabu ba.

Auren namu ya zama tamkar na zobe.

Bai cika gane muhimmancina ba sai na yi masa tutsu.

Babban bak'in cikina idan ya ga wani ya tab'a ni ya hau zuba bala'i da sababi.

Amma shi ya yarda ya taka ni, ya muzanta ni a gaban kowa.

Yau da ace iya ni da shi yake yiwa da na ji sassauci to shi a gaban kowa ma yana iya yi mini tijara.

Ranar yini na zuba leshina na yi kyau tamkar mai shekaru ashirin.

Gabadaya sai walainiya nake yi cikin kwalliyar da na zuba babu karya.

Nadiya da suka iso ta ganni ai gabad'aya sai ta rikice domin tana ganin ita ce yafi kamata ta dinga kwalliyar da nake yi.

A dalilin tana ganin iyayena talakawa ne sannan ta sha gabana a wajen miji.

Nan da nan zuciyarta ta yi bak'i.

Ta yi kicin kicin tamkar ta rushe da kuka.

A ni kuwa ko a kaina sai kai komo nake yi, ina bawa bak'i abinci da abin sha.

Da yake ta zo da yayarta sai na mutuntata na kai abincin gabansu.

Ashe hakan ma laifi ne.

Ta kaikaice ta ce "Ni din ai ba bakuwa ba ce a gidan, domin ta wata fuskar ma na fiki dangantaka da su ke kawai shishshgi da shiga da fita kika kere ni".

Duk yadda maganar ta buge ni.

Sai na murmusa na ce "Tun kafin ayi kwaram aka yi kwandi Nadiya! domin dai Yaya Rabi'u ko ban ajiye masa komai ba ai tuni iyayenmu kinsan yan'uwan junane".

A hassale ta ce "Makwabtakar kawai?"
Na sake murmushi dan na tabbatar mata ta yi kad'an na nuna ta bata mini bare ta yi farinciki.

Na ce "kin manta Annabi ya ce." Ya yi zaton yadda Allah ya yi ta yi masa wasiyya akan sha'anin makoci za'a saukar da ayar da makoci zai gaji makocinsa saboda yadda Allah ya ce a girmamasu."
Ta dauke kai domin ta ji maganar Annabi bata da ja.

Can kuma ta yi tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "An mayar da mazaje saunoni, idan mace ta ga tana da kalar da zata ja hankalin maza ai komai ma sai ta yi don ta dinga samun kud'ad'e tana yin bajintar neman suna tare da saka suturu dan dai ayi fariya".

Ban san ya aka yi ba na juya tamkar zan fita sai kawai na d'auketa da mari irin wadda ake yiwa lakabi da 'barin makauniya.

Na kuma cakumeta da dukkan k'arfin da Ubangiji ya yi mini.

Da yake shammatar ta na yi, ta ji jiki a hannuna kafin ta fara ramawa, ganin hakan da yar'uwarta ta yi sai kawai ta shigar mata.

Basu kai ni k'asa ba amma dukkanmu mun ji jiki.

Domin na fasa mata gefen ido gabad'aya jini ya wanke mata fuska wanda hakan ne ya janyo hankali jama'a suka shigo dakin da muke ciki wanda na Inno ne.

Yar'uwarta kuma na naushe ta a hanci sai ha'bo take yi.

Mafi yawa da ba sa ra'ayina sai salati suke yi suna fad'in "Wannan idan ya zo da k'arar kwana ai sai ta yi kisa, ta had'a tima timan mata ta fitar musu da jini!

Inno ta shigo ta kalli yadda nake huci.

Ta kasa yi mini sababi yadda take yi da
amma kuma jikinta na rawa ta nufi Nadiya tana fad'in "Sannu Nadiya.

Sannu kin ji zuwa yanzu ya kamata ace kun saurara da wasu abubuwan.

Wai har yanzu bitar da ake ta faman yi muku babu sassauci bai shiga kunnuwanku ba?

Ai had'a kashi da kishiya ba abin da yake janyowa a gida sai tsiya.

Ku bari haka nan.

Ke ban da abin ki ma menene zai dame ki ne, kin riga da kin yi k'arfin da dole ke ce a gaba.

To ba na son irin haka".

Na zubawa Yaya ido ina kallonta.

Idan har na fahimci karatun tana jaddadawa Nadiya cewar "Itace da gida.

Dan kawai ta haifi maza hudu.

Ko waya tabbatar mata da hakan, ko sai yaushe za'a gane rayuwar nan gaibu ce ba wanda yasan da me gobe zata zo da shi sai Allah.

Zuciyata ta yi mini nauyi mai tsananin gaske.

Karon farko da na ji na shiga rudani da damuwa akan rashin haihuwa.

Na kasa daurewa hawaye masu nauyi suka tsinke mini.

Inno ta juyo a sanyaye ta ce "To kukan me kuma zaki yi tunda kin kasa daukar girmanki.

Yau ko wata ba'a yi ba, kika mini alkawarin ba zaki sake yarda ki yi dambe ba, ko me zasu yi miki kuwa.

Sai ga shi kin sake yi din a cikin dakina kuma.

Na yi mamaki Malama Kyauta".

Murya na rawa na ce "Yaya hak'urina ya kai geji akan caba mini magana da yarinyar nan take yi ne.

Bazan sake cewa ta bari ko na kai togaciya akan ta ba.

Amma tabbas ta sake kankanbar jifana da mummunar kalma jikinta zai fad'a mata, sai na illata ta, sai na sauke mata dukkan abin da take takama da shi."
Inno ta dauki ki salati mai tsananin gaske tare da ce wa "Sai kin illata ta kika ce Malama?"
Yar'uwar Nadiya da take faman goge hanci da tissue ta ce "Ke ce shaida Inno domin Wallahi ba zamu bar maganar nan ta tafi a banza ba sai hukuma ta shiga, tunda ta riga da tasan me ta taka."
Nadiya bata ce uffan ba illah kuka da take yi sosai tunda Inno ta shigo dakin.

Da fishi suka bar gidan bikin.

Yayin da nima suka rage mini walwalar da nake ciki.

A zuciyata kuma sai fargabar mai zai biyo baya nake yi idan na koma gida.

Nasan tana can tana gunshekin kuka tare da tsarawa mijinta karya da gaskiyar zance.

Tare da Nafisa muka koma gida bayan mun raka amarya dakinta.

Sai gulmar Nadiya take yi mini, ni kuwa na kame bakina domin nasan dan tasu ta hadosu ne akan mukulli amma ai ba yarda zan yi da ita ba, tunda tare suke yak'ata.

A k'ofar gida muka tarar da shi duk yadda hasken wutar lantarki ya haske fuskarsa amma babu annuri ko kad'an a tare da shi.

Na bude kofar falona ke nan, ya shigo a harzuke tamkar kububuwa.

Da tsananin huci ya ce "Allah ya yi wadaran halin ki na tsiya Kulsum!

A ce ba kya jin d'ar din keta mini alfarmata?

Ki kama matar da nake aure ki daka a cikin jama'a saboda ke ce wa?"
Ban ce kala ba, bare na tanka, illah iyaka ina ta maimaita RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIR"
Ganin ban kula shi ba, ya tuntuzura ya rik'e kafadata ya girgiza ni tare da ce wa "Mahaukaci na zama da zan yi magana ki yi mini diban karan mahaukaciya Kyauta?"
Nan ma ban kula shi ba.

Ya fusata ya ce "Tunda kin kore mini tauraruwata ki tabbatar ke ma baza ki ji dad'ina ba, ba dan abu d'aya da na fahimta a tare da ke ba, da na sallama ki na huta.

Ace mace kullum sai ta yi maka sanadin bacin rai!

Na fara gasgata Ilimin ki na son halaka ki, tunda da shi kike fakewa kike yi mini k'ulunboto ".

Na yi murmushin da babu nishadi na ce "Sannu a hankali dai dab'iunka kullum k'ara rikicewa suke yi.

Shikenan ni ba ni da darajar da zaka zauna ka ji abin da ya faru.

Sai kawai ka ji iya abin da aka fad'a maka.

Ka zo ka dirar mini saboda na zama karkatacciyar kuka?"
Ya ja tsaki tare da matsowa yana nuna ni da yatsa tamkar zai doke ni.

Yana fad'in "An ki aji ta bakin na ki!

Ai tunda Ilimin ki bai amfana miki komai ba, to kuwa zan dinga mu'amalantar ki irin yadda ake yiwa jahilan mata."
Na girgiza kai na ce "Dama can haka kake yi, rangwame na samu saboda wata ajandarka.

Jahilci kuwa kasan ba ni da shi.

Na yi boko, arabi kuwa sai dai na koyar da kai.
Chapter 3 · 0% Book details