← Book details Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 16

Sashe 4

Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ina gargadinka kada ka yi kuskuren tsole mini ido ko saka mini hannu da sunan duka."
Bak'in cikinsa ya ninku.

Ya shiga jifa da duk abin da hannunsa ya sauka tunda ya riga da yasan na kerewa dukansa tun rikicin da muka yi na k'arshe.

Na koma gefe na zauna ina kallonsa.

Cikin kwarmato ya ce "Na soke makarantar da kike zuwa, na kuma haramta miki wacce kike tara yara kina koya musu, tunda gidana ne, sannan ban ga ranar da Ilimin na ki ya yi mini ba".

Na kalle shi na yi murmushi mai harshen damo.

Ya ce "Ban isa ba ko Kulsum?

Na riga da na fahimci sana'ar da kike yi ta sanya kina mini kallon ban isa ba, ko kuma na gaza.

Wallahil azim zan baki mamaki, ba zan ce ki tafi ba, amma na rantse sai kin dandani bak'in ciki fiye da wadda kika k'unsan mini.

Kuma Baban titi kika jikawa aiki domin shine zai yi mini jelen bikon Maman Baffah".

Na sake murmushi na ce "Kasan zai iya tunkarar ko wanne mahaluki ne saboda shi din dattijon arziki ne, ka kuma sani baka aike shi bama yana zuwa maka bikon bare ka mutunta shi ka wakilta shi".

Ya rasa inda zai tsoma ransa da takaici.

Domin ya fahimci kullum rage tsoransa nake yi.

Ya yun'kura zai yi magana wayarsa ta hau kuwwa.

Ya duba sai da ya yi tsaki sannan ya amsa.

Muryar Nafisa na ji ta ce "Yau ma zaka raba dare ne a dakinta?"
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!

Wai ke wacce irin halitta ce mai tsananin zargi haka?"
Da karadi ta ce "Zargi ko kuwa gaskiya.

Kana tafe fankam fankam kamar namiji nan kuwa sahorami ne.

Gabadaya mace itace take jan akalarka amma ka k'i gane hakan kullum cikin buyagin iska kake yi."
Ya katse wayar ya fice yana fad'in"Magana bata mutu ba, na shiryawa faruwar komai wallahi.

Ba zai yiwu na zuba ido ki kore mini mace mai wuyar samu ba.

Kalilan din mata ne suke haifar mazaje reras iri ne mai kyau da ba'a wasa da su."
Karon farko da ya yi mini maganar mai kama da gorin haihuwa kai tsaye ba a sakaye ba.

Na kifa kaina a hannun kujera hawaye ya tsinke mini domin sosai maganar ta tab'a ni.

Wai sai yaushe Rabi'u zai mini adalci?

Sai yaushe zai yabe ni, sai yaushe zan ji dad'in da ake ta fad'a mini zan ji, zuwa yaushe ne zan ga d'an kaina?

Rashin tartibiyar amsa ya sake tsananta kukan da nake yi.

Na tab'a ganin haka, babu jin ba'asi sai kawai ka hau sababi dan kawai an tab'a maka uwar mazaje.

Kaina ya d'aure da al'amarinsa gabad'aya yana abubuwansa kamar bagidajen da ya rayu a jeji babu ko wanne Ilimin rayuwa tsabar gidadanci.

Na tabbatar ya kasa cewa na fita na bar masa gida ne saboda abin da ya yi imani na d'amfare da ni.

Abin mamaki 'bacin ran da nake ciki bai yi tasirin da ya hana ni rintsawa ba.

Domin ina idar da sallar shafai da wutiri barci mai nauyi ya yi awon gaba da ni.

Sai daf da ketowar alfijir na farka.

Ina idar da asuba ma na sake komawa na kuma fahimci jikina ne ya yi tsami a dalilin zirgar da na sha, da hidimar biki, ga kuma y'ar k'ashin da muka gwabza.

Ko da na farka ruwa na dumama na yi wanka na gasa jikina, na karya sannan na hadiyi Panadol.

Ko ta kan ta'adin da ya yi mini ban bi ba.

Sai dai me a zabure na farka na ganshi yana huci.

Take na fahimci shine ya tashe ni.

A zafafe ya ce "Barci ma kike yi ko?

Na zuba masa ido gabad'aya ya jirkice ya koma azababben mutum.

Murya babu amo na ce "Yaya Rabi'u ina kwana?"
Tamkar ya rufe ni da duka tsabar tunzura ya ce "Kyauta na rantse miki baki isa ki tayar da zaune tsaye ke kuma ki zauna k'alau ba.

Ki tashi ki tafi gidansu Nadiya ki bata hak'uri, ki dawo mini da ita".

Na yi murmushi na ce ka "fasa tura tsohon nawa ne?"
"Kulsumu ki shiga taitayinki, ba fa wasa nake yi da ke ba".

Na dara kad'an na ce "Hak'uri kam bazan bata ba.

Da ka biyo ta lallama mai zai hana na je bikon kishiya tunda ka gamsu ina da matsayi da kamalar da zan je biko a madadinka".

Ya ja tsaki ya kasa magana.

Can ya ce "Ki tashi ki je ki yiwa yaran wanka, tunda kin kori uwarsu."
Na ce "Ubansu ai yana nan.

Ga kuma sauran matanka masu y'aya' su ya kamata su had'a da su, tunda albarkacin kaza kadangare ke shan ruwa."
"Tabdi ashe kuwa zan ture komai na miki rashin mutuncin da ba ki yi zaton zan miki irinsa ba Kyuata!

Ya fad'a da fishi ainun.

Na ce "Ba abin da zaka yi mini ya ba ni mamaki domin na tabbatar maimaine akan na baya."
Ya rasa yadda zai yi domin yasan a yanzu na wuce dukansa.

Ba kuma zai iya jarumtar fitar da ni a gidansa ba, saboda wata fahimtar da ya yi ammana da ita.

PAID BOOK
#500via 7084653262 Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank.
*GARKUWAR MATA*
*BINTA ABBALE*
[12/12, 9:46 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
*M.W.A.*
*ADVERT*
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/JrVGCbG7R8SFurApPbPilB
*SAMIES KITCHEN*
The Best Chartering Service
*KANO STATE: NO4 ZOOROAD HOUSING ESTATE*
*Jama'a Samies kitchen wurin fita kunya ne da kece raini.

Wuri ne ingantace da ya amsa sunansa domin sharewa ma'abota karamci hawaye a yayin da wata hidima ta same su.

Bari na jaddada muku SAMIES KITCHEN Ya samu sheda da lambar yabo gurin cika alkawari da karrama
jama'a.

Kada na cika ku da surutu bari na tafi kai tsaye domin sanar daku ainihin abinda ya sa nake kwad'aita muku 'kulla alaka da su.

Wato SAMIES KITCHEN sun 'kware wajan shirya girke girke na gida dana waje.

Sun yi shura wurin 'karbar order daga kowane sassa a fad'in Najeria.

Suna yin abincin biki, abincin suna, abinci taro, abincin saukar al'kur'ani, order domin yin Birthday.

Sun gwanance sosai wurin yin cima iri-iri da kayan ma'kulashe duk domin fita kunyar abokan hurd'arsu.

Sannan ba su tsaya iya nan ba suna hada-hadar sayar da manya manyan leces 'kananu da manya kowane irin na'ui.

Suna bud'e dilolin leces irin namu na gida (mama ta mutu) kala daban daban.

Ana samun kayansu da inganci tare da farashi mai sau'ki.

Domin neman karin bayani sai a tuntubi wannan lambobin.*
*08173037544 ko 07044417448*
5&6
Kansa ya girgiza ya kama hanyar fita yana sa'be babbar riga sai kace sabon limami.

Na yun'kura na tashi na fita zuciyata a 'kuntacce na shiga kicin domin lalubar abinda zan sa a bakina.

Kicin din kace-kace babu gyara kudaje sai tashi suke yi ina kuma jin muryar Jummai mai yi mana wanke-wanken da shara a gurin Nafisa suna hira da dariya.

Raina ne ya 'baci ainun domin na san tabbas da Yaya Rabi'u ya lura da k'azantar kicin din a kaina zai sauke bala'i duk da ya san ba ni nake da alhakin hakan ba, zai ce ai ni ce babba amanar gidansa a hannuna take.

Kofar Nafisan na nufa na iske su a zaune durshen suna hira.

Baffah da 'yan'uwansa suna zaune du'kun-du'kun da d'aud'a Nafisa ta yi wa Yaranta wanka tana shafa musu mai.

Babu fara a fuskata muka gaisa sama-sama, na ce." Jummai kin ga kicin kuwa 'kudaje sai bi sukeyi kwanuka duk sun bushe kina zaune kina hira ga sharar tsakargida da gate duk ba ki yi balle ki wanke band'ukuna, lokacin nan fa takaitacce ne, har yaushe ki ka kammala wannan aikin ki ka d'orawa Yara abincin rana, kuma kin riga kin san islamiyarsu ba su da wasa gaskiya Jummai ki canza idan ba haka ba zan sanar da maigidan halin da ake ciki domin wannan shine karo na uku."
Cikin ya'ke ta ce." Yi ha'kuri Uwar dakina bisimillahi bari na tashi na yi aikin da yake gabana.

Nafisa ta dakatar da ita babu fara'a a fuskarta ta ce." Wai Ummi girki ki ne ko nawa da za ki shigar mini hurumi?"
Jim na yi ina kallonta kafin na ce." Girki ki ne amma ba sai na yi miki 'karin bayani ba kin san komai.

Sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa" Ni fa ki daina yi mini katsaladan ina ganin mutuncinki, ranar girkinki bana sa miki Ido saboda haka babu ruwanki Jummai dai ni na kira ta muna magana kuma ba ke ki ke biyanta albashi ba."
Murmushin takaici na yi na ce." Sai ki fad'awa Mijinki idan ya ce na zare hannuna daga kanku dama haka na fi bu'kata."
Ta bugi kirji tana fad'in." Ni fa ba Nadiya ba ce wallahi, kin san ni sarai idan ki ka yi mini ba zan saurara miki ba, ya kamata ki fahimci wannan, zaman aure ki ke yi, zaman aure nake yi, na lura kawaicin da nake yi miki ba kya gani amma idan ba rashin mutuncin ba ina ruwanki da shiga abinda bai shafe ki ba."
Tsaki na ja na kalli Baffah dake zaune yana had'awa 'kannansa jirgin Leda na ce." Ku ta shi Baffah mu je ayi wanka."
Da sauri ta ce." A banza dama ai babban burinki ki kore mu daga gidan, kin kori uwarsa kina kinibibi, ai wallahi Kulsumu tuntuni na dawo daga rakiyarki, ki juya mana miji sannan ki juya mu to ni wallahi ba ki isa ba, kin yi tsararo!

Kuma zama daram a gidan Rabi'u."
Ban tanka mata ba saboda ganin yadda Yaran sukayi tsit! suna kallonmu, kawai na yi gaba ina fad'in" Baffah ku biyo bayana ayi wanka, ke kuma Jummai wata'kila shan ruwanki ne ya 'kare a gidan tunda gulma da munafurci ki ka zo yi."
Ina jin hargowarta tana fad'in." Ba ki isa ba wallahi Jummai zama daram dam! sai ke ki fita ki bar mata gidan.
Chapter 4 · 0% Book details