Sashe 2
Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi wannan da a ta'ba shi a gidan gwara an yi ya'ki, domin ko Uwarsa ce ta yi masa hukunci muddin Yana gidan suna kwasar 'yan kallo.
Kuma nan da can ba ya aikuwa hatta na uwarsa ma baya zuwa shiyasa bana damuwa.
Walida ce Allah ya had'a jinina da ita.
Duk yadda uwarsu take hanasu zuwa wajena sai ta faki ido ta zo mini.
Ni kuwa bana gajiya da mika mata komai nake da shi mussaman da yake Ina sana'ar kayan Kwalam da makulashe.
Domin ina yin albushir na bayar akan sari, ina yin iloka a biyani lada, ina yin kuma ta siyarwa, sai dai ni da yawa nake yi sai azo a sara na bi karamar riba na karbi kudina take.
Sannu a hankali na k'ara da tuwon madara da y'ar kullisuwa.
Dan haka kullum bana rabuwa da kayan dad'i a dakina.
A dalilin hakan sai na yi y'aya' da yawa.
Ko na gidan basu zo ba, to kuwa na makwabta yini suke suna yi mini sintiri.
Domin duk sadda zasu tafi islamiya sai sun shigo sun karbi alawar madara ko albishir.
Hakan ta sake jawo mini iyayensu.
Dan haka ban saka rashin haihuwa a raina ba domin na yi imani ba itace karshen niima ba.
A duk sadda aka guma mini azanci ko bak'in ciki akan yara.
Bana zama na yi kuka domin idan na tuna Nana Aisha sai ta zame mini madubin da take wanke dukkan kumburin da zuciyata ke yi.
Na riga na yi imani da haihuwa dole ce, ko kuma ita ce cikar niima kad'ai da Annabi ya rokawa Aisha tunda gabadaya malamai basu samu sabanin akan itace ta yi rinjaye a zuciyarsa ba.
Hakan bai zame mata nakasa ba, sai ya zame mata kususiya ce mai girma a wajenta.
Ta rungumi k'addara ta yi rayuwa cikin walwala, ta yi ilimi ta kuma yad'a shi wanda har zuwa yau ana cin moriyarsa.
Dama amfanin d'a ai ya cigaba da ayyukan alheri da kake yi da kuma yi maka addu'a bayan ka kwanta dama.
Idan hakan bata samu ba, sai musulunci addinin adalci ya ce Idan ka yi sa'a ka yiwa kanka sadaka mai gudana ko baka nan ladan zai bika har zuwa sadda abin zai katse.
Bayan haka idan ka yiwa mutane adalci, ka kyautata musu, ka ja yara k'ananu da marayu a jikinka ka tallafa musu, Ubangiji kuwa ba zai barka ka koka idan tsufa ya zo maka a dalilin rashin y'aya'ba.
Tabbas ne sai ya turo maka wadanda zasu yi maka abubuwan alfarma na kyautatawa tamkar y'aya'n da ka haifa ko ma fiye da hakan.
Wadannan nasiha da tunatarwar da mahaifina yake yawan yi mini ya sanya na cire bacin rai akan rashin haihuwa, na rungumi y'aya'n gidan da na makwbta da na yan'uwana nake yi musu iya abin da zan iya tare da fatan Ubangiji ya karba.
Na kuma gamsu domin babu damuwa ko kad'an a raina, kullum kuma k'ara samun jama'a nake yi a kusa da kuma nesa.
Tunda ina da islamiyar yara da nake koyar musu a duk ranakun lahamis da juma'a a cikin gidan nake da kebebben waje dan gudanar da karatun kullum kuma makarantan cika take yi, tunda mafi yawa duk yaran da suke zuwa mini ne ma'ana ba makwabtaka.
Ni kuma ina zuwa makarantar asabar da lahadi domin dai na cigaba da daukar ilimin addin da kuma yad'a shi a tsakanin al'umma.
Wani abin mamaki a gidan namu ni kad'ai ce bani da kowa sai Allah sai miji.
Amma na damesu rufin asirin da nake ciki ya zama abin tattaunawa.
Makarantar da nake koyar da yaran a cikin gidana tana matukar ci musu tuwo a k'warya.
Hatta shi kansa mijin namu ya zama abin zargi a wajensu.
Alhali shima sa'i sa'i sai ya yi barazanar zai dakatar da makarantar ana cika masa gida da hayaniya.
Kawai ya ga abin ya girmama ne shiyasa ya yi mukus.
Babban abin da na rik'e kuwa addu'a ne, sannan ban tab'a ayyana na cutar da su ba.
Amma mafi yawa kullum sai sun yi mini sanadin bacin rai.
Misali zan aiki Hajjaju ta ki zuwa, karshe ta bige da yi mini kunkuni amma uwarta ba zata tsawatar ba, idan na hassala na tsawatar a tunanina taya tarbiya na yi sai ya zame mini kalubale.
Dan haka sai na hak'ura da aikenta.
Sai kuma sakayya ta shigo domin sai ta koma take yiwa uwarma babu yadda za'a yi ta sarrafata, uban kawai take shakka.
A maimakon hakan ya zama izna ga sauran matan kowacce ta shiga a hankalinta.
Ina sai suka sake nausawa jeji.
Kowacce akan d'anta babu s'auki.
Wata bata isa ta mori d'an wata ba.
Mata! mata muna da muguntar da take cin kanmu da kanmu Allah ya shiryemu kawai.
Ana cikin haka aka fara auren kanwarsa wacce da ga ita sai autansu.
Shine ya yi komai.
Kuma ni ya damkawa ragamar siyayya da gudanar da komai.
Dama kuma tun farko ya fara yi mini hakan akan y'aya'nsa, da abu ya k'i na ce ya d'ora ko wacce uwa akan d'anta ni ya bar ni Ubangiji ma da yake sona fiye da kowa hakan ya bar ni, ban kuma d'auki hakan a matsayin tawaya ba.
Alhamdulillah da dukkan jarabawa.
Kullum ba ni da sukuni ina tafe tsakanin gidansu da nawa gidan da kuma kasuwa.
Zuwa yanzu na fara samun sassauci da ahalinsa tunda halin kowa ya bayyana a tsakaninmu da abokan zamana.
Da ace zan biya sharrin zuciya da na shaidan da ko kulasu bazan yi ba.
Tunda ba abin da ban ga ni ba a shekarun baya.
A fili na furta wnada Ubangiji ya masa baiwar hak'uri da hadiye da bacin rai ya tara masa dukkan alherin duniya.
Fahimtar da na yi hak'uri ne yasa na cigaba, shine yasa ban zama yadda ake son na zama wato na tozarta na zama Allah sarki.
Sai na dimanci addu'ar Fasbir sabaran Jamila.
Nake yawaita kula'uzai da li'ilafi, domin na gamsu dafa'i ne daga dukkan wani kaidin mai kaidi.
Ta gidan kanwarsa ta uku na biya muka tafi kasuwar tare.
Muna tafe muna hira tana jaddada mini abin da yake cikinta nawa ne ko ta mutu.
Tunda na fad'a mata na ki karban y'aya'n yan'uwana ne saboda yadda gidan namu yake cike da rikitarikita da rashin tsarin tarbiya a wajen matan gidan.
Dan haka bazan yarda na dauko d'a ayi ta tashin hankali da musgunawaa gare ni tare da gori mai ciwo ba.
Ta kuwa ce "ai idan ni na baki babu mai tsinin bakin da zai tayar miki da hankali.
Ni a k'asan raina ma ba so nake yi ba.
Bana damuwa tunda na riga na roki Ubangiji kada ya jarrabe ni da butulce nasa dan ban haihu ba.
Na gode masa da ya sanya ni cikin bayinsa musulmai, ya ba ni lafiya, ya kuma bude mini k'ofofin alherin da zan yi ta neman lahira, da kuma yiwa mutane ihisanin da zan zama ni din ta kowa ce.
"Alhamdulillah" bana gajiya da furta hakan.
Kafin mu kammala siyayyar tuni na yi dinkunan da zan yi hidimar biki tare da bayar da gudunmawata mai kauri.
Addu'a kan addu'a na sha a wajen mahaifiyarsu wadda suke kira da Inno
Amaryar kuwa da tun tana k'arama y'ar dakina ce, kayan gyara takanas na sanya Surayya HALIN YAU ta hada mata.
Saiwowin sanyin da take siyarwa kyaunsu aziman ne.
Bayan haka na shaida sauran kayan ma babu algus.
Daga ni sai ita muka yi abinmu ba'a sani ba.
Saiwowin dahuwar kaza kuwa da yake mutum biyu zasu yi amfani tare na siya na dafa mana kazar nima na sabuntawa d'an sababin nawa
. *08032773332.*
A yanzu tauraruwata ce take haskawa a wajenta.
Har wanda bai sanni ba, zai yi zaton bansan bak'in ciki ko musgunawar uwar miji ba.
Amma da yake kowa ya yi hak'uri za'a yi da shi, sannu a hankali ta gane nice mai rangwamen tsiya a cikin surukanta gabadaya.
Tun ranar jere na fahimci Nadiya na nemana da sababi mai girma, material din da an sanya na Umm Nihla mazauniyar Malaysia ya yi matukar mintsinin ta.
Ni kuma ban ga abin damuwa ba da ta tambaye ni sai na bata contact din kai tsaye ta zabi kalar da take so kafatalin kishiyoyina ba wadda take da takamarta, ba wadda take son fato ni irinta.
Tabbas mun goga da Nafisa domin ita da aka aurota ta zo ne da gillin ita ce zata haifi yara magadan gida, sannan kuma ta zo da niyyar ta fitar da ni a gidan ta hanyar cusa mini takaici da bak'in ciki.
Tabbas na yi kuka, na shiga garari akan aurenta, haka tsananin da na fuskanta a sadda ta samu ciki mai yawa ne, ba daga shi ba, ba daga danginsa ba.
Sai dai tafiyar bata yi nisa ba alkadarinta ya karye tunda mata ta haifa ba maza ba sharri kuma dama d'an aike ne.
Bata tashi ganin gayya ba sai da ya auro Nadiya.
Bansan kuma dalilin da yasa nafi tsayawa Nadiya a rai fiye da Nafisa ba.
Ta damu da ni.
Ana cewa da ta farko da ta uku suke had'a kai su bar ta biyu to ni kam ban samu wannan tagomashin ba.
Izzar Nadiya ta sake kasaita ne da ta ga ta haifi maza a jere.
Sai take ganin zata take kowa tunda ita din d'iyar masu kumbar susa ce, sannan tana ganin itace mai kyallin goshi a wajen miji da danginsa hatta Inno mahaifiyarsa rarrashin zuciyarta take yi.
Matan gidan masu haihuwa Nafisa da Aliya basu shak'e mata wuyan da ni na shake mata ba, na rasa dalilin wannan masifar da take yi da ni.
PAID BOOK
#500via 7084653262 Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank.
A tura sheda 07084653262.
*GARKUWAR MATA*
*BINTA ABBALE*
[12/11, 9:30 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
*M.W.A*
52U/HARVERT NETWORKING BUSINESS
*ALHERI NE
Ina masu sha'awar shiga shahararren kasuwancin nan wato 52U basu da hali? ga dama ta samu SZARIA tazo maku da sabon tsari domin taimakawa marasa 'karfi, wato TEAM WORK. da kud'in ki 'kalilin zaki samu abunda zaki taimaki kanki da 'ya'yanki.
Tsarkakken
kasuwanci ne mai ingantacin da babu asara a cikinsa sai riba mai gwa'bi.