Sashe 1
Ba A Boran Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry
WordDocument
0Table
Data
[12/10, 8:46 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE
*M.W.A*
Yabo da godiya su tabbata ga Ubangijin talikai.
Tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba Annabi Muhammadu S.A.W.
Wannan littafi ban yi shi don wani ko wata ba.
Kama daga sunaye gari kamanceceniya.
Idan an yi katari da hakan arashi ne.
Ban yarda a yi amfani da labarin nan ta kowace irin siga ba, idan aka aikata hakan ba ni da masaniya Allah Ya saka mini.
*SADAUKARWA NE GA:*
*NANAH ABDUL*
*TUKWUCI NE GA:*
*SURAYYA DEE*
( Halin Yau)
*GODIYA TA MUSSAMAN GA:*
Momi Fatima Musa
Hajiya Babbah
Autar manya
Halima wada kura
Prof Asabe Kabir
Halimatu
Amarah
Basira Hamza
Usaina Ibrahim
Zainab Yola
Zainab
Fadima Sani
Hairi
Sakina Jumpum
Rauda Abubakar
Zainab Salisu Umar
Ummi Labaran
Maman Rahama
Ummu Ulfat
Rabbatul-Bait
Rajkumari
Maman Janan
Fatima Gwaram
Asiya Mu'azu.
*KANO STATE*
*UNGUWAR KURAWA*
*Shimfid'a*
1&2
"Kyauta kina ina? fito nan, wallahi yau a gaban kowa za'a yi ta ta k'are na gaji da wannan halin na ki".
Zuciyata ta harba tare da zullumin yau kuma mai aka shiryo mini ni Ummu Kulsumu"
Na fita ina hirji.
Gabadaya matan gidan suna tsaye sun yi cirko cirko tamkar zakaru.
Ya kausasa harshe yana cewa "Kyauta wana d'amkawa ragamar kulawa da sito din abinci?" Murya babu amo na ce ni ce amma me ya fa.....
Ya daga hannu a zafafe yana cewa " Sa aya kawai malama, ta ya ya za'a ce mini babu man gyad'a da indomi a gidan nan?"
Zuciyata ta buga da tsananin gaske.
Domin ni kaina na ka'du da furucinsa.
Idan lissafina daidai ne to
kuwa yau kwanaki goma kacal da bude jarkar mai 25 Lita.
Taliyar yara kuwa yau kwanaki uku da ya shigo da katon biyu.
Sau daya kacal na dafa domin kuwa su ban ga sun dafa ba ma.
Amma ace yau babu.
Lallai dole ya yi fad'a ban ga laifinsa ba a yanda rayuwar nan ta yi tsanani.
A sanyaye na ce "Allah ya huci zuciyarka Yaya amma wallahi ban san komai ba akan wannan sha'anin.
Kuma Dole idan iyalai suka yi yawa sai an yi hak'uri saboda hidima tana k'aruwa za'a gyara In sha Allah"
Ya ja tsaki ya ce "Kina nufin dole na yi hakuri na zuba ido kina neman yi mini sanadin shiga ba'kin talauci?
Nawa ake siyar da kwalbar mai ne bare jarka? wato bak'in cikin da ake cewa kina yi ne yake neman fitowa muraran ko?"
Nan da nan zuciyata ta karye hawaye ya cika idona murya na rawa na ce "Yaya da bakinka kake jifana da yi maka bak'in ciki a cikin gidanka?"
Maimakon ya sassauta sai kuwa ya sake fusata ya ce "Ba iya bakina kad'ai nake magana ba, har da zuciyata.
Domin mugunta da bak'in ciki ya sanya kike kwashe mini kayan abinci".
Kuka ya ke ce mini.
Na kasa cewa uffan domin zuciyata ta yi nauyi ainun!
To na kwashe kayan abinci na kai su ina?
Ya ja tsaki ya ce "Kukan ki ya k'are Kulsumu je ki dauko mini mukullin sito din hannun ki.
Na yi iyakacin kokarina akan na baki girmanki amma abin ya faskara dan haka idan girkinki ya zo sai ki karba a hannun Nadiya."
Kafin na yi magana.
Nafisa ta yi fit ta ce "Ai kuwa idan kana nufin ita zaka bawa mukullin sai dai a raba girki amma tabbas ban yarda da alwalarta ba bare ta ja mu jam'i."
Aliya da ita ce amarya ta ce "Ai kuwa dai ni ma ban yarda ba.
Kukana ya tsaya cak.
A dalilin na fahimci dukkansu sun had'a kai ne dan su kai ni k'asa.
amma kuma da za'a shugabantar da wata a cikinsu ba ni ba, to zasu koma rikici da junansu.
Na yi k'asa da kaina.
Ina jin sauki da jarumta na ratsa ni.
Wato duk da ni kad'aice ban haihu ba a gidan ba ni da ko kaza amma na dame su, na yi musu karantsaye a zukatansu.
Duk wadda ta kwaso makircinta a kaina zata sauke shi.
Abin da yake d'aure mini kai shine; ba ga ni suka yi yana fifita ni ko yana tausaya mini ba.
Asalima wani cin kashin suna yi mini ne dan sun ga yana yi mini kai tsaye babu d'ar.
Nafisa ce kawai take sassauta mini tare da mutuntanta ni itama kuma akwai dalilin hakan ba wai tana yi ne dan na kai ta yi mini ba. ta yi ne saboda yadda nake cire Ido akan yaranta mussaman hajjaju dukda yarinyar bata mutuntani na kan saya mata kayan ado da kwalliya ganin ta fara girma idan na fita duk abinda na gani na mata sai na sayo mata, wannan dalilin ne kadai ya sa take daga mini kafa, amma duk lokacin da ta so rashin mutuncinta mancewa take yi da komai Nafisa fitinnaniya ce sosai domin duk rabin rigimar da take faruwa a gidan itace take haddasawa dan dai kawai maigidan a tsaye yake shiyasa take shakkarsa.
Maganarsa ta katse mini tunanin.
Domin a kausase ya ce "Nafisa ki yi duk abin da kike ganin zaki yi, ita zan bawa idan kuwa kin ga ba zaki bi hakan ba kina iya tafiya ai ba daure ki na yi ba."
Yana rufe baki ta fashe da kuka ta ce "Akan me zaka dinga nuna banbanci tunda ka bawa Kulsum ka ga bata yi maka yadda kake so ba, ai yanzu ni ce nake bin ta, ba sai ka ba ni ba, amma ka tsallake ni ka tafi kan wadda ta zo daga baya dan kawai ita kana jin tsoronta, saboda babanta maigidanka ne!.
Ya harzuka ainun ya ce "Ki tsarkake bakin ki Nafisa domin wallahi zaki koma gida, kin san na ce miki ba zan sake daukar iyashegen ki ba.
Tabbas ba ki yi karya ba ubanta maigidana ne kamar yadda nake maigidan yayunki guda biyu."
Ta sake rushewa da kuka fiye da na farko.
Nadiya ta zabgata mata harara tana cije bakinta ta ce." Nafisa ki iya bakinki fa kada mu kwashi 'yan kallo a wurin nan, wace irin magance wannan ko ubana abokin wasanki ne?"
Ya daka musu tsawa Yana gyara zaman babbar rigar jikansa Ya ce." Ku ka kuskura ku kayi cacar baki a gabana ba zamu wanye lafiya ba." Sai kowacce ta yi shiru.
Ni dai Allah Allah nake yi ya sallame ni na koma dakina.
Ko kad'an ban ji ciwon karbe mukullin rumbun abinci da ya yi a hannun ba.
Asalima sauki zan samu tare da addu'ar y'ar manuniya ta nuna kanta.
Ya Kalli Aliya ya ce." Saboda Nafisa ta ce ba ta yarda ba ke ma ba ki yarda ba ko?
To zan ga wanda zai rusa mini tsarin gidana a cikinku."
Ya ja tsaki ya wuce yana banbamin bacin rai.
Wanda har cikin zuciyata nima na ji takaicin yadda aka kwashe kayan abincin.
Ina matukar kaduwa da bak'ak'en taadodin da matan yau suke aikatawa da sunan kishi.
Ban da haka ka samu mijin da zai ajiye maka abinci ka diba babu fargabar awo amma sabida son sai an yi makirci da mugunta sai a kwashe dan kawai ana son a kai wata k'asa.
Sannan ban da abinsu ni da suke yiwa wannan makircin dan kawai suna kallon bani mukullin wata alfarma ce, bakina ne kad'ai, su kuwa fa?
Nafisa da ita ce amaryar da ya fara yi mini yaranta hudu a yanzu.
Babbar shekrarta sha hudu.
Wacce sunan mahaifiyarsa ta ci muna kiranta Hajjaju.
Sai mai biye mata sunan uwar Nafin ce Aisha sai muke kiranta da Walida.
Tun kuma daga lokacin gwamnatin Nafi ta fara sanyi a wajensa a dalilin ba mata yake so a haifa masa ba.
Ni ban haihu ba, sanadin haka ne k'arin auren.
Ya samu haihuwar kuma sai kuma jinsin da ake haifa masa basu yafi so ba.
Dan Adam da butulci da izgili yake.
Ni da zan bada komai dana mallaka na haifi macen da na yi.
A dalilin haka ya auro Nadiya wacce y'ar maigidansa ne.
Nadiya kyakkwar yarinya ce ta gaske.
Sannan tana zuwa ta haifo masa namijin da yake muradi.
Shekararta bakwai yanzu a gidan yaranta hudu duk maza.
Yayin da Nafisa ma ta sake haifar namiji Khalid a huzaifa yaranta hudu kenan biyu maza biyu mata Ga Nadiya da take da Baffa sunan mahaifinta, Sadik, Umar Usman.
Wadannan dalilan ya sanya da wahala ya yiwa Nadiya wulakanci a gaban jama'a sai dai ko a dakinta tunda ta sha yin yaji ana dawo da ita.
Amma dai yadda ake ga ni tafi mu kyallin goshin a wajensa.
Y'ar babban gida kuma uwar mazaje reras.
Sai Amarya Aliya da take da yara biyu Aliyu da mai sunana Ummu Kulsum.
Tamkar kazar da k'wai ya fashewa haka na ja sayyadata zuwa dakina.
Na fadi tamkar wadda aka ingiza ni kan kujerar falon.
Tsawon lokaci na zama mutum mutumi.
Ba abin da nake yi sai nazarin rayuwa.
Wai menene riba ne idan mace ta sace kayan abinci sannan ta kitsawa miji da mutanan gidan watabce daban ba ita ba?
A da na dauka sai tsofaffin mata ne suke irin wannan makircin ashe yaran mata ma sun iya shirya kaidi.
Ko da yake ai ance kowacce mace da irin nata makircin.
Hawaye ya balle mini a dalilin yadda kullum zaman gidan yake sake tsananta mini.
Shi ya yi, matansa su yi, haka yaransa su yi mini.
A yadda nake gani barin gidan shine yafi alheri a gare ni, tunda Wanda ya ajiye ni ba wani muhimmancina yake ga ni ba.
Yana gigicewa ne idan ya kuntuka mini takaici na gudu gidanmu hankalinsa yana tashi ya dinga tura jama'a har sai an dawo da ni.
Mafi yawa dangina da makusantana gani suke yi hak'urina ne ya yi karanci a dalilin ban samu haihuwa ba.
Amma ai ko dakina aka shigo aka yadda yake a shirye da kayan alatu an san yana sona.
Ni Kuma ni nasan me nake fuskanta a hannunsa.
Ba abu mai wahala ba ne ya yi mini tijara akan y'aya'nsa tunda shi mutum ne mara kawaici da rashin ha'kuri.
Yanzu duk rashin kunyar da Hajajju take yi mini da zan d'an bugeta sai kowa ya ji bare kuma ace Baffah ne shalele.