← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_19/20...._
Sannu ahankali shak’uwa da kusanci sukacigaba da shiga tsakanin mashkur da bunayya, har yanxu baidaina kula daita ba dakuma yimata yan nasihohi akan takare martabarta ta y’a mace, Alhmdllh kuma tanajin maganarsa sosai sbd ayanzu jinsa take kamar d’an uwanta najini.

Idan baiganta wajen karatuba kokuma masjid kokuma restaurant tosaiya nemi hamdallah yatambayeta ina take, nan hamdallah zata fadamasa, haka itama idan tai kwana biyu bata gansaba dakanta take zowa nemansa agun abokanansa jalal da majnun.

Suna acikin wannan yanayin har suka kammala zana jarabawa sukai Hutu.

Kokad’an bunayya bataji dadin hutun ba sbd yanda tafara shak’uwa da sabon brother d’inta.

Bata ankaraba damuwar rashin ganinsa kwana biyu tafara kusantota, saitaji batasan zama acikin mutane any time tana d’aki itakada’ai tana tinanin brother d’inta, gashi tai ragon tinani batada ko number dinsa hakama dik abokanansa bawanda takeda number dinshi bare takira tace a turomata.

Haka taita fama da kewarsa dakuma damuwarta har momy ta fahimci tanada damuwa,amma data tambayeta saitace bakomai gajiya ce kawai ke damunta, saidai momy kam bata yardaba sbd taga tarin canji agun bunayya.

Yau takasance Monday itakad’aice a gida momy da dady dik sunfita office,yanzu tariga tasaba da hayaniya sam bata iya zama itakad’ai,danhaka tashirya tadauki motarta tafice gidansu hajiyar dady, acan tawuni sai dare sannan tadawo.

Haka tadingayi kullum har tai sati daya da dawowa school,kuma tanajin dadin zowanta sbd koba komai tana rage kad’aici da tinane tinanen brother d’inta mashkur.

Yau takasance Saturday danhaka su dady nagida kowama yana gida tinda weekend ne, dady da ya Amir suna waje bakin lambu sunashan iska,itakuma bunayya da momy suna cikin gida a parlor hadimai kuma kowanne yana aikinsa.

Zaune kawai take amma gaba d’aya ruhunta da zuciyarta basa a gangar jikinta,ta lula tai nisa sosai acikin duniyar tinanin MASHKUR, itafa sai yanzuma take hango tsintsar kyanda yakeda harma take ganin dik kyanda ake fadar tanadashi gani take kamar mashkur yafita, komai nasa is accurate from face to his foot, mashkur irinsane yammata ke mafalkin samu arayuwarsu, kai auren irinsama fitinane wlh sbd yammata bazasu barka kai yanda kakeso dashiba.
Wani dan murmushi tai wanda batamasan tayisaba lkcnda tatino da bakinsa mai d’aukeda pink lips sadda tayanke da wuka tayakaita clinic ana dressing din wajen tana kuka shikuma yanamata wasa yana tsokanarta dikdan tabari ayi dressing din agama.

Itakanta tasan yana matuk’ar shagwab’ata tamkar yayanta na gaskiya.

Tanacikin tinanin batasan momy nakirantaba har saida ta tab’ata sannan tai firgigit tadawo hayyacinta, momy tace “what’s wrong with u bunayya....are u okay, me kike tinanine haka bunayya inata kiranki amma bamakya jina” murmushi tai tareda rufe fuskarta cikin yanayin kunya,karo nafarko kenan data farajin kunyar mahaifiyar tata tace “am okay mom...bakomai” momy ta tab’e baki tareda fadin “idan tai wari maji” saitai dariya momy tace.

“Kije dadyn ki yana nemanki a waje” ohk tafada tareda mik’ewa tafice.

Ahankali take tafiya izowa lambu, sanye take da wandan jeans blue iya guiwa da riga mai gajeren hanu pink, kanta yar hulace akai.

Tindaga nesa tahango mutum durk’ushe a kusa da dady suna magana saidai bata hango fuskarsaba bayansa ne kawai take hangowa.
Tana isa saitace “dady...” saiya kalleta cikin murmushi yace “mashkur ne yazo yanzu” saida gabanta yafad’i dataji sunan mashkur.

A fili tamaimaita mashkur cikin tsintsar mamaki, mik’ewa yai tsaye yana dan murmushi,waro dara daran idanuwanta tai cikin tsintsar mamaki tareda rufe bakinta lkcnda sukai ido biyu.

Dakyar taiya cemasa “Mashkur sannu da zowa” sbd tsananin mamaki, cikin murmushi yace “yawwa Fatima, yah kike” tace “lfy klw “ dady ya mik’ewa a tsaye suka fice izowa cikin gida itakowa dagudu tafice bedroom d’inta tana cewa momynta “momy ga mashkur nan yazo”.

Itama momy mamaki tai sosai tace “mashkur fa, wannan zowan bazata fa bako sanarwa”.

A babban parlon dady suka fice inda aka cikashi da abinci kala kala da kayan fruits dana snacks kala kala, dady yasakashi dole saida sukaci abincin atare, bayan sungama sannan momy tashigo tareda bunayya.

Cikin matuk’ar girmamawa yadurkusa yagaida momy itama ta amsa masa cikin faraa da sakin fuska, momy tace “gsky munji dadin wannan ziyarar taka sosai mashkur, Allah yamaka albarka kuma acigaba dayin hakan, tahakane zumunci zai dore” yai murmushi yanajin dadin yanda irin taryanda suka masa.

Gogar kowa sai murmushi take tana satar kallonsa sbd yamatukar yin kyau sosai,shaddah ce gizna light blue ajikinsa d’inkin riga da wando da hula mai ratsin blue ajikinta, watch dinsa silver color dakuma zobon azurfa a hanunsa, kyan fuskarsa sai dad’a karuwa yakeyi yak’ara gyara sajensa hakama sumar kansa baka wulik sai shining take sbd tasha gyara.

Cikin wayo da dabara tagama masa wannan kallon tsabtar,momy tafita hakama dady yayi side din momyn ammar,yarage subiyune kawai acikin parlon.

Kallonta yai ahankali yace “yau kuma kunyata akeyi” saitai dariya tareda sadda kanta k’asa batareda tace komaiba, cigaba yai da magana “nasan kinyi mamakin ganinako” saitace “sosai makowa, am very surprised” saiyai murmushi.

“Toh ba abun mamaki bane agareni sbd nakasa hakura da rashin ganin ya k’anwarta nabiyota har gida domin naganta” dariya tai sannan tace “ai nad’auka ko nikad’aice nai missing dinka” waro idanuwansa yai yace “tabdi, ai namafiki yin missing d’inki” saitai murmushi kawai.

Ahankali yadinga janta da fira sukaita firarsu, yad’an jima anan kamin daga bisani yamasu sallama yafice.

Ranardai acikin farinciki bunayya takwana dan dare kuma saigashi yakirata sukaita shan firarsu, tindaga lkcn basu sakeyin koda wuni daya bane batareda sunsan halinda junansu suke aciki ba.

Sannu ahankali shak’uwarsu tagaiga dik familyn mashkur bawanda baisan lbrn bunayya ba kuma yakesan yaga bunayya da ido, haka itama bunayya dik gidansu kowa yasan da me d’inta kamar yanda take kiransa brother me,saidai shikam har fuskarsa an sani sbd harsu hajiya yaje yagaidasu.

Ahankali har hutunsu bunayya yakare suka koma school suka cigaba da karatu.

Ahalin yanzu Mashkur da bunayya sunzama aminan juna waenda suke fadawa junansu sirrinsu,tini mashkur yai bincike akan bunayya batareda tasaniba,a yanzu yasan wacece ita haka kuma yasan dikkannin halayenta dakuma d’abiunta.

Yana matuk’ar kula daita tamkar k’anwarsa ta jini,yai amfani da k’arfin amintakarsu wajen canjawa bunayya d’abiunta na jajayen fata,kamar saka k’ananun kaya,yawo ba mayafi ko hijab,dakuma saka karatin addini agaba kamar yanda tasaka na zamani, yanzu a MSSS tana d’aya daga cikin shuwagabanni na school din, kai saida takai takawoma aka bata muk’amin AMIRAH dama mashkur shine AMIR shike bada sallah amasallacin school din.

A yanzu gaba d’aya bunayya tacanja,a yanda kasanta da yanzu idan kaganta sam bazakace ita bace, a kullum tana cikin jallabiya tai rolling da veal saita rufe koina nata inda ake gani sannan zatajita daidai.

Dakansa yakaita kasuwa yasiyomata atampopi da riguna masu kyau dogaye da jallabiyoyi da hijabs kala kala, sannan yakaita gun telo akamata dinkuna sannan yasaka aka koyamata saka kaya atampa dakuma d’aura zani, a yanzukam tadawo cikekkar hausa fulaninta.
...................

Dadyn bunayya yafara damuwa da yanda bunayya ta shak’u da mashkur gashi har yan gidansu sunsan mashkur har suna maganarsa,babban tashin hankalinsa shine,yanda yaji hajiyarsu tace wai tabama mashkur dama idan har son bunayya yake da aure to yai gaugawar turo magabatansa sbd yanzu takai munzalin aure.

Dikda baiji amsarda mashkur din yabadaba amma yana cikin matuk’ar tashin hankali,gashi yatabbatar da cewa mashkur da bunayya suna son junansu.

Babban kuskurensa shine,daya bari har mashkur yarab’i bunayya har suka shaku da juna haka,to yanzu miye mafita...? wannan itace tambayarda yakemawa kansa wacca yake neman amsarta.

Acikin yan kwanakin nan gaba daya acikin tashin hankali da tarin damuwa yake, tin yana b’oyewa har momy tafahimta wanda har saida takaiga tambayarsa meke damunsa yace bkmi.
.....................

Kamar kullum yauma zaune suke a restaurant sunacin abinci, bunayya hamdallah dakuma mashkur, suna cikin ci sai aka kira hamdallah a waya ta tashi domin amsawa.

Mashkur yadubi bunayya yace “bunayya mai kama dakefa ta dameni akan saina kawo masu ke sunganki, haka kuma nafada maki momy na tanaso taganki,bama sukad’ai ba dik yan gidanmu bawanda bayaso yaganki sbd jin labarinki dasukeyi a bakina,sbd haka yanzukam yadace ace ki amince muje koda wuni daya ne saimu dawo koh, dan Allah please....! haba yar k’anwata” murmushi tai ganin yanda yaketa mata magiya gashi tasani yai kanwa uku ko hudu daita tinda yanzuma degree na biyu yakeyi anan wato masters degree.

Cikin shagwab’a tace “nidai bazaniba,salon naje suce banida kyau kafini kyau” waro idanuwansa yai yasake baki har saida tai dariyarsa sbd yanda yai abun yace “ni...rufamin asiri yar k’anwata,idan inada irin kyanki ai sainai yanga kamin nazab’a mata”.

Hararansa tai tace “to yanzinma mekakeyi banda yangar, yan 200level da yan 300level nawane keyoman shopping dik dan nace ka amince kasosu,shekaranjiyar nan aunty badiya tasiyoman sweets da chocolate kuma kasani,kawai kaidai bakatashi bane saikagama yanga, kokuma ni saina gaji da wannan yangar taka nazab’ama dakaina ba” takarisa tana hararansa.

Dariya yakeyi yakai hanunsa yaja doogon hancinta tai yar k’ara tareda yin kukan shagwaba,aikwa nan yashiga rarrashinta,saidayadinga bata abinci dakansa abaki sannan tahakura, yana dariya yace “my yar shagwabana kin amince zakije kigasu ruwaida koh...?”.

Gyada masa kai tai alamar eh sai yai murmushi tareda fadin “dik ranarda mukaje sainabaki wani surprise mai girma,zan sanardake wani sirri wanda tsawon shekaru bakisanshi ba” kallonsa tai cikin rashin fahimta saiyai murmushi kawai batareda yasake cewa komaiba.

Bayan sungama sannan suka tattara suka koma school.

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_21/22...._
Tin ranarda sukai maganar zuwa gidansu mashkur yaketa shirye shiryen tafiyar, itakam gogar indama akai zancen anan tabarsa tama share zancen sbd batawani d’aukesa serious ba.

Zaune take abakin room d’inta tana gyaran k’umbarta saiga hamdallah tazo,wata leda tamik’a mata ta amsa sannan tace “da me yana nemanki pa tin d’azun,yana nan abakin get” ohk...kawai tafada sannan tamike tashiga ciki,
Wani k’aton hijab tad’akko tasaka kasancewar towel ne ajikinta sannan tasaka takalmanta tadauki wayarta tafice.

A jingine da bangon gini ta taddasa tarungume hannayensa, yana ganinta saiya gyara tsayuwarsa,bayan taiso cikin faraa tace “da me...yadai” cikin murmushi yace “batun tafiyarmune,shine nace bara natinamaki yaune fa” waro idanuwanta tai alamar mamaki sannan tace “yaufa...?” yace “Eh...” hmm...tasauke numfashi tareda dan b’ata fuska sannan tace.
“Ni gsky banshirya tafiya yauba” hararanta yai kamin yace “sbd me” ta tab’e baki tace “haka kawai” saiyace “indai bakida wani dalili to ba’abunda zaihana tafiyarnan yau,tinda dai naga alamar bakyasan zowa bayan nafad’amaki hadda momy na tace tanaso taganki”.
Chapter 9 · 0% Book details