← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wowww.....thanks sooo much my brother, tnx allot da mee...na am very proud of u nd’ am very appreciate to u my big brother” hamdallah ma wage bakinta tai cikin mamaki sbd sudika sunmanta da ranar.

Bunayya tace “kaga wlh nifa harnama manta wlh, amma nasan koda kowa zai manta momy na bazata tab’a mantawa da wannan ranar ba komai rintsi, shys nake k’ara k’aunarta acikin zuciyata nake kara santa fiye da kowa nawa a duniya, ina matuk’ar kaunar momy na” murmushin farinciki suke sudika.

Hamdallah tace “am sorry nidai tawa kyautar sai munkoma school sbd yanzu yazoman a bazata ba shiri” sukai dariya tace “bakomai yar uwa” ahankali ta bud’e kyautar mashkur saiga wani tsadajjen zoben gold yana kyalli yana shining tsabar kyau tana kara bayyanar masa.

Kara matsowa dab daita mashkur yai sannan yamiko cikin tafin hanunsa yakuma duko da fuskarsa suna kallon juna,ahankali yafara mata magana cikin tattausar murya da tausasan lafuzza waenda bata taba jin irinsu agaresaba “and then ina rok’on kibani dama k’anwata domin mallakarki amatsayin matata ta sinnah kuma uwar y’ayana insha Allah, the all what I mean is...I really love u with all my hert with full confidence my sister” tashi yai yagyara wandansa sannan yakarayarda k’afarsa d’aya d’ayar kuma yaduk’a akan guiwarta sannan yad’ora hanunsa daya tareda furta.

“Please my sister, will u marry me.....?” yajefamata tambayar kai tsaye kuma a lkc d’aya.

Tinda yafara magana har izowa yanzu a dazk’are take tana kallonsa cikin tsintsar mamaki, gaba daya yacikata da mamaki,tinda take dashi koda da saud’aya mashkur baitab’a nunamata alamar wai yanasanta da soyayya kokuma aure ba sai yanzu, danhaka abun yazomata a bazata,hakan yasa takasa gasgata abunda ke faruwa a yanzu.

Batasan sadda kwallah suka fara zubomata ba waenda kasa bambance shin na farinciki ne kokuma akasin hakan, saidai tatsinci kanta dajin wani irin farinciki dakuma jin nishad’i had’e da kunyarsa ta mamayeta,mamaki take wai itace mashkur dinnan mai girman kai da rashin kula y’ammata harma da wulak’antasu wani lkcn,shine wai agabanta a durk’ushe yana neman soyayyarta.

Rufe fuskarta tai da tafukan hannayenta cikin yanayin kunya,mirtsinarta hamdallah tai cikin dariya da farinciki saita kyalkyale da dariya tareda rungume hamdallah d’in, hakan ya bama mashkur amsar cewa ta amince kenan.

Murmushin jin dad’i yai tareda mik’ewa tsaye sannan yakamo hanunta na dama yasanyamata zoben gold din a yatsanta nakusa da k’arshe saika yamata kyau sosai,hasken yatsunta suka had’e dana zobenwsaiyake bada wata kalar kyan mai d’aukan hankali, kissing dinsa yai sannan yace.

“Inaso ranarda za’amin walimar kammala second degree dina ahad’e data aurena insha Allah,nanda d’an lkc k’ankane zan mallaki k’anwata fatima amatsayin matar aurena kuma uwar yayana insha Allah” kunya dikta k’ara mamaye bunayya hartakasa kallonsa yanzu,shikwa ba abunda yake sai dariya yana kallon kyakkyawor fuskarta.

Suna a zaune kwatsam saiga ruwa yasakko nanfa kowa akafara guduwa domin kiyaye kai, itakam bunayya zamanta tai acikin ruwan yana ware hannayenta tana juyi acikin ruwan,damacan bunayya tanasan ruwa sosai kamar kifin cikin rijiya tariga tasaba dasu sosai bare kuma yau datake acikin farinciki.

Wasa tadingayi sosai acikin ruwan tana dariya tana tsalle,shikwa gogan tsaye yai acikin wata rumfa dasuke aciki yazo yakwashe sauran kayan hamdallah nacikin mota itakad’ai.

Kallonta yake yana murmushi yanda take wasa acikin ruwan, veal dinda tai rolling dashi ya kwance sumarta a waje,hakama abayarda jikinta bottoms din rigar sun b’alle wandanda ke ciki na jeans da yar singlet dinda ke ciki yana hangosu sosai,ruwa ya kwantarda singlet din har tai showing kana ganin shayin brez d’inta, kallonta yake yajingina da bango ya hard’e hannayensa gu d’aya, shifa ji yake kamar ma yaune yafara ganinta, cikekken halittar k’irjinta yake kallo dakuma bayanta idan tajuya.

Wannan shine karo na farko daya fara jin yana sak’a abu a zuciyarsa akan bunayya, musamman yanzu dayake kallon kyakkyawor surarta musamman halittar k’irjinta dasuka fara d’aga masa hankali sbd ganin cikarsu,gashi a rayuwarsa ba abunda yafiso agun mace kamar dukiyar fulani sannan matasan zama.

To saigashi bunayya tahad’a dika biyun koma nace uku, kyau gaba dakuma baya dika,rauninta kad’an ne wanda yasan idan yajajirce dik zai taimaka mata wajen gyarasu koda bazasukai 99% ba.

Yana cikin wannan tinanin saiya tino da hamdallah danhaka yakwallawa bunayya kira ta waigo tagansa,dasauri tagyara abayarta sannan taje suka fice tana wani sinne kai.
Acikin mota ma kanta a k’asa yake takasa had’a ido dashi,tamayishu tak’i magana dik yanda yaso yajata fira amma tak’i sai hamdallah ce kawai ke tayasa firar har suka iso school.
...................

Tindaga wannan ranar bunayya tashiga wasan b’uya da mashkur,tinda sukaje park yau kusan kwana uku kenan baisake sakata a ido ba har yau.

Nemanta yake ruwa a jallo amma baigantaba kuma yasan bataje gidaba,dik inda yasan tana zama yaje amma baya ganinta,
Baisan cewa bunayya tashiga kullene ba,tasakawa kanta sark’ar k’arfe da pard lock tarufe kanta daga lecture sai lecture take fita,dasun dawo kuma tashige shkn,wai ita dik dan karyaganta ne yanzu kunyarsa takeji sosai.

Around 8:30pm bayan sundawo daga masjid saitaje wani d’an kanti dake cikin school din, street sket ne ajikinta na roba sai wata yar singlet pink color,k’aramin hijab ne ajikinta wanda bai wuce yadi biyu ba.

Buiscuit ne ahanunta da ice-cream da chocolate da sweet acikin wata bakar leda, tana cikin tafiya tana rera yar wak’arta,hankalinta nakan wayarta datake jin music kawai saitaji anjanyota da k’arfi anmanna bayanta da bango,rintse idanuwanta tai dasauri acikin tsintsar tsoro da tashin hankali sbd tama d’auka fad’uwa zatayi ak’asa saitai saurin furta “Innalillahi wainna ilaihi rajiun”.

Dariyarsa taji yana kallon fuskarta dakuma yanda jikinta yashiga rawa sbd tsoronda taji, jin sariyarsa yasa tagane ko waye, danhaka ta bud’e idanuwanta ahankali sai akan fuskarsa tasauke idanuwan nata.

Kallon kallo suka faramawa juna kamin ita tad’auke nata idanun cikin yanayin kunya, wani killer smile yai kamin yakai yatsansa tindaga kan goshinta har izowa kan doogon hancinta har izowa gementa yana fadin “tsalki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakkyawor fuskar”.

Dan murmushi tai tareda juya fuskarta gefe d’aya,ahankali yafara mata magana “bunayya meyasa kike b’oyemin kanki,bayan kuma kinsan ganinki yazameman tamkar cin abincina,rashin ganinki kuma tamkar rashin shan ruwanane,tsawon kwana uku kinsakani nadawo kamar mahaukaci,dik na karad’e school dinnan da inda muke zama harma da inda bama zama dik naje nemanki amma bake,haba so kike kishirwar rashinki da yunwar ganinki sukasheni” dasauri ta girgiza kai alamar bataso saiyacigaba “to meyasa kike b’oyeman kanki, nifa wannan kunyar tana nema tafara cutardani,gsky bazan iya jure wannan ba,yanzuma hamdallah ce tafad’aman inda kikai shine nabiyoki hadda guduna” dariya tasub’uce mata lkcnda taji yafadi wai hadda gudunsa dan kawai yaganta.

Shima dariya yai sannan yagyara tsayinsa tareda fadin “muje narakaki” sai itama tagyara sannan suka jera sunacigaba da tafiya.

Magana yake mata tana saurarensa “am....dama jiyane nakira dady na nafad’amasa komai tsakanina dake,nakuma cemasa kina matuk’ar k’aunata har cikin zuciyarki nima kuma ina matuk’ar kaunarki har cikin b’argo na, danhaka munbasa dama yaje yasami abban ruwaida suje sunemaman aurenki agun dady,kuma inaso nanda wata biyu kacal kizamo matata uwar yayana”.

Wani murmushi tai Na farinciki hadda rufe fuskarta kamin tace “waya fad’ama ni inasanka,to kayi kuskure dabaka fara neman izininaba dakuma jin amincewata ba, ma’ana inasonka ko bana sanka, sbd haka kai saurin kiran dady kafad’amasa yadakata har saina bada izini” tana maganar tana masa wani kallo cikin murmushi, tana gama maganar kuma saita juya tashige hostel dinsu.

Murmushi yake yana kallonta har tashige sannan yashafa sumarsa da sajensa yajuya yafice yana fadin “zaki gane kurenki idan kikaji ansaka rana nanda wata biyu kacal.
.......................

Labari mai dad’i yarizk’e abban ruwaida, shikuma abban ruwaidah yakira su abban ramada yasanardasu yaran sun had’a kansu sunkuma fahimci junansu,a yanzu haka sune suka bada damar atsayar masu da zance d’aya.

Nan hajiyarsu dady tabada damar sati na tafe azo ayi komai,tanaso ayi komai lkc daya hadda saka rana dakuma sadaki,amma za’ayanka sadakin ne kawai baza’a biyaba har sai ranar d’aurin auren.

A dika ahalin biyu bawanda baiyi farinciki da murna da wannan lamarin ba,musamman momyn bunayya dakuma su dadyn mashkur,abban ruwaida saida yai sadaka ranar sbd gdy ga ubangiji daya tsaramasa wannan lamarin acikin ikonsa da buwayarsa.

Tofa dik wainarda ake toyawa dadyn bunayya baisaniba,hakan kuma yafarune ta umarnin hajiyarsu,tace kar wanda yafad’amasa har sai ana gobe zaayi tambayar, danhaka abban ramadan dasu ya ammar bawanda yafada masa.

Toh rana bata k’arya saidai uwar d’iya taji kunya,gobe Friday itace ranarda zaayi engagement din bunayya da mashkur had’eda yanka sadaki dakuma saka rana.

Shiri na musamman momyn bunayya keyi,danginta kusan su goma da yara yammata sa’annin bunayya dama yayyaenta waenda sukai aure dik sunzo,gidanfa yacika taf da mutane sai shirye shirye ake ana girke girken namu na kaji dana raguna da snacks kala kala.

Dady side din momyn ammar yake shys baisan wainarda ake toyawa ba, sai kusan 1pm sannan yafito yashigo side din na momy, abunda yaga anayi yamatuk’ar bashi mamaki sbd shidai baisan ana wani bikin a dangin momy ba, gashi kuma yaga su yaya hauwa dasu aunty kuluwa dik sunzo.

Bedroom dinsa yafice yace akiramasa momy tasamesa d’akinsa.
Koda taje ta taddasa yana neman wani file d’in,batareda yad’agoba yake tambayarta “maryama tawa,wane biki akeyi a gida hala dahar akek’in fad’aman saidai naga ana shagali” hararansa tai dikda baya ganinta tatsuke baki sannan tace “ai wlh kyaleka kawai nai ina duban hankalinka, kana nufin kai bazakayi shirin tarban bak’inda zasuzo bane koyane” d’agowa yai yamatso kusa daita sannan yace “hajiyaaa....nifa banma fahimci abunda kike nufi ba” mamakine yacika momy ganin zahirin gsky a fuskarsa.

Gyara tsayuwarta tai sannan tacigaba da magana “Alhj kana nufin kaceman bakasan gobene zaayi baikon bunayya da mashkur ba hadda yanka sadaki dakuma saka rana ba” files dinda ke hanun dady ne suka fadi lkc daya tareda furta “what.....!!! har saida momy taja da baya cikin firgici.

Nantake idanuwansa suka kad’a a lkc d’aya,k’afafuwansa nema sukai sukasa d’aukansa hakan yasa dasauri yadafe gado sannan yazauna, tsorone yakama momy dasauri tarikosa tareda fadin “kadel lfy kowa, wai meyake faruwa ne daga nafadama zaayi baikon su bunayya shkn mood dinka yacanja” kasa cemata komai yai sai mik’ewa yai tsaye yafara zarra acikin dakin kamin yadubeta yace “waye yai wannan had’in” momy tace “yaradai sune suka had’a kansu sannan manyansu suka shiga gaba,hajiya kuma itace tasaka ranarda zaayi baikon” waro idanuwansa yai tareda furta “hajiya kuma,kardai kiceman hajiyarmu” tace “Eh ita”.
Chapter 14 · 0% Book details