← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar bunayya saidatai kwallan farinciki sbd lbrnda momy tabata, nan taji k’aunar momyn tata tak’ara mamaye zuciyarta, tayi tinanin abunda yafaru yan uwan momy zasu gujeta su daina sonta kamar yanda suke santa abaya amatsayin y’a d’aya tilo agun yaruwarsu,ashe abun bahaka bane har yanzu suna k’aunarta basukuma daina d’aukanta matsayin yarsu tajini ba.
.....................

Ahankali komai yafara dawowa daidai sbd shirye shiryen shagalin babban bikinda zaayi wanda ba’atab’ayin irinsaba atarin ahalin uku,dika b’angarorin uku shirye shirye akeyi musamman momy datafi kowa farinciki da zumud’in zowan ranar.

Tini tatura kud’i Dubai domin ayomata kayan d’aki set biyar,yayinda shima abban ruwaida ke nasa shirin domin nuna tasa bajintar,dadyn mashkur kowa kantamemen gida yake ginawa d’ansa naji da gani upstairs hawa biyu had’eda tikitin zowa honeymoon natsawon wata biyu.

Ab’angarensu uncle Muhammad kowa,hotel hotel yake kamawa domin manyan bak’inda zasuzo nasa dana momy tindaga bagudo har kebbi ak’alla yakama hotel goma sha biyar tareda zirga zirgan bak’in, saikuma shirin garar gidan miji dayad’auki nauyi wacca zaiyi, aunty kuluwa shahararriyar mai gyaran amare tad’auki nauyin d’akkowa daga mai duguri domin tagyaramata y’arta amarya bunayya.

Hakama b’angaren abban ramadan suna nasu shirye shiryen taryan bak’insu dakuma shirin ranar d’aurin aure sbd ana zaayi tinda nan ne gidan uban amarya.

B’angaren umman ruwaida ma nasu shirin suke,saikuma b’angaren ango daketa faman shirye shiryen angonci amma b’angaren amarya kam shuru kakeji ita karatintama tasaka agaba,
Kai zan yacemaku koinama shirye shirye ake sosai na shagalin bikin y’a d’aya tilo agun hajia maryam jolde.

Dadyn bunayya abun duniya yataru yamasa yawa,komai yajagulemsa lissafinsa yajagule gaba d’aya yarasa yanda zaiyi,neman momy yake ruwa a jallo sbd yanzu gaba d’aya tadaina fita office tinda wannan lamarin yafaru,yanzu jinyar kanta take dakuma rainon cikinta.

Yarasa yanda zaiyi gaba d’aya yafita hayyacinsa ga rashin bacci gakuma abubuwa dasuka k’ara jagulemasa waenda yasani tabbas momy ce kad’ai zata iya warwaremasa su sbd damacan itace abokiyar shawararsa.

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI...._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_33/34....._
Rayuwa tacigaba da tafiya cikin farinciki da walwala,bunayya karatinta tasaka agaba sbd yanzu kwana biyu kacal suka ragemasu sufara zana jarabawa,yayinda a b’angaren ango mashkur kowa yaketa k’okarin ganin yakammala project dinsa nanda sati d’aya kacal zasu kammala komai na degree dinsa nabiyu.

Kimanin sati d’aya kenan rabon mashkur yasaka bunayya a ido sbd yanayin karatinsu sudika gaba d’aya,bawanda keda lkcn kansama acikinsu kowannensu k’okarinsa yaga yasamu sakamako mai kyau.

Saidai mashkur kam gaba d’aya bayajin dad’i sbd rashin ganin hasken idanuwarsa kuma sanyin idanuwansa,haka itama bunayya tana kewar yayan nata amma kunya tahanata tanemesa bare ta tambayesa koda agun abokanan karatinsa ne, a wayama bawani cika yin waya sukeba,hakan yasa kewar junansu tamasu katutu acikin zukatansu.

Sannu ahankali har su bunayya sukafara zana jarabawan first semester ta 200level, abun ba sauk’i kokad’an saidai ace Alhmdllh amma sunashan fama kam,any time suna wajen karatu dikta rame tak’arin haske sbd dama can bunayya badamuwa tai dacin abincin kirkiba sai mashkur yaita fad’a koya sakata agaba sannan takecin tuwo ko shinkafa,ita bartadai da kayin mak’u lashe,to bare yanzu da exam tasa ruwanta shkn sai k’arisawa kawai.

A ranarda sukacika one week da fara exam aranar mashkur yakammala komai suka fara shirin tafiya gida,tin 3pm yasaka anemomasa bunayya amma baagantaba kaf school din sai kusan 5pm sannan akazo aka fad’amasa suna cikin exam,kokad’an baiji dadin hakanba yaso matuk’a yaga bunayya sbd yana k’ishirwarta sosai,gashi kuma tin 2pm akazo d’aukansa amma sbd ita yahana sutafi har wannan lkcn, neehal k’anwarsa ta uku da’akazo d’aukansa daita tace “haba brother,kazo mutafi mana,aunty bunayya fa takace nanda wani d’an lkc za’akawoma ita kaita ganinta kana kallonta har kagaji,tomeyasa zaka wani tsaya kace dole saikaganta yanzu,wlh mungaji sosai ni yunwama nakeji momy kuma sai kira take inacemata har yanzu bamuko tasoba bare har mu’isa gida” sauran yan uwanta najin tayi magana nan suma suka saka nasu bakin sunamasa magiya.

Aiko badan yasoba dole yashiga mota suka fice batareda yaga abar k’aunarsa ba.

Bayan su bunayya sunfito hamdallah kefad’amata mashkur yasaka akirata amma lkcn tana d’akin jarabawa harya wuce,yaune suka kammala dik sun wuce gida yan masters degree din nan, bunayya kamar tai kuka dataji lbrn nan hamdallah taita mata dariya.

Haka itama suka cigaba da zana exam dinsu ahankali,dik bayan kwana biyu mashkur yakan kirata susha soyayyarsu kamin daga bisani yabarta tacigaba da karatinta na exam.

Sannu ahankali lkcn biki ke k’ara k’aratowa yayinda aketa cigaba da shirye shiryen shagalin bikin.

Aunty kuluwa tini takira mai gyaran jiki domin tafara aikinta sbd sati biyu kacal yarage afara bikin sbd haka tanaso amata gyaran tsawon sati d’aya,itakuma bunayya gashi basu kammala exam ba.

Dahaka aunty kuluwa tahak’ura har suka kammala exam din sannan tadawo gida dikta rame.
......................

Kamar koyaushe momy ce zaune akatafaren parlon ta tanashan fruits tana kallon news a aljazeerah channel, bunayya kowa kwance take akan center carpet tanacin tufa,sanye take da kayan bacci riga da wando iya guiwa,kanta bakomai sumarta dikta barbaje akan pillow dinda kanta yake akai.

Ahankali momy takalleta tace “waikekam bakya shirin komaine,naga bakima damuba matsayinki na amarya” wata iriyar kunyace taji takama saitai d’an murmushi murya k’asa kasa tace “toni wane shirin zanyi ne bayan wanda ku kukeyi” waro ido momy tai tace “lallai yarinyar nan,amaryace zatace wane shiri zatayi na bikinta,koda yake bazanga lefinki ba tinda bashiga mutane kikeba bare kisan yanda akeyi” saitace “to kingani,nikam ina nasan shirinda akeyi”.

Momy tasake cewa “to batun k’awayenki fa,su wayene zasumaki k’awayen amarya ne?” d’an tinani tafarayi sannan tace “kingadai hamdallah itace babba saikuma nabila da nafisat kannen ya ramadan,to saikuma su rufaida da rumaida yayan uncle Muhammad, sukenan sun isa” momy tace “shkn,akwai five hundred thousand naira zan baki dik abunda suka fad’amaki yakamata kuyi saiku diba kuyi,uncle Muhammad ma ya aikomaki da two hundred thousand yace abaki,saikuma k’awata hajiya mamu ta yobe ta aikoman da fifteen thousand naira gudumawa,anfa turoman da kudi sosai gudumawa anjima idan mun zauna dik zan fad’amaki insha Allah” murmushi tai na farinciki da jin dad’i tace ok kawai.

Cigaba ake da shirye shiryen shagali ta koina b’angarorin hud’u,momy tazage sai faman kashe kud’i take domin ganin tayiwa y’arta tilo gomasha na arziki.

Bayan kwana hud’u da dawowar bunayya abban ramadan yazo yabama momy hkr akan dan Allah tashirya taje tabama hajiyarsu hkr ita da bunayya sbd yanaso yazamana koda za’amayarda magana wata rana yazamana batada lefi,kuma yanaso ad’aura auren bunayya anan gidansu dady amatsayinta na y’ar dady.

Momy dafarko taso tak’i amincewa da buk’atarsa amma daga baya data tino da martabar y’arta bunayya ma zata k’aruwa idan har aka d’aura aurenta anan gidansu dady saita hkr tabama zuciyarta hkr ta amince zataje d’in.

Washe gari kowa tashirya tareda bunayya da driver sukaje gidan,fuskar hjy ba yabo ba fallasa ta taryesu abun harya bama momy mamaki yanda taga tasake masu fuska hadda tambayar bunayya ya karatinta tace Alhmdllh.

Batareda b’ata lkcba momy tagabatarda abunda yakawosu nan ta durk’usa agaban hajiya dikda d’an matashin cikinta amma bata damuba tashiga bama hajiya hkr akan abunda yafaru, abun mamaki saiga hajiya tana fadin “bakomai ai sharrin shaid’an ne,Allah iyafemana baki d’ai kuma a kula da yanayin jiki sbd kare lfyr abunda ke ciki” cikin yanayin sakin fuska momy tace toh taredayin gdy.

Basu wani dadeba suka koma side din hajiyarsu ya ramadan,hajiya taji dadi sosai da yanda hajiyarsu dady tahak’ura,haka shima abban ramadan yaji dad’in abunda momy tayi har yaita mata gdy sosai tareda addu’ar fatan Allah yak’ara nisantarda shaidan atsakaninsu.

Ranar kusan gidan suka wuni sai kusan la’asar sannan suka koma gida,bunayya tahad’e dasu nafisa akaita yawo ana zumunci anakuma firar yaushe gamo.

Labarin auren bunayya da mashkur yarizk’e dady a bazata,wani abokinsa ne yakirasa yana zaune a office yana signing kan wasu files,cikin rashin jin dad’i abokin nasa kemasa magana “haba kadel,yanzu amintakarda ke tsakaninmu tacancanci ace katashi aurarda y’arka har ana saura yan kwanaki amma baka sanardamu ba,wlh kabani mamaki Alhj kadel” dasauri dady ya mik’ewa tsaye tareda dakata yin signing din.

Mamaki ne yabayyana a fuskarsa sosai amma saiya b’oye yacemasa “Am...am....dan Allah Alhj zayyad kayi hkr,abubuwane sukayi yawa shys banturo maku da invitation card ba,but....am very sorry please...!” sai mutumin yace “Ok....no problem,Allah isanya alkhairi” yace ameen sannan sukai sallama.

Dady yakasa zaune yakasa tsaye acikin office din,daga k’arshema saiya fice daga office d’in kawai.

Kimanin sati d’aya yarage afara gudanarda shagalin bikin,gida yafara cika da bak’i na nesa dana kusa,hajiyarsu dady ta aiko aka d’aukarmata bunayya aka kaimata,saida tai kwana biyu acan tana mata nasu gyaran na tsofaffi sannan aka maida,washe gari kuma tafice bagudo gun aunty kuluwa domin afaramata gyaran amare.

Su ruwaida sun iso tareda ramlat kanwar mashkur hakama nadiya k’awar bunayya ta London tazo tareda momynta da nabil kanenta,hamdallah tazo tareda bunayya suka tafi bagudo,kai mutanedai sai zowa suke daga k’asashe daban daban dakuma garuruwa daban daban.

Bayan tafiyar bunayya dakusan 9hrs saiga kiran aunty kuluwa yashigo wayar momy,bayan tad’aga tana batun tafara magana sai aunty kuluwa tafara da cewa “wai jolde me bunayya ke nufine,wlh kifad’amata idan yaturo a d’auketa bazataji da dad’i ba,haba dan Allah,wannan wane irin iskanci ne tin yaushe matar nan kejiranta afara abun nan amma har yanzu tak’i tazo” mamakine ya bayyana a fuskar momy kamin tace “banganeba aunty, bunayya fa tin 9am sukabar birnin kebbi zowa nan bagudo,yanzu kuma kusan 9hrs kenan da tafiyarsu amma ace har yanzu basu isoba” itama aunty kuluwa mamakin ne yabayyana a fuskarta tace “tin 9am sukabaro birnin kebbi fa kikace” tace “Eh wlh,amma bara nakirata naji” tace toh sannan takatse layin.

Nan tashiga kiran layukan bunayya amma dik akashe suke,dasauri takira layin hamdallah sai wani namiji yad’aga,dasauri momy tace “hel...hel...helo hamdallah” sai yace “baita bace Malala,ni sunana Inspecter faruk,muntsi yaran nan ne a kan titi su biyu dika a some a yanzu haka suna babban asibitin FMC dake cikin birnin kebbi l/gvmnt,sbd haka kuyi hanzari kuzo” dasauri kwallah nazubomata tace “amma inspecter su uku ne had’i da driver ina d’ayan” saiyace “to mudai su biyu muka gani mace da namiji” ai dasauri momy tace “ohk...gamunan zowa” sannan takashe.

Dasauri takira aunty kuluwa tafadamata sannan tafada anan cikin gida halinda ake ciki.
Chapter 17 · 0% Book details