← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 24

Sashe 7

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itakam bunayya dataji batawani damuba tacemawa ramadan karya damu zatai magana da dady,tasan zai amince sbd tafi kowa sanin dadynta.

Bayan sunyi magana dashi ramadan saita kira dady,dik yanda tai amma haka dady yakafe yace sam bai aminceba, tin abun yana wasa harya b’aci,kuka taketayi tana rok’onsa amma yakafe daga karshema saiya kashe wayar kawai.

Daren ranar haka tayisa cikin bacin rai dakyar tasamu safiya tawaye dan bata iyayin baccin kirki ba,
Washe gari kwatsam saiga takardan samun admission dinta a Federal university dake kalgo l/gvmnt acikin kebbi state.

Jifa tai da takardar tafice dagudu bedroom dinsu tafada kan gado tareda fashewa dawani matsanancin kuka, safiyya tashigo ta taddata ahaka gashi hajiyarsu batanan,taitai tadaina kukan amma taki danhaka ta tashi tafice izowa dakin ya ramadan sbd tasan shikadai ne zai iya rarrasanta bayan hajiyarsu.

Tana kawowa parlor sai taci karo dashi zashije kitchen,nan tafada masa abunda ke faruwa sannan tafice zowa aikinta, dafarko kamar karyaje saikuma dai yadaure yatafi.
Koda yashiga dakin har yanxu kukan take,ahankali yazo yazauna kusa daita tareda zubawa kyakkyawor surarta ido.

Aslm....my fans, kuyi hkr dajina shuru jiya wlh mamana ce batada lfy dan Allah kusakata acikin adduoinku,ngd sosai dakulawa.

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_15/16....._
Dik yanda yake tausayawa kansa na rashin iya mallakarta amatsayin matarsa ahalinda yaganta yanzu yafi tausayinta,yasani tabbas bunayya na sansa haka shima sonda yake ganin bak’aramin wuya zasushaba idan har akace dole saisun rabu.

Ahankali yakira sunanta cikin tattausar muryarsa mai ratsa jiki da sanyawa gangar jiki kasala,wacca a dik lkcnda ta daki dodon kunnenta koda acikin bacci ko cikin duhune zata iya ganesa kai koda ma acikin dibbanin mutane ne “BUNAYYA....!!!” jin muryansa yasa ahankali tadan sausauta kukan nata “tashi muyi magana” ba musu kowa ahankali ta tashi a zaune kwallah bazubar mata sai sheshekar kuka takeyi, shuru yai yana kallonta yayinda itama tai shurun nantake d’akin yad’auki wani yanayin tsawon yan dak’iku sai sheshekar kukanta kakejiyowa.

Ahankali kuma yafara magana “bunayya inaso kiyi hkr kidaina kukan nan haka,wannan kukan yana matuk’ar d’agaman hankali banasanshi kokad’an,wannan abun daya faru damu mud’aukesa amatsayin k’addararm...” bai k’arisaba tai saurin taryesa da fadin “mekake nufi ya ramadan..? kana nufin wai murabu kenan?”.

Gyara zamansa yai yana fuskantarta sannan yacigaba da fad’in “bunayya inaso kisani bawani d’a nagari dayake cin nasara arayuwarsa batareda yanayin biyayya wa mahaifansa ba,shin baki example ga iyayenmu,dik girmansu da matsayinsu idan har hajiyarsu tai magana koda abun bai masu dad’iba bazasu taba k’etare wannan maganar ba bazasu taba mata musuba saidai su rungumi abun su karb’esa komai d’acinsa komai rashin dadinsa,sbd haka muma inaso muyi koyi dasu bunayya”.

Saiya janye fuskarsa daga kallonta sannan yacigaba da fad’in “dikda nasan rashinki agareni tamkar babbar asarace wacca hamshak’in d’an kasuwa yakeyi, wlh wlh wlh bunayya inasanki so mara misaltuwa amma bazan iyayin musu da mahaifana ba,tinda dady bayasan aurenmu shkn muhak’ura watak’il ma wannan rabuwar tamu shine alkhairi a tsakaninmu”.

Kalmarnan ta rabuwa dataji saida k’irjinta yai wani bugawa dak’arfi wasu kwallah masu zafi suka zubomata bakinta na rawa tace “kak...kak...kaima yanzu ka goyi bayan murabu kenan,haba ya ramadan idan kamin haka bakamin adalciba wlh” dafe kansa yai dayake masa ciwo mai tsanani sannan yace “kifahimta bunayya, mai biyayya wa iyayensa har abada baya tab’ewa maybe rabuwar tamu itace mafi alkhairi a tsakaninmu,kiyi hkr bunayya Allah yahad’a kowa da rabonsa” yana gama fad’ar haka yamike sauri zai fice.

Dasauri ta tashi dagudu taje ta rungumesa ta baya tana fadin “ni wlh bazan iya auren wani bakaiba karka barni ya ramadan dady baisan irin sanda nakema bane shys” rintse idanuwansa yai wasu zafafan kwallah suka zubo masa,ahankali yarabata da jikinsa sannan yafice dasauri.

Tsaye tai tana kallonsa harya fice,anan tazube tasake fashewa da wani sabon kukan,haka taita rerasa tsawon lkc anan bacci yakwasheta batareda tasaniba.

Washe gari tin 8am ramadan yabi jirgin safe yafice agadaz gun dangin mahaifiyarsu kasancewar ita buzuwace yar agadaz hajiya maccha kenan,bunayya batasaniba sai bayan kusan kwana uku sannan taji abakin su nabila,anan takara tabbatarda lallai tarasa ramadan har abada,aikwa ranar takara tino da abunda tabari kwana uku yadawo mata sabo,har safiya tawaye bata iyayin bacci ba,
Nantake damuwa ta bayyana a jikinta idanuwanta suka kukkumbura sbd yawan kuka.

Sannu ahankali tintana kuka harta fara hkr dole hajiya kuma tana k’okari sosai wajen mata nasihohi masu ratsa jiki dakuma irin riba da nasararda mai hakuri kesamu acikin rayuwarsa,dahaka tasamu harta fara hkr tana sakewa.
......................

Sannu ahankali har aka kwashe kimanin wata biyu da faruwar wannan lamarin.
Wannan shine rabuwar bunayya da yayanta ramadan, tini tafara karatinta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali gakuma shirye shiryen shagalin bikin ya Amir da aunty mardiyya da yaya affan da nabila sunfara,gida haryafara cika da bak’i na nesa dana kusa sai faman shirye shirye suke.

Yanzu komai yamata sauki sbd idan taje school tin 8am sai 6pm take dawowa, gida kuma yanzu acike yake gwanin birgewa danhaka yanzu tafara mantawa da damuwarta saidai idan ta tinane takejin damuwar tazomata amma datai adduah kokuma tasami abunda zaisa tamanta shkn nantake saita mantarda abun acikin zuciyarta.

Sannu ahankali akafara gudanarda shagalin biki,yanzukam bunayya anfara saka atampa, jiya akayi kamu suka saka material ja gown har kasa akamasu make-up, wow Masha Allah naso kowa kuganta yanda tai kyau sosai,ko amare basufita kyauba,
Yau kuma tinda sassafe akamasu lalle ja,abunka da fararen fata kuma jinin shuwa arabs lallen yamatukar yimasu kyau sosai musamman ita,dan itakam diktafisu kyau, yau kunshine kawai zaayi danhaka suka saka kid’ansu sukaita cashewa abunsu sunayin nishad’i.

Washe gari akai bridal shower suka saka gown ta atampa yellow white and black color, sunsha make-up sosai sunyi matuk’ar yin kyau bakad’an ba,abun gwanin birgewa bunayya sai nishad’i suke,sunsha rawa sosai, sai kusan 6:30pm sannan aka turo motoci suka d’aukesu.

Washe gari asabar around 10am dot aka d’aura auren 12pm dot aka fice royal event inda zaayi Arabians day,amare biyu mardiyya da nabila dakuma matan ya amir da yaya affan suka saka gown fara tanaja akasa gwanin ban sha’awa kowacce da tata designe,sukuma su bunayya suka saka jallabiyoyi masu shegen kyau difference colors,hakama su momyn bunayya wato iyaye mata jallabiyoyi suka saka masu tsadar gaske,suma su dadyn bunayya jallabiyoyin suka saka da alkyabbu,yaukam antina da al’ada ahalin gidan kebir kemel,ansha shayi anyi rawar arabs daga bisani akaci abinci akai picsis sannan aka watse.

Da dare around 10pm aka kai amare gidajensu.
Dik wannan shagalin da akayi ashe mahabub d’an abokin dadyn bunayya yana nan yakafe bunayya da ido batareda tasaniba, tini yasamu phone number d’inta sannan yafadawa mahaifinsa yaganta kuma tamasa yana santa.

Bak’aramin dad’i mahaifinsa yajiba harma yace “damacan wlh inatasan namawa Alhj kadel mgn,inasan nahad’a zuriah dashi kodan mukara dank’on anokantakarmu, ashe Allah yana sane da abunda ke raina,to Alhmdllh naji dadin wannan abun wlh Allah yasanya albarka aciki” mahbub yace ameen.

Washe gari dadyn mahbub yasami dadyn bunayya a office dinsa,dady yamatukar jin dad’i daganin abokinsa,bayan sungama gaisawa da yar fira,sai dadyn mahbub yafadawa dady abun alkhairinda ke tafe dashi.

Toh kamar dai yanda yayiwa abban ramadan yanzuma haka yayiwa dadyn mahbub yakuma kara da fadin “kagane maishaddah, bunayya fa bawata mai shekaru bace yarinyace sosai girman jikin ne kawai mutane kegani amma batada wasu shekarunda zaace har amata aure ba,gsky ni banshirya yimata aure ba sai zowa nan gaba,kaga yar uwarta saida takammala karatinta na matakin degree sannan namata aure to haka itama haka kuma sauran yan uwansu,sbd haka ayi hkr dan Allah, Allah yabashi wata wacca tafita kawai, that’s all”.

Bak’aramin mamaki dady yabama dadyn mahbub ba, shifa yana ganin amintakarda ke taakaninsu tawuce ma yazo yafada masa wai d’ansa yanasan yarsa takaiga saidaima yafadamasa yayiwa yarsa miji kawai,ashe abun bahaka bane,tsananin mamaki hanasa magana yai kawai saiyace.

“Ohk...no problem Allah yahad’a kowa da rabo na alkawari” yace ameeen.

A b’angaren bunayya sam batamasan wace wainar ake toyawa ba,kwatsam sai lbr taji agunsu mariya wai abban ramada yafadawa hajiyarsu shima kuma dadyn mahbub ne yakirasa yafadamasa abunda dadyn bunayya yamasa sbd sam baiji dadin abunba kokad’an.

Itafa bunayya wannan al’amarin na dadynta yafara bata tsoro, takasa gane dalilinsa nayin wannan abun,saidai itakam tinda yarabata da yayanta ramadan to komawa zai rabata dashi indai ba momyntaba toko ajikinta.
....................

Bayan sati daya kacal dafaruwar wannan lamarin kwatsam kuma saiga wani d’an mak’otansu Dr. Jamal yazo yanasan bunayya, ranarkam su bunayya sunsha mamaki,dik irin tsoro da gudun zuciyar hajirasu dady dayakeyi baihana yazage yadinga cin mutunci da masifa agabanta ba kawai sbd yaron yaturo wani uncle dinsa har gidan yanaso abashi dama yafara zowa gun bunayya,itakanta hajiya abun yamatukar bata mamaki.

Yana gama masifarsa kawai yafice fuu cikin tsananin fushi da bacin rai.

Mamaki yamatukar cikasu gakuma tarin tambayoyi tinjim a zuciyoyinsu, shin miye dalilinsa nak’in amincewa ya fitarwa da bunayya miji...? Shin miye manufarsa nak’in amincewa a aurarda bunayya dawuri....? Shin menene dalilinsa nak’in amincewa samari su rab’i bunayya dasunan soyayya ko aure....? waennan tambayoyin ne suke neman amsoshin su.
........................

Ahaka rayuwa tacigab da tafiya tana gudana cikin walwala.
Izowa yanzu bunayya sunkusa fara exam ta first semester, danhaka yanzu karatu suke ba wasa, tini takoma hostel da zama sbd karatu yafara zafi.

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_17/18...._
Zaune suke acikin room d’in hamdallah sabuwar k’awarda bunayya tai anan FUBK, wata yar mitsitsiyar rigace ajikinta ta bacci sai d’an pant,itakuma hamdallah towel ne ajikinta da’alama daga wanka take.

Abinci sukeci atare indomie da dafaffen kwai,sunaci bunayya na chart itakuma hamdallah tana duba wani littafenta, bunayya tace “yar uwa” kamar yanda suke kiran junansu kenan “kinsan Allah idan bamuyi dagaskeba Mr habeb saiyabamu mamaki da muguntarsa,kinga dama yanajin haushinmu da surutu awajen lecture” hamdallah ta tab’e baki tareda fadin “hmm..bari kawai yar uwa,nima naga alamar idan bamu nunamasa munsan kanmuba bak’aramin mamaki zai bamuba wlh”.

Bunayya tace “bari kawai,aikwa zamu bashi mamaki insha Allah, Allah dai yataimakemu yakuma azamu akanshi,sbd bak’aramin mugu bane wlh,zai iya cutarmu koda gb dinmu yai kyau” hamdallah takara gyara zamanta tana fadin “Allah yafisa yar uwa,muyita addu’ah kawai dakuma karatu” nan suka sake dakko wata firar har suka kammala cin abincin.
Chapter 7 · 0% Book details