← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 24

Sashe 12

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dadyn mashkur yace “to Alhmdllh tinda baku wani wahalarda shari’ah ba, to atak’aice dai yarona mashkur wanda school daya da yarku shine yai tsawon bincike harya gano cewa tabbas bunayya jininsa ce,to yanzu kunga ainahin iyayen bunayya” abban ruwaida ne yai saurin karban zancen dafad’in “kusani wlh kun cutarda mahaifiyarta haka nima kun cutarda ni bakad’an ba,amma kunci arzikin baku renarmana ya acikin k’unci ba,alama tanuna cewa ta tashi acikin jin dad’i amma badan hakaba wlh dasaina d’aureku har abadah banga kuma wanda yaisa yafitardaku ba, amma dikda haka inaso nasan yanda akayi yata taje hanunku?”

Numfashi dady yasauke sannan yafara basu lbrn komai,tindaga haihuwar ainahin d’anda momy tahaifa har izowa satar bunayya tahanyar tacanjata da nasu babyn” cikin tsintsar bacin rai dadyn ruwaida ya mik’ewa tsaye cikin fushi yaje yadamko hanun bunayya tareda fadin “baku cancanci nabarku haka kawaiba batareda nasaka maku da mafificin alkhairi ba, tindaga kan wannan doctor din har izowa ku namaku alk’awarin sakayya mai girma” yana gama fad’ar hakan yakama hanyar fita, dasauri momy taje gun dady tana cemasa “karka bari yatafiyarmin da y’a dan Allah,yata kadel ka karb’oman abata please wlh bazan iya rayuwa babu itaba dan Allah kadel” tana magana cikin matsanancin kuka, dady tarungumeta yana fadin “come down jolde,kidaina kukan nan kada kijanyowa kanki matsala,kamar yanda kike kaunar bunayya haka nima nake kaunarta kuma bazan taba bari yatafi daita ba harsainai yanda dik zanyi nadawo daita hanunmu sbd mune iyayenta,wlh koda zan rasa dik abunda na mallaka ne sainadawo da bunayya gidan nan,just come down jolde”.

Itama bunayya kuka mai tsanani takeyi tana kiran momynta,haka itama momyn kuka take sosai wanda tama manta rabonta da tai irinsa.

Bayan yafita sai mashkur yacewa su momy “dan Allah kuyi hkr dady,insha Allah zamu shawo kan dady zai hkr,bunayya zata dawo hanunku insha Allah, just come down momy” momy kam takasa hkr sai kuka take kaman ranta zai fita.

Itafa bata taba tinanin wannan ranar zatazoba shys ma batai shirin zowanta ba,gashi yau anrabata da abar kaunarta farincikinta,shin wace amsace zasubama duniya a lkcnda aka fara tambayarsu,shin tayama zata iya rayuwa babu bunayya akusa daita,sam hakan bazai taba kasancewa ba.
.................

Tinda aka tafi da bunayya har izowa yanzu kuka take,tak’i ci tak’i sha idanuwanta dik sun kukkumbura sbd kuka har wata yar rama tai sbd wahala.

Daga d’aki sai d’aki bata fitowa koina,mahaifiyarsu tayi iya kokarinta amma takasa shawo kanta sai kiran momy da dady take.

Bayan kwana biyu kacal da faruwar wannan lamarin mahaifinsu bunayya yashirya tareda dadyn su mashkur suka tafi k’asar Uganda.

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI...._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_25/26....._
Har izowa yanzu bunayya takasa kwantarda hankalinta,banda kuka da kiran momynta ba abunda take,koda umman su ta ankara wani zazzab’i mai k’arfi yarufeta gashi tana fama da ciwon maranta lkc yayi,takasa fad’awa kowa sai ramlat ce tagane kasancewar atare suka kwana dan ruwaidah nagidansu mashkur.

A gigice taje tafad’awa ummansu tazo,haka suka b’allamata magunguna amma tak’i sha gashi sai murk’usu take gakuma jikinta yai gaja gaja da zazzabi yai zafi sosai gakuma amai datakeyi.

Tak’i tasha magani haka kuma tak’i yarda akira doctor kokuma aje hospital daita sai kiran momynta take tana kuka.

Tintanada k’arfi har k’arfinta yafara raguwa,hankalin ummansu yatashi matuk’a gashi dadyn ruwaida bayanan, cikin tashin hankali takira mashkur sbd dadyn mashkur sunyi tafiya outside.

A hargitse mashkur yazo gidan,koda yazo wani mini towel ne ajikinta amma dikya b’aci da amai gashi sai murk’ususu take tana kuka tana kiran momynta,jinin period kuma yafara zubarmata sbd takasa iya tashi bare tagyara jikinta, hankalinsa ne yamatuk’ar tashi ganinta ahaka,gaba daya rikicewa yai ya rud’e yama rasa mezaiyi gashi itama ummansu kuka take sbd ganin halinda yar tata take aciki, gashi tasani rabonta dataci abinci tin ranarda lamarin ya auku,sbd haka harda yunwa nadamunta.

Gaba d’aya mashkur rikicewa yai sai kawai yakwasheta yawuce toilet sannan yakira ummanta yace tazo tagyara mata jikinta shikuma yafito yacewa ramlat taciromata riga mai saukin sakawa zasuje hospital ne.

Dasauri tad’akko daidai lkcnda umma tafito da bunayya tana taimaka mata suka fito,rigar kawai umma tazuramata mashkur yazo baijira komaiba yad’auketa suka fita,gaba daya tagalabaita yatsanta bata iya d’agawa sai sunan momy kawai take kira,umma kawai tashiga motar tace ramlat takula da gida da sauran kannenta.

Kai tsaye hospital din momyn mashkur mai suna Sir haroon memorial hospital suka fice,suna isowa olready mashkur yakira momynsa danhaka koda suka isa ana jiransu,yana fitowa yazo yad’akkota yadora kan gadonda ake d’aukan majinyata sannan aka fice daita,emergency aka fice daita inda doctor zainba haroon wato momyn mashkur tashiga domin gudanarda aikinta.

Cikin b’acin rai umman ruwaida tafara magana “mashkur dan Allah kayaimaka kabama iyayenka hkr amaida yarinyar nan tinda dai anriga angano komai gsky tafito suyi hkr sumaidata inda tafi sani inda tai rayuwa,shin taya rana daya zasuce surabata dasu,dama ace sunmata mugun riko ne dasai ace mumaidata hanunmu amma harma munsamu sun rik’ata cikin amana,wlh ni namafi tausayin ita uwar tata sbd ance tanacan hawan jininta yatashi rai hanun Allah dik sbd anrabata daita,shin yakake ganin a lkcnda aka raba uwa da y’arta batareda wani daliliba,rabasufa tamkar raba hanta da jinine”.

Nannauyan numfashi mashkur yasauke kamin yace “abunda kika fada gsky ne umma,nima kuma nayi wannan tinanin,insha Allah zanyi iya kokarina naga bunayya takoma hanun iyayen rik’onta,yanzudai bara mufara ganin komai yazama normal tukuna”.

Tsawon 1hr dashiga da bunayya momy tafito tamasu bayanin tasamu bacci,gdy sukama Allah sannan suka zauna zaman jiran farkawarta.

Mashkur bin bayan momynsa yai suka tattauna matsalar dakuma yanda zasu shawo kan matsalar dake tasowa a ahalinsu,acikin k’ankanen lkc suka samo mafita dakuma yanda zasu shawo kan matsalar.

Sai dare sannan bunayya tafarka,koda tafarka mashkur bayanan sai faman rigima ake daita akan tasha magani tashi abinci sannan amata injections dinda ba’akarisaba, itakwa sai kuka take tana fadin “dan Allah narok’eku kubarni natafi gun iyayena kubarni natafi naga mahaifiyata,nasan yanzu tanacan acikin wani mawuyacin hali sbd rashina,wai meyasa bakuda tausayine meyasa meyasa” tasake fashewa da kuka.

Tausayinta ke ratsa jikin umma da momy umma harta kasa hkr da ganin yar tata acikin wannan halin saita fita waje dasauri tana sharar kwallah,
Anacikin wannan yanayin mashkur yadawo daga masjid,a kofa yatadda umma tana sharan kwallah,dasauri yashiga tambayarta abunda ke faruwa nan tafadamasa,numfashi yasauke sannan yashiga ciki.

Har yanzu kuka take sosai ta fizge cannula dinda aka sanyamata drip daita hanunta sai zubarda jini yake,dasauri yaje yad’akko plaster da kad’a sannan yariko hanunta yasanya mata jini yabar zuba,kuka take sosai tana fadin “da me kataimakeni ka maidani gun iyayena dan Allah nasan yanzu momy na tana cikin mawuyacin hali sbd rashina akusa daita,dan Allah ka kaini gun momy da me” tausayinta yamamaye zuciyarsa da gangar jikinsa gaba d’aya, janyota yai ya rungume yana bubbuga bayanta alamar rarrashi,ahankali ahankali kowa ta sausauta kukan.

Ahankali yajanyeta daga jikinsa sannan yatallafo fuskarta da hannayensa suna kallon juna yafara mata mgn “Is okay bunayya,zan maidaki gun momy da dady amma saikinsha magani kinci abinci kuma kinbari anmaki injection,kinga jikinki ba kwari ga zazzabi sosai,so kiyi hkr har kwana biyu kacal jikinki ya warware saina kaiki dakaina gun momy da dadyn ki,kinji ko” gyada masa kai kawai tai tasan zai maidata tinda dai yafada sbd tasan halinsa zai yi tinda yace zaiyi.

Dakansa yad’akko maganin yabata tasha sannan taci abinci sosai,daganan aka mata injection din sannan ta kwanta hanunta sakad’e dana mashkur har bacci yadauketa.

Da darema haka yasakata agaba taci abinci sosai sai a lkcn tatina da wayarta saidai wayar tanacan hanun dadyn ruwaida, mashkur yasakata agaba yana janta da fira hartad’an fara sakewa tana yar dariya idan akayi abun dariya.

Saida akayi sallar isha sannan yafita,suna sallah akafara kiran wayarsa,koda suka gama anmasa kusan 7miss calls kuma new number ce,danhaka bayan yagama yafito masjid saiya kira layin, ringing d’aya ana biyu aka d’aga, muryar dadyn bunayya yaji acikin wani yanayi yana magana “mashkur.....nine dadyn bunayya” cikin girmamawa mashkur yace “au....dady kaine” yace “eh nine mashkur,naita neman layin bunayya amma baya shiga shine naje school d’inku nanemo number d’inka sbd kai nasan zakafi saurarata” mashkur yagyara tsayuwarsa sannan yace.

“Incedai lfy dady?” dady yacigaba da magana “mashkur nasan mun aikatawa iyayen bunayya babban laifi, laifinda bakowane bil adam ne zai iyayin yafiya wa wanda ya’aikata irin wannan laifin ba, kuma wlh nayi nadamar aikata wannan laifin ahalin yanzu, jolde batada laifi acikin wannan lamarin,dik nine ummulhaba’isin wannan lamarin, tsintsar son yaya dakuma kaucewa tashin hankalinda ya fuskantomu a lkcn shys na aikata hakan, ina matuk’ar kaunar maryam kuma banasan rabuwa daita,nasani koda maryam bata haihuba bazan taba rabuwa daitaba amma gori da wulakanci ne nakemata gudu shys nad’auki wannan matakin,

Sannan itama a lkcn batada wani buri daya wuce taga gudan jininta maana ta haihu tasamu yaya kota halin kakane,shys kawai nayanke wannan hukun a lkcn, a yanzu kuma gashi abunda na aikata yazameman nadama da dana sani, a yanzu haka muna hospital da maryam rai a hanun Allah hawan jininta yatashi yanzuma yafi na da din,anyita kiran layin bunayya amma baya shiga sbd dikta farka bunayya kawai take kira shys naje school dinku domin kaucewa zargin mutane sbd banasan kowa yasan wannan lamarin,dan Allah mashkur kataimakeni domin shawo kan iyayenka,kuma kataimakeni bunayya tadawo”.

Nannauyan numfashi mashkur yasauke “Hmmm....!” sannan yafara magana “shkn dady,dama munyi magana da momyna akan lamarin,yanzu jira muke su dady sudawo sbd sunje Uganda acan hospital dinda abun yafaru, amma very soon zasu dawo insha Allah,zamuyi dik yanda zamuyi domin ganin anmagance wannan lamarin insha Allah, bunayya kuma batada lfy itama tak’i kwantarda hankalinta sai kiran momy take a yanzu hakama muna hospital daita ammadai taji sauki Alhmdllh”.

Jin bunayya ba lfy nantake hankalin dady yatashi matuk’a fiyeda d’azun dayace momy batada lfy,cikin damuwa yacewa mashkur “mashkur dan Allah ka kulamin da bunayya sosai karka bari wani abun na damuwa yasameta kajiko” dan murmushi mashkur yai sannan yace.

“Toh insha Allah, gobe insha Allah zankawo bunayya gun momy” jin haka yasanya dady cikin farinciki zaiga abar k’aunarsa” dasauri cikin mud’i yace “Ohk...toh saikunzo” mashkur yace “Ok....Allah ibama momy lfy” yace ameen sannan sukai sallama.
Chapter 12 · 0% Book details