← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin bunayya Alhmdllh danhaka washe gari mashkur yashirya yakai bunayya kebbi gun momynta kamar yanda yai alk’awari bisa amincewar momyn sa dakuma izininta dana umman ruwaida, yanda bunayya taga jikin momynta sai kuka yadawomata sabo, dakyar mashkur ya rarrasheta yasamu tadaina kukan, dazasu dawo dakyar yasamu yadakkota sbd tace bainda zataje tabar momynta cikin wannan halin,dakyar yad’akkota suka dawo yola adamawa.
...................

Tafiyarsu dadyn mashkur Uganda tazoda tashin hankali,suna zowa kai tsaye gun gomnar k’asar sukaje suka fadamasa abunda yake tafe dasu,nan aka kira shugaban hospital din,kundin jariranda aka haifa a shekara goma sha tara dasuka wuce aka d’akko nantake kowa aka gano file dinsu bunayya tareda yar uwarta ruwaida sannan aka d’akko na d’anda momy tahaifa dik a ranar, nan aka tabbatarda cewa bunayya itace yar uwar ruwaida wacca tace abokiyar tagwaicinta.

Ta hakan ne kuma suka gano doctor haji mansur wanda dady yasamu sukai aikin canjen jinjiraye guda biyu wato bunayya da babynsu, aikwa nantake aka saka cigiyar nemansa,acikin yan kwanaki aka ganosa aka gurfanardashi agabansu dady.

Dafarko maganar taso tayi zafi amma da’aka fahimci juna sai abun yasakko aka fara fahimtar juna, mahaifinsu ruwaida yanada zafi sosai shi soyai yakai zancen kotu,dakyar likitan yasamu yashawokan abban ruwaida tareda taimakawar gomnan jihar,tarar kud’i akacisa sosai sannan asibitin ta koresa tareda makasa kotu domin kwatar hakkinta na b’atamata suna dayake tsawon shekaru ashe aikinsa kenan.

Sudai abban ruwaida anbiyasu tararda aka doramasa kuma Alhmdllh tinda sun tabbatarda bunayya yarsu ce itace wacca aka masu exchange da mataccen d’a wanda banasuba,
Bayan ankammala komai saisuka tattaro suka dawo gida Nigeria.

Bayan dawowarsu ne momyn mashkur tasami dadynsa tarokesa akan yaroki abban ruwaida yabar bunayya tacigaba da rayuwarta da iyayenta na rik’o sbd zahirin gsky bazata iya rayuwa babusuba haka suma, nantabashi lbrn halinda momy take ciki a yanzu dan suma sunje dubata.

Dadyn mashkur yamata albishir dacewa sunbarmawa su dady bunayya har abada tinda dai basumata mummunan rik’o ba, hasalima suna matuk’ar k’aunarta, momy taji dadin wannan zancen matuk’a.

Tana batun takira umman ruwaida saigashi itama takirata,ashe itama zancen ne take batun tafadamata, mashkur ma lbrn yarizkesa yai farinciki matuk’a har saida yakira bunayya yatayata murna.

Tinda yake baitab’a ganin tsintsar farinciki a fuskar bunayya ba kamar yanzu, dik halinda take na k’unci tanajin wannan lbrn saita wartsake kamar baitaba sai farinciki take tana murna,nantake tafara shirin tafiya gida.

Washe gari harda su dady suka shirya suka tafi kebbi gaba daya, koda sukaje har ansallami momyn bunayya tana gida kuma Alhmdllh tasamu sauki kwananta biyu da dawowa.

Anan dai aka jajantawa juna tareda bawa juna hkr akan abunda yafaru, daga bisani abban ruwaida yadamka bunayya ahanun dady da momy amatsayin babbar kyauta yace “nabaku ita har abada kuma kusani nayi matuk’ar farinciki da irin rik’onda kukamata,so gatanan nabaku amana kucigaba da bata kulawa kamar da, Allah yayafemana kura kuranmu yabamu ikon bautamasa da karfinmu da lfyr mu” nan kowa ya amsa da Ameen.

Gdy mai yawa momy tadingayiwa abban ruwaida harda durkusawa kan guiwowinta dan farinciki saida tazubda kwallah bunayya tazo tarungumeta tana dariyar farinciki abundai gwanin ban shaawa, basubar garin kebbi ba saida momy tashiryamasu liyafa tagani tafada inda kowa yai hani’am da cikinsa,baya nan kuma tabi kowa da kayatacciyar kyauta.

Sun rabu da juna cikin farinciki bunayya na mak’ale da momynta kamar zata koma cikinta tasake haifota,yau da’alama shagwabar tamotsa,tana makale daita takemawa su mashkur bye bye, da zai wuce saida mirtsiketa a ciki tamasa gwalo tana dariya dan cewa yai tazo suje yola saisu koma school atare tace tak’i.

Suna kallon motocinsu har suka kure sukabar unguwar sannan suka koma ciki.

Ranar dai kwanan farinciki momy da bunayya sukayi,yau dady yafewa bunayya momy yai dan atare suka kwana d’akin bunayya dan yau shagwabar tamotsa.
.....................

Bayan faruwar wannan lamarin wata zumuncice mai k’arfi tashiga tsakanin iyayen bunayya nagaskiya dana raino, a yanzu sundawo tamkar yan uwan jini, yanzu dik su bunayya sukai hutu a yola take k’arisa hutun,tasaba sosai da yan uwanta.

A yanzu tasan yanda zumuncinsu yake da mashkur,wato da mahaifinta da mahaifin mashkur uwa d’aya uba daya suke, hajiya maimoon da Alhj murtala sune iyayen bunayya nagaskiya, doctor zainab haroon da doctor Abdallah sufi sune iyayen mashkur wanda doctor Abdallah shine Vice President a jihar yola shikuma barrister murtala shine PA din governor na garin yola,mahaifiyar bunayya tanada wani poundation na tallafawa gajiyayyu dakuma marayu.
To wannan kenan.
..................

Amintakar bunayya da mashkur sai k’ara k’arfi take a yanzu tinda sukasan matsayin junansu agunsu.
A yanzu bunayya takammala 100level zasu shiga 200level,inda shikuma mashkur yake acikin shekararsa ta k’arshe takammala masters degree dinsa, to Alhmdllh.

A yanzukam rayuwa mai cike da dad’i da tarin farinciki ke gudana a tsakaninsu.

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI......_*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_27/28....._
Ahalin yanzu bunayya sunshiga 200level danhaka karatu suke sosai ba kama hanun yaro,tana matuk’ar san karatinta sosai shys take k’ara burge mashkur yake k’arajinta da wani matsayi acikin zuciyarsa.

Bunayya da mashkur ne zaune akan kujeru agunda su bunayya kezowa karatu,wajen k’arkashin wata bishiyace mai bada kalolin iska masu dad’in gaske,musamman yanzu dayake yanayin damina,anyi ruwa yau da safe kusanma wuni akai ana ruwan,danhaka yanayin garin gwanin dad’i da bansha’awa,
Ba rana sai lushi ga gajimare dik sunrufe sararin samaniya.

Mashkur wani aikin yake kan laptop dinsa inda itakuma take game da wayarsa tata wayar tanakan cinyarta,surutu taketa zubamasa shikwa yana binta da ummm...um...um.

Tintana maganar itakad’ai harta gaji tafarajin yunwa, shagwab’e fuska tai kamar zatai kuka tace “da meeee....” batareda yad’agoba yace “na am, menene?” cikin yanayin shagwab’ar tace “uhm...uhm..nifa nagaji wlh yunwa nakeji”.

Batare yakalleta ba yace “Ok....je kici abinci mana,ni ina nan,idan kingama kizo ina nan so nake nak’arisa aikin nan naturasa zowa anjima” wata harara tamasa tareda turo d’ank’aramin bakinta kamin tace “what do you mean wai...nifa restaurant nakeso muje wlh,ni bazan iya zowa nai girki yanzuba,nagaji dacin indomie dinnan kasani kuma hamdallah taje weekend nikuma ba iya girkin tuwo nai dayawaba” yar dariya yai mara sauti sannan yace “Shkn naji,muje restaurant din” dariya tai tareda mik’ewa tsaye cikin farinciki hadda d’an tsallenta.

Shikowa sai dariyanta yakeyi a zuciyarsa yana fadin “bunayya...bansan yaushe zaki girmaba,koda yake shekara 19 ai baza’ayi mamakiba dan kinyi yarinta gakuma tsabar shagwab’a datamata yawa ba” yana tinanin har suka kama hanya suna tafiya tanamasa shegantaka harda cewa yagoyeta wai.

Hararanta yai yace “idan nagoyeki ai yau bazan iya tashiba sai amun gyaran targad’e a bayana” shagwab’e fuska tai tace “kai da mee...danka goyeni shine zaamaka gyara,nida ko wani k’ibar kirki banida shi,kuma banida nauyin kirki” dariya yai sannan yace “tabdi, kece bakida nauyi da kiba, ranar dana d’aukeki zan saka a mota dabakida lfy ko,saida nakusa fad’uwa k’asa dan nauy...” aibaiko k’arisaba tasakamasa kukan shagwab’a.

Dariya yadinga mata harda rik’e ciki, juyawatai tayi fushi bazataci abincinba, dakyar yasamu tahak’ura tajuyo suka tafi.

Yau takasance weekend suna hostel a zaune,fitowarta kenan daga wanka tana d’aure da towel a jikinta, biscuit takeci pure bliss mai dad’in gaske tanasan biscuit din sosai.

Hamdallah nagefenta tana had’a miya ta abincinda take dafa masu,kallan bunayya tai tace “waike bazaki tashi kije kisaka kayaba,kinyi wanka amma har jikinki yabushe baki shafa koda mai ne ba bare kisaka kaya” tab’e baki tai sannan tace “Allah ni yau ganda nakeji wlh, man ma idan zan samu ashafaman inaso wlh” dariya hamdallah tamata tace “lallai kanwar mashkur dinnan,yayan nan naki yana k’ara shagwab’aki da momy” itama dariya tai tana fara shafa man.

Bayan tashirya acikin wata abaya maroon color tasaka skin tide dark blue na jeans aciki da yar singlet fara aciki sannan ta taje sumarta gu d’aya hasken fuskarta yafito fas...golding eyes d’inta suka fito sosai goshinta sai haske yake yana shining, hamdallah bayan itama tashirya saita sakata agaba tamata simple make-up powder jan baki sai kwalli, hmm aikwa readers naso kuga bunayya a lkcn,tai matuk’ar kyau ba d’ankad’anba kamar kasaceta ka gudu, nan tamata rolling da veal maroon nantake tafito shuwa arabs ta asali.

Cikin murmushi hamdallah tacemata “kinyi kyau matuk’a yar uwa,gsky kinada kyau sosai tubarakallah masha Allah,wannan shine ake kira da tsintsar kyau na asali,inama da mee...d’inki yana kusa yaga wannan kwalliyar, kai barama nakirasa da wayata” dariya take tafizge wayar tana fad’in “ba da mee ba,ni gun sabon saurayina zanje nanunamasa yaji dad’i yai farinciki”.

Dasauri hamdallah tab’oye wayar tana dariya tafita,
Bayan yan mintina sannan suka fita atare,itama hamdallah yau abaya tasaka red color amma itakam tai make-up sosai sbd yau weekend ne dole sufita yawo.

Koda suka iso bakin get mashkur nanan yana jiransu acikin mota,ashe hamdallah nakiransa yakira wani abokinsa yakawomasa wata galleliyar mota Lang rover mai kyan gaske baka wulik sai shining take.

Mamaki ne yacika bunayya daganinsa hamdallah takashemata ido daya sai itakuma ta harerata sannan tabude marfin gaba tashiga itakuma hamdallah tashiga a baya.

Tana shiga yai murmushi tareda gyara zamansa yana fuskantarta,tasan halinsa sarai yanzu zai fara mata sharri saikawai tasha mur,aikwa wabakin boka,cikin murmushin tsokana yafara fadin.

“Am....hamdallah gsky kina kokari sosai,Allah dai isakamaki da alkhairi,kina kokari sosai wajen had’eman k’anwarnan tawa, gashi make-up yana matuk’ar yimata kyau amma kokad’an batasanyi bare takoya taiya,but...don’t worry insha Allah zansan yanda zaayi muma muiya wannan make-up din” hararan gefen ido tamasa saiya kwashe da dariya.

Tana hararansa tace “kagane da mee...idan baka tashiyin tafiyar nanba saina fita nabarma motar wlh” yana toshe bakinsa sbd dariya yace “Allah yahuci zuciyar sarauniyatar kyawawan k’asar kebbi,tuba nake sarauniyata, da girman kujerarki” nan yatada motar sannan suka wuce.

Kai tsaye wani had’adden park sukaje wanda yake d’aukeda wuraren hutawa da shak’atawa masu k’ayatarwa acikinsa, gu d’aya suka samu suka shimgid’a wani carpet mai kyau da laushi sannan suka zauna.
Ordering kayan fruits yamasu different colors had’eda juices kala kala aka cikamasu gabansu dasu.

Ahankali suka fara sha suna yar fira ahankali ahankali, bayan y’an mintina sai mashkur yamatso kusa da bunayya kasancewar a gefen damansa take,hanunsa yasaka acikin aljihunsa yaciro wata yar akwati akan kwalin akwatin antubutu “special gift”.

Mik’awa bunayya yai yana fadin “happy birthday to uuuu.....happy birthday to uuu...happy birthday happy birthday, happy birthday to uuuuu....., happy born day my lovely sister nd’ my bride to be insha Allah” waro idanuwanta tai tareda wage d’an k’aramin bakinta tafurta.
Chapter 13 · 0% Book details