← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 24

Sashe 4

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kimanin kwana hud’u dady yai a London sannan yadawo, aikwa koda yadawo daga momy har y’ar tata sunyi matuk’ar yin missing dinsa haka shima, kamar yanda yake al’ada agunsa dik yaje idan zaidawo saiyayowa abar k’aunarsa tsaraba, to yanxuma hakan take.

Hakan wasu english wears ne yasiyo mata masu kyau kala kala kasancewar tafisan wandina shys yafi siyomata su, zan iya cemaku Alhj kadel shine wanda yake bama bunayya gudumawa wajen tasaka kaya irin na arna, wai acewarsa haka yanayin k’asarda suke yake ai idan sunkoma gida Nigeria zata bar sakasu, hmm.

Shys tinda taso har izowa yanzu batasan saka kayan yarenta ba batamasan miye atampa ba sbd itama mahaifiyarta ba sakawa takeba, haka dik wata mace yar asalin Nigeria datazo kasar bawacca kesaka kayan hausawa ko yarenta saidai English wears hakama yayan nasu suma.

Yanxin ma wani tsingilallen wando ne ajikin bunayya girmansa iya cinya kai baima k’arisa rufe cinyoyinta ba, sai wata yar singlet fara mai gajeren hanu kanta sam ba mayafi ko d’ankwali, kai idan kaganta sam bazakace musilma bace kuma jinin musilmai.

Kwonce take akan kujera tana assignment momynta na a k’asa a kishingid’e tanashan fruits, dady ne yashigo d’auke da wasu kayan a hanunsa,cikin murmushi yazauna yana fad’in “bunayya zomuga kayan nan ko zasu maki” dasauri tamike tsaye tana dariyar murna taxo agabanshi tatsaya.

Wani wando ne yad’akko yad’ora a k’ugunta wanda shima girmansa iya cinyoyinta ne, cikin faraa tace “ai xaiyi dady kagama irin najikinane” momy ma dake k’asa tace “zaimata ai, kasan halin k’ugun nata sai a hankali” dariya sukai sudika dady yace.

“Bakomai,munji dai inkin isa kiyi kamarsa” tai dariya tace “nikam mema zanyi dashi yanzu nida na tsufa” bunayya tace “laaa....kai momy ina tsufa yake anan, wlh yanxu haka class mates dina cewa suke wai ke yayata ce ba momy na ba” daga momy har dady dariya suka kwashe daita.

Bunayya kam tattara kayanta tai tafice d’akinta itama tana dariya, dady yace “sauran kayan suna a bedroom dina kije ki d’akko” toh tace sannan tafice.

Washe gari takasance weekend danhaka kowa yana gida, kamar yanda suka saba weekend a gidan gonarda momy tasiya anan Australia sukeyinsa domin susha fruits kamar yanda suka d’aukarwa kansu shan fruits dik a weekend domin samun wani sinadari a gangar jikinsu.

Danhaka tin 9am suka shirya suka tattara sudika a gidan hadda masu girki da shara da dai gyaran gidan, mota uku suka cika suka fice.

Koda suka isa tini antsabtace gidan danhaka bawani wahala,
Bunayya dai swimming pool tafice taita wankanta sukwa su momy garden suka fice domin shan fruits.

Bayan bunayya tagama sannan taje tacanja kaya izowa wandan jeans bak’i girmansa iya guiwa da riga bak’a mai dogon hanu, bayan tashirya sannan tajegunsu momy.

Da dare sunjima sosai sunashan fira kamar yanda suka saba, dady nabasu labarin yarintarsa shi da yan uwansa sai shan dariya suke hadda rik’e ciki, sai kusan 10pm sannan sukaje suka kwanta shima saida sukaga bunayya tai bacci dan dadyne ma yad’auketa yakaita bedroom d’inta sannan sukuma suka fice.

Washe gari haka suka wuni cikin nishad’i acikin garden, sai 5pm sannan suka tattara suka koma gida.

Haka farinciki da jin dad’i suke cigaba da gudana acikin wannan ahalin.

Bunayya tacigaba da karatinta cikin walwala yayinda iyayenta kuma suke cigaba da gudanarda kasuwancinsu acan, yanzu abun harma yak’ara hab’aka dan sun fara ginin k’aton company a gida Nigeria mai d’aukeda tambarin sunan BUNAYYA, sunce sungaji da yawon k’asashen nan.

Dady kuma yace yanaso yahad’a kan iyalinsa gu d’aya kodan shak’uwa tashiga tsakaninsu kuma susan danginsu dakyau,amma wannan na london wannan Australia tin tasowarsu har girmansu taya zasusan danginsu kuma suso junansu.

Danhaka yamatsawa ma’aikatan ginin dasu matsawa aikin.
Anahakan saiga wani business din yafito masu wanda zasu samu riba sosai acikinsa a London, danhaka suka tattara sukabar Australia suka koma London, saidai ba’a wuri d’aya suke dasu momyn ammar ba.

Kokad’an bunayya bataji dadin dawowarsu London ba sbd yanda tashak’u matuka da friends dinta,takuma saba sosai da k’asar tanajin dadin kasar sosai,
Bayanda taiya haka tacigaba da rayuwa a London inda izowa yanzu harsunyi wata biyu da dawowa harma tafara zowa school a sabon school dinda aka maidata yanzu.

#/Vote nd’ Comment..
#/Aufana for life.
[7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....*_🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_9/10....._
Rayuwa tacigaba da tafiya kamar yanda aka saba cikin farinciki da walwala.

Kamar kullum yauma cikin sauri take shirinta nazowa school, saidai yaukam ta tashi batajin dad’in jikinta,ciwonta na mara yana nema ya tashi, danhaka yau sai a slow,bayan tagama sannan tafito dining room domin yin breakfast,almost 10mnts tab’ata kamin ta kammala break din sbd cin abinci bunayya fa saimai hkr, idan kana jiranta tafara cin abinci saikai hkr sbd bataci da sauri barema yanxu datakejin jikin nata.

Bayan tagama sannan taje ta sumbaci momynta a kunce hakama dadyn nata kamar yanda yazama al’ada agaresu tareda masu bye bye sannan tafice.

Har izowa yanzu takasa sabawa da sabuwar school dinsu gashi mararta sai faman ciwo take mata, abokiyar zamanta sai kallonta take yanda taketa faman murk’ususu amma takasa cemata komai sbd iyakacinta da bunayya hello hy shkn, gashi su biyune kadai akan kujerar kasancewar haka tsarin yake.

Tausayin bunayya yacikata sosai ganin yanda takeshan fama, dakyar tasamu teacher dinsu yagama darasin yafita, yana fita tariko hanunta tareda fadin “fatima meke damunki ne, tashi muje clinic” sbd azabarda takesha yasa bataimata musuba ta tashi dakyar suka fice.

Suna zowa a bayaninda tamawa nurse yasa tafahimci period dinta ne zaizo, danhaka tamata wani injection tabata magani tashi sannan tad’oramata drip, bayan angama sannan suka kira iyayenta.

Hmm...zo kuga abun mamaki readers koda momy taiso school din hawaye faca faca a fuskarta harda gudunta sbd tasan yanayin ciwon nata gashi kuma tanada asma mummuna irinta dadyn ta, aikwa tana isowa tarungume bunayya dikda bacci take, saida taji kyakkyawan bayani agun nurse sannan takwantarda hankalinta amma da hartace zata d’auketa izowa big hospital.

Zama tai anan har saida bunayya tafarka sannan hankalinta yakwanta dakyau, bunayya takalli yarinda takawota clinic din wato seatmate dinta tai murmushi sannan tace “thanks allot yar uwa,dikda bamusan junaba amma kin taimakeni” takalli momyn ta tace “momy kimata gdy itace takawoni wannan clinic din” itama momy ta kalleta cikin murmushi tace “sannu da kokari yata, Allah yasakamaki da alkhairi kinji kema Allah yataimakeki kamar yanda kika taimakemu”.

Yarinyar murmushi tai tace “bakomai momy ai yiwa kaine, Allah dai yabaya lfy” tace “ameen” bunayya tace “yah sunanki ne hala” cikin faraa tace “Nadiya Abdussalam” cikin murmushi itama tace “Ok...nikuma fatima kadel kabir amma ana kirana da BUNAYYA” tai murmushi tace “nice to meet u bunayya” itama tace “nice to meet u too nadiya”.

Momy kam kallonsu kawai take tanajin dadin sosai aranta abar k’aunarta tafara dawo da farincikin ta, sbd tinda suka dawo nan gaba daya walwalarta tagushe.

Sai kusan 3:30pm sannan suka fice, har gida suka kai nadiya suka shiga sukamawa iyayenta gdy sosai sannan suka fice.

Tin daga lokacin Nadaiya da Bunayya suka zama k’awaye gashi tasu tazo d’aya daita kusan halayensu d’aya dik barkatarsu iri d’aya ce, atare suke zowa party da dare hakama night club atare suke zowa gashi itama tanada tsintsar kyau sosai kamar bunayya saidai bunayya tafita hasken fata da cikar k’irji.
......................

Sannu ahankali karatin bunayya kecigaba da tafiya inda yanzu dika dika sati biyu kacal yarage sufara zana jarabawan karshe ta kammala secondary school dinsu.

Danhaka yanzu a koda yaushe cikin karatu suke, gashi tini ankammala ginin company dakuma sabon kantamemen gidanda aka ginamasu wanda zasu zauna aciki idan sunkoma.

Danhaka suma su dady shirin tafiya suke gida Nigeria acikin kwanan nan zasubar Bunayya a gidansu Nadiya harsu kammala exam dinsu sai dady yazo yadauketa su fice.

Ranarda zasu fice kowa har airport su bunayya suka masu rakiya bayan jirginsu yadaga sannan suka kamo hanyar gida.

Bunayya ke driving danhaka yanda taga dama haka take driving din, a maimakon su koma gida sai suka fice yawonsu wuraren shak’atawa da shan mak’u lashe, kowannensu sanye da wandan jeans da riga matsattsu dik surar jikinsu a bayyane take musamman bayansu, hips din bunayya kamar sutsaga wandan, sumarta da ribom daya ta tufketa.

Sai kusan 7:30pm sannan suka koma gida, abunka da k’asar jajayen fata dakuma d’aukan rayuwar wasu mahaifiyar nadiya ko tambayarsu inda suka fito bataiba,a dole su sungirma sun mallaki hankalin kansu gasu kuma yayan gold yan ido ba’amasu fada baasan ba’asan b’acin ransu, itama nadiya su biyu ne agun iyayensu ita sai najib kanenta.

Hakama suka b’ata dare sunata yin chart dinsu, nadiya tanada samari amma bunayya kam ko d’aya batada hasalima bata taba kula saurayi ko d’ayaba dikda kowa yanda samari keta mata rubibi amma taki bada had’in kai, hasalima haushinsu takeji.

Sai 2am sannan nadiya ta kwanta bunayya kam tadad’e dayin bacci.

Washe gari dasukaje school sai aka basu hutun sati daya domin suhuta kamin lkcn fara exam yai.

Hakan bak’aramin dadi yamasuba dan dai ranar a club sukai dare sai 3am suka koma gida, dasuka koma ma shisha sukadinga sha har 4 basuma san sadda bacci yad’aukesu ba, Sai kusan 8am sannan suka farka.
...................

Yau takasance Monday kuma itace ranarda zasu fara zana jarabawa,
Danhaka 8am suka fice school sbd by 10 zasu shiga exam din.

Sannu ahankali suka fara zana jarabawa cikin nasara, yau biyu kacal sukayi danhaka by 5pm suka koma gida, koda suka koma dik a hajiye suke danhaka wanka sukai suka canja kaya bunayya tasaka k’aramin wandan jeans girmansa iya cinya da riga wacca ko cibiyarta bata rufeba dan kana ganinta azahiri, nadiya kuma wata rigace tasaka girmanta iya cinya batama rufe cinyoyin dika ba.

Sbd gajiya yasa basuyi batun fita ba,bayan sunci abinci sukai zamansu a parlor suna kallo da chart.

Around 9 suka fita shan ice-cream,basu wani jimaba suka dawo gida.

Haka suka cigaba da gudanarda rayuwar su yanda sukeso,yayinda kuma a b’angare d’aya suke cigaba da zana jarabawansu.

Kimanin wata daya da sati daya suka kwashe suna zana jarabawan sannan suka kammala, ranarda suka kammala kowa hadda biki school din tamasu tareda basu kyautittika kala kala wanda bunayya ta amshi kusan uku,sunyi hotina kala kala da teachers dinsu dakuma principal dinsu da kuma sauran d’alibai yan uwansu.

Daga bisani kowacce tai nata itakadai domin tarihi, bayan angama komai sannan kowa yawatse.
Chapter 4 · 0% Book details