← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batajira komaiba tai cikin momy da masifa da zage zage da cin mutunci “wawiyar banza wacca bata gaji arziki ba mai farar k’afa dangin mayu, shine kikaje kisamo y’ar wasu kikazo kika lak’abawa d’ana amatsayin jininsa,to wlh k’aryarki tasha k’arya maryam,Allah yatoni asirinki yau kuma wlh saikin fuskanci mummunan hukunci agareni kamin kifara fuskantarsa a kotu,wlh babuke ba d’ana har abada,ki tattara kayanki da shegiyar y’arda kika d’akko mara asali kamar yanda kema kike mara salin kufitarmin daga gidan d’ana” daga momy har bunayya har hajiyar ramada dasu nafisa kannen ramadan dik kuka suke sosai, dakyar abban ramadan yasamu ya lallaba hajiyarsu yafice daita side d’inta jikinta sai rawa yake kamar yar danbe.

Saidai tace bataso momy da bunayya sukara minti d’aya acikin gidanta, bayanda suka iya suna kuka sudika momy taja bunayya suka fice.
Suna fita kai tsaye wani shahararren gidanta data ginawa bunayya suka wuce, gidan k’atone upstairs hawa daya, suna isa bunayya takira mashkur tafada masa halinda take ciki.

Kankace me wannan lbrn yabaza koina na dangin dady da momy, mahaifiyar momy kuka take sosai tana taisayawa momy sbd tasan dik rashin haihuwa ne yasakata acikin wannan halin, amma tasani Allah yana tareda ita baimanta daita ba.

Momy tayi kukan b’akin ciki harta godewa Allah,haka itama bunayya tsintsar tausayin mahaifiyar tata yamasa tadaina tausayin kanta, anan tak’ara d’aukan alk’awarin komai rintsi tana tareda momyn ta har abada.
......................

Dady yai dik yanda zanyi har saida aka fasayin baikon mashkur da bunayya a yanzu haka haryaci k’arfin dadyn mashkur da abban ruwaida wajen fasa aurarda bunayya wa mashkur,saidai suncemasa zasuyi shawara akan buk’atarsa, mashkur da bunayya basusan da wannan sabon zancenba.

Washe gari mashkur yai sammako birnin kebbi,koda yazo daga momy har y’ar tata sunfita hayyacinsu, nan bunayya tajasa izowa wani parlon domin sanin mafita wa wannan bakon al’amarin dayazomasu, suna zaune suna cikin magana sukaji momy na kwalla masu kira.

Dasauri suka fita saisuka taddata tanata kwarara amai kaman zata amayarda abunda ke cikinta, tintanayi da k’arfi harta gaza takai zaune bunayya na rik’e daita, sai abun yatsaya saikuma yadawo tacigaba dayi, kankaceme tayi laushi sosai,ganin haka yasa bunayya takira family doctor dinsu,saidai kash wayansa baya zowa danhaka suka d’auketa izowa hospital.

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_31/32...._
Mashkur ke driving bunayya kuma tana rik’e da momy, gaba daya momy tafita hayyacinta tarike hanun bunayya gam tanaso tamata mgn amma takasa,bunayya kowa kuka take sosai tana fadin “am sorry momy,am sorry zaki samu sauki momy” jikinta karkarwa yake sosai,hakan ya tabbatarwa da bunayya hawan jininta ne yatashi gakuma yunk’urin amanda takeyi har yanzu.

Bunayya gani take kamar motan bata gudu hakan yasa cikin kakkausar murya tacewa mashkur “mashkur kai sauri mana” ai koda suka ankara momy tasuma, hakan yakara d’agawa bunayya hankali kukanta yak’aru sosai tarungume momy tanata kuka mai sautin gaske.

Hankalin mashkur yatashi sosai,dakyar yaga sun iso hospital, yanayin parking yafito yai cikin asibitin yakirawo nurses sukazo aka fito da momy ciki aka fice daita cikin hospital din.

Jikin momy yai tsanani sosai bunayya sai kuka take mai tsanani sbd ganin halinda mahaifiyarta take ciki, kankace me itama asmanta yatashi tazube k’asa wanwar somammiya, a gigice mashkur yad’auketa aka shiga daita emergency room domin bata taimakon gaugawa,numfashinta nema yake yamata k’aranci hakan yasa suka sakamata oxygen domin yataimaka mata wajen samun wadataccen numfashi.

Gaba daya hankalin mashkur yakai kololuwa wajen tashi, inyaje nan yaje can,badanda yake namijiba shima dayanzu yasuma d’in,ganin shikad’ai a hospital din yasa yakira mahaifsansa yasanardasu halinda bunayya da mahaifiyarta suke ciki,aikwa ba b’ata lkc abban ruwaida da umman ta dakuma momyn mashkur suka iso birnin kebbi.

Sunmatuk’ar tausayawa momy sbd yanzu itace abar tausayi fiyeda kowa, momyn mashkur tace “ammadai wlh dadyn nan na bunayya yabani mamaki matuk’a,shys sai kaita ganin mata dayawa suna zagin halayen maza,amma ni wlh bantab’a d’aukansu amatsayin masu hankali koku nad’auki maganar serious ba sai yanzu,lallai kam yanzu natabbatarda gskyr abunda suke fad’a,namiji kanen ajali” murmushi mashkur yai umman ruwaida tace.

“Wlh nima yabani mamaki matuk’a,dan Allah yanzu shi ko cewa akayi da wasa zai iya cewa ma yana san bunayya ai wlh nad’auka zaice aa koma ya wulak’anta dik wanda yafurta wannan zancen,amma harma shi dakansa wai zaice yana santa harda maganar aure,yarinyarda tace batada wani uba bayan kai,haba haba wannan wane irin rashin kunya ne” momyn mashkur tace.

“Ke nifa bamashi yafi bani haushi da takaiciba kamarsu dadyn mashkur,wai kawai yasamesu yazubamasu banzan zancensa kawai suka fasayin engagement din, da ace ina wurin hmm....”.

Shidai mashkur kallonsu kawai yake yana saurarensu,abban mashkur yafita yaje gun abban ramadan.

Around 7pm bunayya tafarka kuma Alhmdllh jikinta normal asmar ma tasauka numfashin ne dai da k’irjinta takejinsu har yanzu badaidaiba, momy kam har yanzu abun saidai addu’ah kawai, hankalin bunayya har yanzu yakasa kwanciya sbd tasan matsalar hawan jinin momy,amma abunda yafi d’agamata hankalima shine amanda momy takeyi wanda bata tab’ayinsa ba tinda matsalar tasameta.

Around 10pm suna zaune momy da umma bunayya kuma tanakan gado a kwance da oxygen a hancinta amma ba bacci takeba,momy kuma har yanzu tana emergency nurses na kula daita,mashkur da abban ruwaida kuma sunfita tin d’azun.

Yar fira sukeyi ahankali ahankali saiga mashkur yashigo d’aukeda wata takarda a hanunsa fuskarsa kuma d’aukeda faraa da murmushi dakuma farinciki tsintsa.

Ko sallama baiyiba yashigo yana fadin “momy wani abun alkhairin yasamemu, dama ance dik kaga tsanani yai tsanani to sauki yana taredashi, Alhmdllh momyn bunayya dai tana d’auke da juna biyu harna tsawon wata uku da kwana biyu” bunayya dake kwance idanuwanta a rufe dasauri ta tashi a zaune tana cire oxygen dinda ke hancinta, momy kowa dasauri ta karb’i result din tana dubawa cikin farinciki.

Umma tace “kai Alhmdllh masha Allah, Allah kaine abun gdy Allah maji rok’on bawansa, natabbata idan yan uwanta sukaji wannan maganar bak’aramin farinciki zasuyiba” bunayya kowa wani irin farinciki taji yamamayeta itama takarbi result din tana dubawa, tabbataccen ciki natsawon wata uku da kwana biyu saikuma jininta daya.

Ahankali tafara magana cikin yanayin rashin kwarin jiki gakuma yanayin rashin lfy dake tattare daita “tabbas Allah shine abun gdy,Allah maji rok’on bayinsa mai karb’an addu’ar bayinsa tahanyarda basu zataba, ashe Allah yanufa momy na zataga jininta itama nima nakusa nazama aunty nasamu k’ane kokuma k’anwa abokiyar shawarata, Alhmdllh....Alhmdllh....Ala kulli haaliin gdy da jinjina sukara tabbata ga fiyeyyen halitta” dikansu murmushin farinciki suke mara misaltuwa,bunayya wayarta tad’akko tashiga neman layin hajiyar momy.

Saidai kash bata samuba hakan yasa bataji dad’iba sbd taso ace itace mutum tafarko dazata farajin wannan daddad’an lbrn, layin aunty kuluwa tashiga nema,bugu daya ana biyun ta d’aga nan suka gaisa sannan tasanarmata momy na asibiti batada lfy,bayan nan kuma tafad’amata cewar a yanzu haka momy na d’aukeda juna biyu.

Tsalle aunty kuluwa tai tareda fadin “keh...! y’ar nan,kisake fad’a bad’i ma, maaasha Allahu barakallah,kai Alhmdllh incedai tana cikin koshin lfy koh” bunayya tace “Eh Alhmdllh,ammadai yakamata kuzo gobe momy sbd nikad’aice anan saisu umman bagudo” aunty kuluwa tace “karki damu gobe insha Allah zamuzo bara nakira su yaya baffa da hajiya nafad’amasu” tace ok sannan sukai sallama.

Kankace me lbrn cikin momy yakarad’e gari hatta can bagudo dik ahalinsu kowa saida yaji,aikwa murna da farinciki baya misaltuwa musamman hajiyarsu momy dan itakam saida tai sujudul shukr tagodewa ubangiji.

Anama dik masoyin momy yajimata dad’i,hajiyarsu ramadan tinda sassafe tasaka akai breakfast mai kyau tashirya ta taso ramadan dasu feena sukazo asibiti, ta matuk’ar nuna farincikinta bakad’an ba,sund’an jima anan kamin daga bisani suka wuce.

Har izowa yanzu momy bata farka ba kuma anhana kowa shiga inda take sai nurses da doctor kawai.

Around 12pm dot mutan bagudo suka sauka,hmm.....abun mamaki agun y’an kallo,mamakine yacika mutanenda ke cikin asibitin ganin yanda dank’ara dank’aran motoci tsala tsala ke roshing acikin hospital d’in kuma dik na ahalin gidansu momy ne, uncle Muhammad ne wato babban yayan su momy wanda takebi yazo,shahararren d’an kasuwan nan wanda duniya tasani tareda k’annensa biyu maza uthman da Aminullah tareda mahaifinsu Alhj Ahmad, saikuma kannensu mata uku wato manyan hajiyoyin nan masuji da naira tak’ama dakuma alfahari,aunty kuluwa da yaya hauwa sai kuma kanwar momy Rukayya.

Atare suke da bodyguards d’insu suna take masu baya har suka iso gun momy, bunayya naganinsu taje da gudu tarungume uncle Muhammad tana fadin “oyoyo my uncle” shima yarungumeta tareda shafa sumarta.

Bayan sun gaggaisa dasu abban ruwaida da dadyn mashkur dan shima yazo sannan yaje sukai magana da doctor.

Acikin yan mintina aka kammala komai sannan aka d’auki momy aka fice daita India.

Mashkur yakoma school tareda bunayya,uncle Muhammad dasu abban ruwaida sune suka tafi India din,
Tsawon sati daya da kwana uku suka kwashe acan ana kula da momy,Alhmdllh kuma tasamu sauki sosai,a ranarda suka cika sati biyu aranar suka dawo gida Nigeria momy har y’ar k’iba tayi masha Allah gakuma hasken ciki datai wanda yak’ara fito da yarintarta dakuma ainahin kyanta, bak’aramin dad’i bunayya tajiba aranarda suka dawo itakuma washe gari tazo tinda sassafe sbd yanayin karatinsu yafara zafi gakuma mashkur sunagab da kammala karatinsu.

Uncle Muhammad yazauna dasu abban ramadan da abban ruwaida dakuma dadyn mashkur had’eda sauran yan uwan momy maza,inda ya tattauna dasu akan matsalarda take faruwa a yanzu har yanzu momy tana gidanta bata koma gidan dady ba.

To magana tai nisa har suka kaiga yanke shawara akan za’a aurawa mashkur bunayya nanda wata d’aya kacal, batun dady kuma abban ramadan yace abarmasa komai hanunsa shi zaisan yanda zaiyi dashi momy kuma tacigaba da zama a gidanta har izowa lkcnda zasu zauna da hajiyarsu dady domin shawo kanta tinda dai ba’asaki da ciki sannan yanzu komai ya daidaita ayafi juna kawai.
To Alhmdllh anan shawara tatsaya akai addu’ah sannan aka watse.

Haka kowa akayi momy tacigaba da zamanta acikin katafaren gidanta dakuma d’ankaramin cikinta wanda yakeshan kulawa sosai dakuma y’arta abar k’aunarta.

Bayan kwana uku dayin zamansu uncle Muhammad akai k’ayataccen baikon y’ayan shahararrun y’an kasuwa dakuma ma’aikatin gomnati had’e da yanka sadaki dakuma saka rana wata mai zowa, mashkur da bunayya.

Baikone akayi nagani na fad’a idan kaga yanda akai baikon kaikace wani d’aurin auren d’an sarki ne,uncle Muhammad yasaki naira yanunawa momy tsintsar sonda yakemata a fili amatsayinta na k’anwarsa shalelensu, hakama sauran yan uwansu dik sunyi tasu bajintar,mashkur da bunayya suna school labari yarizk’esu.
Chapter 16 · 0% Book details