← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 24

Sashe 11

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tini kwallah sungama wankewa bunayya fuska dakyar taiya gyada masa kai alamar tayarda,nan suka dunguma suka fita,sudika akai tafiyar dasu,dayake unguwar batada nisa da wannan unguwar nantake suka isa,atare gaba daya hadda momyn mashkur dakuma security’s hudu suka tafi.

Shima gidan kam sai kallo kawai sbd shima bak’arami bane,amma shi yafi kama da gidajen sarautu,sbd komai nasa irin na gidan sarauta ne, daisarsu mahaifin ruwaida Alhj sunusi suka fara cin karo dashi yana alwalar magrib,yana ganinsu baiko k’arisaba dasauri yamike tsaye arazane,waro idanuwansa yai tareda dafe kirjinsa kamin yakwallah kiran “Hajiya...hajiya maimuna kina inane?” wacca yakira da maimuna tafito daga wata kofa dasauri a firgice sbd irin kiranda yake mata.

Tana zowa taga bunayya da ruwaida atsaye gu daya,tsananin mamakine ya bayyana k’arara a fuskarta kamin tamatso kusa dasu ta tab’a bunayya takuma taba ruwaida, dik hakan baimasuba har saida tariko hannayensu atare,kwallah ne suka fara ambaliya a fuskarta kamin tajanyosu sudika ta rungume tana fad’in “tabbas naji ajikina wannan ranar zatazo,naji ajikina komai daren dad’ewa zan ganki da idona ko araye ko amafalki kokuma a lahira,ashe araye zan ganki” shafa fuskar bunayya tai cikin wani irin yanayi naban tausayi tace,

“Bansan miye dalilinsu ba narabani dake,bansan memuka masuba suka rabamu dake” kwallah sungama wankewa bunayya fuska tas bakinta har rowa yake tafara magana “in..in...inaso kibani lbrn ya’akayi kuka rabu dani tin ina acikin tsumman goyo wato jinjira..?” momyn su mashkur ce tai saurin cewa ku dakata, Is okay...wannan zancen ba’anan yadace ayisaba,kuyi hkr gobe mushirya gaba daya mutafi kebbi gun iyayen ita bunayya,acan yadace ayi wannan zancen domin gano gskyr wannan lamarin,yau by 8pm VC zai dawo insha Allah,so kunga gobe saimu tafi gaba daya”.

Nan suka d’unguma suka shiga cikin gida atare, Alhj Mahmoud mahaifin ruwaidah yakasa zaune yakasa tsaye da farinciki sai nan nan yake da bunayya,haka itama ruwaida da momynta,kai incemaku kowama sai nan nan yake daita kamar suhad’iyeta.

Saidai ita dik wannan baya gabanta,tarin tambayoyinda ke gabanta sunma hanata sukuni,tamatsu safiya bata wayeba taganta kebbi,abincima k’inci tai gashi su ruwaidah sunhad’amata kala kala kuma dik waenda takeso ne dan mashkur ne yabasu wannan satar amsar.

Dik yanda sukaso bunayya tasaki jikinta takasa sunyi sunyi tak’i daga karshema saita sakamasu kuka,danhaka suka kyaleta ruwaida bataji dadin hakan ba taita rarrashinta tak’i,cikin b’acin rai takyaleta,dataga tak’i dainawa saitaje tafad’awa mashkur.

Kuyi manage da wannan mahade anjina da maraice, ngd sosai da k’auna.love u all my fam.💋💔

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_23/24....._
Dawowarsa kenan da masjid sallar isha,jallabiya ce ajikinsa maroon color da carbi kansa ba hula,koda yashigo parlor ammin sa dasu ruwaida dik suna zaune anacin abinci kamar yanda yake al’adar gidan bayan sallar isha a babban parlor ake had’uwa aci abinci atare, gaida ammin sa yai ta amsa su ruwaida ma suka gaidasa sai ammi tace.

“Mashkur yarinyar nan takasa sakewa damu,kaje kaida tafi sabawa dakai kagani abincima tak’ici tin d’azun,ni airport zamuje da yaran nan d’akko dadyn ku” ohk momy....yafad’a sannan yafice izowa dakinsu ruwaida inda bunayya take.

Ahankali yatura k’ofar d’akin yashiga cikin sallama,can yahangota ta tattakure akan gado,k’arisawa yai ciki yaje yazauna sannan yamata alama da hanu yana cewa “zonan” ba musu kowa kamar kazarda kwai yafashewa a ciki ta taso tazo tazauna tareda sadda kanta k’asa.

Matsoda fuskarsa yai daidai tata sannan yafara mata magana “meyasa kikak’i cin abinci bunayya?” cikin murya irinta marasa lfy tace “banajin yunwa kaina ke ciwo” hanunsa yakai yatab’a goshinta saiyaji yanada zafi, kallonta yai wanda itama shid’in take kallo amma yana kallonta saitai saurin d’auke idanuwanta akansa, numfashi yasauke kamin yace “ina zowa” tareda mik’ewa yafita.

Bayan yan mintina yadawo d’auke da magani a hanunsa da ruwa a glass cup, bayan yazauna saiyace “oya...karb’a kisha” juyamasa kai tai alamar aa tareda fadin “nifa komai nawa baya ciwo,iyayena nake tinani inaso naga momy da dady domin jin gskyr abunda waennan mutane suka fada, shin taya akayi har izowa wannan lkcn basu sanardani cewa basune iyayena na gsky ba, kai mashkur nifa har yanzu ban gasgasta abunda kuka fadaba,sbd da’ace momy da dady basune mahaifanaba da tini nasani koda su basu fad’amanba dole wata rana duniya tafad’aman sbd nasan dole momyn ammar taman gorin wannan abun,amma hakan bata taba faruwa daniba,bawanda yatab’a ceman su dady basune suka haifeniba,

Mashkur tinda nataso bayan so da k’auna dakuma tarin gata bansan komaiba,bantaba sanin miye d’acin rayuwa kokuma bakin ciki ba har izowa yanzu,momy da dady sun nunaman gata fiye da kowa a duniya,hakama ahalina biyu dangin mahaifina da dangin mahaifiyata,a yanzu haka inada tarin miliyoyin kud’i a account dina waneda dangin mahaifiyata suka bani a lkcn haihuwata,haka kuma inada motocinda suka kai bakwai ko takwas waenda mahaifiyata da mahaifina dakuma dangina ke bani a dik lkcn birthday sbd tsintsar kaunarda sukeyi agareni,natabbata da sunsan ni ba yarsu momy bace dabazasu bani suba,har gobe bawani abu a duniya wanda momy na keso fiye dani,hakama dady na yafisona sosai akan sauran yayansa,tsintsar sonda yake nunaman yasan yan uwana sukejin haishina,

Mashkur taya zan yarda da wannan labarin da kukazoman dashi, tayane mashkur...?” nannauyan numfashi mashkur yasauke batareda yace komaiba sbd kuka take harda ciccika,gashi shikowa baya k’aunar kukanta kokad’an, saida ta sausauta sannan yafara mata magana.

“Bunayya inaso kigane wani abu,itafa rayuwa ba abunda bazata iyayiba domin cimma burinta,sannan inaso ki fahimci wani abun,kiyi duba da koda kamanceceniyar da kikeyi da ruwaida sannan idanma ace wai kamanceceniya ce kawai to kiduna mahaifiyar ruwaida wacca itace ruwaidan tabiyo sak,sannan kiduba sauran yan uwan rwaida guda uku,dikansu kunada kamar jini dasu,itakuma ruwaida kamarku tama b’aci wanda inba tagwayeba baza’ataba samun irin wannan kamarba,kamar jini bahaka takeba, sannan bunayya kiduba dangin can dadyn ki dakuma momynki akwai wanda akace kike kama dashi koda ba momynki ko dadynki ba..?” shuru tai tana tinani kamin tafurta kalamr “a..a” saiyace “to kingani,sannan mahaifiyar ruwaida bata taba saninkiba kuma bata taba ganinkiba saidai taji lbrnki agunsu ruwaida amma tana ganinki tagane cewa ke yarta ce wacca tahaifa acikinta” saiya gyara zamansa sannan yace “So yanzudai koma miye kiyi hkr kici abinci har gobe muje muji gskyr lamarin agunsu dady, danhaka kisakko kici abinci sannan kiyi wanka kifito parlor” girgiza masa kai tai alamar bataci.

Hanunsa yakai kan cikinta tareda fadin “wannan cikin nakine zakice bazakici abinciba,ina maza sakko nabaki dakaina kinsan banasan kina zama da yunwa koh” badan tasoba kuma bayanda taiya sbd da me d’inta bayasan musu,bata sakkoba shiya dibo abincin yazo yafara bata tanaci,saida taci sosai ashe wata wahalalliyar yunwa takeji batasaniba sai a lkcn,bayan taci sannan tasha ruwa.

Dakansa yad’akko mata towel yabata sannan yacire mata mayafinda tawani lullube kanta dashi yace “oya...tashi kiyi wanka” ba musu tamike tareda karban towel din sannan tashige bathroom.

Koda tafito harya kawomata kayanda yasiyo mata d’azun,nan tabude tadakko wata sleeping gown mai kyau pink color mai hade da wando,sakawa tai sannan tafeshe jikinta da tirare sannan ta kwanta.

Washe gari ma bata fito breakfast ba sai kaimata akayi,saida dadyn mashkur daya dawo gida da dare shine yaje sakansa har gunta yaganta tagaidashi cikin girmamawa.

Around 10am dot kowa yashirya aka fara shirin tafiya,iyayen ruwaida sunzo acikin dank’ara dank’aran motocinsu har uku,anan kuma aka fitarda hudu,saidai mashkur yahana sutafi da security’s ko bodyguards yace wannan matsalar cikin gida ce.

10:30am dot sukabar garin yola izowa kasar kebbi state.

Saikusan 3:30pm sannan suka iso kebbi state,kai tsaye gidansu bunayya suka nufa wato gunsu momy kenan, koda suka iso masu gadi suka tabbatar masu da dady yafita tin d’azu,nandai aka bude masu get suka shiga,mota natsayawa bunayya tabude tafito tafice dagudu tana kiran sunan “momy...momy...momy naaa....” hajiya jolde dake kitchen tana aiki jin muryar farincikinta yasa tafara murmushi sannan tafito tana fadin “na aaam....abar k’aunata” dagudu tazo tarungumeta tareda fashewa dawani sabon kuka.

Hankalin hajiya jolde ne yafara tashi tashiga tambayarta abunda ke faruwa,tana shirin fara mata bayani saigasu mashkur sunshigo.
Ganin ruwaida da momynsu yasa tawaro ido cikin tsintsar tashin hankali,kallon bunayya tai tace “bunayya a ina kika hadu da waennan ne,su waye su?” ammin mashkur ce tace “dawaennan tambayoyin naki dafara bamu wajen zama kikai tukuna dazaki samu amsoshinki dika kuma a nitse” ba musu kowa momy tamasu bismillah suka zauna.

Wayarta tad’auka takira dady tacemasa dik inda yake yadawo gida yanzu,har yatsaya tambayarta abunda ke faruwa saita katse kiran,tsawon 1hr bawanda yakecewa komai har dady yaiso.

Kansane yad’auki jiri a lkcnda yagasu ruwaida musamman ma dayaga bunayya kusa da momy saikuma yaga ruwaida kusa da mashkur,shikanshi badanda suke a rarrabeba dabazai iya gane wacece bunayya ba sbd yaga dik fuskarsu iri daya ce hatta hasken fatarsu ma iri d’aya ne.

Yana ganin haka yatabbatarda lallai ranarda suke gudu tazo,ahankali yakariso parlon sannan yaje yabama su dadyn mashkur hanu suka musabaha suka gaggaisa sannan yazauna, bayan yazauna saiya fara magana “am...meke tafe dakune...?”Dadyn mashkur ne yafara magana.

“Toh dafarko dai munayiwa Allah gdy, saikuma abunda yakawomu shine,munaso muji daga bakinku,shin wacece bunayya agurinku, kunsandai tinda kuka ganmu ahaka to tabbas babban al’amarine yakawomu,munhana kowa yasan wannan lamarin sbd matsalace ta cikin gida,to sbd haka kufad’amana gskyr wannan lamarin sbd bamasan abun yakaimu ga b’acin rayuka namu ran yab’aci haka kuma naku ran yab’aci” shuruu dady yai batareda yaiya cewa komaiba yayinda momy ke zubda zafafan kwallah,haka bunayya ma ganin momynta na kuka yasa itama takasa daina kukan.

Nannauyan numfashi dady yasauke sannan yafara magana “toh dafarkodai kamin nafara cewa komai inamai baku hkr dakuma neman yafiyarku akan babban lefinda muka maku tsawon shekaru goma sha tara, tabbas bako tantama shekara goma sha tara ne cif cif, tabbas fatima bunayya yarmu ce,amma azahirin gsky bamune ainahin iyayentaba sbd bamune muka haifetaba.....” wannan kalmar tadaki k’irjin bunayya har saida wata kwallah tazubomata a ido d’aya.

Dasauri ta mik’ewa a tsaye tareda fadin “karka gasgata abunda suke fada dady,karka biyemasu dan Allah,wlh ni bazan yardaba banida wasu iyaye a duniya bayan ku,kune iyayena dady dan Allah kada kuce bakune kuka haifeni ba” saita kalli momynta tariko hanunta tace “please...momy ki k’aryata abunda dady yake fada dan Allah” janyota tai tarungume sbd matsanancin kukanda take sam bazata iya juresaba.
Chapter 11 · 0% Book details