← Book details Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 24

Sashe 15

Aurenta Zanyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafe kansa yai tareda furta “innalillahi wainna ilaihi rajiun,shkn sungama dani,to amma wlh anyanka ta tashi” cikin tsintsar mamaki momy tace “mekake nufi da hakan kadel...?” batareda yadamu dakowace yake magana daitaba yace “ina nufin bazan taba amincewa da wannan had’inba, sam bazan amince da wannan lamarinba” mamakin momy karuwa yai.

Tacika taf da mamakin dady, cikin mamaki tace “kadel meyasa bakasan dik wani namiji yarab’i bunayya,meyasa kake k’in amincewa dadik wani namiji dayazo neman auren Bunayya,meyasa...meyasa kadel” dasauri yafurta “sbd AURENTA ZANYI....maryam” yafad’a dak’arfi har saida momy taja da baya dasauri tareda dafe bango, nantake kwallah suka fara zubomata na mamaki da rakaici.

Gaba d’aya dady yafice acikin hayyacinsa yadawo tamkar mahaukaci,cigaba yai da magana cikin kakkausar murya yana zazzaro idanu yana nuna momy yace “bawani d’a namijinda yadace da bunayya, nine nan namijinda yadace ya aureta, inaso kisani maryam, tin lkcnda bunayya tafara mallakar hankalinta girma yafara kamata tin lkcn matsayinta yacanja a zuciyata,nikaina bansan lkcnda zuciyata takamu da tsananin SO dakuma K’AUNAR bunayya ba,bansaniba maryam”.

Kwallah momy keyi masu zafin gaske bakinta har rawa yake hakama jikinta karkarwa yake kamar maijin sanyi, bakinta na rawa tace “kak...kak...kadel,yau kaine dakanka kake fad’ar kanasan y’armu bunayya da aure, kadel wace amsa katanadarmana wacca zamubama ahalinmu biyu,kadel kayi tinani mai kya mana,koda badan kaiba,kodan ni kadel”.

*Aslm...my fam.
am kuyi hkr kwana biyu najina shuru,jikin ummanmu ne sai ahankali,amma Alhmdllh tafara samun sauki sosai,muna gdy da adduoinku,kucigaba da sakata acikin adduoinku dan Allah,Allah ibata lfy mai d’orewa Ameen.👏

#/Comment nd’ Share
#/Aufana for life.
[7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_29/30....._
Kuka momy keyi mai tsanani tana fad’in “haba kadel haba haba...wannan wane irin gurb’ataccen tinanine zuciyarka keyi,kada kabari zuciyarka ta rinjayenka mana,katinafa bunayya y’a take agaremu ba k’anwa ko y’ar uwa ba,kadel taya zaka furta wannan kalmar ta SO tsakaninka da bunayya” shikansa kwallah yake zubarwa waenda yakasa sanin namiyene.

Cikin muryar kuka yake fadin “nima bansan sadda abun yashiga zuciyata ba Maryam,nadade ina d’awainiya da SON bunayya,wannan dalilin ne yasa nahana kowanne namiji ya rab’eta dasunan soyayya ko san aure badan komaiba saidan naji saukin samun kanta wajen amincewa dani, wlh maryam bazan taba iya rayuwaba idan ban auri bunayya ba,nikad’ai nasan irin k’aunarda nakemat....” bai k’arisaba momy tai wata k’ara mai sautin gaske tareda furta “ya’isa haka kadel,banasan nasakejin wannan maganar”.

K’ararda tai yasa hankalinsu aunty kuluwa yatashi sukayo d’akin dagudu domin ganin abunda ke faruwa, momy naganinsu taje da gudu tarungume aunty kuluwa tana kuka mai tsanani,gaba daya hankalinsu yatashi matuk’a ganin momy da dady suna kuka,tambayarsu suka shigayi a firgice abunda ke faruwa.

Dakyar momy taiyayin magana cikin sheshekar kuka “kufad’amasa yajanye k’udurinsa na auren bunayya dan Allah,nayi nayi amma yadage akan saiya aureta wai,nikuma wlh bazan iya zama da y’ata a matsayin kishiyata ba,wlh mutuwa zanyi dik yak’i daina wannan maganar”.

Gaba daya sun rikita kwakwalwar su aunty kuluwa sam sunkasa fahimtar inda zancensu yadosa,cikin rashin fahimta yaya hauwa tace “wai jolde me kike nufine,kunsakamu acikin rud’u kun rikitamuna kwakwalwa, kumana kyakkyawan bayaninda zamu fahimta dan Allah mana” momy kuka take sosai kamar ranta zai fita,shikowa dady yadafe kansa da hanunsa d’aya.

Dakyar momy ta sausauta kukanda take sannan tafara masu bayani sbd tasani yau ranar bayyanar asirinda suka dad’e suna rufewa ce tazo,saidai bata tab’a tinanin kadel ne silar fallasar wannan sirrin ba,nannauyan numfashi tasauke had’eda shesheka sannan tafara magana cikin muryar kuka.

“Kuyafeni aunty kuluwa, dan Allah kugafarceni sannan kuyiman kyakkyawor fahimta akan kuskurenda na aikata abaya wanda babuwani mahalukinda yasani sai kadel da doctor haji,saikuma ainahin iyayen bunayya dasuka sani yanzu” mamakine yabayyana k’arara a fuskokinsu aunty kuluwa,sai momy tacigaba da magana.

“Hak’ika sai yanzu ne nake nadama dakuma dana sani mai tarin yawa,batareda dogon nazari dakuma zurfin tinaniba nabiyewa kadel muka aikata babban lefin wanda akarshe yanzu nine narufta aciki,saidai wlh insha Allah koda zan rasa dik abunda na mallaka ne bazan taba bari hak’ar kadel tacimma ruwa ba” yaya hauwa tace “munajinki jolde” sai tacigaba da magana “a lkcn shekarun baya lkcnda nake neman haihuwa ido rufe a lkcn ne na amince akamun dashen kwayayan haihuwar kadel a mahaifata, cikin ikon ubangiji kowa saiga ciki ya bayyana a mahaifata,nayi matuk’ar farinciki hakama ku dangi musamman ni sbd koba komai zan rabuda gori da wulakancin uwar mijina wacca a kullum takeda burin rabani da mijina, bayan cikina yaisa haihuwa mukaje asibiti nahaihu,

To saidai wani iko na ubangiji sai haihuwar tazo da matsala sbd babyn yamutu tin aciki,dagani har kadel munshiga tsananin tashin hankali musamman ni sbd a lkcn banaji bana gani idanuwana a rufe suke domin samun d’a, to hakan ne yasa kadel yasamu wani doctor haji yarokesa yakuma biyasa mak’udan kud’i domin yab’oye mutuwar babyn mu tahanyar yin exchanging babyn mu dawani babyn, haka kowa akayi sai aka canja namu babyn da bunayya.

Amma asali mu namu babyn yamutu, nad’auki bunayya nakuma so ta tamkar y’arda nahaifa acikina kai har gobema jinta nake a zuciyata amatsayin d’ana dana haifa yamutu,saidai ashe shi kadel bahaka yad’auketa ba, bunayya tahad’u da mashkur makaranta wanda yana ganinta yafara bincike akanta sbd tana matuk’ar kamanceceniya da wata kanwarsa ruwaida,koda komai ya kamkama ashe bunayya tagwayece ita ruwaida itace abokiyar tagwaicinta, dafarko abun yadauki zafi daga karshe Allah yadaidaita komai iyayenta na haihuwa suka barmana ita har abada.

Mashkur da bunayya sun hada kawunansu,shine yanzu akesan amasu aure,saiga kadel yafitoman da wannan sabon lamarin wanda kwakwalwata takasa d’aukansa, dan Allah aunty kuluwa kutaimakeni kurokaman shi karya bari wannan maganar tafita waje” takarisa cikin kuka.

Wata iriyar harara dady ya wurgamata kamin yace “ina fadamaki maryam, kidaina fadin najanye wannan maganar,shin kinkowasan irin kaunarda zuciyata keyiwa bunayya,to kisani auren bunayya babu fashi matuk’ar ina numfashi”.

Cikeda mamaki momy take kallonsa kwallah nazubarmata tace “nikwa indai ina numfashi a duniya wlh wlh wlh bazaka taba auren bunayya ba koda zan rasa komai nawane kowa” saiya tab’e baki taredayin dan murmushi sannan yaduka yadauki files dinsa dasuka fadi sannan yafice abunsa.

Kallonsa momy take harya fice cike da tsintsar mamaki kamin tafashe dawani matsananin sabon kuka, al’ajabi da tarin mamaki yacika su aunty kuluwa.

Dakyar yaya hauwa tace “hmm....lallai jolde kinyi babbar asara dakika amincewa namiji d’ari bisa d’ari kika d’aukesa tamkar ubanki dakika rasa shekarun baya,to yanzu kinga yamaki halin nasu ko,namiji...namiji....namiji d’an kunama dik wanda yad’auki namiji uba tabbas zai mutu maraya har abada,yanzu gashi y’arda kika raina da hanunku yakesan yamaidamaki ita tazama kishiyarki” aunty Kuluwa tace “kuma wlh idan batai dagaske ba saiya nunamata cikekken hakinsa sbd kina nan kwance kina kuka zaije yai yanda zaiyi ya aureta sbd kunyace ke garesuba mazan nan, dik yanda kikaga anamaki laf laf laf aikin banzane bazai hana gobe yatsulamaki tsiyarda harki mutu bazaki saki yarda dawani d’a namijiba”.

Yaya hauwa tasake cewa “danhaka yanzu bazama zakiyiba kinata kuka tashi zakiyi kiyi tinanin mafita” cikin disasshiyar murya momy tace “toni yanzu mezanyi ne, idan nagad’i wannan lamarin awaje asirinmu zai tonu ne” cikin takaici aunty kuluwa tace “to ina ruwanki,yatonu din, ai tinda kuka aikata dole asirinku yatonu komai daren dadewa,sbd haka kid’auka kawai ranar tonon asirin ce tazo” momy tai shuu natsawon mintina.

Can tadago tadakko wayarta takira bunayya,ringing daya ana biyu tadaga,batajira komaiba tace “bunayya kidawo gida ina buk’atar ganinki bada jimawaba,komai kike kidawo yanzu kuma kekadai” tana gama fad’ar hakan takatsen kiran.

Bayan dakamar 3hrs kowa saiga bunayya taiso a firgice, momy naganinta tafashe da wani matsanancin kuka aikwa dagudu bunayya taje tarungumeta nantake itama kwallah suka fara zubomata tana tambayar momy cikin tashin hankali abunda ke faruwa,dakyar momy taiya fadamata komai ba abunda ta b’oyemata.

Dasauri bunayya taja da baya cikin firgici da yanayin mamaki tareda furta “what....! meya sami dady na momy,sbd natabbata akwai abunda ke damunsa kokuma wanine yamasa asiri,taya dady dayake mahaifina zaice wai nice zai aura,kai ina momy wasa yakeyimaki” momy ta jijjigata tace “kidawo hayyacinki bunayya dagaske yakeyi babu alamun wasa a tattare dashi kokuma wani yanayi na sihiri ko maye, a yanzu haka har yaje can gun hajiyarsu yafad’a gabad’aya ahalinmu dika biyun ba wanda baiji wannan lbrn ba”.

Kuka bunayya tafashe dashi tana fadin “wannan wace irin k’addara ce,wace irin kaddara ce wannan,yau dady na dabakinsa ke furta kalmar SO izowa gareni,koda acikin mafalki bantaba tinanin wannan ranar zatazoman ba, innalillahi wainna ilaihi rajiun,Allahumma ajirni fil musubitii haza wa akhlifni khairan minha” takarisa tareda fashewa dawani kukan.

Itama momy kukan take zuciyarta cike da nadamar amincewarda tayiwa dady.

Suna cikin wannan halin saiga dady yadawo, aikwa yana ganin bunayya dasauri yaje gunta yafara magana kamar zauracce “bunayya y’ata karki yarda dadik horewar kunnenda jolde zata maki kinji,nine namijinda yafi dacewa nazama mijinki,ina matuk’ar k’aunarki bunayy....” bai karisaba bunayya tai wata iriyar k’ara tareda dafe kunnayenta tana kuka.

Rik’o hanunta yai tai saurin kaucewa tareda mik’ewa tsaye taja da baya tana kuka,shikowa binta yake yana fadin “karki gujeni bunayya,wlh zan iya mutuwa idan har ban aureki ba,ina matuk’ar Sonki ina kaunarki acikin zuciyata bunayya” juyawa tai dagudu tashige d’akinta tarufe tafada kan gado tana kuka matsananci,itama momy kuka take sosai kamar ranta yafita.

Gaba daya dady yafita a hayyacinsa,zowa yai kan k’ofar dakin na bunayya yaita bugawa yana fadin “I really love u more than allot bunayya, dan Allah kitaimakeni ki aureni” tanajinsa saita dafe kunnayenta tana kuka mai tsanani.

Dakyar momy taiya mik’ewa tsaye taje tad’akko key car tafito sannan taje tafito da bunayya bayan wucewar dady,mota suka shiga momy taja suka fita.

Kai tsaye gidan hajiyarsu dady tawuce sbd yanzu tasan komai yariga daya b’aci, bayan sun iso saita fara shiga side din hajiyarsu ramadan,hajiyar ya ramadan ta matuk’ar tausayawa momy akan halinda take ciki,itakam sam bataga lefin momy ba kokadan tabbas dady yafita laifi.

Suna zaune acikin parlo kwatsam saiga hajiyarsu dady tashigo fuskarta d’auke da tsintsar fusi da bacin rai saikuma ga abban ramadan yabiyo bayanta dasauri.
Chapter 15 · 0% Book details