← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 56

Sashe 53

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aisha ma da cikinta Farook murna ba a magana,haka Sabeer matarsa har ta samu ciki sai amai take fama,Nabeela ma tana fama da nata.
Yau Shehu ya sanarwa Landlady zai raba musu kwana ya gamsu da shiryuwar matarsa ya Kira Mama ya kira Landlady ya musu nasiha sosai da yaransa ma ya tarasu sun Sha nasiha sannan yau ya Fara kwana a dakin Mama yaji ta zam zam Kamar ba ita ba to ta Sha gyara,Kuma Mama haka suke gaisawa da Landlady ba gaba sai dai dan kishi na Mata Wanda baza a rasa ba dole.

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

99-100

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

Hafsa Abdullahi
Fateema Farouk

Nusaiba tana zaune yau Mama ta aiketa kasuwa zata Yi Mata cefane ta shiga Napep sai me Napep yace Zan Sha Mai Hajiya tace to,gidan man da Affan yake nan ya shiga,Yaron Affan Salahu Wanda Suka Yi hatsari da Raudah akan machine dinsa Yana gidan man Affan ya sashi aiki da machine dinsa a gefe yaga Nusaiba a Napep sai kallonta yake Yi sai ta Masa Kama da matarsa data mutu da ciki wajen Nakuda,Kawai ganin tana Kama da matarsa yaji Yana sonta,Yana ta faman kallonta Kamar maye,wajen Napep din ya karasa yace Yan Mata sannu,Nusaiba rabon da wani Namiji ya kulata a duniya har ta manta sai yau,farin ciki ya kamata amma ta danne tace yawwa,yace dan Allah ya sunanki? tace Nusaiba yaji sunan matarsa data mutu mamaki ya kamashi yace ikon Allah dan Allah Dan yi dariya na gani,dariya ya bawa Nusaiba ta murmusa yace har dariyar iri daya wlh sannu baiwar Allah wallahi birgeni Kika yi haka Kawai naji Ina sonki Sunana Salahu,Nusaiba a ranta tace ji wani suna dan Allah sai ace Nusaiban Salahu ko dadi,kallonsa tayi sama da kasa Salahu matashi ne Kamar su Affan wankan tarwada ba laifi baida makusa kuma Yana gayunsa da tsafta Dan birni ne, a ranta tace karfa kiwa kanki tace na gode a fili,Yace dan Allah Dan bani number dinki idan ba damuwa,Nusaiba harda Jan aji sai da ya dinga rokonta sannan ta bashi da kyar tana yanga,Salahu Kuwa haka yake son mace me yanga sai ta birge shi tuni ya Kara Jin sonta.

A hankali waya Suka Fara da Salahu kafin wani lokaci Salahu ya siye zuciyar Nusaiba yace shi da gaske yake daga nan ya dage da zuwa zance da machine dinsa yace yafi son bazawara yanzu sunfi hankali sunga rayuwa,Yana zuwa zance an kusa turo manya aka samu munafukan layi Suka fadawa Salahu tsiyar da Nusaiba ta shuka aka sake ta,shi yasa ake so ka shuka Alkhairi duk tsiyar me hassada bazai samu abin fada akanka ba,gashi Nusaiba ta kamu da mugun son Salahu Kawai taga ya daina zuwa Kuma ya daina kiranta a waya idan ta kirashi sai yace zai Kira bazai kirata ba,Addua taci gaba da Yi ba dare ba rana tayi ta kuka a boye ba tare da wani ya sani ba,Soyayya ta sa Nusaiba kuka sai yanzu tasan mene so akan Salahu,sabo da sauran Wanda ta aura kudi Kawai ta hango Basu samu damar zuba soyayya da ita ba sai Salahu talaka me rufin asiri.

Tun Mama bata fahimci haka ba har ta gane bata tambaya ba ta rabu da ita,Shehu ne ya Kama Nusaiba tana wanke wanke tana kuka bata San ya shigo ba,Kujera Fara ya ja ya zauna ya dakko lemonsa na roba ya balle Yana kurba Yana kallon Nusaiba ya harde kafafu,Mama ce ta fito tace yau me Zan gani Nusaiba me ya faru,Ka gani Abban Ameer, Shehu dariya ya dinga Yi Yana kora lemo abin Yana Masa dadi yace sai kin tambaya akan mene yarki soyayya ta fada talakan da kuke gudu a kansa take wannan an zuga shi ya daina zuciya dama bata San so bane shi yasa da kudi ne a zuciyarta ba soyayya ba yanzu Kuma da damarta ta gudu ba me kudi talakan ma Neman sa akeyi Ido rufe to an same shi da kyar Kuma ya subuce ga sonsa take sosai,Mama taji tausayin yarta Jin Nusaiba ta sake rushewa da sabon kuka tace yarka ce dai wallahi ba daidai bane,Shehu Yana kora lemo Yana tuntsira dariya Nusaiba da Mama an shiga wani hali Yana kallonsu Mama tana lallashin yarta.
bangaren Salahu yana mugun son Nusaiba amma abinda aka fada Masa shi ya hanashi ci gaba da nemanta amma zuciyarsa ta kasa hakura da ita.

Siyama cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe,washe gari Monday Aslam Yana da meeting ya fita da sassafe ko bacci bata tashi ba nakuda ce ta tasheta, Jin ciwon na musamman ne Kawai bata nemi Aslam ba sabo da tasan meeting ne da shi akan wani contract zai iya rasa wa sai ta Kira Aunty,Aunty da sauri tazo tare da Yayarta Suka Kai Siyama asibiti,Kamar jira ake ana basu daki Siyama ta haifo danta Kato Namiji kyakyawan gaske,Kuma ta haihu lafiya Kamar ba ita ba, nan da nan aka Mata duk abinda ya kamata zuwa 2pm aka sallame su duk Aslam bai San me akeyi ba,Aunty gidanta ta wuce da Siyama a can tayi Mata wanka da towel ta koya Mata sannan tayi na sabulu da kanta,Aunty ce ta wanke jariri tsaf aka sa Masa sabon kaya farare masu tsada da kyau aka sashi a showel fari Yana kamshi,Siyama ma shiryawa tayi cikin doguwar rigar atamfa sabuwa a gidanta Aunty ta dakko mata ta shafa turaruka ta zauna taci abinci ta koshi,Jariri sai cin hannunsa yake Yana Jin yunwa,tana gamawa Aunty tace a bashi nono,Siyama ta dauki jaririnta tana washe baki ta tsura Masa Ido tace yanzu Aunty dana ne wannan? Hararta Aunty tayi tace nono akace ki bashi,Siyama ta saka hijab Wai baza a gani ba,Nusaiba ce ta shigo ganin yaro taga me jego an lulluba da hijab,tace malama ki fito da nono ki ba yaro,Siyama tace Aunty na rasa bakin yaron fa,Ina Zaki ganshi kin lulluba,Da kyar ta samo bakin yaron tace Bismillah dan yaro kayiwa ubanka kaka gida,Aunty ce ta maketa a kafada tace ke dai anyi marar kunya wlh,Siyama tace Aunty ai gaskiya ne shike nan ubansa yau sunyi handing Over,Nusaiba ta fisge hijab din data rufe kanta,Siyama ta Fara masifa wai mene haka Zaki ga sirrina ta jawo ta sake rufawa kanta da jariri,Nusaiba tace ga yaron irin ubansa, Sai da ta gama bashi nono ko koshi baiyi ba tace ya isheka haka karka yi katon ciki, ta mikawa Nusaiba yaron tace gashi kalli danki Kamar zai ce min Mummy, Nusaiba ta karbi dansu tana gani tace wannan yaron wayo zaiyi,Siyama tace bakya ganin idonsa Kar Kamar zai Kira sunana,kalli girarsa cewar Siyama,Nusaiba tace irin ta ubansa ce ya fiki karfin jini,Aunty ce ta tashi Jin rashin kunyar da suke yi

Siyama a hankali tace ba dole ba ya fini karfin jini ai ansha aiki ayi fama anyi gumurzu,Nusaiba tace ai aikin maza kenan ni kaina yanzu da kyar nake bacci Sabo da ba harka yo na Saba da wanga lamari,dariya sukayi sai tafawa suke suna iya shege wani abin Aunty tana jinsu,Kawu ne ya shigo Suka Yi mukus,ya dauki jariri yace Siyama ashe asibiti aka kaiki? tace wallahi Kuwa kawu na haihu,Kawu yace to rasa kunya ai na gani,Shuru tayi,Makwafta da Yan uwa ana ta zuwa barka,Aslam ya Kira yaji ya matarsa tana dagawa yajita da murna tace Ina gidanmu fa kazo sai ka daukeni mu koma gida,yace lafiya? Kuma shine baki fada min ba ai na gama meeting dinma Ina hanyar gida tace gidanmu zaka taho bani da lafiya,da sauri ya juya Kan motarsa sai gidan su Siyama Yana zuwa yaga Nusaiba ta fito daga gidan ta Shige gidansu wasu matan suna ta shiga wasu na Fitowa harda Maman Nusaiba,Fitowa yayi zai shiga gidan Yar uwar Aunty harda ce Masa an samu karuwa Allah ya raya,Aslam yace ta haihu ne? Au baka sani ba ai tun safe Muka kaita asibiti tana nan lafiya kalau da jariri,Aslam ai ko gama ji baiyi ba ya kutsa Kai cikin gidan,Yana shiga Yan barka duk sun Gama sun fita Kawu ya shigar da shi tsohon dakin Siyama Wanda yanzu ya Sha kujeru da tiles,Zama yayi sannan Aunty taje Suka gaisa,Siyama ta mike da yaronta har da pillow din da take zama a kai,ta Shiga inda Aslam yake,Murmushi ya sakar Mata itama haka jaririn ya karba Yana kallonta yace Kamar bake ba Anya ma kin Sha wahala Kuwa
Chapter 53 · 0% Book details