← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 56

Sashe 49

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Nusaiba gajiya tayi da rashin mahaifiyarsu ta tattara kannenta suka koma gaban Abbansu tare da durkusawa,Shehu yace Yaya aka Yi ne? Nusaiba tace zuwa Muka Yi mu roke ka dan Allah Abba ka dawo da Mama gida badan halinta ba ko don mu,Amarya Landlady tana ji,Shehu yace babu ruwanku Kar na sake ji Kun min maganarta Indai maganarta Zaku kawo min to karku zo inda nake,ku tashi ku bani waje ya musu tsawa suka mike sum sum Suka bar wajen,Nusaiba babu abinda take da buri face ta samu mijjn aure ko ba me kudi ba amma ta rasa me sonta yanzu duk irin farin jininta yanzu babu ko wani ya fara tunanin zuwa a unguwar za a fada Masa gaskiya halin Nusaiba da uwarta sai mutum ya fasa zuwa,akwai mutum biyu ma sunzo amma tun daga zuwa daya Nusaiba bata sake ganin sun Zo ba an zuga su a unguwar ,wannan karon Ido rufe take Neman miji ko ba me kudi ba ma amma talakan ma ta rasa shi.

Yau tana part din Amarya tana Mata uban aiki Landlady taga tana hawaye,tace Nusaiba lafiya? Nusaiba ta zauna ta bawa Landlady labarin abinda ta shuka kaf tana kuka tace yanzu miji nake nema ko talaka ne wlh Zan zauna na rike mijina amma Kinga talakan ma na rasa duniya me yayi, Landlady tace wlh kin bani takaici ko Mene ke Kika jawowa kanki Nusaiba yanzu ai an waye kina gani yanzu manyan mata ma kula suke da mazajensu bare Yan matan yanzu,shawarar da Zan baki ki yiwa iyayenki Biyayya har Maman taki ki samu Wanda Kika batawa ki tabbatar sun yafe miki sannan ki dukufa da addua ba dare ba rana Allah zai kawo Miki miji kin samu dama me kyau har biyu kinyi watsi da ita ai gashi nan yanzu son kudi da son zuciya da hauka sun kaiki sun baro yanzu wa gari ya waya? Nusaiba tace Inshaallah zanyi yanda Kika ce,Nusaiba haka ta sake gyara halinta tana ta Addua tana yiwa mahaifinta biyayya amma ta kasa zuwa Neman yafiya wajen Sufyan da Aslam sabo da kunyar abinda ta aikata.

Mama tana Kauye lokacin da Nusaiba ta kwashe kudin tsohuwa Yan gidan Suka samu Mama Suka zo Suka tasa ta gaba lallai sai an biya su kudin me daddawa Suka kwace karamar Wayar Mama tare da siyar da ita dubu hudu Suka dauke dubu Uku dubu Daya Suka jefawa Mama canjinta,ita kanta Mama wahala ta isheta baza ta iya ba gashi lokaci Yana ta tafiya haka ta hado komatsanta ta dawo ta tafi gidan su Siyama tana rokon Kawu yasa baki Shehu ya maidata wallahi ta gane kuskurenta baza ta sake ba,Kawu yace ai Kinga irinta yanzu gashi kalleki dan girman Allah kin dawo sai kace dodanniya ,kin ganki Kuwa sai kace horror ba kyan gani da ace da dare ne na ganki ai sai na Suma idan nayi arba da kamanninki sabo da zance gamo nayi,Kawu ya gama Mata tatas sannan yaje ya samu Yan uwan Shehu ya lallabasu aka Kira Shehu aka zauna dashi akan yayi hakuri ya maida Mama,aka buga aka buga Shehu yace bai yarda ba,an rasa inda za ayi da Shehu har Mama ta kwashe kwana uku gidan su Siyama Shehu bai San da zamanta bama,sai da ta daidaici Sanda yake dawowa daga masallaci da sassafe da sauran duhu ta fice ai Kuwa taci sa'a ya dawo ta tare shi,zubewa tayi a kasa tace dan Allah Shehu ka yafe min wallahi bazan sake ba na tuba kayi hakuri dan girman Allah, Shehu ko kulata baiyi ba ta rike rigarsa tana kuka tana rokonsa ya fisge rigarsa ya shige gida bangaren Amarya,haka ta dawo jiki a sanyaye.

Duk dangi da duk me fadawa Shehu yaji yaje wajensa akan Maganar maida Mama dakinta Shehu yaki landlady da kanta tayi Masa magana yayi hakuri ya dawo da Mama ko dan yaranta amma Shehu yace ba ruwanta wannan tsakaninsa da Mama ne dole ta kyale shi.
Kawu ne yace yanzu shawara ta karshe ki tafi gidan Aslam ki roke shi yayiwa Shehu magana Indai Aslam ya sa baki to aurenki zai koma dai dai amma Indai ba Aslam ba Sai dai na fada Miki ta bature Sorry Sorry.
Mama tsoro ya kamata tace Aslam din da ya tsane mu ko naje bazai kalleni ba karshe ma ya ci min mutunci Aslam baya kaunar mu ko daidai da kwayar zarra ne,ai yayi dai dai mene ne baku Yi Masa ba lokacin Yana auren yarki idan zaki je kije idan baza ki je ba to gobe ki bar min gida na gaji cewar Kawu,Aunty tace idan tsoro kike ji zan rakaki,Mama tace dan Allah ki rakani wallahi idan naje Ni kadai Aslam zai iya harbe ni da bindigarsa ni tsoronsa nake ji yanzu ban taba sanin Shu'umi bane sai da ya rabu da yata sai da ya rama abinda Muka Masa babu irin bakanta Mana zuciya da baiyi ba abin nan ya min ciwo karshen cin mutunci Aslam ya kashe kudi me yawan gaske aka Yi min kishiya kalli gidanta kalli namu ta fashe da kuka Aunty sai da abin ya bata dariya Aslam yayi dai dai cewar Aunty.
Chapter 49 · 0% Book details