← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 56

Sashe 3

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa dare dukkan matan a daki daya suke kwana da iyayensu sabo da rarashin zuciya irin ta Shehu, dukkan yaran basu bacci ba sabo da Babu abincin da zasu ci Shehu suna saman gado shi da Mama su Kuma su Nusaiba suna kasa a kwance saman tabarma, mazan Kuwa suna kitchen a gefe daya suke kwana gefe daya Kuma kwanika da tukwanen abinci, washe gari da rana babu abinda su Nusaiba zasu dafa har ta lallaba kannenta suka tafi Islamiyya wacce dama ita kadai suke zuwa gwara ma kannen Yan primary suna zuwa ta gomnati ita kuwa rabonta da makarantar boko tun mda ta Gama primary,Bayan sun dawo babu abincin da zata ci Ameer Wanda ke binta yace wlh Aunty Nusaiba yunwa muke ji Babu komai da dare,Mama tana jinsu suna zancen ta kalli yaran nata cike da tausayawa tace bani da komai a gidan Nan sai masara sai dari da hamsim,kanwarsu me bin Ameer wato Ihsan tace mu Kai Nika Mana Aunty sai ki Mana tuwo ko ba Dadi sai muci haka tunda mama wake da geron sana'arta take gyarawa

Mama tace wannan shawarar tayi ta zaro dari da hamsim tare da mikawa Yasmin ta karba ta siyo waken Miya na hamsim,manjan hamsin sai Maggi dama da daddawa sai wani ragowar tattasai guda uku suka Yi miyar kuka tuwon masara,Suna cin tuwon Mama tana furta Allah ya baki miji me kudi Nusaiba wanda zai kaini paris,Nusaiba tace gwara da kika ce Paris irin su Dubai inda tourist ke cika gari,me za ayi da London Mama baki ta tabe tace tsoron ai London bata Yi ba kasar leburori ce Kuma ko kin samu me kudi karki sake ki taimakawa Shehu ya Gama zaluntar mu,dama wa zai bawa Abba ko sisi cewar ameer suna ta labarinsu,Ihsan tace Ina ruwan Abba Kuma ma ai uba ubane ko me yayi ai taimako Zakayi sai Allah ya buda miki,Nusaiba tace hmm tunda muka taso cikin kuntatawar Abba muke,to ba sai muyi hakuri ba cewar Ihsan,duk abinda ya faru akwai dalili shi yasa idan Kika ji Mata ko Yaya suna abu wasu dole akwai dalili, Siyama ce ta shigo tare da kwada sallama,Nusaiba tace shegiya Charity ce,Ziyama wacce aka fi sani da Charity tafawa sukayi da Nasaiba, Nusaiba ta Fara tsokanarta Charity,itama Siyama tace begin at home, Charity we dey begin at home,Dariya sukayi,Siyama ta kalli Nusaiba tare da furta Wai kayan nan basa isarku ne kullum Hijab da su Atamfa,Nusaiba tace kalleki wa zai kalleki yace Yar musulma ce Kuma bahaushiya kin wani saka Riga da wando ga pcap Kuma wasu tsofaffin da ace ma sababbi ne da sauki,Charity ta kalli kanta tare da furta baza ki gane bs Nusaiba,ya yau me kuka dafa? Mu fa gidanmu yau ko gafzar ma Babu ga jarin Ummi ya karye,Nusaba ta kalli babbar kawarta Charity tace muma yau zero sai kokon safe,Miko min kokon na samu na rage,Mama ce ta zubowa Charity koko ta banka tana cika cikinta tace shike nan sai tsula fitsari Sallama tayiwa Nusaiba tace gidan kanwar Ummi Zan biya duk da bata taimako dole na Kai Mata ziyara ko banza na cika tumbi na...

Nusaiba tace ah tsayani mu tafi yau ko bata Nan sai mun leka makwafta mun cika cikinmu,tafawa sukayi Charity tace Kuma gashi 1:30 ko waye yanzu sun sauke abinci suka fita Wanda kawai cewa suka Yi Mama zasu je karbo bashin da suke bi...

Suna fita a kafa suka dinga tafiya har zuwa GRA dake cikin Kano,Ba kowa a layin sai manyan motoci dake shige da fice a unguwar suka shiga gidan kanwar maman su Charity suna zuwa me gadi yace sun tafi Umrah,Nusaiba ta kalli Charity suka ce bad luck, Charity tace Kinga mu shiga gidan ko uban waye a haka har mu samu abincin ci inda za a sauke mu da abinci...

Fitowa sukayi suka samu wani katafaren gida hadadden gida na gaske Suka kwankwasa,Me gadi ya leko yace Kai Yan uwan Alhaji ne daga Kauye? da Sauri Charity tace ae,megadi ya Bude musu kofa suka shiga ciki,motocine hadaddu gasu nan anyi parking nasu iri iri,suna ta kallo suna faman zare Ido har suka hadu da wata me aiki tace bayin Allah lafiya? Nusaiba tace wajen masu gidan Muka Zo kice Yan uwansu ne daga Kauye,Me aiki tace to tare da Shiga ciki ta Kira Wayar bedroom din Ogan nata tace Sir kayi baki Yan uwanka ne daga Kauye,Tsaki yaja tare da furta maybe yan uwan Mum ne nasan itace me alaka dasu,yanzu Mum ta koma Turkey nayi nayi ta dawo taki and now tana jajibo min yan kauyensu,anyway ki kawo su palona a Basu abinci da komai bazan iya ganinsu yau ba sai gobe sannan ki fadawa gageman Kar ya Bude musu kofa su fita sabo da zasu iya bacewa a city su jawo min matsala kamar yanda last year wasu Dangin Mum na kauye suka jawo min,Kar a barsu su fita sannan na gaji ki fadawa megadi Kar ya sake barin kowa ya shigo daga yanzu,cikin Sauri me aiki ta amsa da an gama Sir ta fice.

Yanda Oga yace haka me aiki ta isar da sako sannan ta dawo ta shuryawa su Charity abinci ya sha nama ko Ina ga lemuka da ruwa me sanyi,Nusaiba da Charity sai Murna sukeyi, Charity tace gaskiya masu gidan nan sun iya karrama baki ji girki dan Allah muci mu koshi mu ware gida,Loma Daya Charity tayi ta kalli Nusaiba tace gyara min pcap dita ta kalli gabas girkin ya hadu, Nusaiba ma tana ci tace wayyoo dadi lallai da ace Hamisu zai dinga bani irin wannan to Zan iya aurensa, Charity ta kyalkyale da dariya tace ni Kinga akan girkin nan Ban ki na bawa Basiru kirjina sau goma ya taba ba Suka kyalkyale da dariya gaba Daya sun cika gidan da hayaniya kamar gidansu, sai da suka koshi harda hutawa suna Shan ac karshe Suka fito zasu tafi Megadi ya Hana yace Oga yace ba shiga ba fita

Tunda Farooq yayi Sallar asuba bacci yaka kasancewar Yau Sunday ba aiki har 11am Aisha ta shigo bedroom Duke da tire ta zuba gayu kyau Kam ta zuba shi,shayi ne da yamballs sai bread ta Fara tashin Farooq Honey... Honey wake up ya kamata ka karya,Farooq ya farka cike da mamaki domin yasan halin Aisha bata Masa soyayya sai da dalili dukkansu babu na zaba a cikinsu,Aisha tace tashi ka karya Baby ba sai kaje Dining kayi wahala ba,Mamaki ya Kama Farooq sai ya tuna da wani abu yace Kinga ma Ina so na fada Miki kudin jiya da dubu dari Uku Wanda na bayar bashi nace da abokin nawa na fasa karba ma ya barsu sabo da irin mutuncin da muke bai kamata na karba ba Yana magana ya dauki Bread zai Fara ci kenan Aisha cikin bala'i da masifa tafisge Bread din tare da dauke tire din tace dalla bani ance Kai kadai ya kamata ka karya a saman gado ni wato na mutu bana so na karya ne a Kan gadon tsaki ta ja ta fice tana cewa wani ya bar Masa kudin wato ni bazan ci kwandala ba lusari,baki bude ta bar Farooq Yana mamaki duk da yasan halin Aisha....

Bayan satikai Farooq yayi parking Yar motarsa gidansa na me rufin asiri,Aisha ya iske a Palo tana kallo sanye cikin Riga da wando masu kyau yace fito muje kiga abin mamaki,Aisha ta kalli Farooq yasha shadda tace karka bata min lokaci fa muje na gani,tana Fitowa taga wata sabuwar mota me kyau ba laifi,key ya Mika Mata yace surprise taki ce,Ai Aisha haukacewa tayi tana ihu da tsalle ta rungumeshi tana zuba godiya,Yace maza Zo muyi hoto so nake muyi maganin makiya a layin nan,dama bashi na karbo ta na wata biyu idan muka bawa makiya mamaki a layin nan sai na maida musu abarsu mota ce me tsada ta milliyan biyu shi yasa na karbo Miki aronta zuwa Yan watanni ya Kika ce dole makiya su Sha mamaki,Takaici ya Kama Aisha sai data Gama muryarta ashe ta aro ce kudi ya bayar ya karbo aronta na wata biyu,ranta ya baci haka ta tsaya Suka din pics a jikin motar aro suka dinga posting a WhatsApp da Facebook etc, mutanensu masu bibiyarsu ana ta congrats sun faso gari

Affan kayansa ya fito da su Yana wanki a jikin pampom katon Compound dinsu kaya akw uku amma tunda safe yake faman aikin wanke su sabo da du fito kal Kal,har Raudat taje aiki ta dawo Affan Yana wanke kayan Nan,har itama ta fito da nata tazo inda yake ta fara wanke nata bata San ta hado bra ba a ciki Affan ne ya tambayeta yace duk wannan karyar da kike da 36 kike sawa? Dama ba komai a kirjin? Kina nufin a haka Kika Yi Kasuwa harda samun Sugar Daddy har ya iya siya Miki mota,Tsaki Raudat ta ja tace idan bashi kake so a baka kayi magana har bashi muna bawa talakawa irin ku,me kake so a ciki ka taba sai a baka bashi,Affa yaji kunya Sabo da bai taba kula mace ba ko da wasa yace ba ruwana Ni ba Dan Iska bane

Kiyu hakuri yau bana Jin Dadi

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

16-20

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne
NAJIDA ALIYU BICCA
Chapter 3 · 0% Book details