← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 56

Sashe 37

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Siyama Amarya washe gari ta riga Aslam tashi da asuba Yana jikinta ta Fara masa Kiran Sallah a kunne idonsa ya bude a hankali ya kalleta murmushinsa me tsada ya sakar Mata tare da sake rungumeta kam Yana magana a hankali yace ki barni a haka ni,tace anyi Kiran Sallah tun dazu,makarar angwaye zanyi yau,no yaushe ma kasha zakin tukun da zaka Fara makara,dariya ta bashi ya mike zaune Yana kallonta sannan ya sauka ya shige toilet, brush yayi da alwala sannan ya fita masallaci, bata Sallah baccinta ta koma taci gaba da Shaka har ya dawo ya kwanta a jikinta shima ya dora baccin sai 9am ta tashi tare da zare jikinta a nasa ta shiga toilet brush tayi sannan ta sheka wanka ta fito ta zauna shafe shafenta sannan ta saka doguwar Riga Yar kanti marar nayi me hannun vest sama ta dame kasa ta dan bude ta fito tana kamshi ta saka hijab ta Shiga zaga gidanta tana murna kugu ta rike tace da na zauna a bikina Ina kukan banza dama Ina sani na dinga yin wani kukan har da Kari ma don ace Ina jimamin rabuwa da Kawu nan Kuwa ba ruwana,dan ba a San zuciyata bane ta zaga ta baya ganin babu me ganinta ta cire hijab din ma ta kwashe da gudu a gidan tana shawagi,tayi juyi ta juya ta tsaya cak tana ta ganin katafaren gidan ta rasa ma wanne murna zata Yi tayi tsalle yafi biyar tace gidana gidan mijina,dawowa tayi ciki ta iske me gadi a bakin gate Suka gaisa,sai me aikinta mace tana ta gyara gidan Suka gaisa da ita cikin fara'a da mutuntawa, kitchen ta shiga ta Fara soye soye tana yiwa kanta Waka Amarya Ce Siyama,Charity ki Sha sha'aninki...tace wallahi duk Sanda Naga Nusaiba ta zo ko unguwar nan ko layin nan sai na ci ubanta Kai ko wucewa zata Yi ma, tana aikinta tana zancenta har ta gama hada breakfast dinta ta shirya a dining,Me aikin ta tambaya abinci fa tace ai ni nake yi Mana tare da me gadi tun tuni ma mun karya Kuma abinda muke so oga yake siyo Mana Yana kitchen din part Dina komai Muna da shi,Siyama tace Masha Allah an gode Masa ya kyauta ai mutumin kirki ne,kinyi dace wlh cewar me aiki,Siyama tace ni kuwa nasan nayi dace ke Kinga love gashi da hakuri wlh ba ruwansa,Haba ke dai bari Aunty baki ji yanda ake yabonsa ba cewar Yar aiki Siyama ta dage sai yabon miji takeyi kwana Daya kacal da kawota,ko Ina an gyara dakin Oga Kawai ta gyara da kanta,sai da ya gama baccinsa ya tashi tare da shiga toilet yayi wanka da brush sannan ya shirya cikin wani sabon yard me shegen kyau coffee color ya fito Yana zuba kamshi,Siyama ta fito dauke da flask tayi sauri ta ajiye a dining tana cewar takawarka lafiya barka da fitowa,dariya yayi ba shiri tace me kudi uban matsiyata na Siyama sa gabanka inda kake so,Wanda ya gaji arziki ba taka haye ba kenab,kaga na Charity me komai 100 ba dozen ba ,dariya ce ta kwacewa Aslam,Siyama taci gaba da cewa ga amaryarka me kayan aiki ya sake fashewa da dariya,ta nuna kirjinta da hannu biyu tace Kai kake da nan, a taba can a latsa nan sai na Siyama ikon Allah ta furta tana nuna Boobs dinta ,Affan Yana dariya ya rungumeta tare da dagata sama,tace ban gama kirarin ba fa,a lafiya dai....Baki ya rufe Mata da nasa yana sha

Tace yau fa mu fita zamuyi yawo ba batun wani amarya duk inda zaka je sai na bika, yace to duk abinda kike so,Siyama ta Fara murna zata fita ba kulle,bayan sun karya a Palo Suka zauna yana zaune a doguwar kujera ya bude kafafunsa daya kafar a mike a saman kujera Daya kafar tana kasa Siyama ta kwanta a tsakiyarsa gadon bayanta Yana saman kirjinsa Yana koya Mata game a waya sun rike Wayar tare da hannayensu duka tana gwadawa suna ta fama suna nishadi.
Zuwa Yamma Suka dau wanka kamar zasu je party tasa wata arniyar Arabian gown black taji ado silver color, takalmita da jaka Silver shi Kuma shadda ya Sha Silver me tsadar gaske kana gani kasan ba karya ya rike hannunta Suka fita wata rantsatsiyar Jeep dinsa,wani katafaren Joint Suka je duk Wanda ka gani a wajen to ya Isa,suna shiga rike da Hannu Suka iske Nusaiba a wajen mijinta ya kaita amma Abokinsa ya kirashi ya fita yace ta jirashi nan da 30mnt Yana fita su Aslam Suka shigo,sun ga Nusaiba amma kamar Basu ganta ba Suka zauna a kujera Aslam ya jawo Siyama ta zauna a saman cinyarsa yana sani yayi hakan,Siyama ta kasa Zama sabo da kunya ta koma saman kujerarta ta zauna,Nusaiba ta firgita taga Aslam Kamar a wata hadaddiyar mota Suka fito amma bata kula ba sosai lokacin,Siyama ce tace Honey bani key din motarka na ajiye maka a handbag dina,Nusaiba mikewa tayi ta kalli motar duk wajen babu me irinta tunani tayi tace maybe arowa ma yayi karya ne talakane har yanzu wai ni za a yiwa burga ta ja tsaki ta zauna tare da gallawa Siyama Harara,Siyama ko kallon Nusaiba bata Yi ba,ganin Nusaiba tana ta kallon Aslma tace please Ni ka canja mana joint muje Cenema kallon film yace alright ya riko hannunta yace sai abinda Kika ce ai shi za ayi Baby yaja hannunta Suka fita,Nusaiba tace karyar banza bibiyata sukeyi shi yasa Suka zo za a min burga ni Ina mamaki ma da har yanzu yake kamshi me dadi haka sutura me tsada ya kamata na Fara ganin wuyan rigarsa ya kode ya yage Yana wari amma kullum mutum kamshi Kamar namijin karuwa,harda aro mota azo za a rude ni Yan Iska Yan karya Yan Yan yan...ita Kuma Wai sa car key din a jakata sabo da naji suna da mota fake....ta ja tsaki,tashi tayi ta leka bata ga kowa ba motar da take tunani a ita Suka Zo bata ganta ba tace sun shiga taxi matsiyata Yan karya me motar ya dauki abarsa ta juya ciki.

Siyama kuwa zasu shiga Cenema Kawai Aslam yaji sha'awa shi bazai iya jira ba,matarsa yake so ya murza,order ya musu na take away kaji da su ice cream da sauransu tana rike a hannunsa yace muje gida an fasa kallon Watarana sai mu zo bazan iya barin sabuwar Amaryata ta huta na hours ba ace bana taba komai ke muje bazan iya ba na fasa yaja hannunta Suka Shiga mota,Siyama tace mun fasa? Yace ae Nima ai ganganci nayi da na fito da Amaryata bazan yarda ba gaskiya wayo zaki min muje gida haka Kawai kowa idan yayi aure Yana hutawa ni shike nan na zauna a kallon film zaki min wayo,dariya ya bawa Siyama yace haka Kawai sai kalle min matata akeyi a banza...

Masu sharhi Ina godiya

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️

76-80

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne

AUTARESS

Kofar gidan da Mum take yayi parking sai gasu ita da Hajiya Zainab sun dawo daga unguwa,Aslam Suka gani ya fito daga cikin hadaddiyar motar ya dakko Leda da flask,Mum tace daga Ina haka? ciki Suka shiga gaba Daya Yana cewa daga gida Mana,sai da Suka zauna a Palo ya gaishe su,ya ajiyewa Mum flask din da ledar a gabanta tare da cewa gashi inji Siyama,Mum tace me Muka samu Kuma ta bude flask din taga farfesun kaji ledar ta Bude ta washe baki tace an gode Mata Allah ya Mata albarka,yanzu nasan Ina da suruka,Aslam yayi murmushi ganin Mum ta Kira Zainab ta kawo plate ta ebi nata ta bawa Zainab nasu,Mum ta Fara yagar kaza tana cewa wannan yarinya Allah ya mata Albarka,Zainab ma tana ci tace haka ake son suruka wasu Kuwa Kai da kayan danka ya gagareka,Aslam yace ni baza ku sa min albarka? Mum tace Kai Dan Allah rufe mana baki muna Jin dadin mu wannan motar ma ta waye ne nasan baka aro kayan wasu,Aslam yace tawa ce Mana ya Fara bawa su Mum labarin komai har ya gama,Mum tana tsotse Kashi tace amma ka wahalar damu har hawan jini sai da yakamani,kiyi Hakuri Mum kin San dalilin da yasa nayi haka yanzu,ae hakan ma kayi dai dai gashi Yanzu mun samu Yar arziki irin albarka,amma cuta sai da ta kamani,Ki zabi kasar da kike so Mum na kaiki ki huta,tace ba yanzu ba aure zanyi na tafi da mijina,Dariya ta bawa Aslam yace kina son aure Mum?wa yaki ibada da ace Ina da mijina ai bazan dinga yawo kasa kasa ba da sauran kuriciyata fa,Aslam yace Mum na Miki miji, Waye? Ki auri Shehu Baban Nusaiba,Mum tace Kai nifa bana son kazami Indai tsoho ba me tsafta bane karka kawo min shi bare wannan Yarinyar tasa marar kunya bada ni ba,dariya Suka yi,Baffa Shehu ai Dan gayu ne kin girme shi fa sosai sai dai yayi manage dake cewar Aslam,Mum tace tashi ka tafi ka San inda dare yayi maka tunda magana zaka fada min,Yace Flask dinmu fa? Hajiya Zainab tace ai ba bata zaiyi ba in ka dawo sai a baka,yace idan tana son amfani da abinta fa matar gidan,Mum tayi dariya tace duk cikin zumudin Amarya ne rabu da shi Aslam kuwa kitchen ya shiga da Kansa ya dakko wani flask din da Kansa ya juye ragowar a ciki ya dauke flask dinsu ya rufe ya musu sallama ya tafi
Chapter 37 · 0% Book details