← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 56

Sashe 4

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun gama wanka suka yi Nusaiba kwanciya tayi sabo da gajiya Charity ce ta fito Palo ta iske Oga Aslam ya fito sanye cikin Jallabiya Yana hutawa gaida shi tayi Yana zamansa na takama ya kalleta kadan yace kin iya girki?zabura Charity tayi ta nuna kanta tace girki Ni? Ah kasan Kuwa yanda na iya girki? bari kaji Oga sanda Ina cikin mahaifar babata ka gane lokacin da Ina cikin Mahaifa da na samu damar Fitowa Zan shigo wannan duniyar lokacin Babata tana tuka tuwo na taho Zan fado duniya Saura kadan na fada cikin tukunyar tuwo Allah ya kiyaye ta tare ni ban fada ba kaga Kuwa wanne kalar abinci ne bazan iya ba,Allah ya min basira farko ma fa da tuni Yar kwallon kafa ce Ni,lokacin da Kanu yayi tashen cin ball ba shi ya kamata yaci wannan ball din ba lokacin Atalanta cup nice ya kamata,ana wani zancen Ronaldo wani Messi dan ba a Sanni bane na iya ball amma makiya sun hana naci gaba,Ina da makiya da yawa shi yasa,Aslam Yana ta dariya a ransa,yace to me Kika iya dafawa a ciki? Na iya Alala,tuwo,danwake ga sarkin Dadi shinkafa da Miya duk na iya,Yace hmm duk ni bana cinsu me yasa kike sa kananan Kaya kina Yar musulma bahaushiya?

Sabo da na nuna musu Ni ba sa'ar Mata bace mace ce ni me kamar maza kwari ne Babu,Ni Yar jam'iyar what man can do Woman can do better ce,to Kuma kina da saurayi? Charity tsaiwarta ta gyara ta Fara zuba Murmushi tace haba Ina da shi har da Ridwan a cikinsu yaudararsu Kawai nakeyi Ina cin kudinsu,Rannan Ridwan din ma yazo daga karbar kudin ankonsa shike nan ya rungumeni zo kaga kiss hmm kamar maye ni kuwa na ci masa mutunci nace babarsa me tsatsar hakora,Aslam dai Jin labari Kawai yake ratata tun a nan yace Charity bata kirki bace, Nusaiba ce ta fito ta dakawa Charity tsawa tace Charity kiji tsoron Allah Ridwan din baki taba sauraronsa ba yaushe ma a masifarki Zaki Bari ya Miki kiss Naga rannan Abdulhadi daga yace ki rungume shi Kika fasa Masa Kai da dutse, Enough kuje kuyi girki cewar Aslam,komai na Kitchen din kasa amfani sukayi da shi sai siyo musu abinci yayi,washe Gari suka dinga kuka tafiya zasu Yi yace to ba damuwa yasa Driver yace ya kaisu Tasha Kuma ya tabbatar sun Shiga mota,ya mikawa driver kudin motarsu sannan ya Basu dubu ashirin ashirin kowacce,da sauri Nusaiba suka Shiga motar,suna tafiya aka zo saitin layinsu Nusaiba tace nan zamu sauka,a sauke mu a nan,driver yace ai oga yace dolene a saku a motar Taraba Kar a samu matsala su Charity suna ji suna gani aka wuce layinsu har zuwa tasha aka sasu a mota tare da biyan kudin,sai da suka tabbatar driver ya tafi suka fito daga mota suka ce sunyi mantuwa ko tsayawa karbar kudin motar Basu Yi ba Suka Shiga Napep zuwa wani gidan amarya kawarsu ce Suka bata ajiyar kudinsu sannan Suka tafi layinsu

Kafin su karasa gida lungun da ba mutane suka tsaya Suka sallami me Napep suka shafawa jikinsu toka har gashinsu hular Charity ta cire ta wullata cikin wani gida itama Nusaiba ta jefa dankwalinta gashi sun samo toka wajen masu girki a tasha sun shafe jikinsu tare da shafa bakin gawayi a hannayensu da kafafun su cikin katuwar bolar dake layinsu suka Shiga tare da tsugunawa a ciki kamar birarrika,kowa ya wuce ana cewa Allah sarki ga wasu can mahaukata kalli Yan Mata dasu Allah ya Basu lafiya,ana ta musu addua har Yamma likis sai ga Ameer kanin Nusaiba zai wuce suka ki magana har ya wuce sai da ya wuce Charity a hankali ta daga hannu Ameer gamu nan karya muke,Nusaiba ce ta bige Mata baki suka Yi Shuru,har Yan unguwa suka gaji aka nemo Yan sanda da me unguwar layin aka je inda su Charity suke dukun dukun suna soshe soshen karya,me unguwa yace a fara bincike ko a Nan akwai Wanda ya sansu,Shehu yazo wajen Yaga yarsa Nusaiba da kawarta Siyama,Shehu yace Wannan ai Yata ce data bace da kawarta Yar gidan Dauda,mutane aka dauki Salati

Shehu yace Wanda Suka sace su ko me ya faru oho Nusaiba da Charity sunki magana ba uhmm Babu Uhmmm Uhmm Dan Kar ma a musu fada a gida,Yan Sanda Suka ce sai dai Wanda Suka sace su ne Suka musu tsafin da baza suyi magana da wuri ba,Shehu yace tunda Sun fito Alhmdllh kaga aikin Addua ko sun sace su amma Addua tayi tasiri sun kasa yanka su ko tsafi da su Addua kenan ai ba karamin kudi na kashe ba Sadaka masallatai Masallatai cewar Shehu yaja Hannun Nusaiba suka tafi gida Charity ta faki idon Shehu ta radawa Nusaiba Kar muyi magana sai gobe,Mama harda ihu sabo da murnar ganin yarta karshe ta fashe da kukan farinciki tana oh ashe Zan sake ganinki Nusaibata,Shehu yace basa magana yanzu amma kafin mutane su Fara shigowa suyi wanka Bari naje na Kira Dauda ya fita cikin Sauri,Su Ihsan Suka dinga ihu suna fada a unguwar anga su Nusaiba a bola aka tsince su.

Mama ruwan wanka ta hadawa ko wacce Suka shiga kowacce ta wanke toka da bakin gawayin da Suka shafawa kansu sai gasu fes ba alamar wahala a jikinsu duk sunyi wani kiba ma fatarsu ta murje amma sunki magana juyin duniya sunki magana a Haka Shehu ya siyo musu shinkafa da wake da Miya Wai sun Sha wahala hannun Yan mafiya bari a basu me dadi,suna Fara ci Anty tazo tare da Dauda Suka zauna a tsakar gida Nusaiba da Charity suna ciki suna cin abinci,ganin ba kowa kasa kasa Charity tace ba dadi abincin na Saba dana gidan Oga,Nusaiba tace ji kazar da aka sa Mana jiya a cikin shinkafa,Charity tace habawa ai sai lemon shekaran jiya ga sanyi ga dadi yanzu shike nan mun dawo cin gafza Kuma ga wanka da ruwan botiki can a shower Muka saba,ta kalli gidan su Nusaiba tace Kai Kan uba kalli gidanku dama haka yake duk dirty painti ma ba a Gane wanne kala ne,dariya sukayi yanda baza aji ba Nusaiba tace Nima sai yanzu na kula gashi mun dawo kwanciyar Kai da kafa gobe da sassafe sai tallan kosai,Charity tace idan Muna so mu huta da talla gobe zuwa jibi Kar mu sake muyi magana hauka muke cewar Nusaiba Suka sake Yin Shuru abinsu.

Juyin duniya sunki magana haka bayan sunci abinci Dauda da Aunty Suka tafi gida da Charity,washe gari ma basuyi magana ba a Rana ta uku Charity sai ta Fara magana tace Aunty daga nan bata sake magana ba,Aunty tace Dauda yarka ta Fara magana Alhmdllh wlh yanzu tace Aunty ta Kira sunana,Dauda yazo kusa da Charity yace Siyama me Kika ce kinyi magana dazu Nima Kira sunana ba sai kince Baba ba ko Dauda Kika Kira ba matsala ai duk cikin lalura ne, Charity a ranta tace dama haka nake so wlh sai na more sunanka tace Dauda,Dauda ya kyalkyale da dariya Alhmdllh Nima ta Fadi sunana asiri ya fara sakinta, Charity ta sake cewa Dauda Iliyasu,Dauda ya sake shekewa da dariya yace haka ake kirana da a makaranta, Charity Kuwa a ranta dadi take ji dama ta gaji da kiransa Baba,yace Fadi sunan Auntynki Fadi muji, Charity tace Hajara Musa Aunty tace to hankalinta ya fara dawowa jikinta,daga Nan Charity ta Fara magana sai me ma'ana wacce ta Zama dole sai tayi magana a Haka a haka ta dawo normal itama Nusaiba haka ba Wanda ya Musu fada ko Daya da aka tambaye su ma Suka ce wani ne ya fesa musu wani Abu a Fuska Basu sake sanin inda suke ba sai a daji Suka tsinci kansu,Nusaiba tace yan Yankan Kai Suka ce a dawo da wannan matan sunfi karfin mu matan manya ne shike nan daga nan basu sake ganinsu ba sai a bolar unguwarsu,Mama tace Addua ce tayi maganin tsafinsu, Haka aka dinga zuwa tayasu murna har suka dawo bakin tallan su.

Raudat ce ta dawo daga Office ta fito da ledar kayan makulashenta Affan ya fito zai tafi Neman kudi ko zai samu,Tsaki ta Masa tace kullum mutum sai fita kullum amma kudin haya ya kasa biya,kallonta yayi yace you are very lucky yanzu fita zanyi Ina da aikin yi da yau sai kin gane kurenki ya juya ya tafi abinsa,Yana fita wani kamfani yaje hadadde ya tambaya Oga yazo Kuwa? Manager yace bai Zo ba yayi tafiya jiya yace Dubu dari biyar zaka bani ka fada Masa,Manager jiki na rawa ya bawa Affan dubu dari Uku ya tafi,Affan kudin haya ya biya ya siyo kayan abinci da sababbin Kaya kala kala kanana da shaddoji da yadika harda takalma,Sai ganin Affan suke Yi Yana shiga ya fita cikin Kaya masu kyau,Raudat tace Amma Dan fashi ne Kai ba a sani ba da alama sana'a tayi kyau an kwaci kudin wani,Affan yace ke da kike karuwanci budurwa me zaman kanta kowa ya ji labari ai yasan karuwanci kikeyi motar ma mun San waye ya siya Sugar Daddy ne ya Gama tabeki Ina tausayawa Wanda zai aureki Yana nan zai ta wahala akanki sai ya aura yaji ya Sha wata mahaukaciyar corner kinji kunya,baza ki iya hakura da talaucinku ba,Raudat taji cin mutuncin yayi yawa ta fashe da kuka yace ai baki ga komai ba ma Sai an Miki dukan tsiya an zagi iyayenki a bariki sannan Zaki San kin Shiga duniya am warning you ki koma gida yafi Miki mutunci,ga inda larabawa ya kamata su sakawa suna Shari,ai ke titin maza ce kowa bi yake abi ta Shari sittin a fito ta Shari Mansir ko mai kin bayar a waje,Raudat tace kaima ai kwarto ne,gidan wa Kika ji na taba haurawa? Allah ya Isa ta furta tare da shigewa part dinta ya dinga dariya yace ki fito muyi mana matsoraciya yaja Tsaki ya shige bangarensa shima.
Chapter 4 · 0% Book details