← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 56

Sashe 2

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani kanti yaje inda suke siyayya kusa da gidansu Suka tafa da me kantin yace a wannan wanka haka Affan Ina zaka je ne? Affan yace tafiya zanyi Ina so zanje Abuja ne akwai wani business da nake ya zuba karya yace gashi ma kaga Atm dina yaki aiki,me kanti sabo da yasan Affan Yana Masa ciniki Yana ganinsa cikin kyakyawar shiga ya zaci me kudi ne yace gaskiya kana tafiye tafiye Oga ko yaushe a Hanya, Affan yace ya za ayi Harkar Business ai in kana Business ba zama yanzu ma bank Zan koma Ina so zanyi siyayya kudi yaki fita dan Allah zan karbi kaya idan na dawo daga tafiya sai na kawo ma kudin, nan take me shago yace ba damuwa komai normal ebi abinda kake so,Affan ya kwashi manyan manyan madarar gari su gwagwanin Milo kayan tea sosai ya hada sannan ya kwashi su tumatir din gongoni,shinkafa yasa ya auna Masa kwano biyar,wake,taliya, macaroni komai ya har su Mai da kwai sai da ya hada akayi Total aka rubuta a list din Yan bashi ya fita,Yana kaiwa gida ya zauna ya shirya girki me rai da lafiya yaci ya koshi sannan ya fito sai gidan Mallam Wanda ya karbi Address.

Affan ba kudin mota a kafa ya dinga tafiya sai da yaci bakar wahala kafin ya Isa gidan Mallam Yana zuwa yaga gidan Mallam hadden gaske sama da kasa,bai Sha wahala ba aka kaishi har part din Mallam,Mallam Yana zaune shi da wani Yana fada Masa karya dan ya karbe Masa kudi,Bayan ya sallameshi Suka gaisa da Affan, Affan yace Mallam ka firgita ni shi yasa nazo da wuri kaganni sauri nakeyi zanyi tafiya yanzu ba kudi a hannuna Kuma tafiyar wani kudade Zan karbo shi yasa nazo yanzu ka bani dubu Hamsim kafin na dawo sai na baka dubu dari biyu ma kaci harda riba,Mallam Yana Jin Haka ya haukace zai samu kudi ba bata lokaci ya irgo kudi dubu Hamsim ya bawa Affan ,yayi godiya tare da cewa sai ya dawo ya fice,Yana fita yazo ya biya me shago kudin kayan abincinsa tas harda samun canji ya shiga harkarsa.

Mallam Shuru Shuru Babu Affan ba labarinsa bai San Kuma inda zai ganshi ba,Affan yaci wanka cikin wani yadi me kyau Yana taku dai dai sai ga Raudat ta taso daga aiki ta tsaya kusa da shi tare da sauke glass tace Affan shigo na rage ma hanya Naga Kamar gida zaka je,cike da rashin mutunci yace ke kin Isa ki taimakeni,akan wannan banzar motar taki har kin Isa ki rage min Hanya ya juya da Niyyar tafiya Katsam sai yaga Mallam shi da wani suna ta magana juyawa yayi da sauri ya bude motar Raudat ya Shiga gaba taja mota suka tafi Babu Wanda ya kula wani,sai da Suka Yi nisa tace da kace baza ka shiga ba me yasa ka canja? Cikin bala'i yace to sabo da na Shiga motarki shine Zaki Raina min hankali motar ki din banza motarki din wofi,Parking Raudat tayi tace amma baka San mutunci ba fitar min a mota,Tsaki yaja ya Bude kofa ya fice tare da furta banzar mota bayan ma ba da kudin halak Kika siya ba maza ne Suka siya Miki Karuwar banza da kudin karauwanci Kika mallaki mota tunaninki bamu sani ba Alhaji Sanata ko dan majalisa ya siya Miki ya daki motar da kafa yaci gaba da tafiya cikin gadara,Raudat ce ta leko ta window tace mutumin da ya kasa biyan kudin gida talaka da Kai baza ka taba iya siyen mota irin tawa ba Never, wace zata kulaka a haka Kai a dole kyakyawa kana daukan wanka ba abinka ka iya sai siyen Kaya kana nan kayan ma duk na gwanjo ne ta fisgi mota taja gaba,yace stupid girl Wai ita me mota Allah ya kiyaye na shiga motar haram.

Raudat yau da takaicin Affan ta dawo tana zuwa bayan taci abinci ta fito ta faki Ido kowa ta taka tsani tayi disconnecting wutar gidan Affan ta danna switch dinsa ta sakko ta koma gidanta,Yana dawowa ya kunna ko Ina duf babu wuta ya rasa dalili gashi gudun Landlady yake tana ganinsa zata ce ya biya ta kudin haya,shima Fitowa yayi Raudat tana ganinsa ta window tana ta kyalkyala dariya Yana dubawa yasan itace sai ya kunna nasa ya kashe nata wutar itama sai gata ta fito da masifa Affan kana neman masifa abinda kakeyi ka takura min a gidan nan Zan dauki mataki a kanka, Affan yace amma ke banza ce wawiya Naga alama so kike nace Ina sonki to wannan bazai Yi tasiri ba,nafi karfinki kije ki samu dai dai dake, me zanci da Kai me zaka iya siyawa matarka kudin gida ma ka kasa biya me zaka iya,Hajiya Mairo me gidan itace ta shigo da dalleliyar motarta ta fito tace Wai ku meke damunku ne baku da aiki sai fada a gidan nan me ya hada ku? Affan ya bude baki zaiyi magana Hajiya Mairo tace rufe min baki Kai har kana da yanci a gidan nan kudin haya ma ka kasa biya,kana da bakin magana rufe Mana baki,ai Kuwa sai yayi mukus baida bakin magana,Raudat ta kyalkyale da dariya sanye take cikin Arabian gown me kyau tana kamshi tace ka biya kudin gida? Ko kudin gida ka kasa biya ai Kai ba Dan gida bane ihu ta Masa wooooo ko kudin gida ya kasa biya get out, Affan sadaf Sadaf ya koma cikin part dinsa bai da sisi baida inda zai samu kuma.

Kuka tafashe da shi tace wlh Shehu Allah sai ya tambayeka yaranka shida amma ka kasa ciyar damu kullum sai Yar sana'a ta nake cinyewa,Tsaki Shehu ya buga yace ai yaranki ne ke Kika haife su yanzu Dan kin basu kudinki shine matsala,amma Shehu kasan ni ke daukan nauyin kaina da yarana kana da kudin ba Babu ba baza ka iya ba,gasara nake siyarwa itace sa'a ta amma Watarana har da rana Koko muke sha ga yarka Nusaiba har ta girma ta Zama budurwa ko yaushe Yarinyar nan kamar almajira haka take yarinya kyakyawa amma kamar almajira Shehu kaji tsoron Allah,Nusaiba ce ta shigo cikin jemammun Kaya da katon botikin kosai a kanta tayi sallama tace Mama na manta da yajin kosan,Yajin Nusaiba ta dauka ta tafi tallanta wurin tasha inda mutane ke taruwa,Nusaiba tana ta ciniki tana irga kosai a Leda ga duk Wanda ya siya,ta mike tsaye tana mikawa wani drivern babbar mota,wani bugagge yazo ta Bayan Nusaiba ya taba mata duwawu,Nusaiba tace Ina Wasa da Kai,Ni Yar iska ce? Ka taba ganin Ina wasan banza? Ni ba irin yan Iskan Yan talla bace neman halak na fito,zaka taba min duwuwu tayi fatali da ledar kosanta bundle sabo da masifar Nusaiba ta shatile Masa kafafu ya zube a kasa ta dinga dukansa ta rufe shi da Naushi a Fuska sai da ta farfasa Masa baki mutane ana ta bata hakuri,wani yace kiyi hakuri Nusaiba sabon zuwa ne bai sanki ba,Nusaiba cike da masifa tace ba ruwana ni tunda kaga haka dama ba mutumin kirki bane yazo ya taba min duwawu ta ja tsaki tare da tara Yara Almajirai ta raba musu kosan sadaka ranta ya baci haka ta koma gida

Tunda Mamanta taga ta shigo ranta a bace tasan wani ya tsokaneta,Shehu Abbanta Yana zaune Yana shan shayi a gaban yaransa kanana su Kuma yaran kokon da babarsu ta dama na siyarwa shi suke Sha,Shehu ne ya kalleta yace to jarababbiya masifaffiya uban me aka miki marar kunya kullum baki da aiki sai fada da mutane,kiyi fada da mace,kiyi da Namiji,kiyi da Yara gaba Daya zubar min da mutunci kike yi a layin nan,Nusaiba tana kumbura da tashin hankali tace Kai ka sani Abba, Mama kema kin sani bana fada sai da dalili Abba ai dole nayi fada kosan ma na bada Sadaka,Abba yace uwarki Kika yiwa asara ba abinda ya dameni abinda nake so na ji Mene dalilinki na dukan wani? Nusaiba tace duwawu ya taba min duwawun da ba a tabawa sai da sadaki abina me kyau ko uban waye ba sai na illata shi ba,Abba Yana ji shima ransa ya baci Yana son yarsa bai so a lalata masa ita Shuru yayi yace kina da gaskiya,Mama tace kinyi dai dai ya zaci irin yaran nan ne yan talla lalatattu amma laifin mahaifinku ne da ya dauki nauyinku ai da haka bata faru ba

Itama Nusaiba Koko ta zuba tasha Amma ubansu a gabansu yake Shan shayi me kauri Kuma uwarsu zai sa ta dafa shayin ya siyo Madara da komai ya hada abinsa da kauri ya Sha a gabansu suna kallo yaran kanana Nusaiba ce Kawai Babba,Babar Shehu ce tazo daga kauye da Leda katuwa ta mikawa Mama tace gashi kanzo ne da nake shanyawa na taho muku da shi kwa rage zafi,ta Mika Mata Sabulun wanki da Omo da yawa sai masara kwano uku da gero kwano biyu,ga wake kwano daya,barkono har da kuli tace nasan halin Shehu ga wannan kwa rage zafi ba yawa,Mama tana ta godiya,su Nusaiba sai Murna sukeyi Watarana sai su kwana Basu ci komai ba lokacin Nusaiba ta ebi Kanzon ta musu dafadukansa suka ci Suka koshi shi kuwa Shehu dama a waje yake cin lafiyayyen abinci yaransa da matarsa ko oho.

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

6-10

Official

By
AsmaBaffa

page naku ne
Chapter 2 · 0% Book details