Sashe 27
Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Satin Nusaiba biyu da aure tayi kyau ta Kara kiba duk da cewa tana nuna Hali amma Sufyan wani abin Yana Dan biye Mata,Mama ce tace ta fadawa Sufyan Kar ya fita yau zata zo tace to,Yana zaune tana kwance tayi pillow da cinyarsa tace Honey Mama tace karka fita zata Zo yau,yace ai kuwa ya Zama dole na fita Sabo da Ina da aikin da zanyi yau a Office in tana so tazo da yamma ko ta jira ni,Nusaiba tace what Honey Mama ce fa yace to sai na fasa zuwa aiki kin San muhimmancin aikin nan a wajena Kuwa mikewa zaune Nusaiba tayi tace kaga Malam saurara aure fa ba hauka bane, Dan Kana mijina baka da damar taka ni yanda kake so,dama Ina Jin haushinka nace muje Kasar waje Honey moon kace na jira sai ka Gama wani aiki na hakura Ina jira Shuru na dawo nace tunda America baza ta samu ba ka kaini Moroco Nan Africa Abu yaci tura okay na dawo nace ka kaini nan Niger ko banza maga Sahara,ga Sefa dinsu me daraja sabo da bakin Hali kana min story story, kace muje yawon shakatawa ka wani siyo min English gown me araha kana nufin na saka na fita ga latest nan da ake kawowa daga manyan kasashe na fada maka ka dauki rigarka ka kaita inda zaka kaita ban sakawa wani muje Abuja nayi me a Abuja,a Abuja Zan bude Ido mene a ciki na gida Nigeria fa,yanzu Mama baka kyale ba zaka ci min mutuncin uwa wlh kaci mutuncin uwata sai na rama a Kan taka,Tsaki Sufyan ya ja yace kina haushi Kamar karya kullum haushi wan wan wan banda lokacinki na fuskanci ke kanki na rawa ko jahilci yana taba ki ya dauki wayarsa da key din mota ya fice ya barta tana zage zage
Tana haka Mama ta shigo tace lafiya Nusaiba daga aure? Tayani ji Mama wannan Sufyan din,Mama tace ki kwantar da hankalinki har yanzu fa bamu ci kwandalarsa ba ki Bari tukun mu Fara morarsa Mana zai ci ubansa kyale shi kin San fa wannan Bai kai Aslam kudi ba haka bai Kai Aslam kyauta ba,jeki ki shirya min girki me Dadi ki tabbatar yaji nama,Nusaiba tace Kai Mama suna dariya su a dole duniya ta samu sabuwa,Bayan Mama taci ta koshi tace Karo min karfin ac na Sha kafin na tafi,tana karewa gidan kallo tace oh God ta turawa yata kinyi dace Allah yasa ki Haihu da shi danki ya samu gado me tsoka,Nusaiba tace Ameen Mama kuma namiji Zan Haifa
Sai Yamma likis Sufyan ya dawo ya iske Mama a Palo,Zama yayi tare da gaisheta da ladabi Yana Mata Sannu da zuwa,Mama tace dama yanzu nake Shirin tafiya gida sai gaka,dama zuwa nayi Naga gida sannan na muku Nasiha,Dan Allah ka zauna da yata lafiya Ni nasan yarinyata Yar albarka ce bata da matsala Matukar ka kiyaye hakkinta kayi Mata abinda ya kamata abinda ya dace tayi Murmushi hehehe abinda ya dace wato duk abinda ta nema kana yi to zaku zauna lafiya zaka sameta me biyayya,Sufyan yace Inshaallah Mama,mikewa tayi zata tafi ya bata dubu goma ta karba tana tabe baki suna signa da yarta Nusaiba Wai baiyi abin arziki ba dubu goma kacal haka Mama ta tafi,tana tafiya Nusaiba ta rungumeshi tana shafa kirjinsa tace Kamar kudin da ka bawa Mama sunyi kadan,Sufyan Yana son Nusaiba shi yasa in tayi wani abin shi baya ganin laifinta yace karki damu idan munje gaida ta sai a Kara mata yafi haka tace sai mijina Suka haura sama suna dariya cike da so da kauna.
Aisha bayan barin da tayi bata fi wata ba ta sake samun wani cikin,ai Bashir Yana ganin ta Fara laulayi ya sameta a zaune duk ta gama lalacewa,yace Aisha tunda ke baki da kwakwalwar ganewa na nuna Miki haske kin kasa fahimta bari na fito kuru kuru kiji bana son haihuwa dalilin da yasa na auro ki naji labarin tunda Kika Yi aure da tsohon mijinki baki taba haihuwa ba ni nafi son mace juya,tunanina ke juya ce shi yasa na aureki sabo da na huta da jikinki amma ana taba ki sai samun ciki daga anyi abu sai ciki bazan iya ba,idan kina so mu zauna tare ki zubar da cikin nan idan Kuma bakya so to kije na sawwake Miki,Aisha tana kuka tana nadamar barin gidan Farooq tace ina son cikina,ya nuna Mata kofa yace jeki na sakeki saki daya ya rubuta takarda ya Mika mata,Aisha tana kuka ta hada kayanta sai gida.
Ummanta tana ganinta gabanta ya Fadi tace Aisha me Zan gani ba dai an sakeki ba? Aisha ta fashe da kuka,Umma tace ba kece da kuka ba nice da kuka Aisha,yanzu Zaki zo ki addabeni ki buwayeni ki damu rayuwata,ki dinga wulakantani nayi nadamar rabaki da gidan mijinki Farooq,Nice na zugaki laifina nane dama ance Indai yarinya ta wuce zaman gaban iyayenta to idan ta dawo sai ta kusa dukan uwarta,Aisha tace ai kece Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala kalli yanda na koma sai kace Jimina,wa yace ki yarda da shawara ta,ai da kina da hankali tunda ni Kika ga na kauce Hanya sai ki gyara min ai Nima ban wuce ayi min fada ba tunda na Fara manyanta kullum kwakwalwata sake kwancewa takeyi Saura kadan Aisha tayi dariya yanda Umma tace kwakwalwarta ta kwance, Aisha ta kwashi kayanta ta koma ciki wani sanyi taji a rayuwarta.
Farooq Kuwa da Nabeela amarci suke Sha amma zuciyar Nabeela Babu dadi tunanin Affan takeyi Ina zata ganshi ta nemi yafiyarsa sanna son Affan take kamar hauka ko sex sukeyi da Farooq sai ta tuna Affan take gamsuwa sunayi tana ganin Farooq kamar Affan ne ke Mata sai tayi ya jin Dadi,Indai bata tuna Affan ba to baza ta gamsu ba ranar, gashi kunyar Affan take tunda yazo ya samu an daura Aurenta da dan Uwansa bata sake farin ciki ba a rayuwarta wannan yasa ta tsani Yusuf gaba daya basu zauna lafiya ba,ta dinga nunawa Yusuf halin ko in kula tun Yana binta har ya gaji Suka Fara fada kullum basu da kwanciyar hankali har ya koma wulakantata karshe ma ya saketa hakki ne ya Kama su kwata kwata Allah bai bari sunji dadin auren ba,Farooq Kuwa zuciyarsa tana ga Aisha Kawai gangar jikinsa ce a wajen Nabeela nan ma dai Nabeela bata Yi dace ba.
Kamar yanda Raudat tace Affan ya shirya suje garinsu ranar na zuwa wani wanka Affan ya dauka da jakarsa ta kaya me kyan gaske in ka ganshi ka rantse turai zai tafi,Raudat kuwa wata doguwar Riga tasa na leshi dinkin manyan Mata masu ji da kansu ta Sha dogon takalmi da Jakarta ta kayan sawa sai hand bag komai coffee and white,tana Fitowa ta mikawa Affan flight ticket,wani yaron Affan ne yazo a motar Affan ya kaisu airport suka shiga jirgi ranar farko kenan da Affan ya Shiga jirgi tsabar gayu sai kace Wanda ya shekara dari Yana shiga yanda yake tafiya Yana gabatar da komai nasa,ga sit dinsa ga na Raudat suna zaune idan ya saci kallonta sau daya sai ya dauke Kai itama sai ta juyo ta saci kallonsa haka suke faman Yi har suka sauka lafiya,suna zuwa wani driver ne da mota me tsada Yana jiranta,suka Shiga mota da Affan ta Fadi sunan wani Hotel a garin ta rigada ta Masa booking Bai kashe kwandala ba,suna zuwa Hotel ne me tsada da kyau har room dinsa sannan tace Zan tafi zan dinga kawo maka abinci daga gida idan Kuma kaci a nan baka bukata ka fada min a waya tana kallonsa tana Murmushi,yace to sai ki ta min abu da kudinki karfa Watarana a min gori ni bana so nasan halin Mata bana Jin Dadi ki dinga kyaleni Ina biya Mana please bana so idan ba Haka ba Zan koma gida Kawai kin maidani yaro,Dariya tayi tace afwan to ka huta ,yace karki kawo min abinci nifa ba yaro bane ba Kuma duhun Kaine dani ba sannan Ina Jin turanci,tace to sorry na daina tace zanzo da dare muje yawo ta Kai hannu zata ja Masa gemu ya goce yace wannan fa raini ne ke ba matata ba sannan ba budurwata ba Zaki lalatani ya juya tare da rufe kofarsa,ta tafi tana Murmushi dama tsokanarsa tayi tasan fadin ransa.