← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 56

Sashe 13

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Charity ta kalleta Kawai ta yafa mayafi ta fice ta siyo salat da tumatir da kudinya ta siyo kifi manya soyayyu ta dawo ta iske Nusaiba inda ta barta ta samu Aslam a dining Yana jira,a gurguje ta yanka salat da tumatir da cucumber ta wanke ta kawo Dining,tana zuwa Nusaiba ta taso ta zuba abinci tasa Mai da yaji ta barbada Maggi zata kwashi salat Charity ta rike hannunta tace kinyi kadan yarinya wannan ba kudinki bane sai ki bari sai na zuba Miki,Nusaiba tayi zuciya ta mike tace bazan ci ba na fasa cin abincin gaba daya,Wacce Nusaiba ta zuba Charity ta ja gabanta ta saka kifi da Salat sannan ta zubawa Aslam shima da kifi da Salat ya fara ci,Nusaiba Kuwa ta WhatsApp tace anjima Sufyan saurayinta yazo ya kaita zata ci Dinner a restaurant da rawar jiki yace an gama.

Aslam Yana fita Sufyan yazo da Yamma likis Nusaiba ta dauki wanka har bakin gate ya dauke ta ya kaita hadadden wurin cin abinci,Suka ci Suka Sha harda ciko Mata Leda da snacks Suka dawo har bakin gate ya sauketa Suka Yi sallama,lokacin Aslam bai dawo ba a taxi ya fita Charity tana kallonta basu kula juna ba.

Bayan kwana biyu Aslam Yana gudun Kar azo a musu wulakanci Nusaiba tana gyara kayanta yace Baby ki shirya gobe zamu tashi daga wannan gidan zamu koma gidan Dana Kama Mana haya,Wani Takaici ya kama Nusaiba,Aslam yace kaddara ce kiyi hakuri kinji,Kuka Nusaiba ta rushe Masa da shi tace ka cuceni da ka min karya na aureka,me yasa baka da Imani burinka ka jefani a wahala,Aslam yace kiyi hakuri,ranar kwana Nusaiba tayi tana kuka dama yanzu bata bashi hakkinsa ta daina tunda taji ba kudi ta daina yarda da shi Watarana sai yayi Kamar zai Mata kuka take yarda da kyar.
Washe gari taxi ya Nemo Siyama ta fito da kayanta itama ta sa a Bayan mota,Dukkan kayan sawarsa da na Nusaiba mota guda aka Yi aka Kai gidan,kayan abinci da komai aka kwashe da abin bukata sauran duk a gidan aka bari,kayan kitchen na amfani duk ya tattara komai ankai,Nusaiba tana hawaye ta fito ta Shiga taxi ya zauna a gefenta Charity tana gaban mota,mota na tafiya Nusaiba tana hawaye tana cewa babu ac ne tana fifita da hannu,Siyama ta furta Aslam Wanda ya Saba da ac baiyi complain ba sai ke sama ta Kai da can kin San ac din ne, ki min Shuru munafuka cewar Nusaiba.

Hanky Aslam ya mikawa Nusaiba ta dauka da bala'i ta jefar,wata unguwa Suka Isa wacce ta masu rufin asiri ce da talakawa a Kano,wani dan karamin gida ne Wanda na bulon siminti ne gidan hayane Wanda ke dauke da Palo da one room kacal sai toilet da kitchen shikenan gidajen haka suke a jere iri Daya sun Kai guda goma wani me kudi ya Gina yake zuba Yan haya,Yan makaranta ma sunfi yawa a wajen Sabo da irin kankantar gidajen,Nusaiba taki Fitowa daga taxi tana kuka sai da me Taxi ya daka Mata tsawa,dama an diga an kawo kayansu duka, Ciki Suka shiga kujeru ne a palon matsagaita amma masu kyau ne sai karamar plasma tv,dama duk tiles ne har dan tsakar gidan,bedroom din Kuma gado ne shima Kalar kujerun da labile Kalar komai kala Daya Kamar wani gidan Yar maryar talaka,kitchen Dan kut da shi,Yace ki daina kuka ki shirya kitchen,Nusaiba ko kulashi bata Yi ba Siyama ce ta shirya Kaya ta gyara komai har bedroom din ta shirya sannan ta dauki jakar kayanta tace Yaya Aslam na tafi sai na sake leko ku,Yace dan Allah ki dinga dan zagayowa, Inshaallah cewar Siyama,Ya bata dubu biyar da kyar ta karba Dan Kawai bata da ko sisi ne,a nan ta bar Nusaiba a zaune tana shirga kuka.

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

31-35

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

BK
MMN MUNIBA
HAFSA ABDULLAHI

Kallonta yayi tana ta kuka shima yayi shuru ya gaji yace kaddara ce ta afka min ba haka naso ba ki daina wannan kukan daga karshe ya tashi ya fita abinda Babu na ci ya siyo musu ya sake zubawa a kitchen amma Nusaiba ko kallonsa bata yi ba har azahar tayi lokacin yace kin San dai lokacin Sallah yayi ko,kanta ta dago idonta jajir ta watsa shi a saman fuskarta,tashi yayi tare da daura alawala ya fice ya barta nan tana zaune sai da aka idar da Sallah sannan ta iya tashi ta shiga bedroom din ta jefa hand bag dinta saman bed din ta shiga toilet tana Jan ajiyar zuciya kamar wacce aka nadawa duka.

Siyama Kuwa tana komawa gida ta shiga da sallama Aunty tace ba dai an koroki ba? Siyama bata boye musu ba ta Basu labarin komai Aunty tace amma Nusaiba ta bata wayonta ka samu miji haka irin mijin Novel zukeke ga kudi amma ta dinga irin wannan rayuwar gaskiya na tausaya Masa shike nan zauna mu koma siyar da alalar mu inda Muka fi wayo amma Nusaiba ta bani mamaki samun miji haka,Dauda yace to anji kin damu mutane da miji kyakyawa ne ni bani da kyan ne?kina ta wani yabon mijin wata ga naki amma baza ki yabe shi ba,Siyama tace to ai Kaine Kawu lebe Kamar sakatar kofa,zanci Ubanki Dan ubanki lebena ne kamar sakatar kofa? Siyama ta sake cewa ba lebeba hakora kamar goslow a hanyar Lagos wasu sun taho ta nan wasu ta can,Dauda yace Zaki ci ubanki ni ba ubanki bane Zaki dinga maida Ni kakanki ki kiyayeni wlh,Aunty tayi dariya tace gwara da yarka ce ta fada da nice cewa zaka Yi sai kaci mutunci na

Mama ce a zaune tana waya da Nusaiba tace me nake ji Haka gida daki daya chab dama karyar tasa ta Kai haka,Bari dai sai nazo ta furta lokacin Shehu Yana gida kusa da Mama a zaune,yace Wai ke me kike nufi ne? Nusaiba kin hanata sakewa naji labari jiya Ameer ya fada min komai yanzu tsakani da Allah ki kalli gidan nan da a kuntace muke amma yazo ya Kara Mana dakuna ya Bude Miki shago bafa ni ba ke ya budewa shago ya bani jari Kuma na koma kasuwa sosai ya auri yarki yanzu tsakani da Allah dan karya zai iya yin wannan taimakon,a tunanina ke me yiwa Nusaiba fada ce ashe ke kike zugata, Babu abinda zaka fadamin Shehu dakata kana ciyar damu?, Tunda na taso a gidanka wahala nake Sha Ni da yarana,Sanda Ina da hali ba kece kika cinye kudin ba suka Kare Kika tsaneni komai nayi Miki ban birge ba ya Zan Miki face na zura Miki Ido ke da yaranki tunda kince ba abinda nake tsinana muku,Hakkin Yara a kanka yake kwarai kuwa na sani amma idan na baki kudin cefane kina bari ki basu abincin ba kadan kike dafa musu ba ki siyar da sauran komai na baki siyarwa kike yi,Mama tace to ka kyale min yata ba ruwanka yace Ina da hakki na fada Mata gaskiya,yanzu bazan magana ba tunda bai kawo kararta ba amma duk Sanda ya kawo Kara Nusaiba zata Gane kurenta auren me kudi hauka ne da arziki da talauci duk na Allah ne Kuma wlh kuji tsoron Allah ya mike tare da sa takalminsa ya fice.
Mama Kuwa Ameer ta samu ta balbale shi da fada akan me zai fadawa Shehu.

Charity Alalarta taci gaba da yi amma yanzu tallan ma bata fita ake zuwa a siye a gida,Nusaiba tunda Suka koma gidan haya bata girki ficewarta takeyi su hadu da Sufyan saurayinta a restaurant in taci ta koshi ta dawo gida,Aslam da Kansa yake dafa ma Kansa abinci bai iya ba amma haka zaiyi jagwalgwalonsa ya ci,yau da Yamma Siyama sai gata a gidan sanye da hijab har kasa da Leda a hannunta tayi sallama ta shigo Murmushi ya saki shi ta iske a palo yace manyan kasa ne yau a gidan, Charity dariya tayi ta rusuna tare da gaida shi ya amsa,Ina matar fa? Ta fita ta tafi gidansu yace,Siyama tace okay dama abinci na kawo maka ban sani ba ko tana girkin,yace wow na gode Kamar kin San yunwa nake ji,ledar ta Bude ta dakko abinci a robobin take away har kala biyu tace kaga wannan Fried rice ce dazu Muka Yi da Aunty wannan Kuma tuwon shinkafa ne miyar Egusi,Kawuna nane ya samu kudi shine yau Muka ce bari muji Dadi kaci kaji da Dadi harda nama,mikewa tayi ta dakko spoon a kitchen tace gashi ya karba Yana kallonta cike da mamakinta tafi matarsa sau dubu,Fara cin abincin yayi gaskiya yayi Dadi ya furta Yana ci Siyama tana Kare Masa kallo,kallon fuskarsa takeyi Yana ci har ya cinye daya ya Sha ruwa pure water yace dayan sai dare tace to,Charity ta tura dayan kasan kujera tace gashi a nan na boye maka Kar marar Imani tazo ta dauke,dariya yayi yace na gode ta hada ledarta da roba tace tafiya zanyi tunda bata nan, yace da wuri haka kiyi zamanki ki tayani hira dama na gaji da kallon film,tace to ta zauna tare da tambayarsa har yanzu baka samu aiki ba ka fara?
Chapter 13 · 0% Book details