Sashe 9
Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aslam Yana compound Yana hutawa ya zaci Charity ziyara ta kawowa kawarta ma yace sai yau Zaki zo munyi Fushi,Charity ta kalle shi Suka hada Ido gabanta ya Fadi ya hadu karshe,gaida shi tayi ya amsa da fara'a suka shiga ciki Nusaiba ta fada Saman kujera tana huce gajiya tace wash Kinga Charity zo ki min tausa Charity kamar gaske ta tsuguna ta Kama kafar Nusaiba maimakon Tausa sai ta lankwasa kafar iya karfinta zata balla ta,Nusaiba ta kwala ihu tare da kwace kafarta tana zagi ke wacce Dabba ce,Charity ta samu ta gallawa Nusaiba Mari ta dungure Nusaiba tace shegiya ke din banza na Miki bauta wlh kinyi kadan ta juya ta sake tallafewa Nusaiba keya ta baya ta wuce ta Shige bedroom din da Suka taba zama a gidan tare,Nusaiba ta taso a fusace tace fito ai ba gidan ubanki bane,Charity tace ai ke shi yasa Naga Shehu ne ya Gina gidan har kinyi clean Yarinyar da ni nake koya Miki daurin dankwali,Nusaiba sai dura ashar take Yi.
Washe gari da yamma Aslam yasha suit farare ya dawo daga Office ya iske Charity zaune cikin riga Yar kanti doguwa red,Nusaiba an cakare cikin Super green,Yana shigowa Nusaiba tace karbi jakarsa ki Kai masa bedroom,Charity ta duka tare da cewa barka da zuwa Sir ta karbi brief case din ta wuce sama ta Kai har cikin dakinsa,mamaki ne ya hanashi magana ya kalli Nusaiba yace Wai meke faruwa ne?Nusaiba tace Yar aiki na Karo guda Daya ta min kadan,Kuma best friend dinki? Rokata Suka Yi dan Allah a dauki Yar su aiki kullum Charity sai ta bugo min waya,ya zanyi dole nace tazo ta Fara Kuma kawarki Baby,haba Nusaiba bai Dace ba me yasa baki da tunani ne,ba ruwanka tunda na fada maka gaskiya kaki ji,Charity ce ta fito Aslam ya Kira sunanta Siyama tace naam,Dan Allah ki koma gidanku hakan bai Dace ba ni bana ma bukatar Yan aiki, Charity tace ko na koma Babana bazai kyaleni ba dole sai nayi aikin nan Kawai idan akace yau baka da iyaye to ka shiga Uku karka damu zanyi aikin,Aslam ya buga ya buga Charity tace Zama daram,Nusaiba tace ka kyaleta na fada maka tana so
Washe gari da wuri Charity ta tashi ta shirya musu lafiyayyen Kari waccen Yar aikin Kuma tana ta gyara gida me gadi Yana aikin compound ko Ina na gidan ya dauki kamshi...
Affan ne a zaune Yana waya ya mike ya fito daga part dinsa Yana cewa Yaya kayi hakuri na rigada na karba kudin,Wanda ya Kira da Yaya masifa Kawai yake ma Affan tunda Kai ka kashe zuciyarka baza kayi aiki ba ka daina kassara Ni kana zuwa ka karbi kudi yanda kaga dama,an baka aiki da komai kaki Yi,na samo maka har Offer a gomnati kaki yi na baka babban matsayi a company na kaki yi,na saka a Kan business kaki uban me kake so ayi maka Kai a duniya baza ka motsa jikinka ba mace ma ta fika kokari sai dai kaci me kyau ka sha me kyau ka saka sutura ka zaga gari,Affan ka kiyayeni karka sake zuwa ka karbi kudi a wajen ma'aikatana kaje kayi rayuwarka,Affan da shagwaba Kamar dan yaye yace ni bazan iya aikin nan naku ba na wahala idan kudinka ne bazan sake karba ba ya kashe waya,Raudat tana wajen tana ji sai dariyarta yaji tace anji kunya kayi asara Kuma Namiji da Kai ka kashe zuciyarka ka zauna zaman banza zaman kashe wando, Affan yace a gidan ubanwa na kashe wandon? Wandunana fes suke kije ki gani Designers ne,Allah ma ya kiyaye ranar da za ace na kashe wando na ban canja sabo ba Idiot ya juya ya wuce dan shi Affan bai gane hausar me take nufi ba
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️
26-30
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
MARYAM T BALIYA
UMMU ISMAIL
Ranar Affan ya Kira Landlady dinsu yace window nake so a Kara min a part Dina daya windown ya fito ta gidan wannan Raudat din Sabo da Algungumai dayan ma ya fito ta cikin gidanta Sabo da munafukai,Landlady tace palon Raudat ne fa Daya Kuma bedroom dinta ta Nan za a maka windunan?Affan yace ae ko ki min ko a bani kudin haya dana biya, Landlady tace Banda kudin da Zan biyaka yanzu na yarda Kawai Zan maka windunan amma sai ka biya kudin da za a kashe kwandalata baza tayi ciwon Kai ba,Ba matsala ya furta,Landlady sai da ta bari Raudat zata fita tace dan Allah bar min key dinki a hannuna Zanyi girki a gidanki gas Dina ya Kare,Raudat mutuniyar Landlady ce shi yasa Kai tsaye ta bar Mata key ta fice,masu aiki ta Kira Affan ya biya kudi aka huda katon Palo ya fito ta palon Raudat aka sa glass da komai cikin kankanin lokaci,aka sake huda wani window ta bedroom dinsa ya bullo ta cikin bedroom din Raudat shima an sa glass anyi komai,Raudat tana dawowa taga palonta ya koma wani iri ta duba taga windo ga palon Affan, bedroom ta shiga nan ma mamaki ya kuleta ta tafi wurin Landlady da sauri,Me gidan tasan zance shi yasa ta kulle bangarenta gaba daya ta fece ganin gida sai tayi sati zata dawo,Raudat ciki ta koma .
Affan ne yake ta faman shara da kalkale kalkalen gida sai kace mace haka part dinsa yake da tsafta komai a shirye a gyare Raudat tana ganinsa ta window Yana ta faman goge goge ya gama ya Shiga kitchen ya dora abinci harda fasa kwai ya dawo jikin window Yana karkadawa Dan Kawai ya tsokani Raudat, tana kwance a saman 3seater window din ya bude ya leka ta ciki yace ke Balagaggiyar akuya,kaine balagaggen dan akuya kwarto dan taure ka isheni Malam ka kyaleni da wulakancin da aka min aka hada min window da Kai wanne irin masifa ce wannan har windown bedroom,ae ai gwara naji munsharinki ba a ja damu idan na kulla da mutum ya Shiga uku sai na hanaki Shan ruwa,Raudat ta kalleshi tace wlh baka Isa ba Kai din banza ka hanani Shan ruwa,Kitchen ya koma yaci gaba da girke girkensa tana ji kamshi na tashi bata kulashi ba,Bata ko kalli window dinsa ba ya gama ya zubo egg source dinsa da shinkafa Fara harda Naman kaza plate daya ya Mika Mata yace ungo badan halinki ba,ba kunya ta mike taje zata karba ya janye plate dinsa Yana dariya yace yanzu sai ki karba?Dan Allah ka bani na gaji dama bazan iya girki ba yanzu,ai Kuwa Zaki mutu da yunwa ya bar jikin window ya koma palonsa tare da kunna tangamemiyar plasma tv dinsa Yana kallo yana cin abinci.
Aslam ne ya fito sanye cikin farar Jallabiya ya zuba wanka Yana shining da kamshi ya zauna a dining inda Charity ke zaune tana cin nata abincin,Ina kwana tace Masa ya amsa da fara'a sanye take cikin wata barmemiyar t-shirt yellow da wando me Fadi baki duk da haka tayi kyau Dake me kyau ce harda saka hula,dariya take bawa Aslam,Nusaiba ce ta fito sanye cikin kayan baccinta tana Mika kusan tsirara haka take amma ta fito harda yin Mika,Charity ta kalleta ta kalli Aslam tace a rike Mata,Aslam yace me? So take tace ya tallafe ta iskancin ya motsa sai taji kunya tace ba komai,Nusaiba ce ta kalli Charity ko a jikinta ta zauna Wai zuba min tea, Charity tace kinyi kadan wlh ke dai baki Isa kin sani aiki ba,a gidan aure na kike fa,Tattabara ma taci ubanta cewar Charity ,Nusaiba Tsaki ta ja tare da zuba abinda take so ta ja gefe tana ci ko a jikinta ba ruwanta da mijinta Kawai ita kudi,tana gamawa ta mike ta shiga bedroom,Aslam ya kalli Siyama wacce ta mike itama zata tafi yace Charity zo muyi gulma,Dariya ya bawa Siyama ta dawo ta zauna tace to muyi ta furta kasa kasa da muryar rada,yace bai kamata na fada Miki ba Sirrina nane sirrin iyalina amma ba yanda zanyi so nake ki Mata fada ki dinga fada Mata gaskiya ko zata yarda ni Ina son matata Ina so mu zauna lafiya amma na kasa gane kanta ba wani kulawa ba soyayya komai kudi,komai a bata kudi Aslam ya fadawa Charity duk abinda Nusaiba ke Masa yace kuma bata ganin girmana,Bata iya magana ba abinda duk taga dama yazo bakinta haka zata Yaba min,gaskiya bazan boye Miki ba idan nasan haka Aure yake da banyi ba da na hakura nayi zamana a single, Charity ta tausayawa Aslam amma tace kayi hakuri mu Mata da yawa haka muke auren kenan shi yasa ake cewa sai hakuri, Inshaallah Zan dinga fada Mata gaskiya ka Kara hakuri haka ta dinga kwantar Masa da hankali suna haka sai ga Nusaiba ta cakare ta fito tace shopping nake son zuwa,yace baza ki je ba wlh sai naje Kuma nasan Dan Kar ka bani kudi ne Kuma na eba,ta juya zata fita Siyama tace Nusaiba dama haka Kika koma wacce irin hauka ce wannan? Ke a naki haukan ma harda jahilci wlh kin bani mamaki Ashe ke jahila ce haba Nusaiba yanzu idan wani yace me zai ci da Yar talla sai kiji haushi bayan wasu ne ke bata wasu,mijinki yace Bai yarda ki fita ba amma kice sai kin fita bai baki kudi ba kin ebar Masa kudi mene hakan ke nufi,wlh kiji tsoron Allah ki gyara halinki,wani wawan Tsaki Nusaiba ta ja tace to munafuka Sannu uwata ke kin Isa ki min fada karfa ki manta Yar aikina ce ke ta sake Jan tsaki ta fice,cike da bacin rai Aslam ya mike Kawai ya haura sama Yana mugun mamaki ko a film bai taba ganin haka ba da labari aka bashi bazai yarda ba.
Ya dade a sama Charity tana zaune a Palo itama tana Takaici da mamakin Nusaiba,Fitowa yayi yasha wata shadda da alama fita zaiyi Charity tana zaune tace dan Allah kayi hakuri Sir,ka kwantar da hankalinka karka sa damuwa a ranka Inshaallah zata gyara komai zai wuce,Murmushi yayi Kawai yace ba komai na gode ya fita,lunch ta Dora musu tasan bai fiye Zama a Office ba.