← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 56

Sashe 47

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nusaiba ce zaune a gida ta zuba tagumi gabanta tuwon masara ne miyar kuka da rana tsaka domin kudin abincin da Shehu ya bawa Mama na cefane ta kwashe ta kashe wasu Kuma tayi zubin adashi sai wahala yaransa suke sha,Mama ce ta kalli Nusaiba ta tabe baki tace idan Zaki ci ma kici wa ya hanaki duk inda Kika Yi aure ki bari ki haihu ai da yanzu kina da yaro da Aslam ko Sufyan a ciki dole Wanda Kika Haihu da shi ya dinga kawo Miki kudi na ciyar da dansa amma Kika ki yarda da shawarata ke baza ki haihu ba sabo da idan wannan ya talauce ki kashe aure ki auri wani ke baza ki tsufa ba Kika dinga Shan kwayoyin hana daukan ciki babu Wanda kika samu ciki da shi gashi nan ai kin koma marar amfani baki da wani amfani.
Nusaiba ta kalli Mama tace yanzu Mama nice na koma marar amfani sabo da bani da kudi bana samo Miki kudi yanzu nice marar amfani sabo da kin gama cinye kudin Mazajen Dana aura? Mama tace ae baki da wani amfani an fada dan ubanki kuma idan ke Kika haifeni naji labari,amma wlh Mama Zaki gani Inshaallah Abba sai ya Miki kishiya Kuma Inshaallah sai an sake ki kema kiji in da dadi, ruwan mari Nusaiba taji ta ko Ina a fuskarta Mama tace dan ubanki sa'arki ce ni oh sabo da Ina Zama inyi zance dake shine Kika rainani,Nusaiba tace ae din na fada tana kuka tace wallahi Kuma ko Zaki kashe ni sai na fada Inshaallah sai an sakeki kema Kamar inda Kika kashe min aure Kika dorani a hanyar banza,Baki min tarbiyya ba baki ma cancanta ki Zama uwa ba ma,Mama ta mike ta rufe Nusaiba da duka ta ko Ina amma Nusaiba bata fasa fadar abinda taga dama ba.

Affan kuwa Yana Office ya fara tunanen matarsa irin farin cikin da yake kwasa a wajenta tun kafin 5pm ya tattara sai gida,shi da yace sai 5pm Raudah tana kitchen sai ganinsa tayi ya shigo bayan ya Mata sallama ta amsa ya Rungume abarsa a jikinsa,Allah yasa ta gama kwai Kawai take dafawa shima ya dahu tana jira ne ta sauke ya shigo,Gas din ya kashe tare da Daukanta cak Kamar jaririya sai bedroom dinsa,burin Raudah ya cika ya dawo da wuri tace kasan me na tuna? Yace sai kin fada Yana ajiyeta saman gadonsa tana dariya kasa kasa tace fadan mu da kullum bamu da aiki sai fada Murmushi yayi yace sabo da yawan appointment dina ne,dariya Suka yi yace ai kin rainani da yawa ne,tace ai kuwa Watarana da na maka Tsaki ka mareni gaskiya na maru sai da na kwana kumatuna suna zafi tun daga ranar ban Kuma ba,me yasa Kika sa min Ido ne a lokacin? Maybe so ne,a'a ba wani so yanda Kika tsaneni,dariya suke yana shafa cikinta Yana Kare Mata kallo tayi kyau sosai sanye take cikin kana nan kaya wani dan short wando da Yar rigarsa yace halina da ke iya wanka kina birgeni ga tsafta ko Ina kamshi duk wani lungu da sako kamshi yake zubawa har can head of Service clean Yana kamshi tv dinsu dake kunne a bedroom din tana ta wakoki iri iri na Nija,Raudah tace Baby ka iya rawa? Yace rawa ban taba gwadawa ba a rayuwata ba wannan ba girma rawa sai Mata ai amma Namiji me class baya rawa bata cikin swag dina, Murmushi tayi tana shafa sajensa da gemunsa tace Yan gayu, Ido ya zuba Mata itama shi take kallo cike da shauki yace Allah sarki Hussain yayi asara,dariya tayi tace ba ruwana ni da ni na fada sai ka Fara Jin haushi kace Ina zancen tsohon mijina,yace ki daina cewa Hussain mutanen kirki su ake kira da Hussain amma shi Usaini yake su Usaini anyi asara,Raudah ta Masa Shuru sabo da tana magana zai ce tana Masa maganar wani,tashi ki kawo min milk before na fara servicing dinki,tace alright ta mike tana cewa kayi timbidi da yawa,dariya yayi yace dan Allah karki sa na tuno timbidin Yara me karni na kasa Shan madarar,Ni timbidin mazan aure nake nufi,lips dinsa ya lashe tace Allah ya shiryeka suna dariya yace ameen taje ta kawo Masa madarar tare suka shanye tace ka Dade kayi karko duk nasan ba rago bane,kissing dinta ya Fara Yana sarrafata Kamar zai cinye ta danya itama haka har Suka lula duniyar su ta Dadi.

Aslam tunda Siyama ta samu ciki kullum Kansa Yana saman cikin tun cikin ma bai fito ba,ya dinga Tambayarta me take son ci,in Banda gyada me gishiri ba abinda take ci kullum sai abinci Wanda ya Zama dole tana ci ta koshi ga gyadarta a kusa,bayan Mum ta tafi da sati daya Aslam da Siyama Suka tattara Suka tafi yawon shakatawarsu kasashen duniya,Nusaiba sai labari ta ji,ta zauna tana ta faman bala'i ita Daya a tsakar gida tace Siyama baza ta taba ganin dai dai a rayuwarta ba,tsawa kwarantsa sai ta fado Mata a kai ta mutu kowa ya huta,shima Aslam sai ya talauce ya tsiyace da izinin Allah sai yayi bara a gefen kwalta sai yazo wajena ya nemi taimakon Naira hamsim,Mama tace Ameen Inshaallah basu babu ganin dai dai Siyama sai ta dawo tallan goro,Siyama tace Kuma baza ta taba haihuwa ba, Inshaallah cewar Mama bari zata dinga yi jini ya barkewa shegiya sai ta shekara tana zubar da jini mijin bai samu damar saduwa da ita ba suna ta fama su kadai.

Kawu da Shehu watansu kusan biyu a kasar waje ana kaisu yawan bude Ido Suka koma Saudiya a karshe Suka sauke farali can suka hadu da Aslam da Siyama, daga nan gida Suka dawo Suka bar su Aslam a can,Shehu yayi bulbul yayi kyan gani gashi suna ta waya da Landlady ita ta Dade da dawowa Nigeria sun gama shirya aurensu ,sai daga baya yaji ma ashe tana da kudi
Shehu bayan sun huta da sati biyu ya samu Mama cikin dare suna kwance ya tashe ta yace tashi zamuyi wata magana,Mama ta mike tana Jan tsaki wacce magana ce wannan sai cikin dare mutum yana baccinsa Fadi ni naji mene? yace dama fada Miki zanyi Zan Kara aure wani watan idan Allah ya kaimu za a daura min aure,ban gane ba wanne aure? Wanda Kika sani dai shi Zan Kara ma'ana Zan Kara Mata ku Zama ku biyu,banyi dan naci zarafinki ba,ahayye eheheheeeeee heeeeeeyy Mama tayi shewa tace dama ka dade kana cin amanata ban sani ba kwarto a wanne dakin zaka sakata daki uku ne daki daya namu daki daya na Mata daki daya na maza to Ina waje? Shehu yace Aslam ne zai min auren nan fa kwandala bazan kashe ba shine zai min komai yace, yace idan so nake ma zai bani gida na saka Amarya,nace a'a gwara na hada Kan Yara na gida na Zan kawo ta tunda gidan zaiyi part guda yace zai gina min part daban a cikin gidan nan a wancen part din dana katange ban gina ba,Mama ta fashe da kuka da ihu cikin dare tace amma Allah ya tsinewa Aslam Albarka bazai ga annabi ba,Su Nusaiba sunji ihun Mama Suka firfito,Mama cikin tsakar daren ta fito tsakiyar unguwa tana zunduma ihu da kuruwa sai da makwafta suka fito Shehu yace kowa ya koma gidansa akan Zan Kara aure take wannan haukan,aka dinga tir da halin Mama,da kyar su Nusaiba Suka lallabo ta ta dawo gida tace wallahi yau bazan kwana a daki ba a tsakar gida Zan kwana tun suna lallashi har Suka gaji Suka koma daki ita Kuma Mama a tsaye gari ya waye Mata tana faman zunduma ihu,Shehu bakin ciki Kamar ya kashe shi ta gama tozarta shi,Kamar Wasa da safe sai ga motar yashi tana ta saukewa a kofar gidan Shehu aikin Aslam ne,Mama tace Nusaiba ku fita ku barbaje yashin nan a kasa duk ku tirje shi,sauran yaran Suka ki zuwa Nusaiba ce take taya uwarta kishi ta fito Kamar sabon kamu tana eban yashin tana watsarwa a cikin kwata,Allah ya kawo Shehu ya kamata ya nada Mata shegen duka Kamar zata mutu,Shehu Yana shiga gida Mama taci kwalar Shehu tace idan kayi min kishiya shegiya nake algungumi azzalumi Allah ya isa shine ka samo me kudi zaka auro bazan yafe ba sabo da mu talakawa ne wallahi sai ka sake ni ka sakeni,a gaban yaranta tayiwa Shehu haka Shehu hannunta ya cire daga jikinsa ta karfi yace ki tafi gidan ubanki na sake ki saki daya,Mama Hannu ta daura a Kai tana ihu shine ka sakeni Allah ya Isa kuka take ta tattara nata ya nata cikin fushi ta tasa keyar Nusaiba kadai Suka tafi Kauye garin su Mama su biyu,shi kuwa Shehu yace Allah raka taki gona aka ci gaba da gini.

Aslam tsabar muguntarsa ya samu part din Amarya aka kera shi Kamar gidan wani hamshakin me kudi 3room and Palo aka Mata sai kitchen dinta da komai,babu inda za ayi gate wani makwafcin Shehu zai tashi daga unguwar yayi sabon gida Aslam ya siyawa Shehu gidan aka bajeshi tare da hade shi a bangaren Amarya aka mata gate me cin mota biyu abinta ko Ina yasha tiles da Interlock kyau Kam ba a magana gidan ya keru,ita Kuwa bangaren Mama Yana nan sai paint aka mata Kawai shi ma me paint ne yaji kansu ya musu komai siminti ne,Mama Kuwa da Nusaiba tunda Suka koma Kauye garau garau ma da kyar suke samu ga kazanta,daga dankali sai kunu sai tuwo,dambu,danwake shima kadan ake basu,Basu taba sanin da a Rahma suke ba sai da Suka zo Kauye ashe a gidan Shehu ba karamin dadi suke ji ba,sun rame sunyi baki,tsakanin Nusaiba da Mama sai fada suke Yi babu mutunci a tsakaninsu
Chapter 47 · 0% Book details