← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 56

Sashe 17

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aslam Yana zuwa Office din yace sai jibi zaizo ayi magana yau baida lokaci babarsa ce ta dawo daga kasar waje tana airport zaije ya dakkota Suka ce ba damuwa,Nusaiba ta dinga Jin haushi ita ta matsu ya bata takardarta,Mum ce tazo ya sameta a airport,tana ganin danta a taxi ta Fara hawaye,karasawa yayi ya shiga share Mata hawaye ta rungumeshi tana kuka tace haka Allah yaso Dana, yace Mum me yasa kika zo ban sani ba nace sai na samu aiki zance kizo,Hankalina ya kasa kwanciya sai naga dana,kana ganin Mum kasan itace ta haife shi Fara ce tas shi Kam har ya fita fari ma,da sauri ya siya Mata lemo da ruwan roba Suka shiga taxi zuwa gidan hayarsa,Mum ganin gidan shima sai da tayi kuka,suna shiga ciki Nusaiba ta dawo tana zaune tana kallo,Sallama sukayi ta amsa da kyar ko kallon Mum bata Yi ba,Mum tace yata baki ganni bane ko ba Nusaiba bace nasan ai kin Sanni tunda kafin ayi auren nazo ganinku,Nusaiba baki ta tabe tana Mata kallon banza tace Ina yini daga haka bata sake magana ba,Aslam ne yace Mum zauna ya Kai Jakarta bedroom dinsa,yaje kitchen da Kansa ba abinci ba a dafa ba gashi yaji tana cewa yunwa take ji,Fitowa yayi yace Nusaiba dan dafawa Mum wani abu,direct tace na gaji,da sauri Mum ta kalleta tace ke Wai ko baki da tarbiyya ne? Ae sai kizo ki koya min,Aslam ne yaje ya kwashe ta da Mari uwar tawa zaki fadawa haka ya fisgo wayar charger,Mum ce ta rike shi tace kayiwa Allah ka kyaleta Ina da Yan Uwa Ina da gidan Zama wajen dangina karka damu Indai nice,kaga dakko min jakata muje can,Mum hawaye ne ya zubo Mata tace tabbas Aslam Allah ya jarabceka,Siyama ce ta shigo da sallama,Aslam yaji wani sanyi da farin ciki da ya dade bai ji ba yau yafi murna da zuwan Siyama,Tana zuwa ta Gane Mum ta taba ganinta sau daya da bikin Aslam da Nusaiba,Durkusawa tayi ta gaishe ta,Mum ta amsa da fara'a,Aslam yace kawar Nusaiba ce nasan baza ki gane ta ba,Mum tace Masha Allah ziyara Kika kawo? Siyama tace ae,ya sunanki? Siyama cewar Charity,Yaushe ta zo ne ta tambayi Aslam yace yanzu fa Kinga Ina cewa ta tsaya ma ayi Mata girki taci Wai zata tafi gidan Yan uwanta Mum guda tayi Fushi da gidan danta,Dariya Siyama tayi tace ai kuwa girkina Mummy zata Fara ci a kasar nan ta shiga kitchen da sauri,Mum ta kalli Aslam tace ya haka Kuma kawarta ce da shiga kitchen haka? Nusaiba mikewa tayi fuuu ta Shige bedroom,Aslam ya zauna Yana bawa Mum labarin Siyama da komai ma bai boye Mata ba da irin abinda Nusaiba ke Masa da Neman saki da Nusaiba ke yi,Mum tace mu gama gobe Zan je gidan su Nusaiban da kaina karka damu

Siyama ce ta leko tace me Zan dafa mata tana tambayar Aslam da Ido a hankali yace tuwo tafi sonsa,ai da sauri ta sake fitowa ta yafito Aslam da hannu yazo kuwa da sauri ta lissafa Masa abinda babu ya fita bai Dade ba ya kawo Mata tayi tuwon shinkafa miyar taushe,Mum ta dinga godiya tace kin samu ladana yarinya kinji yunwa ta gama dani, Mum ta baje tuwo a plate da Miya tana ci suna Hira da danta shima a kwanon Mum din yasa Spoon suna ci tare,Siyama ta zubo itama tana ci,Mum tace yata miyar tayi dadi kin iya girki,Siyama tace ai Dan Ina sauri ne shi yasa Amma da sai tafi haka Dadi,Mum tace Allah? tace ai yanda na iya girki ko a gidan sarkin garin nan sai haka,Nifa na Gama kwarewa hannuna ya fada,Mum da Aslam suna ta dariya Siyama tana yabon kanta,tace sai ma na yanka Miki salat inda kisan Amarya kin San Mum yankan Amarya ma na daban ne tace kwarai kuwa Siyama,Aslam yace ki bari dai a fada amma kina ta yabon kanki mu baza mu yaba ba.

Masu sharhi Ina godiya

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

36-40

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne
FUTURE RM
RAHMATU ALIYU KUNDE
BK

Siyama Shuru tayi tana jira a yabe ta tunda Aslam yace idan tana yabon kanta su baza su Yaba ba,Sai da Suka gama cin abincinsu Suka koshi sannan Mum tace itafa baza ta zauna a gidan ba dole Suka fito gaba daya har Aslam da Kansa ya Kai Mum gidan Hajiya Zainab Yar uwarta ,Siyama tuni tayi gidansu itama ta samu Kawu Dauda ya dawo ya kalleta yace Siyama Ina mamakinki yanzu yanda kike saka kayanki Wanda duk mace ke sakawa harda hijab sakawa kike Wai lafiya? Dariya tayi tace Kawu ba komai girma ne yasa na canja gaba daya, Amma wannan girman naki ya kyauta kin tashi daga Charity gaki kullum a mutunce kike fita dama Ina bakin cikin kayan nan naki da Kika nacewa gasu su ba masu kyau ba Alhmdllh da Allah ya shirya min ke, Siyama tace Ina aure zanyi reverse wlh sai dai idan baza kuzo gidana ba amma kayan da Zan dinga sakawa Ko Kai Abbu sai kayi Allah wadai da su,Kawu yace a'uzubillah Allah ya tsare uba da ganin yarsa a haka mijinki kadai Zaki sawa ai,Siyama tace to Ni ba Mai hanani sakewa a gidana Wanda baya son gani Kar ya zo,Aunty tana girki tana jinsu tace ke ki bar zubar nan kizo kiyi sauri ki min talge tafiya tayi ta kamawa Aunty girkin

Allah dai ya kawo Miki mijinki kema na gari cewar Aunty tana kallon Siyama wacce ta furta ameen anko wanne kala zamu fitar,Aunty tace yau naga duniya ba mijin ma amma kina zancen anko wacce kala Siyama me yasa baki da kunya ne? Talla ne yasa da baki daura min talla ba ai da idona bai bude ba,Aunty tace talauci ne yasa Watarana kina ganin Kamar Ina takura Miki sabo da baki da iyaye ba haka bane Watarana yanayi shi yasa ake dorawa yaro talla ba kowa bane yake tura dansa talla ba sabo da son abin duniya wasu dole ce ta sa hakan,sannan yanzu ba gashi ba da Kawunki ya samu jari a hannun Aslam mun samu ci gaba yaushe rabon da ace mun yini bamu ci ba,tallan ma gashi an daina sai dai a siya a gida,Gidan Nusaiba da mukace kije kiyi aiki har ga Allah mun zaci da zuciya daya ta daukeki ba wani aiki zaki ba duk da bai dace bama kamarki kije gidan kawa aiki kina budurwa haka Kuma gidan kawarki munyi son zuciya a nan kiyi Hakuri,Siyama tace ba komai Aunty ai nasan bakwa zaluntata takura min da kukeyi da aiki da zuwa makaranta nasan gata ne dan na koya ne ni Kuma a lokacin Banda hankali sai Naga kamar Dan bani da iyaye ake min haka,dama wasu da yawa yaran ruko ba zaluntarsu akeyi ba sune suke ganin kamar Dan an sasu abu Kawai ai basu da iyaye ne yasa cewar Aunty Suna ta hirarsu dai.

Aslam sai dare ya koma gida ya bar Mum a gidan Hajiya Zainab Yar uwarsu Yan maza zar suke da Mum,Nusaiba ya samu ta kamo channel din disco ta kure volume kida har waje tana bi da baki ga malti narta a gefe,Sallama yayi bata ji ba ya dauki remote ya rage Volume, dagowa tayi da sauri Suka hada Ido tace mene haka hutawar ma baza ka bari na huta ba Ni bana son irin wannan mutum baida ko sisi da zai iya daukan nauyina sai takura ta dauki Remote ta Karo karar kidanta,Idonsa kyawawa ya lumshe window ta bude tace gida ko ac babu mutum zafi Kamar zai kashe shi anzo an kawo mutum gida kamar kejin kaji,Aslam Yana zaune Yana jinta,wakar data ke kallo shima yake kallo ganin Yana kallo ma'ana ta birgeshi sai ta kashe tv din gaba daya Wai bazai kalla ba,bai kulata taci gaba da cewa kullum da safe ko dankalin turawa babu tunda nazo mayen gidan nan ba a bani ba,Haka doya ma da Dan kwai duk babu da safe sai dai na karya da shayi da Kosai,Aslam a nan yayi magana yace da shi Kika Saba ai kosai sana'arki ce ke baki ji kunya ba Wai? Dan Allah bakya Jin kunyar maganganun da kike fada bana so na Miki gori baza kiji dadi ba matar da ko kanzo Watarana Babu da za aci amma kina da bakin magana,Yunwa ce ta fado daku gidana har na sanki wannan kaddarar ta aurenki ta fada min,Nusaiba tace ai Babanmu Yana da kudin bamu ne bayayi sabo da haka ba talauci yasa ba,dariya yayi yace kinji kunya wlh Wai kina Maganar ac no ba ac ba kankara za a kawo Miki kalli jikina kalli naki waye yafi Kalar hutu,Kaga Malam saurara karka ci min mutunci nace ka sakeni dole ne auren,Aslam yace ihun banza kike yi ya tashi ya shige bedroom.

Zuwa dare sha'awa ta Kama Nusaiba tana so Aslam yazo rokon ta bashi hakkinsa idan tayi Masa yanga sai ta yarda tunda tana so yau ai Kuwa ko kulata baiyi ba,bata kwana a Palo ba Yana jinta ta kwanta a bayansa tare da rungumeshi jikinsa ya janye,ta sake rungume shi tana goga Masa kirjinta a bayansa Cucumber ta mike sosai Nusaiba tace ka bani hakkina Malam yau wata biyu kenan baka Yi min komai ba,Aslam yace bazan iya ba ni da bani da lafiya Hannu tasa tare da taba Cucumber dinsa tace gata nan ta mike wlh ka bani hakkina,yace wlh baki Isa ba karewar mikewa ta tashi sama bazan Yi Miki komai ba,Nusaiba tace Allah Yana gani bazan yafe ba ta fashe da kuka dan Kawai ta hanashi bacci taci gaba da uban kuka a zaune a Kan gadon tashi yayi da pillow daya ya koma Palo saman kujera a can ya kwanta ta biyoshi tana tattaba hannunsa tana kuka tace wlh yau babu bacci a gidan nan haka Suka kwana baiyi bacci ba itama bata Yi ba Kuma bai Mata abinda take so ba tunda shima wulakanta shi take yi a Kai tun Yana nema har ya hakura.
Chapter 17 · 0% Book details