← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 56

Sashe 16

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mamansu ta rasu da watanni Yusuf ya fara wulakanta Affan kamar ba gidan dan Uwansa ba,karshe Affan har ya gaji ya fara sana'a haka Kawai sai ya saro irin Guava ya dinga siyarwa Yana samun kudinsa baya kula kayan Yayansa,ya koma sarar irin su safa da handkerchief yana bin titin kwalta a hannu Yana siyarwa,ya dawo ya koma koma siyar da su charger a gefen titi da Haka ya samu ya shiga University amma shi BUK ya samu a Kano ya dawo Kano Hostel a school ranar da ba school ya tafi siyar da kayansa a gefen hanya,har ya hadu da wani babban mutum yace yazo ya dinga zauna Masa a shago a kasuwar kofar wanbai Harkar Yan robobi,ya koma can Yana fama a Haka ya kammala degree ga Yayansa can kullum arzikinsa Kara gaba yake amma sisi baya bawa Affan bai ma San Ina yake rayuwa ba,Affan wata yarinya ya samu Yar talakawa Suka Fara soyayya Nabeela,Yana mugun kaunarta Kamar ransa a Kaduna take

Mamanta tana da ciwon zuciya kullum Affan akan taimaka musu yake duk abinda ya samo a wajen Maman budurwarsa yake karewa wajen nema Mata lafiya,Neman kudi yake Yana samu amma Maman budurwa kullum a asibiti can yake Kai kudin,magunguna shine ke siya, Basu da abincin ci shi zai siya musu a Haka jarinsa ya tarwatse babu ko sisi,Watarana Affan yaje zance Sabo da Nabeela ya koma Kaduna,ta rako shi gefen titi kenan Suka hadu da Yayansa Yusuf zai wuce a mota ya tsaya,Affan yace Yaya Suka gaisa ya nuna Masa Nabeela yace itace budurwata yace Nabeela ga yayana uwarmu Daya uban mu daya tace oh suka gaisa Yusuf sai kallonta yake gaba Daya Nabeela ta tafi da imaninsa,bayan Affan ya shiga Napep ya tafi sai ya dawo da motarsa ya Sha Gaban Nabeela yace ta shigo ya rage Mata hanya,Bata kawo komai ba ta shiga motarsa Suka tafi har gidansu har take fada Masa rashin lafiyar mamanta ya shiga gidan Suka gaisa tashi Daya ya basu dubu dari biyu,zuwa sati Yusuf ya koma gidan su Nabeela yace ta shirya zai fitar da mamanta kasar waje India nemo Mata lafiya Suka dinga murna
Affan ma tuni Suka daina ta tasa idan yazo ma bata taba fada Masa Yayansa Yana zuwa ba ko dan kudi ya bata sai Taki karba tace Alhmdllh karka damu yanzu Allah ya hore mana, bata fada Masa zasu je India ba Kawai Yusuf ya musu visa da komai Suka je can ai Kuwa Maman ta warke ta samu lafiya Suka dawo garau da ita,Sabo da irin kudin da Yusuf ke kashe musu Yana cewa zai turo manya Suka ce ba matsala,ya turo da danginsa na zamfara Kuwa aka tsaida ranar aure, Affan Yana ta zuwa zance bai taba sani ba yaji dai Yayansa zaiyi aure,ranar data Kama daurin auren Nabeela da Yusuf sai Allah ya kawo Affan yazo zance da safe Dan lokacin ma a gidan wani Abokinsa yake zaune ai Kuwa ya iske abin mamaki Yayansa ya aure Masa budurwa har an daura aure ma ana ta hotuna,Nabeela ta fito Suka hada Ido da Affan ta fashe da kukan munafunci,Affan mutuwar tsaye yayi Kawai hawaye na tsiyaya a idanunsa tunda ya tabbatar Kawai ya juya ya bar gidan.

Yusuf Yana ta Neman Affan yasan yayi laifi, Affan Kuwa yafi sati biyu Yana cutar so,Abokinsa sayyeed shine ke ta tausarsa har ya dan Fara hakuri ya Sha wahala ya rame sosai ya fita hayyacinsa Yana mugun kaunar Nabeela,lokacin Nabeela ma tuna abinda tayi na cin Amana ya hanata sukuni a gidan miji,Yusuf ya kasa Gane kanta dole ya Nemo Affan yazo har dakin Abokinsa ya samu Affan yace Affan sai dai fa kayi hakuri,na kashe kudi...Affan yace dakata Mallam ni kasan me na musu jarina kaf na karar bani da shi na iya taimakon su Kai Kuma kana da arziki idan kayi ma baka birge ba domin nasan da Kaine a halin da nake ciki na talauci baza ka iya sadaukar da arzikinka garesu ba,Indai akan macece kaje na hakura na bar maka har abada Kai jinina ne amma idan kayi da kyau ma ka sani idan ma baka Yi da kyau ba ka sani kanka Kuma Allah Yana kallonka,Suna haka Nabeela Katsam sai gata itama ta fito daga gidan auren nata tana cewa Dan Allah Affan ka yafe min,Affan ya kalleta yace bazan taba yafe Miki ba Nabeela kinfi Yusuf Laifi tunda da baki bashi kofa ba keda mamanki da Haka bata faru ba na tsaneki a rayuwata nayi nadamar saninki a rayuwata mayaudariya makaryaciya suna kallo ya hada kayansa ya dakko kudinsa da ya Dade Yana tarawa a asusu ya fice da akwatinsa,Yusuf ya rike hannun Affan yace ka tsaya na samo maka aikin gomnati,yace bana so ko karatun Kai ka saka Ni? Yace to ga jari Zan baka Affan yace bana so ya fisge hannunsa,yace Zan baka aiki a company na dake kano yace bazan taba zuwa aiki ba bani bukata,Yusuf yace jarin milliyoyi Zan baka Affan yace bani bukata,Yusuf yace kafi so kayi ta gayunka kana zaga gari ba sana'a? Yace ae ya fice abinsa ya tafi ya shiga motar Kano daga nan ya irga kudin asusunsa wajen dubu dari hudu ya tara asusun ya Dade tun yana secondary yake uban yawo da shi Yana jefa duk abinda ya samu,Yana zuwa shine ya Kama gidan haya gidan da Raudat ta Kama yace yanzu ya daina wahalar da kansa,duk yawan uban wankan da yake dauka yace ya fita Yana da appointment kasuwa yake zuwa ya zauna a shagon wannan mutumin Alhaji da yace ya dinga zamar Masa Yana biyansa Kuma ba laifi Yana samu sai dai abinda ba naka ba Sam baya isarsa komai sai dai Yana kashe Yan bukatunsa kanana,ranar da baya zuwa kasuwa Kuma Friday,Saturday,Sunday to sai yawo wurin Yan abokan arziki,gashi ya Kama gida me tsada Kuma Kaya me tsada yake sawa yanzu yace ya girma ya gaji da Shan wahalar rayuwa dole sai yaji Dadi,shine data kure Rannan ya rasa ta ya zai biya kudin haya yaje company na Yusuf Yayansa yayi awon gaba da wajen dubu dari biyar ya kirashi ya dinga masifa Wai ya bashi ayyuka da jari duk yaki Yi shine zai ebar Masa kudi bai San dole ce ta sa ba badan dole ba Affan baya bukatar abin hannun Yusuf

Raudat bata San ta Sha aiki haka ba sai da safe bayan ta shirya tana karyawa ta tuna da irin aikin da ta Sha jiya sai take ganin kamar a f
Mafarki,fita tayi bata sake kula Affan ba bare suyi fada ta tsorata da lamarinsa,taga lallai da gaske ya daura dambar fada da ita,bata San shi Affan ya tsani Mata ba tun daga Kan Nabeela abinda ta Masa,shima Affan bai San Raudat ta dawo daga rakiyar maza ba tace ita da aure har abada haka soyayya ma baza ta sake ba.

A hanya Suka hadu da Affan ya dau wanka cikin kana nan Kaya Yana taku dai dai ya Sha kyau dukkan matan dake Compound din basa iya dauke Ido da kallon Affan Dan gayu haka,ta fito zata Shiga motarta Saura kadan suyi karo da juna tace Sannu Ina kwana,Kallon up and down ya Mata ba karya ta zuba kyau ta Sha wata Arabian gown me shegen kyau da tsada kamar Yar India kyakyawa da ita dagwas,Baki ya tabe yace Ina da appointment karki bata min lokaci da gaisuwarki in Banda gulma yaushe Kika Fara gaishe ni a gidan nan,Raudat ta tsaya tana kallonsa ya Mata kyau,yace banyi Niyyar aure yanzu ba fa ko kin kalleni a banza duk wata mace tayi hakuri Affan ba yanzu ba na Mai rabo ne,Allura ce a ruwa me rabo ka dauka,Dariya ya bawa Raudat ya kalleta yace no..no.no fari da kwarkwasa basa Jan hankalina ki Adana abinki ga sugar Daddy dinki,Dariya ta sake saki yace baki da aikin yi ya juya ya tafi Yana wani taku cike da takama irin mazaje,Raudat ce ta fito da motarta daga gidan Yana tafiya a gefen titi har wani tattalewa yake Yi tsabar gayu Yana basarwa wani lokacin Kuma asa Hannu a hantsar Jean din a tattaro Cuccumber yanda gayu ke yin wannan iskancin a titi,Raudat a hankali take binsa a baya da motarta tana kyalkyala dariya tana kallon gayu,Masallaci taga ya shiga ashe Sadaka ya saka ta dari biyar a cikin asusun masallaci ya fito ya Kara gaba tana ta binsa har ya shiga Napep tana bin Napep din Yana kallonta ya gane motarta,cumb ya zaro ya shiga taje Suma kamar me,Dan karamin turare ya dakko a aljihunsa ya fesawa sumar zuwa sajensa Raudat tana saitin Napep din,Lekawa yayi da Kansa yace uwarka ya zageta yana turo mata pink lips dinsa gaba,Dariya ta sake yi ta daki sitiyari Yan dubu dubu na dubu uku ta dago Masa ta glass da hannu yace ta Miko su Ina son su,Raudat glass ta sauke kasa tana kallon titi tana Miko Masa kudin ta napep din kowa na kallo a titi ga Wanda ya kula Affan yasa hannu har cikin motar Yana cikin Napep zai karba Me Napep ya taka da gudu,Yace dalla slow down yayata ce zata bani wasu canji Zan siyo Mata kifi,Me Napep yace sorry Malam yayi Slow Raudat ta sake mikowa tana tuki da hannu daya wuf taji Affan ya karbe kudin kamar zai fado daga Napep din Saura kadan Allah ya kiyaye,motarta ta take da gudu tayi youturn ta wuce Office abinta,Shima ya tafi uzurinsa.
Chapter 16 · 0% Book details