← Book details Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 56

Sashe 33

Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aslam kuwa tsohuwar unguwarsu yaje unguwar masu kudi ita Siyama tana ta faman kuka a lullubeta cikin Mayafi har age gida bata sani ba sai da yace fito ta dago da kanta Mamaki ya kamata tace me za muyi a wannan gidan ta kalli gidansa ne katafaren gida na da Wanda ta sani Sanda Yana me kudi,Kuma duka ga motocinsa nan har da wasu sababbi ma,masu aikin gidan tsofaffi Wanda ya sallama ta gani ya dawo dasu kenan,ga inda an Kara gyara shi ya koma wani irin mugun hadadden gida har ya da a baya tsaruwa,baki ta bude yace Baby fito Yana Murmushi ya jawo hannunta ta fito tace ba dai duk talaucin da kace ba karya ne? yace ki saurareni Baby kiji ba abinda ya faru da dukiyata tun daga lokacin da nace Nusaiba ta ebi kudi a cikin kudina ta bawa Mamanta ta kwashe kudin duka na Fara zargin sabo da kudina ta aureni badan Allah ba shine nayi Mata haka Kuma ko Mum da Sabeer ban fada musu komai ba tunaninsu da gaske na talauce,Siyama ta Fara mamaki tace yanzu kana nufin duk banki da kace sun kwace komai karya ne? Yace ae,Fuska ta bata tace amma ka dauki hakkinmu hawaye ya zubo mata tace me yasa kayi Mana haka, rudewa yayi ganin ranta a bace,tace ta ya za ayi ace dama Kawai fada kayi ka shirya zance Muka dinga Shan wahala a kanka muna Jin tausayinka hawaye ya zubo Mata,yace please Baby kiyi Hakuri ke kin San dalilin da yasa nayi haka sabo da na San me so na tsakani da Allah kuma gashi na sani ya karasa Kamar zaiyi kuka kiyi hakuri muje ciki ta shiga yasa me aikin ta shigar Mata da kayanta kaf bedroom din Amarya,ya zauna Yana aikin lallabata ya Sha fama kafin ta hakura ta sakko hannunta ya rike kin zauna a Palo Baby muje sama Suka haura sama jikinta a sanyaye tace ya akayi Naga motar da Nusaiba ta siyar maka Wanda tace Wanda ya siya ya gudu bai bata kudin ba? Yace ai Wanda ya siya motar yarona ne tunaninta ban me nake ba ni na tura shi ya siyi motar ya gudu Kuma,Saurayinta data aura ne kadai ban sani ba ban ma taba ganinsa ba amma komai da takeyi Ina sane

Suna Shiga bedroom dinsa ya rungumeta a jikinsa yace ko za a hanani yanzu? Murmushi ta saki tace yaci gaba da rungumeta Yana shafa wuyanta,tsigar jikinta ce ta tashi Wanda ya jawo ta lumshe idonta,yace kinyi wanka a gida ko yanzu zamu Yi Yana magana yana goga Mata Hajiya Babba wacce ta mike sosai,tace yanzu nayi wanka yace Nima Haka, toilet dai ta Shiga taci gaba da kukan barin gidansu ta wanke fuskarta ta fito tare da zabo rigar bacci ta gaske ta saka shi yayi shirinsa ma,kayan makulashe Suka lashe sannan Suka Yi brush ta Fitowa ya dauketa sai saman bed ya kwantar da ita a hankali...

Nabeela ce ta samu ciki a gidan Farook murna wajen farouk ba a cewa komai,Kamar gaske sabo da bata son Farook taje a boye ta zubar da cikin aka Mata Allura,Bayan ta dawo gida cikin dare ta fara bleeding yayi yayi ta bari a tafi asibiti taki yarda sabo da Kar a ganeta sai da ta kusa mutuwa Farook ya kasa jurewa ya dauke ya dauko Mamansa Suka tafi asibiti,ai Kuwa bayan komai ya lafa likitoci sun samu nasarar ceto ranta, likitan yace Farook ya same shi a Office,bayan Farook ya shiga ya zauna likitan ya dago ya kalli Farook ya Fara fada taya za ayi a Mata allurar zubar da ciki me karfi haka,Farook yace Allura Kuma?likita yace Kai mijinta ne ko kuwa cikin Shege ka Mata sakamako ya nuna Allura ce me karfi ta zubar da ciki,idan matarka ce ka binciketa gaskiya,Farook duk da ransa ya baci amma ya danne bai nuna ba Sam Sai da aka sallamesu bayan kwana biyu taji sauki sosai ta warke ya sameta a bedroom tana zaune,Yace Nabeela wacce Allura Kika yi na zubar da ciki? dama kin San bakya kaunata Kika aureni,kin San wani kike so Kika zalunceni na aureki, Nabeela tace waye ya fada maka? Wayo ya Mata yace Wanda Kika je ya zubar Miki cikin,tunani tayi Kawai da gaske an fada masa tace Ni bana son haihuwar, gau kake ji ya kifa Mata Mari hagu da Dama yace amma ke azzaluma ce Ina son yaran Kika zubar min da ciki, ya zari zai Fara zaneta ta gudu Daya dakin ta saka key tana Cewa Allah ya Isa,idan ya zageta haka ta rama Kawai takarda ya dakko ya saketa Saki daya ya bata takardarta ya sallameta,ita duk Affan take so akansa take kashe aurenta har da murna zata je ta nemi Affan dama taji labarin inda yake Zaune can zata tafi ko Idda baza ta bari tayi ba.

Nusaiba Kuwa soyayya suke bugawa da Sufyan abinda take so yake Mata komai ya samo a gindin Nusaiba da uwarta yake karewa,duk ta rabashi da danginsa Wanda da shi Suka dogara shike Basu ci da Sha amma Nusaiba tasa yanzu ok gaida iyayensa sai yaga dama yake zuwa,Basu da cin yau bare na gobe amma yaki ya taimake su,Ummansa ce ta gaji ta shirya ta tafi gidansa,Lokacin ya tafi Office tana zuwa ta shiga palon Wanda ta iske yar aiki tana ta gyare gyare,Yar aiki ta gaisheta Umma ta shiga ta zauna tace me aikin ta Kira Mata Nusaiba,Nusaiba tana sama taci gayu ta kishingida a saman gado tana latsa Wayarta ac na ratsata,Me aikin ce ta shiga da sallama ta durkusa a gaban Nusaiba tace Kinyi bakuwa Hajiya,Nusaiba da aka Kira da Hajiya tana yatsina tace wace? umman Alhaji ce,uwarsa ce Maimuna Wai?Me aiki tayi mamaki uwar miji guda ake Kira da sunanta gatsal haka,me aikin tace ae itace,tsaki Nusaiba ta ja tare da furta je kice Ina zuwa,tunda me aiki tace gata nan Nusaiba tafi hour guda bata fito sannan sai gata tana sakkowa daga bene tikasai tikasai tana taku dai dai tazo ta zauna tare da furta gani naji ance kina nemana,Uwar miji tace dama Sufyan nazo gani ko Yana gida?kin San Yana wajen aiki bai dawowa sai dare in kuma Zaki jirashi to ta mike tana kunkuni tana cewa miji ma sabo da Masifa baza a barka ka zauna lafiya ba uwar mutum tabi ta isheka ta Shige kitchen,tana zuwa kitchen ta samu me aiki tace idan Kika sake Kika Bata ko ruwa sai na koreki yau,Umman Sufyan tana ji a kunnenta mikewa tayi ma kawai ta bar gidan ta koma gida inda ta bawa Baban Sufyan labarin irin wulakancin da aka Mata,Baban Sufyan yace kyale shi ai Allah shike ciyar da mutum Kuma shi ke raya bawa kyale shi zaizo ya same mu watarana tunda shi mace tafi iyayensa.

Bangaren ango Kuwa Nafila yayi shi daya da adduoi Siyama tana zaune a gefen bed tayi Shuru tana tunani da farin ciki yau itace a gidan nan tangameme haka,gida na gagara,mijinta hadadde ga kudi duk natane Allah take godiya har ya idar Yana sallamewa ya juyo Yana kallonta cike da farin ciki Yana Murmushi ya mike tare da haurawa saman bed din ya jawota jikinsa

AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️

71-75

Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne

Bestynbeelat

Suna dawowa gida mota ya bude ya fita ya zaga tare da bude mata kofa hannunta ya riko ya fito da ita sannan ya bude bayan mota tana rike a hannunsa ya dakko take away nasu Suka shiga ciki ba kowa me aiki ma tana bangarenta,waist dinta ya riko suna tafiya Murmushi tayi tana kallon gidanta Kamar mafarki take gani ta kalli gidan ta kalli mijinta sai farin ciki takeyi tana tunani dama Yan uwanta da akai kaisu ganin gidan Amarya nan aka kawo su Suka kalla da yabawa suna cewa me kudi ne ashe tunaninsu Kawai zuzutun Mata ne, daukan Siyama yayi Suka karasa sama Bedroom dinsa Yana cewa gaskiya wannan rashin tsarkin naki ya min cikas da ace na San Haka ne tabbas sai na roki kawu a daga bikin a Kara sati daya,Kai fa kace baka damu ba auren shine me wahalar,kayan jikinta ya fara cire Mata Yana cewa ki daina sa min bra Indai Kika fahimci Ina mood,kallon sa tayi tace da Ina maka kallon kamili ashe kaima guda ne,na taba ce Miki ni Kamili ne? no na taba cewa bana son wagga harka? Da wani ustaz kike ganina? Siyama tace ae har tausayinka nake,Murmushi yayi yace to ki daina sarkin musulmai ma Yana son sex da Zaki ga Liman dinku sai kin daina binsa sallah,Dariya Suka yi tare da Mika Mata hannu Suka tafa

Yana kallonta yace Ina sonki tana Jin kunya yace bari nayi Sallah ya mike yayi Alwala zai tada Sallah ta mike tare da dagewa ta ture shi tana dariya tace yau baza kayi Sallar Isha da wuri ba sai na karya ma Alwala ta rungume shi,Zama yayi ba shiri saman Sallayar ta koma gefen bed ta zauna,juyowa yayi Yana kallonta Yana Murmushi yace wlh ta karye,Dan Allah da gaske daga dan runguma,Yace ai kina jona min jikinki ta karye ya mike ya fita plate yaje dakkowa me aiki ma ta shigo zata ajiye kwano tace Sannu Alhaji yace yawwa tace Allah ya barka da Aunty Siyama,nan take ya saki Murmushi tare da furta ameen ameen ya zaro 2k yace gashi Kya sa Kati ki Kira Yan Uwa,Karba tayi tana godiya tace Allah ya baku zaman lafiya ya kawo kazantar daki,Aslam yace Banda kazantar dai Yara na gari Zaki ce,to Allah yasa ta fice,ya koma sama ya iske har tayi Shirin bacci cikin wata Nighty blue ta Sha kyau gaba daya surarta a bayyane take,yace my Choice ni kizo mu ci na matsu Yana magana ya riko hannunta ta zauna a jikinsa suka ci cikin shauki,suna gamawa ya Dora ta saman bed sannan yabi lafiyarta Suka fara farantawa juna, Siyama sai kunya take ji.
Chapter 33 · 0% Book details