Sashe 24
Auren Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Siyama kuwa bayan ta Gama kukanta har kwana uku bata ga Aslam ba tana ta faman tunaninsa katsam ta fito daga wanka da Yamma yaro ya shigo yace Wai ance Siyama tazo inji Aslam,da sauri tace kace gani nan, ai ko Mai bata shafa ba ta zura skert da riga na material ta saka hijab me Kama da doguwar riga har kasa ta tafi wajensa,tana zuwa yaga fuskarta duk ruwa tayi wani fresh yace daga wanka Kika fito ne? Siyama tace ae Ina yini ya amsa da lafiya lau,tace rannan kazo Wanda ka gani ba Saurayina bane ba sonsa nake ba,yace in ma kina son abinki Charity me zance ni zuwa nayi na duba lafiyarki tunda yanzu kin watsar dani kinyi hadadde,Siyama kamar zata Yi kuka tace ba Saurayina bane tiryan tiryan ta bawa Aslam labarin Affan,yace hmm kice miji aka miki,a'a nifa ance maka sai na yarda za ayi auren idan bana so shike nan Kuma bana sonsa,Aslam ya sake cewa bari mu Fara ja baya Siyama tace kash kajika da wani zance akan Affan din me aka yi aka yi shi wani banza da shi zaka bani kunya Allah yawa kake yi,Aslam yace to shi kina ganinsa me kudi,kudin me wa yake ta kudinsa nawa ya tara,Aslam Yana ta bugar cikin Siyama bata gane ba,sai da ya gama Jin komai sannan yace to Hajiyar wanka in tafi ko na tsaya akwai labari? Siyama tace jeka,yace oh korata ma kike Yi kenan,Siyama tace nayi Fushi sai ka dinga min wasu maganganu haka marasa dadi,Aslam a hankali yace Ina sonki Siyama.....Baki ta bude tace so kuma Aslam? Yace ae ba sai kin so ni ba Kawai na fada Miki mind dina na gaji da hiding, idan Kika bari Kika auri wani laifinki ne na daina kulaki Kuma har abada ko a hanya gwara ma ki aure ni,Siyama ta rasa wanne irin murna zata Yi ta boye tace tun tuni sai da ka bari aka turo min wani wajena yanzu ya zanyi da Kawu? Yace ki San yanda Zaki yi please I love you,ban taba son wata haka ba sai ke sai Ina kusa dake nake gane ni Namiji ne tun tuni tun farkon zuwanku gidana na zaci ba so bane Kawai yasa Naga Nusaiba tafi min na aureta,Siyama ta rufe baki a ranta tace zuki ta mallen maza kenan sabo da ba Nusaiba,ganin bata da Niyyar bashi amsa ya juya ya Mata sallama ya tafi,Siyama Kuma ta Shige gida da sauri tana zuwa tayi ball da bahon wankansu ya fashe fas,Aunty tace Yar nan lafiya? Siyama ta kankame hannu tace wayyo Yana sona dadi kasheni cikin farin ciki ne, Aunty rungume ni dan Allah Zo ki rungumeni, Aunty taki kulata zuwa tayi ta rike jikin bango tana zan sume Iska zata daukeni wayyo Sanyi dadi Allah na gode maka tayi ihu,Aunty tace wallahi sai kin siyo Mana sabon baho akan Namiji Kika fasa Mana baho,za a siyo karki damu ta fada dakinta harda rawar sanyi tsabar farin ciki sai kace tana Jin sanyi haka take karkarwa.
Aisha watanta biyu a gidan Bashir duk ta rame tayi baki ta fita a hayyacinta gashi Hariji sannan Kuma Babu abincin kirki Yana samun kudi amma ya daina bata ci na kirki,a wata biyun ta samu ciki amma shi Bashir baya son haihuwa,ga mijinta can Farooq Yana son haihuwa basu samu ba taje tayi aure Kuma inda ga haihuwar amma ba a son yaran,gaba daya Bashir ya tsaneta sabo da ciki,ko ya ta bashi haushi sai duka a Haka cikin nata ya zube Aisha tayi barin Yan biyu twins,tayi kuka sosai ga rama ta kekashe ta bushe,Farooq Kuwa har wasu lokuta baiyi aure ba ya kasa kula kowa har ya gaji Mamansa ta hada shi Nabeela bazawara ita Kuma Maman Farooq kawar Maman Sabeer ce a can taga Nabeela,Aisha sai labari taji Farooq yayi aure tayi bakin ciki tayi kuka ta gode Allah har ta samu wani cikin,Bashir tsana ta dawo sabuwa dal
Nusaiba bayan ta Gama Idda da kwana uku Sufyan yazo gaida Shehu,Shehu ya sauke shi yace yaro daga yin iddarta da kwana uku har yaushe ta sanka da zaka ce zaka turo wannan ya nuna cewar tun tana da aure ka Santa dama kana sonta ko karya ne? Sufyan yayi mukus yace bazai yuwu ace daga Gama Idda da kwana uku Wai har kazo daga wata uwa duniya kana sonta Kai ba dan unguwar nan ba a Ina ka ganta sai dai idan dama tun tana da aure kana zuwa,Mama tana ji tayi gatsal tace yata shi take so kuma shi zata aura,Shehu yace ba matsala Kai Sufyan gaka ga Nusaiba duk abinda tayi maka karka soma kawo min kara ba ruwana ya tashi ya fice abinsa,Nusaiba ce tazo tace karka damu dashi Indai Mama tana sonka an gama,Sufyan Yana murna sosai ya tafi,Bayan kwana uku ya turo da kudin aure cikin sati biyu Mama ta yanke aure za a daura,Shehu ba ruwansa a ciki sai da daurin aure yazo sannan ya shige gaba Sabo da yarsa ce ba yanda zaiyi aka daura auren Sufyan da Nusaiba
Nusaiba takanas ta tafi gidan Aslam ta kwankwasa ya zaci wani ne ya bude sai kuwa ta shiga ciki tana yiwa gidan kallon banza harda cewa to Ina Aslam Dan karya gashi na riga ka aure Kuma na sake samun wani me kudin Allah ba Azzalumin bawansa bane bazai barni cikin wahala ba na sake tafiya gida me ac sai naga ta tsiya Kai Kuwa gaka nan tsiya tsiya kalli wannan dirty smelling House din naka nafi karfinka tana Jan tsaki ta juya ta bude kofa ta fice tace aci gaba da Shan talauci lafiya,Aslam baki ya tabe ko a jikinsa yace Wanda ya kulaki shine banza baki da ajin da Zan saurareki,Nusaiba tana jinsa ita Kam tayi gaba abinta.
Masu sharhi Ina Matukar godiya
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️
46-50
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
MRS SAS
YAR AUTA
Sufyan Isa,Dane ga Isa Yan garin Ajingi ne Kano amma a cikin Kano suke danginsu ne a Kauye amma uwarsa da ubansa da kannensa guda bakwai suna Kano kofar Ruwa,Sufyan shine Babba a gidansu talakawane, Allah yasa Sufyan yayi degree ya samu babban aiki na gomnati yayi aiki da shekara hudu haka Kawai ya ajiye aikinsa ya fito takarar Chairman ya koma siyasa,bayan anyi zabe ya Sha kasa ko kansilan nadi ba a bashi ba,karshe talauci ya sake baibaye su ya Shiga Neman aikin kamfani bai samu ba sai da ya kwashe shekara biyar sannan ya samu aiki a wani kamfanin shahararren me kudi ya bashi C.E.O ga Albashi me tsoka yana aikinsa sosai bai da wani aibu sai dai dan Adam kowa Yana da Hali me kyau Kuma ba a rasashi da hali na banza ko ya yake,ana haka ya ginawa iyayensa gida me kyau shima ya gina nasa gidan me kyau sosai amma bai Kama kafar gidan Aslam da bank Suka kwace ba Babu hadi ma,
ya mallaki motarsa me kyau har ya hadu da Nusaiba ya aureta Kuma.
Kwana uku da daura aure Nusaiba ta Sha gyara ta ko Ina tayi kyau sai kamshi take yi,ranar Kuma aka Kai amarya gidan mijinta me kyau kana gani kasan ba gidan talaka bane,zaune take a saman gadonta dake dama Kawai daga ita sai lefenta da kayan sawarta Amma komai na furniture ya zuba abinsa.
Sari ne a jikinta Riga da skert maroon ta yafa mayafinsa kyau Kam tayi,9pm angon ya shigo da Sallama hannunsa dauke da ledar kaji da kayan makulashe,Zama yayi a gefenta yace Alhmdllh Ni Kam nafi ko wanne Namiji dace a duniya,yau na mallakeki burina ya cika,Nusaiba tayi Murmushi tare da bude mayafin data rufa a kanta,yace tashi kiyi Alwala,mikewa tayi ta sheka wanka da Alwala ta fito shima ya shiga,shiryawa tayi cikin kayan baccinta masu daukan hankali sannan ta daura zani tasa hijab har kasa bayan ya fito shima ya shirya ya sa jallabiyarsa sannan Suka gabatar da duk abinda akeyi na addini da na al'ada,ledar ya jawo ya bude musu kaji ne da su Yogourt da sauran kayan makulashe da fruits
Plates ya dakko ya zuba musu ta kalli Naman tace Wai brolas ne ko Maja? Sufyan yace Ina Zan sani ni da na gansu a gashe na siyo,tace maza dai har abada baza kuci gaba ba,tunda aka halicci iyaye da kakanni kowa kaza kaza dai ankonta kuke Yi ko wanne ango ankon kawo kaza,Sufyan Yana Murmushi yace to me kike so? tace Ina laifin ma tattabara tana magana Yana bata naman a baki tana lamushewa amma tana kushewa,sai da suka koshi suka gama komai sannan ya dauketa suka haura saman bed abinka da bazawara tsagera zagewa tayi Suka farantawa juna rai Suka jiyar da juna dadi sosai Sufyan sai yabonta yake yace Yan unguwarku sunyi sakaki na daukeki shike nan,Rungume shi tayi tana I love you a haka har bacci ya kwashe su.
Siyama ce ta zubo shinkafa da wake da Mai da yaji sai salat ta toza wani katon plate kamar mutun uku ne zasu ci tasa a gabanta zaune a tsakar gida saman Sallaya da yamma sanye take daga ita sai vest fara da English skert wani me kyau brown Mai adon fulawowi fari,jikin nan nata sumul sumul komai Masha Allah,ta sa Hannu tana ci baza ma tasa cokali ba,Kawu ne yayi sallama ya shigo sai ga Aslam ma a bayansa sun shigo yasha farin wani yadi me kyan gaske yayi kyau Kamar baza a mutu ba,ya shigo Yana takunsa na Izza,Aunty ce ta amsa sallamarsa,Siyama kunya ta kamata sabo da irin abincin data zuba tana ci ya kamata,Aunty ce ta dakko tabarma tare da shimfida Masa ya zauna Suka gaisa