← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da "Toh" na amsa mishi. Magana yayi da wani yare da ban fahimta ba sannan ya cire wayar a kunnensa ya tsugunna a gabanmu yana jera ma Jiddah sannu kamar wata matarsa. Ban san cewa na da wani shiri a ƙasa ba domin bata faɗamin ba, ni a yadda muka tsara jami'ai ne zasu zo su kamashi lokacin da ya tsugunna a wajen, sai dai ba zato ba tsammani batare da dukkanmu biyun mun ankara ba Jiddah ta zaro wuƙa mai kaicin gaske da alama ma sabuwa ce, cikin zafin nama ta kwace a jikina sannan ta caka mishi wuƙar nan a gefen ciki, wata ƙara ya kwalla ya dafe gurin, kafin yayi yunƙurin guduwa tuni jami'an sirri da Gwamnatin Enugu ta bamu suka zagayeshi wasu daga ciki kuma suka damƙi hannunsa suka maka mai ankwa, cikin mintuna ƙalilan sai ga motar asibiti, nan aka sashi a motar tare da wasu jami'ai aka wuce da su.

Bansan a wani yanayi na tsinci kaina ba lokacin da na ga jami'ai sun kama Alpha har sun saka mishi ankwa, wannan ranar na ɗaya daga cikin ranakun da bazan manta da su ba a tarihin rayuwata, bansan me ya faru ba sai dai bude idona nayi na ganni a gadon asibiti, sai a lokacin Yaya Sadiq ke fadamin wai sumewa na yi, a lokacin ne na fara tariyo abubuwan da suka faru ina daɗa mamakin yadda kama Alpha ya zo min da sauƙi haka tamkar a mafarki, dole na gode ma Allah da ya banj nasara akan makiyina sannan dole zan godewa Almajirata.Lol.
Murnar da na shiga a wannan ranar ko runtsawa na kasa yi, kwana nayi ina sallar godiya ga Allah, wannan ranar kadai nake jira dama na ajiye aikin ƴan sanda, ranar da zan kama wanda yayi sanadin mutuwar mutane masu gurbi na musamman a rayuwata, Abbana, Mami, Kakannina, lukutar ƙanwata da kuma rigimammun ƴan biyun ƙannaina, a wannan ranar na ji ni na kammala ba ni da wata sauran damuwa da ta ragemin. Har ƙaramar walimah muka hada a resturant ɗin hotel ɗin da muka sauka, Sadiq ne ya ɗauki wannan nauyin.

Washegari kamar yadda ya zo a hukumance tunda Alpha ya amsa laifin da ake tuhumarsa sannan yayi bayanin inda za'a samu Phalmata da yadda za'a kuɓutar da matan da ya ajiye a Alpha Villa, bayan an damƙo Phalmata da sauran masu yi musu aiki ne aka wuce da su Abuja inda anan za'a yanke musu hukunci, yaran nan kuwa kowa an haɗasu da jami'ai domin a sada su da iyaye da ƴan uwansu, gabaɗaya mu ma Abuja muka nufa inda zamu haɗu da su Daddy acan don zasu zo ganin yadda shari'ar zata kasance.
Sunayen manyan ƙasar nan da suke da sa hannu a miyagun laifukan da su Alpha ke yi ba zasu kirgu ba, sunan Commissioner na daga farko-farko a cikin jerin mutanen, cikin kwanaki biyu aka cafko kowannensu, masu muƙami kowa tuni Gwamnati ta karɓe abin ta, sai dai mu yi fatan gyaruwar ƙasar mu.

Ranar da aka yi zaman kotu kuwa garin Abuja ta karɓi baƙuncin mutane da dama, sai da aka cika kotun nan maƙil babu masaka tsinke domin wasu a waje ma suka tsaya don babu gurin zama kowa nason ganin mutum ɗaya jal! da ya daɗe yana gallazawa mutane, bayan alkali ya zo ne aka gabatar da tuhumar da ake musu inda lauyan Gwamnati ya gabatar da kansa, babu batun lauyan da ke kare waɗanda ake tuhuma domin ba su da shi, cikin sauƙi ba ta re da wahalar da shari'a ba aka zartar musu da hukunci, Al'amin da Phalmata hukuncin kisa ta hanyar rataya inda sauran kuma hukuncinsu zaman gidan kaso na har abada. Daga haka Alƙali ya sallami kowa sannan aka bada umarnin wucewa da masu laifi gidan yari, kotu fa ta hargitse kowa da abinda ke fadi inda mutane da dama su ka so ɗaukar doka a hannunsu sai dai babu hali.

Sosai na so ganawa da Alpha amma Sadiq ya hana ni gudun kada wani abun ya faru, haka ina ji ina ganin muka bar garin Abuja zuciyata sam babu daɗi saboda yadda na so mu yi sallamar ƙarshe da Alpha, sam a wannan lokacin sai nake jin tausayinshi na kamani matuƙa ta yadda mace ɗaya ta lalata mishi rayuwarsa ta duniya, ko da yake shima yana da laifin biyewa son zuciya don bai tsaya a inda Allah ya ajiye shi, yana da kyau na ɗaukar hankali wanda iya shi kadai zai iya zama jarinsa don ga dukkan alamu mutum ne mai farin jini, dole daga baya na cire tunaninshi a raina. Rayuwa kenan ban taɓa kawowa cewa al'amurana zasu warware cikin sauƙi haka ba. Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin talikai wanda baya zalunci sannan baya barin masu aikata zalunci.

Kwananmu biyu da dawowa Gwamnati ta shirya mana ƙayataccen Dinner wanda ya haɗa da ƙarin girma, gabadaya jami'aina an musu ƙarin girma inda ni kuma Gwamnati ta tura ni ƙasar Malasia domin yin course na musamman a harkar tsaro, na so naki karban wannan tayin amma Daddy ya tursasa dole banj da wani zabi daya wuce hakan. Haka dai aka kammala taron Dinner ɗin zuciyoyin mutane cike da murna.

Washe gari gaba ɗaya muna zaune a dinning mu na breakfast, M.J ne kawai bayanan a wannan zaman, cikin nutsuwa kowa ke cin abincin da Momi da kanta ta sarrafa shi, wayar Ammi da ke falo ce ke ta ƙara don haka ta kalleni ta ce
"Little miƙo min wayar nan kinji, na ga wanda ke kirana haka da safe ko karyawa ba za'a barni nayi ba." Dariya muka yi duka kana na miƙe domin zuwa ɗauko mata wayar.
Da sauri na taho na bata wayar sakamakon wani kiran da ya shigo, mijinta da ga ƙasar Egypt Dr. Adam ke wannan kira, cike da mamakin kiransa a wannan lokacin ta ɗaga, bai jira ta yi magana ba ya riga ta, ai kuwa sai gani muka yi ta mike tana faɗin
"Alhamdulillahi Allah mun gode maka Ya Allah kai kadai ke yi a duk sanda ka so ya Allah muna ƙara gode maka da ni'imomin ka gare mu." ba su dade ba ta sauke wayar a kunnenta fuskar ta kaɗai ta isa fallasa farin cikin da ta ke ciki, zuba mata na mujiya mu ka yi cikin son ƙarin bayani, ai kowa fahimtar hakan da ta yi ne ya sa ta ce
"Wani abin farin cikin ya kuma samun mu, wallahi ashe labari mai dadi ne Dr. Ke san gayamin tun dazu shi ke kiran wayar." cike da zumuÉ—i na ce

"Ammi meya faru ne"

Cikin fara'a ta ce
"Rahama ce ta warke daga Trauma É—in da ke damunta, yanzu haka ta dawo hayyacinta harta labarta ma Dr. Abinda ya faru waccan ranar shine ta ke daÉ—a tambayar duk ina muke."

Wani wawan tsalle na daka na rungume Ammi da ke tsaye cikin murna, hamdala duk mutanen da ke wajen suka fara, an É—au lokaci ana maida magana kafin Daddy ya ce

"Ai kamata yayi a kira Rahama É—in ta video mu ganta ta ganmu ko hankalinta ya kwanta."

"Wallahi abinda na ce ma Dr. Kenan amma wai an yi mata allurar bacci saboda kukan da ta ke yi."

"Toh masha Allah sai kuma ayi shirin tafiya koh" cewar Baaba. Dariya muka yi ganin yanayin yadda ta yi maganar. Daddy ya kuma ce wa

"Insha Allahu kuwa sai tafiya a yau É—in nan zuwa dare sai mu wuce. Tunda akwai private jet É—in kamfani na sai mu wuce gabaÉ—aya kawai."

"Haka za'ayi kawai Daddy amma dare kamar yayi nisa fa." Jiddah ta faɗa a shagwaɓe.

"A'a Mamana(sunan da Momi ke kiran Jiddah da shi kenan kasancewar sunan Mahaifiyarta ne) babu kyau gaggawa aikin shaiÉ—an ne a bari zuwa daren mu shirya a nutse, zan kira Hajiyarku (Mahaifiyar Jiddah) na shaida mata nasan itama za ta so ayi tafiyar nan da ita."

"Hakane ya kamata a shaida musu kam."

Bayan mun kammala breakfast ɗin ne duk muka miƙe don fara shirye-shiryen tafiya, inda Saleem ya ɗauki Jiddah suka wuce gida don yin nasu shirin. Bayan na dawo daga rakiyar su Jiddah ne na tarar Sadiq na ƙoƙarin fitowa daga falon don zuwa sashensa, wani tight and friendly hug ya bani, dama nasan ɗazu kunyar su Daddy ya sa bai wani nuna ɗokin shi ba, cike da farin ciki ya ce

"Little ina taya mu murna ragowar farin cikinmu ta dawo hayyacinta, bansan wani irin murna zanyi ba wallahi." sassauta riƙon da yayi min yayi sannan ya riƙe hannuwana biyu ya ce

"Ku kaɗai ne farin cikina yanzu a wannan rayuwar, tabbas a yau na ƙara jaddadawa kaina alƙawarin amanarku da Abbanmu ya bani, zan ɗau alƙawari har a gaban ubangijina bazan taɓa bari ku ji kewa ko maraici ba, zan kasance Uwa, Uba sannan Yaya a gare ku ke da Rahama bazan bari ko ku ƙara yin kukan baƙin ciki ba matuƙar ina numfashi a duniya." hawaye ne ya silalo a kan fuskarsa, hannu na saka na share mai sannan na ce cikin zolaya

"Ka tafi ka shirya ka ji young Abbah."

Doka ya kaimin cikin sauri na sunkuya na wuce ciki da gudu, kai tsaye É—aki na nufa don haÉ—a kayana. Wayata na É—auka na kira Jummai sannan na gayamata ta baiwa Raliya 1million sannan ta sallameta idan da hali ma ta kaita har gaban danginta.

Ƙarfe bakwai na dare muka private jet ɗin Daddy ya ɗaga damu zuwa ƙasar Egypt and here we're tare da Trauma Patient Rahama.

Dukan wasa Rahama ta kaiwa Zarah lokacin da ta kawo ƙarshen labarin. Kana daga baya ta rungumeta tsam a jikinta tare da fashewa da kukan tausayin ƴar uwarta ta, sun jima a haka har sai da Sadiq ya yi magana kafin suka tsagaita yin kukan.

Satinsu Daddy É—aya a Egypt suka koma Nigeria inda aka bar Sadiq da Zarah saboda daga nan zasu wuce Malasia.
Su ma kwanaki goma kacal suka ƙara jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar Malasia.

_Bari mu leƙa amarya da ango._..✍🏻

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 9*
Chapter 9 · 0% Book details